Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 1

Sponsored Links

By…
Oum Aphnan

Bismillahir rahmanir rahim
___________________
001
3.30 Na tsakar dare.
“Salima!
Salima!!
Salima!!!”

Cikin wannan talatainin daren Salima ta jiyo Muryar mijinta Sheikh Al_Miqdad yana kwarara mata kira .
A furgice Salima ta dirko daga kan mashahurin gadonta fari fari tarrr lulluɓe da fararen lausassun zanniwan gado .
Tana haki tayi kichin dinta da gudu ta inda take jiyo muryarsa yana kwarara mata kira ,Duk zaton ta Ya Sheikh ne ya ƙone da ruwan zafi. Ko shocking din lantarki ta kamashi.

Da gudu ta hankaɗa kofar ta shiga kicin ɗin ,tsaye ta ganshi yana tafa hannu yana kaiwa da dawowa Sai kuma ya shafa dogon cikakken gashin gemunsa ya sake rafka salati

“Innalillahi wainna ilaihir rajiunnnn….wohoho ! Uhm uhm….ke duniya ke duniya!!”

Salima ta tsorata matuka gaya don haka a tsorace ta ce “Ya Sheikh ma Asabak?( Me ya faru da kai?)” ta tambayeshi da larabci

Nuna mata dust bin yayi da yatsa ,wannan yasa ta kalli wajen zuba sharan da sauri . Sai kuma tayi turus don bata ga komai ba
“Ya Sheikh manil hadha?” (Menene wannan kenan)

Tsawa ya doka mata da ya saka hanjin cikinta karkaɗawa a tsorace wasu hawayen azaba suka tsilalo mata a ido

“Baƙi_Baƙin me na ke gani a nan?”

Wani sanyayyen ajiyar zuciya tayi kana tasa hannu ta goge ƙwallan tsoron da ya zubo mata

“Ya sheikh Burnt rice ne (Ƙanzo)”

“Mene? Ƙanzo ? Ke kuwa kika zauna kika babbaka mun shinkafa ,a wannan rayuwar da ake ciki? Kinsan yanzun nawa ne tiyan shinkafa a kasuwa? Kinsan fetur yayi tsada kuwa lita 640₦😳amma a haka kika ƙone mun shinkafa duk tulin nan?”

Rausayar da kai tayi cike da ladabi
“Ya Sheikh meye na shouting ,ɗan kaɗan ne fa bai wuce ludayi biyu ba”

Hangame baki yayi yana kallonta cike da mamaki

“Au Salima da so kikayi ki ƙone Kamar plate ɗaya wanda ya isa a baiwa wani magidancin yaci ya ƙoshi?”

Shiru tayi saima ta sunkuyar da kai tana ta salati da addu’ar Allah ya yayyafa ma fitinar nan ruwa a daren nan

“….Ya Salam! Yanzu Ni sai in fita in nemo kudi ,ke da zaki taimake Ni wajen tattalawa amma sai ki babbaka?”
Caɓe fuska tayi da Alamar gundura

“Ya Sheikh Ladainan kharrr sa tasma’una ma aƙul…La dhair lillah….”(Ya Sheikh muna da makota don Allah kayi shiru ,Makota duk zasuji abinda muke cewa ,Plz darene yanzu kowa barci yakeyi….)

Wage Baki yayi yana ihu yana zage glasses ɗin windows ɗin kitchen din

“A ji mana sai me?…sai me? Ina sha nan gida na ne?”

“Sheikh kayi haƙuri kowa yasan jollof rice yana Ƙanzo ba yanda zanyi ”

“Au ke baki da dabarun girki? Meye amfanin abun ƙari da ragin dake jikin gas ɗinki? Ya kamata ,idan kikaga ruwa yayi ƙasa sai ki ta ragewa kita ragewa har ya tsotse ,shikenan fa!!”

“Tom ya Sheikh haka bazai kara faruwa ba ,Isbir lillah (Kayi hakuri don Allah)”

A husace ya wage ƙofar saura ƙiris ya hankaɗe ta sannan ya koma bedroom ɗinsu.

Tsayawa tayi turus tana tunani ,wanda inda sabo yaci ta saba da halin Sheikh kuɗi ne gasunan an tara amma fa baa ci.

A sanyaye ta shigo ɗakin still idonta na rike da barci . Tana shigowa taji yana ƙunƙuni
“Yanzu kana magana kuma sai ace ka cika masifa ,gaskiya ne dai ba’a so mu kuma Inshallah sai mun faɗa”

“Me kuma ya faru?”

