Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 13

Sponsored Links

013
___________________
Ya sheikh cikin ujila yaci abincinsa tsabagen rowa a kitchen sauri sauri ya sake ficewa a gidan ya koma Office saboda karma Ambassador ya biyo bayansa .
Sarai ambassador ya gane inda ya Sheikh yaje musamman yanda ya dinga jansa da hira suka ƙi zuwa gida har yunwar cikinsa ya ishesa yaje nearby restaurant yaci abinci .
Fitar Sheikh ba jimawa Salima ta saka hijab ta leƙa waje da bazket din abincin Adnan jikinta nata rawa kar ya Sheikh ya dawo ,yace ta leƙo gate ba tare da izininsa ba . Tana nan tsaye Saiga house maid ɗin maƙociyarsu ta zo zata wuce da alama dai aikenta akayi.

Yafitota tayi ,ta roketa arziki ta mika ma Dr abincin,saida taga ta shiga gidan sannan ta juya gida tana hamdala. Haka ta juya gidan hankalinta wasakayau.

***
4.35pm
All of the Sudden sayyida Salima taji horn ɗin mota a can wajen gidanta ,da sauri ta saka hijabi ta fita taga ko wane baƙo sukayi ,sbd tasan in ya Sheikh ne da kansa yake fitowa ya buɗe gate ya shigo da motarsa .

Motar gidan su ya Sheikh ta gani ,da sauri tasa takalmi ta fita da gudu zata bude gate din Hajiya ta daga mata hannu ta cikin motar ,kana Driver din su ya zo ya buɗe suka shigo gabaɗaya .

“Oyoyo hajiyata”
Ta fada jikin dattijuwar cikin tsantsan so da yarda .
Kamilalliyar mace fara tas kamar Sudanese din nan ta naɗe jikinta da lafaya hannu da ƙafafuwarta sun sha red henna ,ta saka medicated glasses dinta sai zuba ƙamshi takeyi.

Inka ganta baza ka taba cewa ta haifi sayyida ba ma ,balle ya Sheikh ,ƴar gayu ce ta gaske ga tsantsan wayewa da sanin darajar mutum.

A nutse ta lumshe ido tana washe baki ,takai hannu dokin wuyar sayyida “Ɗiyata kin warke? Ai ya cemun kinji sauki ba sai nazo ba ,nikuwa nace dole inzo…”

“Na warke hajjaju na,kinji gwara da kikazo naji daɗi”

Suna shiga falo ta doka ma ya Sheikh kira ga Hajiya nan.

A mamakance yace “Hajiya kuma,ba nace kar tazo ba?” bata bashi amsar sa ba ta kashe wayarta ,sanann ta juya tana kallon Hajiya tana murmushi “Hajiya bari a kawo ruwa”

Ta zumbuɗa da gudu zuwa kitchen ,hajiya ta ɗauka da cewa “Hankali ,Hankali dai”

“To Hajiya na” Murmushi hajiyan tayi “Uhm hum ƙuruciya”

Bottled water ta soma zuwa ta ajiye mata da glass cup ta tsuguna a gabanta ta ɓincine murfin ta tsiyaya mata ruwan ta duƙa ta miƙa mata

Murmushi tayi ta karba “Allah yayi maku albarka”

“Amin hajjajuna😊” Butt sai ga ya Sheikh ya shigo ,yana ɗage labule “Ina hajiyan?….au salamu alaikum hajiya Ashe Saida kika zo”

Cikin kyakyawar turanci tace“Yes I’ve been here Inga zamanku ma” ɗan yaƙe yayi ,gamida gintse fuska

“Barka da zuwa ”

Ita dai Salima miƙewa tayi ta koma kitchen haɗo abinci.

Ta barsu suna hiransu na tsakanin ɗa da uwa.

Tantantan ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da tray ta ɗaura plates ɗin shinkafa da manyan soyayyun pepper chicken ,Banda watsatsun beef kita Ina a cikin abinci da juice Mai sanyi

“Ehoooo😳” Ya Sheikh ya fadi yana duddulo ido a warwaje yanda yaga tayi dankin kaji shi ya firgutashi ,sam shi bai lura da tayi pepper chicken ba Koda ya shigo ɗazu.

Zabura yayi kamar zai fizgo farantin,sai kuma yayi maza ya daidaita kansa gamida gyara zama a kan kujeran da yake.

