Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 22

Sponsored Links

022
____________________
Salima!
Salima!!!

“Ina zuwa🏃‍♀️” ta dirkako da gudu daga saman benen zuwa bakin main door din ta sa key ta buɗe ƙofar .

Muryarsa yayi rauni sosai kamar abun tausayi ,sam bata iya magana da ƙarfi “Haba Salima kina sane na kwaso rana amma kika barni a gantale duk maƙota sunaji ina kiranki ki buɗe ni”

“Ya Sheikh Alal aƙalla sau biyu ka kirani”

“Yawwa kina kal kal da baki kamar reza iyayen gaddama,ana magana sai kin bada amsa Ni ban hanya….washhhhh” yaje kan kujera ya zauna ya saki tumbi a gaba ya goya hannunsa akan tumbin yana karkaɗa ƙafa in readiness to battle with Salima.

“Har ka dawo daga gidan maman?”

“Hum ki bari kawai ,mama tana da ban dariya ɗan ciwon kai sai tace zata tafi ganin likitan ta a Cairo ,Kamar mai tsoron mutuwa ko yanzu tayi booking new appointment fa Ni bansan wannan abun na menene ba ,ke jiya kinga tana da alamar ciwo?”

“ha’ah jikin girma ne fa Ai sai tana maintaining health status dinta ,Abun da tayi abune me kyau gaskiya”

Ɗaga murya ya somayi cikin masifa masifa “Zakice haka mana , tunda ta fara koya maki yanda ake asarantar da kudi unnecessary..”

Sarai ta Gane a ƙunba yake don haka tace “Allah ya baka haƙuri ,kawai mubar maganar” ta juya zata haye stairs Abinta

“Ehen Salima!” a gajiye ta waigo
“Na’am sheikh”

“🫵🏻Wannan kudin da mama ta tura maki ,ki ƙara adana su da kyau a account dinki kinji”

“Ban gane ba🤨me yasa? ”
“Eh mana🤗 Duk wata sai ki ringa biyan kuɗin wuta da kudin ruwa a ciki da siyan en kayan miya da su maggi ,mu gani ko zasu shekara bai ƙare ba?!”

Daka tsalle tayi ta fara diddirke ƙafafuwarta a ƙasa “Kambu ,ai wallahi bazan yarda ba ,wannan kudin kudina ne kyauta ta bani ”

“Habawa en matana😆Nine fa sheikh dinki…yanzu mama ta Baki har dubu ɗari bazaki tayani hidimar gida ba? Ai da kai da kaya duk mallakin wuya ne ko ba haka ba?”

Soror ta tsaya tana kallonsa cikin tsananin mamaki

Sake washe baki yayi ,sai yanzu ya samu sa’idan zuciya da yaga kudinsa basu tafi a banza ba ,cike da nishadi ya sauke hulan kansa ya ɗaura akan Centre table ,ya saki hamma gami da miƙa.

“Yawwa me kika girka mana?”

Wasu mugayen harara ta shiga tunkuda masa harda murguɗa baki .

Murmushin mugaye yayi irin na saman leɓen nan ,ya mike da sauri yana cire boturan wuyar rigarsa
“Uhm bari inje in duba da kaina tunda hajjajuna fushi take sani,bansan wa ya taɓo kan jirgin ba”

A yanda take tsaye ta rafka tagumi tana kallonsa ,ta zurfafa cikin tunanin yanda dubu ɗari zai ishi dogayen bills ɗin nan da ya faɗa har na shekara guda….kenan maimakon sauki kudin nan tsanani ya kara mata

To kodai in roƙesa ya bani account number ɗinsa ne in maida masa kudin sa in tsaya yanda Ubangiji ya ajiye Ni?

“Hmm ban Account Number dinka kawai in maida maka kudin ka cigaba da hidimarsa,kar ka saka Ni a ciki ma!”

Zuwa yayi ta bayanta ya riƙo cinyoyin hannunta ya ɗaura kansa a kafaɗarta
A kunne ya raɗa mata
“Habawa matar Sheikh ki barsu a wajenki atleast nasan wainnan budget din na gama dasu ko?”

***
Washekari Sheikh cikin ujila ya fita zuwa aiki ko 8 na safe ma bata ƙarasa ba ,saidai yana fitowa ya tuna yayi mantuwa da mukullan Office ɗin don haka da sauri ya faka motarsa a gaban gate din gidansa ya fito daga cikin motar zai juya cikin gidan da ƙafa

Adnan da fitowar sa kenan ya hango ya Sheikh da sauri ya ɗaga masa hannu
“Salamu Alaikum….salamu alaikum”

Cak ya Sheikh yaja ya tsaya yana tunanin wani taimako kuma za’a bukaci yayi a safen nan

“Wohoho Allah bacin tara gashin gemu kwarjini ne kuma Kayan samun ladane matsayina na Ahlus Sunnah ,wallahi da na ɗebe shi na aske nima ina rinƙa tsutsukewa ina shiga kamar ɗan iska ɗan iska haka nan dai…na tabbatar mutane ba zasu taso Ni a gaba da neman taimako ba…amma ynz ko nasa jeans da shirt gemun nan zaisa asan Ni Sheikh ne”

Da wannan zancen zucin da yakeyi har Adnan ya cin masa

Wani ƙamshin deaigners din turare yaji masu tashin kai da mugun tsada ,wow ga masu barnatar da dukiyar da ilahu ya basu nan😕

“Sannu ko?😃Na dade ina son mu hadu mu gaisa amma ku malamai ahlul ilm ,ba zama uzuri yayi maku yawa”

Jinjina kai yayi “Haza haƙƙun…(wannan gaskiya ne)”

“Sunana Dr Adnan sabon maƙocinka…”

Kurrrr yaji cikinsa ya yi kuka
Ohkoo shine makocin da Salima take mun gori a kansa ?
A kasalance ya miƙa masa hannu don su gaisa
“Sheikh miqdad inkinya Abu_sumayya”

Washe baki Adnan ya sakeyi ,yana jin hannunsa na masa raɗaɗi saboda yanda ya Sheikh ya matse masa hannu da ƙarfin tsiya kamar zai karyasu…..mugu yaji hannun butters da suka saba cin daɗi ,jiki duk madara😉😆

“Sannu Abu_sumayya ,wallahi kayi Sa’a Allah ya albarkaci ƴaƴanka da zasu zo da uwa ta gari….Plz ka cigaba da kyautata mata kaji Sheikh?”

Sakaka ya saki hannunsa ba tareda ya karye masa yatsunba kamar yanda zuciyarsa ta sallaɗa masa mugunta .

“Bari inje ko? I’m off to work ,sai anjima” ya juya ya soma tafiya hannayensa suna soke a Aljihu yana bubbuɗawa irin tafiyar matasan nan masu fama da Giyar kuɗi.

Sakin baki yayi sakaka kamar sakarai har saida yaga shigansa mota ,kana yahau ɓaɓatun iska “Dallah ji sakaren nan,yenyenyen uwar yaranka mace ta gari ce ,ina ruwanci? Banza kawai !….mune za’a koya mana kula da mace ? Muda muke tafiyar da iyalan mu daidai da fiɗratul Islam !!!”

Leave a Reply

Back to top button