Qamshi Complete Hausa Novel

Qamshi 36-40

Sponsored Links

 *✨QAMSHI 36-40✨*

 

✍🏿Rashow

 

wani irin ciwo kaina yake min tunda Baba me Zuma ya sanar min da daurin aure na naji kaina ya sara hakan ne yasa na yamutsa fuska na hawaye na cigaba da zubo min dafa kaina Ammy tayi tace”sorry qamshin alkhairi ki kwantar da hankalin ki in sha allahu wannan hadin alkhairi ne acikin sa kuma ni da kaina zan tsaya miki har sena tabbatar da Hatim yana sonki kafun na bashi ke.

da sauri na dago kaina ido na fal hawaye da murya na me sanyi wanda ya dan dishe sabida damuwa da kuma kukan da nakeyi nace”nidai Ammy bazan bishi ba a gun ki zan zauna kuma ni banison aure nan yanzu.na karasa maganar da mugun kuka hakan ya qara tayar ma Ammy da hankali ta kwantar dani a jikin ta tace”shhhh ya isa haka ki daina wannan kukan, yanzu ki share hawayen ki ni zan sauka qasa na hada miki tea da kaina ki samu kisha seki sha paracetamol ko kan naki zai sake miki.hannun Ammy na kama na bata fuska hawayen daya taru a cikin ido na ya gangaro ban damu dana share ba nace “Ammy kaina ciwo yake min sosai. shafa gefen fuska na Ammy tayi tace”sorry yanzu zan kawo miki magani. mikewa Ammy tayi ta jinginar dani a jikin kan gado kafafuwa na suna ta kasa ta sake min hannu ta shafa gefen fuska na tamin murmushi tace ” karki kwanta yanzu zan kawo miki magani.

kifa kaina nayi a kan cinya na inajin zuciya na yana min zafi zuciya na ina jinshi a toshe.

Kwankwasa kofar daki na  da akayi ne ya sani dagowa na zuba ma kofar ido ganin ba’a shigo bane kuma an sake kwankwasawa ne yasa na tashi jikina duk babu karfi na nufi kofar na kama handle din kofar na bude, da ido nabi Thariq dake tsaye a bakin kofar wanda ya daga hannu zai sake Kwankwasa wa Kenan na bude kofar, ganin ido na da Thariq yayi ne ya gane kuka nayi murya a sanyaye yace”qamshin Ammy yaa Hatim yana kiran ki a sashin sa. baki na bude zanyi kuka ganin haka da Thariq yayi ne da sauri yace “is OK qamshi yanzu fa zaki dawo kuma tare zamuje mu dawo tare.

kallon shi nayi don son gaskata abunda yace.

 

Na share Sama da minti goma a zaune ina jiran futowar Hatim da Thariq yace na zauna bari yaje ya gaya mishi amma shiru kakeji,gyara mayafin da yake kaina nayi zan mike na Koma sashin Ammy nayi senaji takun sakkowa daga stairs a hankali na daga kaina dake cikin mayafi na kalli yanda nake Jin takun, yaa Hatim ne dake sanye da farar shadda halp jamfa kanshi babu hula se gefen shi wata matace wacce zasuyi sa’anni ita da Hatim din tana gefen shi ta sakale hannun ta ta cikin hannun shi, a hankali suke sakkowa.wasu hawaye ne naji sun cikamin ido don ganin wanda Baba me Zuma ya aura min, danne lips dina nayi da hakori na don karna bama hawayen idona damar zuba na maida kaina kasa don bana marmarin kara kallon su, zama sukayi akan kujera two setter cinyarsu yana manne dana juna ta kwantar da kanta akan kafadar Hatim hanna yensu yana sarkafe dana juna se wani shige mishi takeyi, Seda Hatim ya dauki tsawon minti biyar kafun yayi gyaran murya kamar wanda baison magana ya bude bakin shi muryan shi a hankali yace na Kira ki ne badon komai ba sedon kusan junan ku ma’ana kisan ina da mata yayi maganar tare da dago idon shi ya zuba a cikin nawa idon dana dago kaina ina kallon shi Jin abunda yace duk da kaina yana cikin mayafi amma tas nake ganin su. Kallon juna mukeyi ta cikin mayafi Jin shirun yayi yawane yasa Safeena dago kanta data kwantar a kan kafadar Hatim ta Kalle shi taga yanda yake kallo da sauri ta juya ta kalli gurin da yake kallon taga ni yake kallo sedai ni fuska na yana rufe jijjiga hannun shi tayi hakan yasa Hatim kallon ta yace”Wannan itace mata na Safeena inason ki girmama ta sabida shakerun ku ba daya bane duk da Kuna auren miji daya to bashi ne zaisa ki raina taba don Sam bani son raini ki bata girman ta na wacce ta girme miki se a zauna lafiya, sannan nasan kin san ita na fara aure don haka zanyi sati daya a gurin ta kafun nan na dawo sashin ki nayi sati daya kamar yanda addini yace idan yaso ku seku fadi kwana nawa ya kamata a cigaba dayi.lumshe ido Hatim yayi yana maida numfashi kamar wanda yayi gudu murmushi Safeena tayi ta shafa saman cinyar Hatim ta maqe murya tace”honey muyi two days kamar yanda sauran gidaje sukeyi ko?kafada Hatim ya daga kamar bazaice komai ba sannan yace”hakan idan ya miki shikenan. sake danne kuka na nayi don ganin yanda Hatim yake min a gabar matar shi yana nuna mata kawai cusa mishi ni akayi. kallon yanda nake Hatim yayi murya a kasalance yace “hope kin gane me take nufi? kaina na daga mishi ina wasa da qasar mayafin kaina.

gyara zama Hatim yayi ba tare da ya bude idon shi daya lumshe ba yace” you can go daman maganar Kenan. A hankali na mike jikina babu karfi na nufi kofar futa”ke baki iya Karin kwana bane ma mutane? Cak naja na tsaya daga tafiyar da nakeyi wani kalan bakin ciki ne da kuka suka tawo min amma na daure Seda na runtse ido na na daidai ta nutsuwa na ba tare dana juyo ba nace”na Kara muku wata uku akan sati dayan.ban jira cewar suba na cigaba da tafiya ta na futa daga falon.

da mamaki Hatim da Safeena suka dago kansu sukabi bayana da na futa Hatim Kam kan shi ya girgiza tare da mele baki.

 

 

Tray na gani a gefen durowan gado na alamun Ammy ta shigo dakin Kenan bata ganni ba rashin ganin ta da banyi a dakin ba seya min dadi  fashewa da kuka nayi nayi wurgi da mayafin kaina,kuka nayi kukan da bansan na menene bane saida naji kaina kamar zai futa daga jikina don ciwo sannan na mike na nufi bathroom na wanko fuska na da bakina nazo nasha magani tea din da Ammy ta hado min ma kadan nasha na ajiye na Koma bathroom na wake baki na sannan nazo na canza kayan jikina na Kara karfin ac nayi addua na kwanta badon inajin barci ba se don kaina daya matsamin da ciwo, Koda na kwanta hawaye ne suke gangaro min ta gefen ido suna jika pilon da nake Kai.

 

 

*Rashow*

Leave a Reply

Back to top button