Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 12

Sponsored Links

012
___________________
Ana yin Sallah ,daga masallaci Ya Sheikh ya sulale ya gudu yabar Ambassador yana addu’a ,A harzuke ya shigo gidan yana kwarara mata kira
“Salima
Salima
Salima”

Daga kitchen ta fito da gudu hannunta rike da ludayin juya stew.
Sai zuba haki da numfarfashi takeyi har tana tuntuɓe da tsikara tsikaran ƙafafun kujeran royals ɗin falon .
A falon sukayi kaciɓis ,daidai yana watsi da jakar hannunsa da hula da malun malun .Like he’s in readiness in battling with her.
“Ya sheikh sannu da dawowa…” kwatseta yayi da masifa.

“Me kikaje kika cema abokina? Mutumin da ko mata baiyi da shi me kika ce masa…hmmm hmmmm hmmmm” ya tsaya yana haki kamar wanda yayi gudu tsabagen ci da zuci .

A nutse tace “Ya Sheikh me kuwa Zan ce masa?”

“Ke dallah yimun shiru,baki masa maganar kudin cefane bane baya isanki zaizo yana mun korafi,wai kina zuwa kasuwa da kafa kudi baya isanki ,baki siyan high tasted food stuff”

Zumɓura Baki tayi “Oh Sheikh me kadauki mutane ne? Suna fa da ido, duk abinda ke faruwa suna kallo…”

“Ke ke karki raina mun wayo ,wani irin magana ne suna da ido , Ambassador ya taba zuwa gidan nan ,for the past 3 years tun bayan bikinmu?….me kike gaya masa ?!” ya sake tambayar ta cikin tsawa .

Kautar da fuska tayi cikin gajiyawa “Ban fada masa komai ba”

Sa hannu yayi ya waigo da fuskarta suna kallon juna ido cikin ido ,itama kar ta tsaida idonta a kansa ,cikin gajiyawa da halinsa

“Karki tunzurani Salima ,Salima karki kaini bango”

Mere Baki tayi 😕“Dama can a tunzure kake ,idan kuma ya wuce haka ai saidai Salima taji duka ko ta ina….so yallaɓai nine zan ce maka kar ka tunzurani😠” ta juya fuuuuu zuwa hanyar kitchen .

Ƙwalla ihun balai yayi
“Heeee iyyyeh🤔Nine Nike magana Matana tana maida mun da magana?…Salima yaushe kika zama haka…Salima…Salima…” ya shiga kwarara mata kira ko waigowa batayi ba ,ta wuce kitchen ta hau zuzzuba abincinta a warmers ta ɗauki mafi tsadar warmers din ta da ya Sheikh ya hanata amfani dashi ta ɗauraye ta goge ta zuba ma doctor kalolin abincincuwansa a ciki ,maman Sheikh ma ta zuba mata nata sauran ta ɗibi nata a plate ta diban ma sheikh a plate Kamar yanda a ka saba.
Yau ranta tururi kawai yake.

Shigowa kitchen din yayi yana cigaba da mata jaraba
“Ni kike maida ma magana?”
Ɗagowa tayi ta masa wani kallo🤨 kana ta cigaba da goge inda ta ɓata
“Salima dake nike magana ,Ni nake Maki magana kina tafiya ki barni?…wait wait dakata” Idonsa ne ya sauka akan kyawawan kulolin da ta jera abincincuwa kamar zasuyi picnic .
Da sauri ya soma bubbudawa yana ganin girki na kece raini gefe ɗaya ga juice ɗin kankana ,Pineapple madara ta saka ƙanƙara sai naso yake a jug din glass .

Kambu…Duk hajiyar kikayi ma wannan to yanzu zan kirata ta fasa zuwa ai ba biki ake ba,inji da maciyin (Foodie) da kika gayyato mun gida… kuma ki Sauya kulolin nan”

Kallon banza ta masa “Ai dayike ma babana ya siya mun”!

“Au Ni kike wa gori?”

“Uhm” ,ta sunkuci warmers din da juices din ta sa cikin basket ta yi reserving ɗinsa a gefe ,ta wuce ɗakinta ta barshi a kasa yana ta buɗe buɗe.

Leave a Reply

Back to top button