Ba sayyida ba harta Hajjaju ta lura da firgita da yayi amma suka basar,cikin sanyinta ta ƙarasa gaban hajiyan
“Hajiya ta ga abinci”

Washe baki tayi har kyawawan haƙoran ta suka bayyana mai dauke da hakorin gold
“Salima….aaaah ,nawa ne?” jinjina mata kai tayi don tabbatarwa

Waigawa tayi ta kalli ya Sheikh shima kuwa abincin yake kallo a tsorace
“MashaAllah Salima kai Nagode” ta maza ta ɗan zamo jiki daga kan kujeran tana gyara saman spoon da fork zuwa gabanta

“Eyyeeeeh….anyah! ? A gidan mikdad! Jollop rice da kaji hmmmm… Bismillah” ta fara kai loma ,lumshe ido tayi tana amsar gardin naman a bakinta kana ta watsa ido ta kalli ya Sheikh

“Wannan daɗin a gidanka?”
Huro hanci ya shigayi kamar ƙofar na’isa ,kai da ganinsa kasan bai da gaske ,cikin maraitacciyar murya yace

“Wannan aikin Salima ne ,nima bansan zatayi ba ai”

“Tafɗi! Ai un bacin na gani da ido na ,da wani zai faɗa mun bazan taɓa yarda ba,kusan gabaɗaya rabi da kwatan abincin kaji ne fa…hmmm”

Ji yayi kamar tana masa yarfin ruwan barkono a jiki “Uhmmmm😕”

“Abunda bai taɓa faruwa a gidan nan ba ,saidai gidan ɗan uwanka”

“Kai mama! Haba abincin? Ai ke surukuwarta ne ,dole ta riritaki kamar sarauniya”

“Hmm kamar ban san ɗa na ba,yarona mai maƙon tsiya,da uban madda! Shine zaayi kyakyawar girkin nan a gidansa!”

“Hmm kazan? Mama ki ringa ma mutum kyakyawar zato!”

Ya kare magana yana zazzare ido ba wanda yake son suyi ido hudu sai Salima

“Muna kyakyawar zaton sauyi….amma kuwa idan ya tabbata kai kayi cefanen nan to lallai a jinjina ma Salima ,tayi ijtihadi ba kaɗan ba ,saidai muyi Addu’a Ubangiji ya biyata da mafificin Alkhairi

“Hmm ”kawai yace don ya kasa magana ,itama daganan tayi shiru tana jan girki cikin santi.

Miƙa wuya ya shigayi ,kamar zai faɗa cikin kwanon sarai tana satan kallonsa ,saida taga abun ba sauki sai hadiyar miyau yake ta ɗago hannunta rike da ƙirjin kaza

“Miqdad kodai zakaci ne?”
Caɓe baki yayi “haba ina ! Abu a gidana…kawai cinye🥹” yayi magana kamar zai tsala ihu .

Dariyar ƙeta tayi aikuwa ta cinye namomin nan tas ta kora drinks Mai sanyi

Sai goshin magriba suka raka Hajiya wajen mota ,acan Salima ta barsu ta koma cikin gida . Ai ya Sheikh yana ganin tafiyar motarsu ya shigo gidan da gudun gaske. Ya wuce bedroom ɗinsa a karce,yaje ya buɗe closet din kayansa ,ya Zaro akwatin da yake adana kudi
Ya jijjiga yajishi a ɓame gam ,bako alamar motsi bare ya buɗe .

A ƙagauce
Ya saka pin number din akwatin ya buɗe kuwa,nan yaga shiryayyun daloli lamɓas yanda ya ajiye ,ya koma ya rufe ya saki ajiyar zuciya gamida dafe ƙirji

“Ahhhh Alhmdullahi ”

A guje Salima ta fito daga toilet wacce ta shiga ɗauro alwalar magrib
Sakamakon jin gudu daga matakalen bene ,kaf kaf kaf,Kamar an biyo barawo.

Tana ganin shi tsaye hannunsa rike da murfin drawer kayansa ga akwatin kudinsa akan gado yasa ta Zaro ido

“Sheikh kaine da gudu kuma?…haba ka bani tsoro wlh“

Dafe kirji yayi yana ajiyar numfashi
“Nima ai kin kusa saka mun hawan jini…ina kika sama kudin da kikayi girkin nan?”

Murmushi tayi na jin dadi ,saidai kafin ta ɓara tayi magana ya zarce da bala’i

“Kudina kika dauka ko?..me yasa zaki daukar mun kudi ba tareda izini na ba”?

Rau rau rau 😔Idonta suka kawo ruwa

“Innalilllahi wainna ilaihir rajiunnnn…nikam me zaisa in ɗaukar maka kudi ? Tsawon zaman mu ban taba daukan maka kudi ba sai yau da rana tsaka…Duk wahalar da nasha a baya lokacin da ban saba da wuyar ba amma na jure sai yanzu da na saba da izayar ka?”

“Ni dai ba dogon turanci na tambaya ba…amsa mun tambayata ,in ba kudina kika diba ba to wa ya baki kudi?”

“Allah sarki ne! To Allah ne ya ji tausayina ya hana mun jin kunyar mama,ya turo makocinmu ya rokeni in masa jollop rice ya dauko dubu goma sharrrr ya bani to shine na cika nayi cefanen da ka gani…………….”

 

 

Oum Aphnan✍🏽
#BAD BOYS

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button