Hamshakiya 17
*🌸HAMSHAƘIYA*🌸
Na
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 17*
“Faruk bugun hannunshi yayi a jikin mota sannan ya shiga ciki ya fara tuki yana bin bayansu, har police station suka isa tare dashi, sai kallon kallo ake tsakanin Umar da Amrish, bayan sun isa akace ta cire kayan jikinta tasa uniform na prisoners, karɓa tayi tana murmushi tana kallon Umar wanda yake aika mata kallon tsana hannunshi ɗaure da ankwa, shiga ciki tayi bayan ta cire duk wani abin jikinta harda zobe basu barta da komai ba, uniform ɗin tasa riga dogo ne da wando a kasa, yayi mata kyau sosai gata fara sol a cikin kayan, dawowa tayi domin mika musu kayan data cire, time ɗin an cirewa Umar ankwa an bashi kayan maza ance yaje yasa, ta gefenshi tazo zata wuce ya rikota ya haɗata da jikin bango, wuyanta ya shaƙe yana buga kanta da jikin bangon yana huci, da gudu police Suka karaso suna kwatanta, sai kallonshi take idonta yana hawaye, har yanzu dariya take tana kuka, ba karamin shaƙa ya yiwa wuyanta ba, ƴan sanda sun kai biyar sun kasa kwatan ta, kwantar da ita yayi akasa so yake ya kasheta shima su kasheshi, shaƙuwa ta fara,ya bita ya danne yana cigaba da shaƙe wuyanta, Faruk ne ya shigo office ɗin da gudu, ganin abinda yake faruwa ya zaro ido yaje yana janye Umar daga kanta, da kyar suka kwaceta daga hannunshi, a hankali ta mike wuyanta yayi ja, tari tayi tana haƙi ta miƙe, ji tayi jiri ya ɗibeta a harharɗe ta fara tafiya yana tangal tangal hannunta akan wuyanta kamar zata faɗi, da kyar ya isa wurin macen ƴar sanda da take tsaye tana jira tazo ta kaita cell, juyowa tayi ta kalli Faruk wanda ya tsaya yana kallonta, murmushi tayi mishi hawaye yana sauka daga idonta sannan ta juya taci gaba da tafiya, jingina yayi da jikin bango yana kallon Amrish har ta ɓacewa ganinshi.
ɓangaren mata aka kaita ɗakin su biyu ne a ciki suna isa matan ta wullata ciki saida kanta ya bugu da jikin bango, zama tayi a kasa har yanzu hannunta a wuyanta tana jin zafi sosai, matan dake gefe tana kallonta batayi mata magana ba ta mike ta ɗibo ruwa a wani ƙaramin randa ta kawo mata, karɓa tayi tasha tace “na gode”
kwanciya tayi a kasa ta lumshe ido tana jin sanyi yana shiga jikinta.
a hankali ya koma cikin mota ya ɗauko goran ruwa yazo ciki, tafiya ya fara har zuwa ɓangaren mata ganinta yayi kwance a kasa tasa hannu ta rufe kanta ta lumshe ido kamar me bacci, kanshi ya ɗauke sannan yace “Amrish”
bata buɗe ido ba tace “na’am”
“ga ruwa”
juya mishi baya tayi ta ɗaura hannu akan goshinta inda ya fashe yana fitar da jini, jin bata amsa mishi ba ya juyo yana kallonta, hannunta yaji ciwo sosai yana jini da alama wurin faɗanta da Umar ne hakan ya faru, lumshe ido yayi ganin batada niyyan tashi ya juya jiki a sanyaye yabar wurin.
Umar ya canja kaya izuwa na prisoners kallon faruk yayi wanda ya jingina da jikin bango yace “dan Allah kada ka nunawa kowa kaine faruk ka bari na karɓi wannan hukuncin”
baiyi magana ba sai idonshi daya cika da hawaye, yana kallo aka shiga da Umar ɓangaren maza, jiki a mace ta fita daga prison ɗin ya shiga motan daya zo dashi wanda yake mallakin Amrish be ya nufi gida.
yana shiga ya nemi hanyan ɗakinsu so yake yaje ɗaki ya kwanta yayi kuka ko zaiji sauƙin abinda yake damunshi, Ammi tace “Faruk?”
tsayawa yayi bai juyo ba yana share hawaye, saida ya kakalo murmushi ya juyo yace “na’am Ammi ya akayi kika ganeni?”
