Labaran HausaNews

Gwamna Badaru Abubakar ya amince da nadin Muhammad Hameem a matsayin sabon Sarkin Dutse.

Sponsored Links

Jigawa

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya amince da nadin Muhammad Hameem a matsayin sabon Sarkin Dutse.

Ya gaji Nuhu Muhammad Sunusi, wanda ya rasu a wani asibitin Abuja a makon jiya.

Aminiya ta tattaro cewa Sarakunan Dutse sun zabi sabon sarki baki daya daga cikin ‘yan takara uku da ke neman kujerar sarauta.

Sanarwar da Majalisar Masarautar ta fitar ta ce an mika sunan sabon Sarkin ga Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa wadda ita ma ta amince da hukuncin da sarakunan suka dauka, amma ta aike da sunayen sauran wadanda suka tsaya takara biyu ga gwamna domin amincewarsa.

“Daga baya gwamna ya amince da Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon sarkin Dutse daga yau 05/02/2023,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Back to top button