Labaran HausaNews

‘Yan Bindiga sun kashe Mutum 4 sun raunata da Dama a Jihar Katsina

Sponsored Links

'Yan Ta'adda

Wasu gungun mutane da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne a ranar Talata sun kai hari kauyen Jajar Kanwa da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina inda suka kashe mutane uku.

Kazalika ‘yan ta’addan sun jikkata wasu mazauna garin biyu, inda suka yi awon gaba da dabbobin gida tare da kwashe kudade, wayoyin hanu da abinci.

Wata majiya ta bayyanawa jaridar DAILY POST cewa ‘yan ta’addan sun mamaye kauyen ne da misalin karfe biyu na dare a kan babura, yayin da suke dauke da manyan muggan makamai da suka hada da bindigogi kirar AK-47 kuma suka fara harbe-harbe kai tsaye.

‘Yan ta’addan sun yi garkuwa da mutane shida, ciki har da wata mace mai ciki.

Majiyar ta kuma bayyana cewa ‘yan ta’addan sun bukaci mutanen kauyen da su bayar da gudunmuwar Naira 20,000 kowannensu nan da kwanaki bakwai masu zuwa ko kuma su fuskanci mummunan sakamako.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutane biyu sun mutu, uku kuma suka jikkata.

Ya ci gaba da cewa, “Yawancin ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga suna shiga Katsina ta cikin Zamfara saboda ayyukan da ake yi a Sakkwato da Zamfara.”

A cewar PPRO, a lokacin da suke shigowa ne suka far wa wasu mutanen kauyen Kanwar Jaja, karamar hukumar Jibia amma babu wanda aka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

Back to top button