“nasan kaine kake iya shigowa gida ba tareda ka nemi kowa ba ka wuce ɗaki, saɓanin Umar da sai yaje har ɗakina ya dubani”
da gudu ya karasa wurin Ammi ya rungumeta ya fashe da kuka, bubbuga bayanshi ta fara a hankali tana cewa “is okay ka daina kuka”
saida yayi me isanshi sannan ya ɗago kai yace “an kama Umar”
shafa kanshi tayi tace “naga komai a news kada ka damu insha Allah zai fito nan bada jimawa ba, amma wannan yarinyar wacece?”
kanshi kasa yace “budurwa ta ce, itace wacce nace muku ina sonta”
riko hannunshi tayi suka zauna akan kujera tana danne wa ne kawai amma itama tana cikin tashin hankali, kallonshi tayi har yanzu yana sharan kwalla, tace “nace kukan nan ya isa haka”
shiru yayi ya kwantar da kanshi a kan kafarta yace “ina sonta Ammi”
hannu tasa a bakinshi tace “shiii banson jin wannan maganan daga bakinka, let’s focus akan damuwan da Umar yake ciki”
shiru yayi badan yaso ba, waya Ammi ta kira cikin harshen turanci tayi magana sannan ta ajiye wayan tace “ba zai kai sati a cell ba zai fito, ita wannan yarinyar me yamata da zatayi mishi sharri haka?”
“Ammi ba sharri bane”
“oh gaskiya ne kenan? kenan ka yadda Umar shine yake tayata duk wani laifi data aikata? da fari na ganta a gidan marayun she’s innocent amma da naji labari a kanta ta bani mamaki ba kaɗan ba, bansan dalilin da yasa take aikata wannan manyan zunuban ba”.
“Ammi…”
“banson jin komai daga bakinka faruk Umar zai fito ita kuma saina koya mata hankali ba zata kara yiwa mutum sharri ba daga kanshi insha Allah”
“Innalillahi” yake amtaba a ranshi”
Elham ce ta dawo daga school hannunta rike da jakanta wanda ta goyashi a baya, jikinta a mace domin abinda yake faruwa baya mata daɗi, zama tayi a gefensu tace “ya Umar barka da gida”
amsawa yayi “kin dawo?”
“eh wallahi ba labarin ya Faruk har yanzu?”
“wannan ba Umar bane Faruk ne elham Umar yana prison”
dafa kirji tayi “prison kuma Ammi? meya kaishi prison?”
Ammi tace “jeki ɗaki ki cire uniform ki huta ba magananki bane wannan”
tashi tayi zata tafi taga an nuno a tv lokacin da Umar ya shaƙe Amrish sai maimata wurin suke ana cewa yayi attempting kisa, kallon Ammi tayi sannan ta kara maida hankalinta kan tv taga sun fara maimaicin labarin da suka bada ɗazu na laifin da Umar ya aikata yana da sa hannu akan duk wani abinda Amrish takeyi.
“Ammi wacece kuma Amrish? wace irin muguwace ita?”
hoton Amrish aka nuno lokacin da take gidan marayu da kuma wanda take jikin mota tana murmushi, da mamaki ta zauna akan kujera tana maida hankali kan new ɗin saida suka gama bada labari tass sannan tace “Ammi yanzu ba zamu kara zama da ya umar ba shima kasheshi za’ayi?”
“a,a gobe ma zamuje mu dubashi zasu sakeshi nayi waya da commissioner ajnima zan kira governor adamawa zaiyi musu magana ku kwantar da hankalinku”
“to Ammi”
ta faɗa ta tashi daga wurin taje ɗaki ta cire uniform tasa riga guntu da hula ta fito, zama tayi a gefe tayi tagumi tana kallon Faruk wanda yayi shiru yana kallon silin ha kanshi har yanzu akan kafar Ammi, da alama ya zurfafa cikin tunanin.
*Jiddah Ce*