Hamshakiya 10
Na
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 10*
“Kanshi kasa yana duba kafarshi har saman takalmin ya huje ba karamin taku ta yiwa kafarshi ba, ɗagowa yayi ya ganta yaga bata nan ta tafi, coffee da baisha ba kenan ya mike ya fita daga wajen yana ɗingisa kafa yana cije leɓe, kallonshi tayi ta cikin bakin glass ɗin tited dake jikin motan, zata iya hangoshi ta ciki shikuma ba zai ganta ba, daɗi takeji domin yadda taga yana cije baki alaman yaji zafi sosai, murmushi tayi a ranta tace “saina rama duk abinda ka yiwa Teema”
jan motan tayi tabar wurin, gidanta taje ta kwaɓe kayan ta ɗau takaddun gidan ta ajiye a wuri keɓantacce ta ɓoye, canja kaya tayi izuwa wanda yaji jiki ta fita da hijabi fari a jikinta, taxi ta tara ta hau, a kofan gidan marayu ta sauka, shiga ciki tayi ta samu Unty sadiya tana yiwa yara wanka, karɓa tayi ta fara yimusu tanaji Unty sadiya tana tambaya ina kikaje haka kika jima? yi tayi kamar bataji ba taci gaba da yi musu wanka, Najma ta ɗauko tayi mata wanka me kyau kafin ta juya ta koma ɗaki, zama tayi a bakin katifa ta fara shafawa yaran mai, saida ga gama tasa musu kaya tace suje suyi karatun kur’ani, tare suka fita sukaje suka fara karatu.
kallon unty sadiya tayi tace “naje kasuwa ne kuma ban samu abinda ya kaini ba”
“to ki daina jimawa idan kin fita kinji?”
jijjiga kai tayi tana kallon wani koɗaɗɗen riga da Unty sadiya take sawa Najma, yarinya karama babu surutan kirki, ɗauke kai tayi kafin ta mike ta fita daga ɗakin taje banɗaki, waya ta ciro ta danna call, cikin kasa da murya tace “gobe da safe zaku fara aiki”
amsawa akayi da “tom hajiya”
murya ƙasa tace “hamshaƙiya ba Hajiya ba”
murmushi tayi jin ance hamshaƙiya, fita tayi daga toilet ɗin ta fara tafiya tana kallon cikin gidan, ɗakinsu teema taje taga kawayen teema a zaune sunyi tagumi, wacce sukafi shaƙuwa da teema itace Abida, zama tayi a gefen Abida tace “ku daina tagumi idan kun zauna insha Allah muma mun kusa zama mutane, zamuyi rayuwa kamar yadda kowacce mace take rayuwa”
“har yaushe? har zuwa yaushe Amrish? masu kuɗi saide suzo su kwashemu su biya buƙatarsu damu, kowa bayason aurenmu saboda bamuda gata, bamuda masu kula damu, ya zamuyi da rayuwarmu?”
shiru tayi bata kuma cewa komai ba, batason ganin ƴan uwanta a wannan halin, a hankali ta mike ta fita, waje kofa taje domin dolene ta kashe wancan ɗayan likitan wanda shine ya fara jefa zainab a wannan halakan, abin mamaki ta ganshi yau ya fito daga mota yana kallon kofan gidan, ɗauke kai tayi shina yana ganinta ya haɗa fuska yana kallon gefe, wucewa tayi ta samu taxi ta shiga, asibiti taje akayi mata kwatancen gidanshi, batayi kuskuren cire facemask ba, saida ta samu information akanshi kafin ta juya ta koma gida.
ajiyan zuciya ta sauke ganin baya wurin, ta shiga ciki ta zauna tana jiran dare yayi, abinda zai hanata kisan yau saide ikon Allah.
aikinta ta gama da yamma sosai ta shirya yara ta gama komai itama tayi wanka ta zauna ta kara musu karatu.
