Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 24

Sponsored Links

024
____________________
Turaki mutsirtsuke ido yayi cikin jan rai yace “Eh sabda kaine! Yareema mufa iyayenka ne,Amma ada garinmu na zaune lafiya sanda kake wajen aikin sojanka a ƙasar waje shekaru uku baya amma tunda ka dawo komai yayi tsanani ….. Adon haka Bazai yiwu mu zuba ido muna ganin abunda ke faruwa ba,mutane daga wasu daulolin suna zagin masarautarmu sbd kai tun asali,to bare kuma ace masu kaine Sarkin…”

Komawa yayi luu ya kwanta akan kujerar mulkinsa ,kana ya lumshe ido cike da ɗagawa ,ya ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya
Da wani sassanyar murya mara Hayaniya yace “Hmm haka ne kuma fa🤗Saidai zaɓi biyu Gareku ,kodai ku zaɓeni a matsayin sarkin ku ,ko ku soke Ni a matsayin sarkinku….” still idanuwarsa suna lumshe ba tare da ya buɗe ba har ya gama maganar

Waziri sassauta murya yayi “Yarona ba maganar zama sarki shine matsalar ba ,ka sauya halinka mu shine damuwar mu,bakajin abinda Turaki yace ne? Mutane na kuka da baƙin halinka…muma iyayenka bamajin daɗi wannan zubar kimarmu ne”

Ai yanayin shiru suka soma gungaguni dake nuna duk sunji daɗin yanda waziri ya gaya masa magana kai tsaye.

Yareema da idonsa ke kulle ,Gwale idanuwar yayi , yana kallon sararin samaniya ,yana sauraron gunaguninsu da baka iya fahimta ,
kana ya gyara zamansa da sauri , gamida ɗaure fuska tamkar bai taɓa dariya which defect Jeopardy

“Uhumm” yayi wani gurnani kamar naman daji

“Jabeer !!”

Ya Kira sunan yaronsa

Ɗan rusunawa Jabeer yayi “Allah yaja zamanin yarima”👍🏼

“Dakkomun Littafin Mutuwa!!!😡”

“Ok yarima na” ya falla da gudu ,zuwa wajen mota.

Diddilo idanuwa duk sukayi ,cikin whispering Galadima yake tambayar Ciroma ,meye littafin mutuwa kuma? Ciroma da yaji yana jin zawo ,watsa hannunsa a cinya yayi ma’ana bai sani ba …duk haka suka cigaba da kallon kallo.

Har jabeer ya dawo hannun sa ɗauke da ƴar stool Kamar na ajiye cofee ,ya ɗauko wani fankacecen littafi Mai Kamar album ɗin hotuna ya ajiye akan ƴar stool din ,Saida ya saka handgloves sannan ya buɗe tsakiyar littafin.

Kyakyawar bindiga ne er ficila ,duk sukayi tozali dashi a cikin littafin an ɗaura bindigar a saman farin ƙyalle.

Sa hannu Yareema yayi ya ɗauki bindigar yasa tsinin bindigar a saman sajensa yana sosawa ,ba alaman damuwa ko tashin hankali a fuskarsa

“Idan kuna raayin Yareema ya zama sarki a bi nan…” ya nuna masu ɓangaren damar shi da bindiga

“Idan baku goyan bayan Yareema ,ai nan ɓangaren” ya nuna masu ɓangaren hagu da bindiga

Galadima shi ya fara miƙewa sai Ciroma da duk sauran suka je can nesa dashi ɓarin damansa sukayi layi .
Ma’ana sun yarda ya zama sarkin su.

“Gwuiwoyinku a ƙasa”
Tsayawa sukayi wannan ya kalli wannan wannan ya kalli wancan

“Kneel down I said!” a furgice sukayi ƙasa da sauri suna rububin soka gwuiwoyinsu a ƙasan,abunda kowanensu yafi shekara arba’in baiyi ba..

