Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 35

Sponsored Links

035
___________________
Yana fita Salima ma ta juya cikin ɓacin rai ,ta rasa wanann wani irin rowa Allah ya jarrabi mijinta dashi,mutum ya kashe maka maƙudan kudi ya kawo maka kyauta kai da matarka amma kai bazaka iya bashi dama yaci lomar abinci a gidanka ba? Allah yayi mana tsari!
Ƙumewa tayi a bedroom Taki fitowa ,sai hawayen nadama take ɓulɓulo mata ,ada tana ma ya Sheikh tunanin shiriya amma wanann yasha mata hankali.

***
Ambassador waigawa yayi ya kalli ya Sheikh
“Amma kaidai bakayi ba wallahi bakayi ba…ka kwafsa!”

”Ban gane ba, kuma me nayi ?”

“Wai date ɗin bikinku ma ka manta sai wani bare yazo ya taya ka celebrating ,ka zageshi yabaka abu ba kunya ka karɓe,Kuma still kana so ka hanashi abincin gidanka ,anya nima kuwa ba cika maka ido nayi ba ,kan dole zaka barni inci?”

“Ji wani magana dai? Inda banso kaci abincin sai kuma in ɗauko ka da kaina?…kawai bana sonsa ne,jinin mu baizo daya ba ,banason yanda yike shishige ma Salima ,ka kalli yanda duk ta wani damu ,ko baka lura fushi ba tayi ta barmu? Shiknn yau ya siya mata kaya gobe sarka gaba-daya yana nema yasa Matana ta fanɗare mun ”

“Ohoo kace ga inda ɓarakar ta taso kenan…to yanzu shawarar da zan baka maza muci abinci muje kayo mata shopping da ya ninka kudin nasa sau uku,ka haɗa mana kayattaccen party anjima da dare ka gayyato shi da matarshi yazo ayi danashan Arziki ,na tabbatar zaka burge Salima ,shima kuma zai gane ka damu da matarka kuma kana farinciki da rayuwar auren ku”

Tunda yake magana ya saki baki galala yana kallonsa ,har yakai karshe

“Gaskiya ban taɓa sanin ƙwaƙwalwarka bata ja ba sai yau! ,Kawai saboda kar a zargeni sai in asaran kusan miliyan guda takan Salima?! Haba…haba ba gunma in buɗe mata shago ba ma”

***
Ya Sheikh knock yayi a bedroom dinta ya shiga da kaya niƙi² a manyan baƙaƙen leda masu zanen fari ,ciccike da ɗinkakkun Atamfofi da lesuka .

Sayyida a hankali ta amsa sallamarsa ciki² ,sbd har ynz bata huce abinda yayi mata ba.

“Matata sayyida…bazaki iya zuwa ki amshi mijinki ba?”

Miƙewa tayi fuskarta ba yabo ba fallasa taje ta amshe ledan hannunsa ta ajiye akan gado ,masu kirtanin laces irin na matan zumuntan da da ake masu ɗinkin riga da zani(Ciki da alaku) ta ga set ɗaya ya faɗo

“Meye wanann kayan waye?”
Tana nuna masa kayan tana caɓe baki kamar zatayi amai

“Naki ne mana,set biyar na shiga gwanjo na siyo maki ,kinsan gwanjon Kayan atamfofin nan da lesukan nan sirri ne dasu ,kayan matan masu kudine sai suyi dinki susa sau daya biyu su ajiye mu kuma a kawo mana nan a farashi mai arha….ya kike gani in kika sa? Wow nasan zai maki kyau ,kuma za’a rantse da tsada kika cire kudi kika siya….”

Ƙuuurrr ta kafeshi da ido Saiga ƙwalla na Shirin zubowa

“Yanzu talaucina ,fatarana ,da rashin suturana ya kaima ka siyo mun gwanjon mama ta mutu!!!? Kayan da ake fitarwa na matattun mata shine zaka bani Ni Salima in sa?”

“Haba ke baki da wayo wallahi ,kaima tailor zakiyi ya rage maki carasras Zaki fito tas da ke ,duk wanda yace maki kayan mamata ake saidawa ƙaryane…bari fa ki gansu ƙila don A leda ne kike masu kallon tsofaffi tas suke da ƙwarinsu ”

Ya fara zazzago mata su a kan gado
Wani ihu tayi ta yi tsalle tasa hannu tana tunkuɗesu suna zubewa a ƙasa

”Aah karka zuba mun a kan gado”

“Meye haka sai kace kinga najasa! Suturune fa masu ƙwari da kyau”

“To Ni bana so ,ko ana dole ne ? Kai ka sa mana..Abu sai zuba wari yakeyi ,Ni har kaina ma ya fara mun ciwo ka fitar mun dashi!!” tayi magana da ƙarfi

Ɗaukan ɗankwalin atamfar yayi ya kanga a hanci “Wainnan kayan ne zakice da warrriiii” jan sunan warin yayi saboda yanda warin gwanjo ya daki hancinsa a take yaji ƙwaƙwalwarsa ta hautsina ,da sauri ya sauke a kusa da hancinsa.

“Aah maida dai ai bakaji komai ba shaƙa da kyau..” marairaice fuska yayi kamar zai rusa Ihu.

“Ai naji …hummm hummm..na shinshina Ni banji komai ba ,rainuwa ne dai irin na matan zamani a ƙi maku kuyi ƙorafi. Ai maku kuma ku raina,Salima kin sauya wannan ba itace salimar da na aura ba”

“ya Sheikh Nagode ba sai ka fada mun ka gaji dani ba nima na gaji da wannan Auren ,da gatana ka ganni da Suturu na ,bazan zauna yunwa da rashin walwala ya zama ajalina ba kai daidai da kwanciyar aure bayi kake ba ,so kake ka jefani a halin zina?? Wani hakkin aure daya da Ubangiji ya baka kake iya saukewa fully ya sheikh ehmm ,a hakan ma fa ban fara ajiye ƴaƴa bane ba ,tun azo biyar kudin makaranta ya Sheikh inajin saidai su ƙare a public school,to zuwa yanzu mu haƙura ,Kar in cutar da kaina in cutar da yarana ,Suna da hakkin tarbiyya da ilimi a wajena , kawai aja layi daga nan kafin in fara maka kallon kaskanci mu haƙura da auran nan”

Maimakon ya nuna kakabi sai ma yayi Murmushi “Duk fushin nan saboda na siyo maki gwanjo? Lallai kina da high teste siyama ,bari in tattare kayana in maida a bani kudina”

“No ba don kaya bane Sheikh kawai na gaji ne, jiba ɗazu wai anniversary dinmu Saida Adnan yazo ya tuna muna…Sheikh wai auren dole akayi maka dani ne? Fadamun don Allah ko kuwa auren sadaka ne ,an maka talla na…to in ma haka ne yau na gaji zan bar maka gidan ka ka huta da ciyarwa daga kai sai cikin ka ,don na lura sarai tun da ka aureni rama kake yi ,saboda abincin da kake ci a da ,kamar shi dai kake bamu muke ci mu biyu saboda tattali da tsoron kar arzikinka ya kare”

Fuuuuu ta fice ,ta ɓamo ƙofar ɗakin
“Salima!
Salima!!”

 

0um Aphnan
#Bad boys
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button