“Ji ba fa ,kin fito ɗaki ,kin bar AC a kunne,bazaki iya kashewa ba in kin dawo ki kunna? Wai kinsan nawa ya ja kuwa? ”

“Haba Sheikh naji kana ihun kirana da salati ,na ɗauka ka ƙone ne ko wani matsalan shiyasa nayi gudu naje …”

“Shiru! 🤫 Karki sake fitamun daki baki kashe AC ba ,koda mutum zai mutu ki kashe AC kafin ki fita ,ko kuwa rayuwarsa yana hannunki ne? Me yasa baki ganewa ne ehen ,bawa bai isa ya tunkuɗe ƙaddarar da Allah zai ma wani bawa ba,don haka karki fake da wannan ki jamun asara!”

Cikin gundura tace “To shiknn naji nidai inaso inyi barci” ta wuce kan gado taja bargo” .
Tsaki yaja ya ɗauki remote ɗin Ac en ya kashe ya dawo ya shige bargon Shima.

“Ha’ah🥹Sheikh meye na kashewa kuma?”

“Ina sha sanyi kike ji? Karewa ma gaki a cikin bargo,ki bari in kinajin zafi sai a kunna ,du Allah ku koyi yanda ake tattalin kuɗi ,Ni koda nayi rayuwa ta a Sa’udiyya fiye da shekaru goma ,bana Almubazzaranci ina ganin Ac a kunne nake kashewa har a maktibah(Library) To balle nan nigeria….Don haka in ke Baki tausayina zan fara tausayin kaina !”

****
Ynz Dai kowa yasan Talatainin dare ne.
Ko’ina yayi shiru bakajin kukan komai ,gari yayi Lilis .
Kaso 85% Na talakawa masu fagauniyar neman na kansu ,sun samu natsuwa,ta hanyar yada kafadunsa don warware gajiyar yinin ranar .
A yayin da manyan masu kuɗin duniya suka nitsa cikin meeting tare da manyan masu kuɗi Don haɓɓaka arziƙinsu …Ƴan siyasa sun nitsa cikin tunanin mafitar cigaban Mulkinsu da yanda zasu cigaba da cusa tsoro da kwarjininsu a cikin ƙirajen Talakawansu…,Mugayen Mutane kuma tuni sun nausa wajen niman arziki ta hanyar amfani da dodanni da zubda jini don neman duniya(Cultism) wasu kuma ta hanyar ƙwacen Arzikin Al’umma,ta hanyar amfani da muggan makamai harma da kisa (Arm robbery)…..Kuma a daidai wannan Lokacin ne bayin Allah suka sunkuya kan darduman su cikin tsananin ƙanƙan da kai Don neman biyan buƙatunsu da neman kusanci daga wajen me duka…(ALLAH)

DUNIYA! Zaman ƴan marina kowa da fuskar da ya dosa!!

Yaro ɓata hankalin dare kayi suna ,wannan karin maganar tayi daidai da rayuwar Yarima ABBAD Ɗan Sarki,kuma ɗan takarar GWAMNAN jihar Kaduna a halin yanzu,Daya kasance cikin sujuda Sanye da fari tar ɗin Jallabiya,da hirami da ya lulluɓa a saman kansa ,wannan yasa sam komin ƙwaƙwan mai karatu bai isa ya gano Fuskarsa ba.
Ɗakin yayi tsit banda sanyin Ac dake hura daddaɗan turaren ɗakin babu abinda zai ringa dukan fuskar ka.
Yayi Liiissss a sujudi tamkar ba wannan ARROGANT Prince🤴 ɗin ba ,the Almighty gomna da mutane ke masa inkiya da ZAKI (Lion)

Shekarunsa 34 ,Amma ya shiga cikin manyan masu kuɗin Nigeria ,banda shugabanci ,ya samu Izzah da buwaya da take duk wani talaka dake ƙarƙashin yankinsa,wannan yasa har wasu suke Alaƙantashi da Mugun Yarima😡
Su biyu ne tak ɗiyoyin mai martaba Shi da ƙanwarsa Gimbiya Jasmine .
Kuma duk sun fito ne daga ɗakin uwargidan srki ,Gimbiya mai babbar Ɗaki.

A sanyaye ya ɗago daga sujudan yayi tahiya ya sallame sallah ,kana ya ɗaga hannunsa sama,har zuwa sannan baka iya ganin fuskarsa saboda ƙanƙan da kai

“Ya Allah ka bani Mulki ,Mulki da baka taɓa baiwa wani makamancin sa ba a wannan ƙarnin ,Ya Allah ka bani Sarauta in zama Sarki a lokaci guda in Kuma zama GOMNAN Al’umma,abune da ba’a taɓayi ba ,amma Allah ka nuna musu isuwarka ya Allah!🤲”

Topah🤔Haka zai yu? Zalamar batayi yawa ba? Ga mulki ga sarauta?
Muje zuwa!.

Muje zuwa

Leave a Reply

Back to top button