*Tsakiyan dare*
Tafiya take cikin shirin data saba yi, fuskanta rufe da bakin kyalle jikinta sanye da kaya irin na maza, gidan da akayi mata kwatance ta tsaya duba ko ina tayi taga ba wasu masu tsaro sai me gadi, shima ya fara gyangyaɗi, cikin sanɗa ta shige ciki, kai tsaye inda tasan shine bedroom ta wuce, yana bacci matarshi tana gefenshi, kallon matar tayi taji ta bata tausayi akwai zafi rayuwa ba miji amma ya ta iya? mijinta ne ya janyo hakan, cikin sanɗa ta karasa cikin ɗakin, pillow ta ɗaga a hankali ta ɗaura akan fuskarshi, hannu ya ɗaga zai bigeta tasa wuƙa ta yanka hannun, zaiyi ihu ta danna kanshi da pillow nan suka fara kokawa yana son kwatan kanshi tana dannewa da pillow, ganin ya suma ya daina numfashi ta ɗago wuƙan ta daɓa mishi a ciki, bata cire Pillow a kanshi ba ta kuma ɗaba mishi a ciki, a hankali ta kai bakinta kunnenshi tace “bada sona na kashe ka ba, kune kuka jefani a wannan halin”
cire wukan tayi ta ɗaga pillow ta tafi dashi, dan tasan idan anzo bincike zasu auna pillow kuma zasuga shatin hannunta, barin gidan tayi, ta koma gidan ɗayan mutumin shima a daren ta kasheshi, bata dawo gidan ba saida ta kashe mutane shida kafin ta kama hanyan gidan a galabaice tana tafiya tana layi dan jini yana shirin hawa kanta, tafiya take kamar zata faɗi, da kyar ta isa gidan marayun hannunta rike da babban jaka wanda yake cike da manyan kuɗaɗe taje ɗakin ta ɓoye kafin ta cire kayan tanajin kanta yana nauyi, da kyar ta koma ɗakinsu ta faɗi kasa.
Zazzaɓi ne ya rufe ta kanta ya fara sara mata, bargo ta janyo ta lulluɓa tana ɓarin jiki har hakoranta suna haɗuwa, cikin nishi tace “Unty sadiya ruwa”
tana kwance a gefe taji muryan Amrish tana kiran a bata ruwa, da sauri ta tashi ta ɗibo ruwan tazo wurinta, ɗagota tayi taga sai ɓarin jiki take, “zazzaɓi ne? sannu”
Girgiza kai tayi, ruwan ta bata ta ɗauko paracetamol ta bata hadiyewa tayi kafin ta koma tana bacci, har yanzu jikinta bai daina rawa ba, ga wani zafi da jikin yayi, ruwa Unty sadiya ta ɗibo tazo da tsumma ta fara goge jikin a hankali ya fara yin sanyi, rufata tayi da bargon Najma tana cewa “sannu” har bacci ya ɗauketa.
komawa tayi ta sauke najma akan katifan tazo ta tashi Amrish tace ta koma katifan kasa akwai sanyi, ba musu ta mike ta faɗa kan katifan taci gaba da bacci.
*Washe gari*
Ta makara tashin sallan asuba domin zazzaɓin daya dameta jiya da dare, kafin ta tashi anzo gidan an fara rushewa, ba’a taɓa part nasu ba, saida aka gama kafin ta tashi tayi alwala tayi salla, fita sukayi su duka suka tsaya a waje wasu daga cikinsu har sun fara kuka sun zata koransu za’ayi daga gidan tunda shugaba ta mutu, Amrish tana kallonsu batayi magana ba, hatta Unty sadiya ta tsorata saide kawai batayi magana bane dan batason hankalin su Amrish ya tashi.
Saida aka gama rushewa a ranan aka fara gini, anan ne hankalinsu ya kwanta, gini me kyau upstair zasuyi a wurin.
a bakin masu gini taji suna cewa an fara gudanar da bincike akan kisan da akayi jiya da dare kuma komai yana hannun captain Faruk, cikin ranta tace “wannan gayen shine captain Faruk ko?”
wurin Abida taje tace “miye sunan saurayin Teema me rasuwa?”
“sunanshi Umar”
godiya tayi kafin ta koma ta zauna a karkashin bishiya “UMAR FARUK?”
sunanshi Umar kuma sunanshi Faruk, Umar Faruk kenan, mutumin daya lalata rayuwar yarinya har ta kashe kanta shine zaiyi bincike akan mutuwan wasu? baima dace da aikin soja ba yafi dacewa da zaman hotel.
tunanin ta yadda zata ɓullo mishi tayi, ta zurfafa cikin tunani kafin ta tashi tana kallon masu ginin wani daga cikinsu yace “ke bamu ruwa”
kallonshi tayi yadda yayi maganan da gadara zakace shi ya haifeta, ganin ta zuba mishi ido yace “ba zaki kawo bane? ina duk wahalan da akeyi saboda ku ne, ko mune zamu zauna a gidan idan an gyara?”
