Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 47

Sponsored Links

047
___________________
“Good Evening ma’am ”
“Evening”
“Ykk ya Sheikh hope kinci abinci da yawa kuma baki fushi ba yau”
“Eh Sheikh na gaishe ka”

Kullum iyakar chat din Salima da Adnan knn ,Sam taƙi faɗa masa auren ta da Sheikh ya kare tuni ta koma makaranta ta samu aiki a babbar companyn ɗangote an bata muƙamin marketing manager🤓Ba case ya sheikh ya koya mata tattali .
Salima fa ta soma zama babes ,tana wanka sosai ,amma bana fitsara ba ,is either abaya ko tasaka jilbab da transperent glasses ,sai manyan zobunan Golds da suke yatsunta ,she’s bae🥰Amma Sam Bata da samari , saboda sam maza sun fice mata arai zuwa ynz tsoran su take

Zaune take a office dinta ta kunna karatun ƙurani ta rage volume din dai dai kunnenta aiki take sosai akan laptop dinta ,saƙon Adnan ne ya shigo ta gmail

”I landed in Nigeria ,Naga gidan ku da alamun datti duk shukuki sun firfito alamun an daɗe babu mutane a ciki ,kina ina ne?”

Ta maimaita sakon yafi a ƙirga saidai ta kasa bashi amsa ,wani kewar mijinta taji ya bijiro mata,shin kam ya Sheikh yana ina ne?tun bayan rabuwarsu bai sake kiranta ba.

Zare glasses din fuskarta tayi tana share hawayen da batasan dalilin zuwan su ba.

Saida tayu kukan ta Mai isarta sannan ta kwanta lamo akan table tana sauraran karatun ƙuran ,a hankali take sauke ajiyar zuciya wani sakina da nutsuwa na shigarta.

Bata bashi amsa ba har ta dawo gida .tana kunna data messages dinsa ya fara masa karakaina ta wxp mssgr

“Ashe aurenku ya rabu da ya Sheikh tun ranar da ba bar garin nan amma baki shaida mun ba,kika barni kullum cikin kewa da Zullumi?”

“Anya Salima kinsan so kuwa?”

“salima say some thing plz”

“Salima zanzo gidanku yau ,Inason magana da baba ,bana son rasa ki a wannan karon”

Ba’a yin awa sai ya turo sako dukda ya ganta offline Amma ya kasa hakura

Tunda ta bude take karanta sakon ninsa har ta gaji ta ajiye wayarta ta tafi falo wajen mamanta su taba hira don ta lura saƙon ninsa bazai kare ba

An shiga Masallaci ,suka rabu zuwa sallah ,saidai shigarta ba wuya Saiga Baba tanbaya ta leƙo ɗakinta

”Uwar ɗakina in kin idar kina da baƙo a ƙasa ,mun bashi ruwa da drinks”

“Uhum tayi mata gyaran murya mai kama da magana😃 irin a dole ta sallameshi din nan kar ta bari ya zauna”

Bana tambaya dai bata fahimce ta ba“Au a kai masa abinci? Wai kunga kamar baƙin balarabene😂bai iya cin abincin mu ba,ke dai sai kin idar ,maji me za a bashi”

***
Abayan dake jikinta dashi ta fito army green ƙirar Cairo ,yayi azaban mata kyau fuskarta fayau ba kwalliya a nutse ta shigo ɗakin bakinta da sallama hannunta rike da wayoyinta duk 13 pro

Yana ganinta yayi zumbur ya miƙe
“Salimart Are You?”

Murguɗa masa baki tayi “Meye kuma”

“Hum you’re a bae…Har naji na fara kishinki…amma Allah na gode da kyawunki ya dausashe sanda kike tare da Sheikh da bai rabu dake ba har in samu”

A miskilance tace “Kana ta Surutu ko gaisuwa”

“Humm ina maganar gaisuwa zuciya taga muradun ta ,idanuwa sunga kyakyawa,Ke nifa inajin gaskiya a satin nan za’a daura mana aure ai nikuma na zama ɗan nigeria”

“kasarku fa?”

“Mata na ta ƙwaceni dama baki ganni Caramel ba,kalan en Nigeria? Da naji Hausa shikenan,kinga duk wanda aka tambaya ina Adnan sai ince Adnan ya zama mijin tace Matana ta janyeni na dawo kasarsu”

“waikai kana ta wani mata…mata Ni ance maka aure zanyi ne? Infact Ni kayi mun yaro ”

“Yaro🤓? In girmeki da fiye da shekara goma kice mun yaro?”

“Eh na girmeka da aure”

“Shikenan ynz sai ki aureni sai in ƙwato mutunci na dama gori ya isheni kinga sai a daina cema mijinki gwauro”

“Kai bazanyi aure yanzu ba”

“Baki isa ba ”
“me yasa”
“Becouse you’re a durling ,idan ma na kyaleki ina zaman jira wani zai mun wuf dake Allah na gode da nazo Nigeria da yanzu saidai inji a oxygen”

***
Lokaci mai zuwa da sauyi iri da kala mai ma’ana da kishiyar hakan,a yau tururuwar Al’umma suka shaida ɗaurin auren Adnan da Salimart akan sadaki mafi ƙanƙanta ,bayan ɗaurin aure aka zarce da walima,dangin angon da sukazo maza biyar mata uku saida sukaje har gidan Salimart na Abuja gidan manshon mai azaban kyau an narka maƙudan kuɗi. A cewar Adnan gari ɗaya ma da Sheikh bazai yarda su zauna ba saboda shifa yana da kishi.

mashaAllah amarya dai ta tare a gidan mijinta ,ango an gabatar da duk wasu sunnoni da Musulunci suka tanadar ,daga nan kowa yayi wanka suka sauya kaya zuwa Nighty da pyjamas Adnan ya kashe masu fitila.

Fatan Alhairi ya adnan🤓kar wanda yace mun komai,Abarsu suyi sirri in an kwana biyu kowa ya saba an yage kunya ma feso maku rahoto.

 

 

 

0um Aphnan
#Bad boys

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button