Zumbur ya miƙe tsaye yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya ,da sauri kowa ya sunkuyar da idolanuwarshi a ƙasa.

“Babana mutum ne mai rauni ….shiyasa ya zaɓi ruɓaɓɓun mutane irinku su zama muƙarrabansa….amma yanzu ga yanda ya ƙare nan ,gashi can a kwance ba amfanin da kuke masa….

Yanzu sabon gomnati ne kuke gani a nan !
Idan har na faɗi magana to tabbas umurni ne!
Matsawar ka karya doka na ,ko ka nemi jayayya da hukunci na… To abu na farko shine inga kanka a ƙasa ka zama Gawa…. Bayan na kasheka ,bazan tsaya a kanka ba ,zanbi duk wani ahalinka inbi in yanyankasu zuwa gunduwa gunduwan Nama…. Gutsigutsi zanyi daku wallahi😡😡” jikinsu rawa ya shiga yi ɓal ɓal ɓal.

“Wannan masarautar nawa ne, Don haka zan fara ƙaddamar da manufofina a kanku a yanzu don ya zame ma ƴan baya Izinah!!!……Ahmmmm waye me Alhakin tara taron nan?” a furgice suka ɗago wannan ya nuna wannan ,wancan ya nuna wancan….

Wani wawan tsawa ya ƙara doka masu ,wanda yasa Galadima sakin fitsari a wajen.

“Waye shugaban naku?!!!”

Waziri cikin ƙwalla yace “Ni na tara amma kaine shugaba…” suma duk sauran suka maza suka amsa da cewa “Kaine…Kaine🫵🏻”

Haɗe rai ya sake yi Yana magana with authority “Waye shugaban wanann masarautar”

”Yareeman Al’ummah Sarkin gobe da yardan me duka!” suka bashi amsa gaba-dayansu bakinsu na rawa.

“Idan kuna goyan bayana kuce yareema”

Duka ɗaga hannu sukayi kamar masu saranda “Yarima✋🏻🤚🏻”

“Idan bakwa goyon baya na kuce Nooo”

Tsit sukayi kamar ɗaukewar wutar Nepa

Tsaki yaja dogo na kusan second biyar ,wanda suke jinsa kamar ana fatattaka masu hanji.

A zafafe ya juya ya kalli ƙaton elargement window size mai ɗauke da hoton Waziri,ya shiga sakin ma hoton harbi

Ji kake tushhhh!
tushhhhh!!
tushhhhh!!

Ya fice a ɗakin da saurin gaske ,daidai nan kayan ƙawar ɗakin suka shiga rikitowa ,hoton ma ya fado kasa timmm! Alburusan guda uku suka watso ƙasa .

Ba wanda yayi ƙwaƙwaran motsi ,duk sun toshe kunnensu da hannuwarsu kowa na sauraren yaji saukar bindiga a ƙirjinsa.

Ai sunajin tashin motarshi suka mike da sauri ,suna cewa junansu “Barka ….Barka”
“Amma yariman nan ya cika shaƙiyyi!” cewar Ciroma.

“Yi mun shiru ,kafin ya sake dawowa ya kasheni a banza ,don Ni ina tunanin Yareema yina da Aljannu masu kimtsa masa magana…” waziri yana magana yana kallon hotonsa da ya dagargaje har jikin garun ɗakinsa yayi rami zuƙuƙu…yana tunanin da yanzu hanjayensa ne suka ɓuɓɓurme.

“Amma dai ai bazaa ɗinke mana baki ba ko?” cewar Galadima dake durƙushe male_male cikin fitsari ,har ynzu ya kasa tashi.

“Eh haka ne kuma amma kafin nan jeka ka wanke jikinka…sarkin masu zuciyar fada ,nan kace in aka bari kuka gamu kakkarya Yareema zakayi ,sai gaka da fitsari a wando”

 

 

Oum Aphnan
#BAD BOYS
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button