cikin tsawa yake maganan bata mishi magana ba taje ta ɗibo ruwan ta kawo mishi, karɓa yayi yana cigaba da surutu “ana shan wahala akanku baku gani, ire-iren yaran da suka taso a irin wannan gidan su suke girma su zama karuwai wasu kuma su zama mashaya wasu su fara kawalci duk ba abinda basayi, gashi basa ganin darajan mutum, iyayensu su haifesu shegu su yar dasu a titi a ɗaukesu a taimaki rayuwarsu suzo suna watsawa mutane kasa a ido”
barin wurin tayi bata taɓa jin tsanan iyayenta ba kamar yau, wata kila itama shegiya aka haifeta, haɗa kai tayi da gwiwa ta fara raira kuka, saida idonta da fuskarta sukayi jajur kafin ta mike zata tafi wurinsu unty Sadiya taji yace “zo kije ki siyomin gyaɗa”
karɓan kuɗin tayi ta fita zuwa waje, har yanzu idonta jawur tana cigaba da share hawaye, a hankali ya zuba mata ido jikinshi yayi sanyi ganin tana kuka, ganin babu me gyaɗa anan kusa ta fara tafiya zataje gaba ta duba, da mota ya fara binta har ya iso inda take, tsayawa yayi bayan ya mata sallama, a hankali ta juyo ta amsa, cigaba tayi da tafiya yace “idan ba damuwa ki shigo na kaiki inda zakije”
kin shiga tayi tace “ba komai zan iso yanzu nan ne ba nisa”
Murmushi yayi “ko baki yadda dani bane madam?”
a ranta tace “wa zai yadda da mugu azzalumi irinka?”
a fili kuma tace “a,a kawai de zan isone ba damuwa”
“dan Allah ki shigo ba abinda zai faru dake”
a hankali ta tsaya tana kallonshi buɗe mata marfin yayi ta shiga ta zauna tana wasa da yatsun hannunta kanta kasa, murmushi yayi yace “sunana faruk”
a ranta tace “na sani ba sai ka faɗa ba”
a fili tace “ayya”
“ke kuma ya sunanki?”
“Amrish”
“wow suna me daɗi, anan gidan kika taso?”
giɗa kai tayi kafin a hankali tace “a nan gidan na taso tun ina yarinya inada kawaye inada ƴan uwa wanda bazanso wani abu ya samesu ba, idan ma abin ya samesu zan rama musu kota wani hali”
murmushi yayi “ashe madam ɗin tana da surutu, nima ina yawan ziyartan gidan amma yawanci da dare nake zuwa gaskiya”
wani irin kallo ta aika mishi “kenan da dare yake zuwa shi yake zuwa sauke Fatima?”
“me zakije siya?”
“gyaɗa”
tsayawa yayi ya fita gyaɗa dayawa ya siyo ya ajiye mata a gefe kafin ya juya da motan suka kama hanyan gidan, juyawa yayi ya kalleta tana kallon gefe, murmushi ya kumayi haka kawai yana jin nutsuwa yana sauko mishi daya zauna da ita, yau ya yini hankali tashe akan case na mutuwa wanda yayi yawa a cikin kwanakinnan, ya rasa yadda zaiyi gashi sai kashe mutane ake babu shaida babu hanyan gano makashin, kallonshi tayi “kai soja ne?”
“Eh ni soja ne me binciken gawa”
murmushi tayi tace “me binciken gawa kuma? kenan kana iya gano wanda yayi kisan”
“eh ina iya ganowa koda a ido ne”
dariya tayi sosai harda ɗan tafa hannu kafin ta juyo tana kallon cikin idonshi tace “kalli idona to mutum nawa na taɓa kashewa”
Kallon dara daran idanunta yayi wanda suke ɗauke da dogayen eyelashes yace “mutum shida kika kashe jiya”
gabanta ne ya faɗi da kyar ta daƙe tace “wow ka gano kaman ka sani ciki harda kai, ko kuma kai sai wani lokacin zan kashe ka”
dariya ya kwashe dashi kafin yace “kinada barkwanci, yau na wuni cikin ɓacin rai haɗuwata dake yasa nayi dariya kuma naji farin ciki a raina”
“Meya saka ɓacin rai?”
“case ne yamin yawa gashi babu wani abinda za’ace an gano me kisan, gaba ɗaya kaina ya kulle”
“Allah ya bayyana me kisan”
cikin dariya yace “gashi Allah ya bayyana wata kyakkyawar mace a gefena”
dariya tayi tace “kaima kyakkyawa ne”
“Ban kaiki kyau ba”
“harma ka fini”
daga nan basu kara magana ba har suka isa kofan gidan, bayan ya tsaya ya ciro kuɗi ya mika mata, ido ta zubawa kuɗin “da wannan ya cuci Fatima nima haka yakeso ya cuceni”
Kallon tayi tace “a,a na gode”
shima kallonta yayi yace “ki siyawa yara sweet dan naga kinason raba musu”
“Kenan idonshi a kanmu? duk wani motsin gidan yana kallo?”
murmushi kawai tayi tace “saide n karɓi rabi”
karɓa tayi ta cire rabi ta ajiye rabi a gefenshi, yace “ke ƴan biyu ne?”
