Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 34

Sponsored Links

034
___________________
2 weeks Later.
3pm
Ya sheikh daga office suka dawo gida tare da Ambassador ,bisa Matsawar Ambassador lallai dole sai yazo yaci girkin Salima ,bayi da zaɓi sai ya kawo shi ko ya yarda ƙwallon mangoro ya huta da ƙuda .
Salima ta ƙuƙe a kichin tana girki ,Adnan yazo gaban ƙofar ya fara knocking a jere Mazan suka amsa da “Yes come in” dararas ! Gaban Adnan ya faɗi Amma bazai iya juyawa ba don haka ya murza handle ya shiga hannunsa niƙi niƙi da kaya .

A ɗarare ya masu sallama, Ambassador da be waye shi ba ya amsa with a broad smile “Zo ga waje ” ya nuna masa kujera ,shikam Ya Sheikh yanda kasan an aiko masa da saƙon mutuwa haka yayi kicin kicin da rai .

Washe baki yayi yana ƙaƙalo dariyar yaƙe “Weldon bros ,ya aiki ya gida”
“Lafiya kalou ”
Sosa ƙeya yayi kamar maijin kunya kana ya maze “Plz Ina Salima…” kafin ya karasa magana Ya Sheikh ya kwatse shi da hargagi da tashin Hankali

“Gata nan a bayana ” Adnan ba hausa ,baisan baƙar magana ba ,sai muskutawa yayi yana leƙen bayan ya Sheikh

Ya Sheikh dukan gadon bayansa ya shigayi da tafin hannunsa “Kasan yarinyar goye ne zo ka cireta…naji mun bala’i uban me kake nema a wajen ta ,eyyeh jarababbe?”
Ƙiƙƙifta idanuwa Adnan ya shigayi ,shidai yasan masifa yake amma bafa ya fahimta ,sai ma Ambassador ne yake bashi baki haba Now,daga zuwa neman matarka sai zagi? Ina laifin wanda ya damu da naka?..”

“Sharaff…”

“Food is readyy…” Salima ta fito tana faɗa cikin barkwanci tayi gayunta da ɗaya daga cikin kayan da Adnan ya Bata ,tana ganin Adnan zaune da manyan jakuna a gabansa tasan ba lafiya a sanyaye ta cigaba da sakkowa,daga matakalen benen

“Dr kaine ? Amma ynz ka shigo ko?” ta masa magana da larabci a sanyaye kamar tasan ana tsaka da cin masa mutuncine.

Gyada mata kai yayi fuskarsa kadaham kadaham

Miƙewa yayi ya cicciɓi madaidaicin jakan gabansa ,ya miƙa mata

“Happy wedding anniversary…Allah ya ƙaro zaman lafiya a aurenku ya baku zuriya masu Albarka these are the little gift I can offer…” ya nuna mata tarin kayan da ya zo dasu bayan ɗan madaidaiciyar jakar da ya bata

Cusa kanta tayi ta leƙa ,agogone na mace da namiji iri ɗaya sai wani box ɗin ɗan kunni da yarin gold”

Ihun murna ta fashe dashi “Yeeeeh ta runtuma gaban Sheikh tana nuna masa gift din da aka basu tare dukda sauran masu nauyin batasan ko menene ba amma basu wuce sutura ,don shine abinda Salima take ƙaranci.

Ba kunya ya Sheikh ya washe baki “Kamfanin Rolex ne ko me? Kai wanann agogo da ɗaukan ido yake ,ya akayi kasan yau ne ma ranar….” buge masa hannu ambassador yayi ,wanann yasa ya Sheikh shiru yana zare ido .

Waigawa Salima tayi ya kalli Adnan “Ya akayi kasan yau anniversary dinmu?”

“A IG Naga post din hotunan bikinku” girgiza kai tayi cikin jimami yana tuno mata da memories.

Kauda kai yayi “Bari inje ko?🤨”

“Aah no abincinmu a table tare zamuci duka” Ambassador ya karɓe da sauri.

Ya Sheikh ji yayi kamar ya kashe Ambassador don haushi ,zaija a cinye masa abincin da yayi budgeting zasu ɗumama da safe,in yayi ragowa.

“No Yanzu na dawo daga Office inaso inje inyi wanka”

“Aah kaga ka dawo da empty stomach kenan ma…” ambassador ya cigaba da insisting
Da sauri ya Sheikh yasa hannu a gefen cinyar ambassador ya manna masa mintsini wanda yasa Ambassador zabura

Sarai Adnan da Salima duk sun lura da halin da ya Sheikh ya shiga ,don Adnan ya gama gane Sheikh ba ƙaramin zumbuli bane ƙarewar rowa.

“Bari inje inyi wankan zan dawo” Ya amsa tayin Ambassador da gayya ,yau saidai in yaci abincin Ya Sheikh ya hadiyi zuciya ya mutu.

 

 

 

Oum Aphnan
#Bad boys
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button