Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 44

Sponsored Links

044
___________________
I see,Kaine Wanda kake ƙoƙarin rabani da sarauta na ? Kai nayi dakon jira tsawan shekaru….

“Yarima karka saurareshi kazo muje ba fada a mission dinmu ka gano yarinyar shknn” a sama yaji Muryar jabir ashe ya biyo shi

“Jabir bani littafin mutuwa yau bindigana za tayi aiki akan yaron nan”

“Yarima na Aah”

Tsawa ya daka masa
“Ka bani bindiga na”

Da gudu yaje ya ɗauko bindigar ya miƙa masa ,gyara mata zama yayi a hannunsa ya nuna Sulaim
“Matsa!”
Jikinta rawa ya kamayi ta sake ƙanƙame hannun ambassador “Karka kasheshi”

“Tauuu!” taji ƙarar bindiga wannan ya sata faɗi rikicaaa cikin firgici,idanuwarta a rumtse “Nashiga uku ya kashe shi saboda ni”

Yanda bullet ɗin ya daki ƙirjinsa haka ya faɗo. Ƙasa ba tareda ya shiga jikin ambassador ba.

Zaro ido yarima yayi cikin mamaki
Kawai sai ya cigaba da harbinsa fafafafa

Da rarrafe Sulaim ta mike saida tayi nesa ta kwasa da gudu.

Saida bullet din ya Kare a ƙirjin ambassador sannan ya tsaya yana kallon sa ,wani dariya ya sheƙe dashi ,kana yasa hannunsa yana kakkaɓe harsashin a jikinsa ,babu ko daya da ya huda shi.

“Kana magana da magajine mafiyi ,bana jin bindiga Ni wuta ne,I’m a War and I’m a Battle” wani gurnani yayi ya dunkula hannunsa ya watsa masa daƙuwa a fuska .

Wani irin wuta ne ya tashi faaaa ya sauka a fuskar yarima ,ƙara cikin matsanancin zogi.

Da gudu Jabir ya riƙoshi saboda kar ya fadi ,shikuma jabir yarfe hannunsa yayi ya sake dunƙulawa ya ya fesa masa .

Zuwa yanzu yarima ya fice daga hayyacinsa jansa jabir yake kiiii cikin gudun kwatar rai ya samu ya sakashi a mota ya figeta da gudu.

***
“Nine yaron Sarkin da kuke jira ,kuma Ni nafi cancanta da sarautar”
Waziri kafe Ambassador da ido yayi yana tantama

”Bamu sanka ba Bamu taɓa jin labarinka ba a bakin mai martaba dukda kasancewarsa babbar aminina”

“Zai iya faruwa tunda harka ne na asiri ,kurciya akayi ma uwata da ciki…”

***
Ko da zan mutu a yanzu ku tabbata kun cika mun burina na ƙarshe kuje ku ɗauro mun auren yarinyar nan ,in na mutu zaace Ni na kusance ta”

“Bazakayi aure a maƙasƙancin family ba”

“Mama zamu rasa yaya soon, meyasa bazaki sauke girman kanki ba kamar yanda ya sauke nashi? Matar mutum kabarinsa ne ,ki barshi ya aureta meye aibunta don ta zama talaka…”

***
Abba bazan aureshi ba ,a gabana ya kashe wani mutum da bindiga”

“Baki da miji sai yarima bazaki maidani mutumin banza ba ,kuma in har kika nema bijiremun ban yafe ba”

***
4pm
Waziri sake duban Ambassador yayi lokacin ya taro rankatakaf masu alhakin rantsar da Sarki “Maimaita masu abinda kake cewa”
Miƙewa ambassador yayi cike da karsashi ya fara jero masu abinda ya fada ma waziri tun a farko .tsit sukayi suna sauraronshi

Exactly 4pm
Yarima ya soma jin dama dama ,don haka ya je yayi wanka ya sauya kaya zuwa na sarauta ,dashi da Mai babbar ɗaki suka fito suka shiga mota guda bayi da dogarai suka bi bayansu ɗuuuu

“Muje muyi magana da waziri a je a daura maka auren”

***
Jiniyar ababen hawansu ya karyo da hankalin mazauna taron ,kowa yayi tsit ana jiran ƙarasowarsu ,ita aka fara buɗe wa motar ,ta fito sanye da yadin karan miski mai ado ,kuyangi mata sukabi bayanta ɗuuuuu suna mata firfita wasu na ɗage mata rigarta dake sharar ƙasa.

Shima ta bangaren yariman haka ne.

Wani miyau mai kauri ambassador ya haɗiye a ransa yana cewa “Arzikina ne ake wadaƙa dashi haka ai bazai yiwu ba ,kunci taliyar ƙarshe”

Cikin Izzah da ƙasaita mai babbar ɗaki ta isa gaban Waziri

“Na gaishe da waziri I salute you all”

Cikin girmamawa kowa ya gaisheda sarauniyar ,kuma maman Sarkin gobe da yardan Allah

“Nazo ne aje a ɗauko min auren yarona yanzu yanzun nan” ta juya don ta kalli reaction din Yarima .

Can baya ta hangosa ya kasa ƙarasowa suna kallon kallo da ambassador ,idonsa cike da tsoronsa.

“Lafiyanka ƙalau kuwa yarona?”

“Shine baƙon da nike baki labari” dallaro ido waje tayi kamar globe ,Saidai kafin tayi magana Ambassador ya kalli waziri

“A gafarceni iyayena inajin zan tafi yanzu ,zuwa anjima zan dawo ”

Ya fara takawa a ɗage cike da mulki da jijji da kai.

Saida yazo kafada da kafada da yariman da Ambassador din kana yaja tsaki ya cigaba da tafiya.

Cikin hargagi yarima ya daka masa tsawa gamida bashi umurni
“Tsaya daga nan”

Cak ambassador yaja ya tsaya ba tareda ya waiga ba

”Zo ka zube akan ƙafafunka ko roƙi gafara na sannan ka fice mun daga masarauta ta cikin sallama in ba haka ba I’ll cut out your head ,zan yanke kanka in ƙwaƙule ciki in maidashi wajen Shan coffee na” wani kallon banza yayi masa kana ya cigaba da tafiya a harzuƙe yarima abbad ya taka bayansa ya miƙa hannu da nufin ya fizgo kafaɗarsa

Saidai yina ɗaura hannunsa a kafaɗarsa kikaji wani irin sauti kamar na Damisa

Ɓat suka ɓace a tare ba yariman ba ambassy sun ɓace ko sama ko ƙasa.

 

 

 

Oum Aphnan
#Bad boys

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button