“A,a niba ƴan biyu bane ni ƴar ɗaya ce” tayi magana tana kokarin buɗe marfin motan, ganin bata iya ba yayi murmushi ya matso dab da ita ya buɗe, zubawa bayanshi ido tayi ji take kamar ta ciro wuka ta caka mishi ko zuciyarta zata daina zafi, ɗagowa yayi yace “ga yadda zaki buɗe”
jijjiga kai tayi “na gode”
da gayya tayi hakan ta nuna mishi batama iya buɗe mota ba.
tasan tambayan da yake mata kanshi ne ya juyu dan yaga me kama da ita a coffee shop, lekowa yayi bayan ta fita yace ta bashi phone numbern ta.
wata karamar nokia ta ciro ta mika mishi karɓa yayi ya ɗau numbern yasa mata nashi tareda yin saving da Faruk, mika mata ledan gyaɗan yayi cikin sanyin muryanta tace “na gode”
Yan kallonta har ta shiga ciki, tana basu gyaɗan ta juya zata tafi yace “baga irinta ba, basu da tarbiyya ko kaɗan, suna da rainin hankali, kalli yadda taje ta daɗe a wurin aika may be ma tana tare da saurayi ne”
a hankali tace “kayi hakuri”
juyawa tayi tabar wurin, batayi mishi magana ba so yake ya maidata yarinya, bai sani ba lokacin datake karɓan kuɗin gyaɗan taga hannunshi da ink na biro kuma taga takadda a gefen aljihun shi wanda ta zubawa ido taga rubutu da tambarin ƴan sanda a jiki, atake ta gane wannan jami’in sirri ne, turoshi akayi domin yayi bincike a cikin gidan.
tasan yanzu har gidan marayu bazasu bari ba dan gudanar da bincike shiyasa take binshi yadda yaso.
tana shiga toilet ta faɗa tana kuka sosai, bataso zama kusa da saurayin Teema ba balle su canja number, kuka tayi sosai har taji kanta yana ciwo kafin ta wanke fuska ta fito daga toilet ɗin, alwala tayi taje ɗaki ta fara salla, bayan ta idar tayi addu’a ta kwanta akan sallayan.
Faruk yana murmushi har ya isa gida yau yaji daɗi da ya aro jarumta ya yiwa innocent Amrish magana, da alama batasan da zaman me kama da ita ba, zaiyi surprising nata watarana ya nuna mata me kama da ita, cikin farin ciki ya isa gida, yana shiga yaje falo da gudu ganin Umar ya fito da brush a baki yaje da gudu ya rungumeshi ya fara juyi dashi, waro ido Umar yayi yana kallon bayanshi, saida ya gama juyi yana murna ya sakeshi, yaje wurin Ammi ya rungumeta ya ɗagata sama, da sauri ta fara marin hannunshi tace “saukeni karka yaddani”
saida ya juya da ita kafin ya ajiyeta yana dariya yayi mata kiss a goshi kafin ya rungumeta.
har yanzu da brush a bakin Umar sai binshi yake da kallo, yau ya fita rai a ɓace ko fara’a baya yi yanzu kuma ya dawo yana tsalle yana murna? meya faru?”
Ammi daɗi taji ganin Faruk yana murna haka, cikin jin daɗin tace “meya faru babana?”
kanshi kasa yace “Ammi nayi budurwa”
waro ido Umar yayi yana cigaba da goge hakoranshi, ɗauke kai tayi domin ya bata kunya tace “wace yarinya ce me sa’a haka?”
“sunanta Amrish”
“nice name aina take? ƴar gidan waye?”
wayarshi ce tayi kara ya ciro daga aljihu yana dubawa, ganin kirane daga wurin aiki ya ɗaga ana nemansu da gaggawa, sallama yayi musu yana cewa “idan na dawo zan faɗa miki”
fita yayi da ɗan gudu ya koma cikin mota driver yaja suka tafi.
zama Ammi tayi akan sofa tana jin dadi, yau taga murna da farin ciki a tareda ɗanta, saida Umar ya wanke bakinshi ya dawo yace “Ammi Faruk yayi hauka ko? akan soyayya yake wannnan tsallen?”
dariya tayi tace “kasan wanda baya soyayya idan ya faɗa ciki yafi kowa haukacewa”
“Tabbas na gani akan Faruk koma wacece wannan yarinyar tanada babban kyauta daga wajena domin tasamin ɗan uwa cikin farin cikin dana jima ban ganshi a ciki ba”
a mota ya kira numbern ta, cikin sa’a ta ɗaga da muryanta me sanyi ta gaisheshi, amsawa yayi yana lumshe ido, shiru sukayi su duka biyu, ɓangarenta har wani hucin zafin zuciya takeyi, kenan yana kiranta dan ya samu ya fara soyayya da ita har ya fara lalata da ita ko?
a hankali ya fara bata labari sai eh da a,a take faɗi idan abin dariya tayi dariya da haka har sukayi sallama.
*Da yammaci*
Yaje shagon coffee yana kallon inda ya saba ganinta, ai kuwa sai gata nan zaune tasa dogon riga baby pink da headband shima baby pink, tasa glass ma baby pink, sai murmushi take tana chatting da babban wayan dake hannunta.
Sakin murmushi yayi a hankali ya fara takunshi cikin izza da nutsuwa ga kuma kwarjini yana isowa yayi mata tafi, ɗago kai tayi tana taunar cingum ta kalleshi sau ɗaya ta watsar, janyo kujera yayi ya zauna yana fuskantar ta, yace “ko zan iya yin magana dake?”
a tsiyace tace “ina jinka”
“ya sunanki?”
kallonshi tayi saida ta taɓe baki tace “sunana Ameera Ibrahim dikko”
“wow malama Ameera kina kama da wata kawata”
“Oh really?”
ta faɗa tana ajiye wayan, murmushi yayi wanda ya kara mishi kyau yace “yeah da fari na zata ku ɗin twins ne saida na tambayeta tace ita kaɗaice ba twins ba”
“nima ni kaɗaice a wurin mahaifina har ya koma ga Allah bai kuma haihuwa ba, mahaifiyata ta mutu lokacin da take haifa na”
“Allah sarki Allah yaji kansu da rahama”
“Ameen”
“zan iya samun numbern ki?”
murmushi tayi nan ya kara ganin tsananin kamansu da Amrish, wayan mika mishi ya karɓa yana kallon hotonta na gaban wayan, ɗaukan numbern yayi yasa mata nashi yayi saving da Umar.
mika mata yayi yace “sunana Umar”
murmushi tayi ta kalli numbern daya sa mata tace “nice name”
“Thanks”
tashi tayi tace “ni zan wuce”
“Tom malama Ameera sai munyi waya”
tafiya tayi tabar wurin, motanta ta shiga ta jingina kanta jikin kujeran kirjinta taji kamar zai faso ya fito waje, zafi takeji kaman tasa hannu aka tayi ihu, acan yace sunanshi Faruk anan kuma yace sunanshi Umar da haka yake amfani da suna yana lalata ƴammata, bugun kirjinta tayi “dolene na gama da wannan dolene na kasheka Captain Umar Faruk”
jan motan tayi da mugun gudu ta fita daga wajen gidanta taje ta zauna a kan sofa tayi crossing leg tana shan wani tsadadden drinks saida ta shanye kwalba ɗaya kafin ta ajiye tana kallon Tv, news take kalla taga ance ana neman wannan Serial killer wacce take kashe masu kuɗi da masu muƙami, mikewa tayi tana zagaye babban falon tana cigaba da kallon Tv, hannunta ta goya ta baya tana cijan leɓe tana kallon yadda suke nuna Faruk yana bayanin yadda me kisan takeyi da dabara, da yatsa ta nunashi, “saura kai kaima bazan barka ba”
bata koma can gidan ba dan tasan yau ana gyara babu me kula da ko tana nan ko bata nan, kallon katafaren gidan tayi a hankali taje ɗaki tasa kayan shan iska, kofan baya tabi nan ta haɗu da wani wuri na shan iska babba, gefe guda lambu ne me ɗauke da kayan itatuwa ga kuma swimming pool dake gefe, zama tayi a bakin ruwan tana plan na abinda zatayi Anjima.
a fili tayi dariya hadda tafi tace “zaku gane kuranku”
*Ki biya ki karanta cikin salama ₦400 ne ta account nawa 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin mtn ta nan 08144818849 masu vtu kuma kuyi, ki turo katin shaidan biya ta nan 08144818849*