Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 22

Sponsored Links

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣2️⃣

 

……..Koda ya ajiye wayar miƙewa yay zuwa cikin bedroom ɗin sa. Alwala yay domin gabatar da nafilar godiya wa UBANGIJIN talikai mai ƙyautar da kuɗi ko ƙarfin mulki baya badawa a duniya. Gaskiya tunda yake a rayuwarsa baya jin an taɓa masa wani suprice mai taɓa zuciya da jijjiga jinin jiki irin na yau. Bayan ya idar ya jima yana kwararoma ɗan nasa da Lulu kanta addu’oi, tare da fatan ALLAH ya kawo musu dai-daiton wannan al’amari da ƙarshensa cikin sauƙi su cigaba da rayuwa a inuwa ɗaya tamkar sauran ma’aurata. Wayarsa ya sake ɗauka ya dawo falon.

A karan farko Smart yay kiran number Daddy yau tunda yabar Nigeria. Sun gaisa cikin mutunta juna da nuna jin nauyin juna musamman ma shi Smart ɗin. Daddy ne ya fara masa barka, shima Smart ɗin yay masa barkar. Da ga haka Daddy ya bashi haƙuri akan abinda duk ya faru a baya da masa bayanin akwai dalilin yin hakan, zai masa bayani amma ba yanzu ba sai sun haɗu. Sai batun ɓoye masa ciki da inda Lulu take nan ma ya bashi haƙurin kamar yanda Uncle Yousuf ya bashi da masa bayanin dalilin yin hakan. Cikin girmamawa Smart ke roƙon Daddy da ya daina bashi haƙuri shi bai taɓa riƙesa a ransa ba ko ganin laifinsa. Yana masa kallon uban ne da kuma uzuri dan yasan koma minene yanada dalili, ya kuma fahimci hakanne tun a randa Alh. Sulaiman yasa aka satoshi, shiyyasa ma ya haƙura da halayen Lulu ya sake komawa aikin gidan. A yanzun ma yana roƙon Daddyn da ya bar wannan wasan a hannunsa ya kwanta ya huta ya haifa masu masa yaƙin ai, fatansa kawai in har bai shiga hurumin daba nashi ba yana son jin tushen matsalar ne kawai. Murmushin jin daɗi Daddy yayi da ga can har Smart yana iya jiyosa. Da ga haka ya shiga sanya masa albarka da tabbatar masa in sha ALLAH zai sanar masa komai, sannan ya ɗauki kansa matsayin ɗa a garesa koda wasa ya daina jinsa daban a cikin family ɗin sa. Bama shi da suka haɗa jini ba a yanzu ko ahalinsa sun zame musu ahali ai suma. Sosai Smart yaji farin ciki da waɗan nan kalamai na Daddy, tare da sake jin kimarsa da mutuncinsa a zuciyarsa.. da ga haka sukai sallama cikin mutunta juna.
Bayan sun ajiye wayar Smart ya ɗakko laptop ɗin sa ya saka flash ɗin nan a ciki. Ba komai bane face videon yaronsa mai tsananin kama da shi sai Mawaddat ɗinsa da keta kallon jariri tana wani munafukin murmushi tare da motsa lips ɗin ta sai dai baya iya jin mi take faɗa, sai matashiyar matar da ke gefenta tana tofama yaron addu’a. A hankali ya lumshe idanunsa da sakin wata irin raunananniyar ajiyar zuciya ƙwallar ɗinbin farin ciki na sake cika masa idanunsa. Shi yama rasa mizaiyi domin nuna farin cikinsa akan wannan ƙyauta ta UBANGIJI mai tsadar gaske da kuɗi ko alfarma bata badawa a wannan duniya.. ji yake inama zai iya tauntsuwa ya gansa gabansu, kai shi koda muryarta ne yaji ma ta waya zai rage masa nauyin zuciya. Ƙasa haƙuri yay ya turama Uncle Yousuf saƙo akan neman number ta. amma sai ya samu reply cewar babu waya a hannunta amma akwai ta yaron da ya kuɓutar da su mai suna Usman zai tura masa. Duk da ya ɗan ji kishin nasa ya motsa sai ya danne…

*_NIGERIA_*

Sosai ta yi wata irin rama data sake bayyana tsufarta sosai gamai kallo. Ga shi bata da isashiyar lafiya sakamakon tsangwama da rashin kulawar da take fuskanta a hannun matar ɗan nata. Ba komai ya jawo hakan ba kuma sai gara rayuwar surukan nata data jima tanayi a shanun talla. Musamman ma ita matar Uncle Manner ɗin. Itama kuwa sai gashi ALLAH ya bata damar ramawa. Abinda yafi yima Dada ciwo a zuciya makircin Hajiya Aneesa, dan in har Uncle Manner na gida bai isa gane komai akan matar tasa ba, kulawa take bama Dada kamar uwarta mahaifiya, amma yana gusawa kashi ma ya fita daraja. Ta dinga gasa mata azaba da magana kenan masu zafi har sai hawaye sun cikama Dada ido. Ga shi ta hana ƴaƴanta raɓar Dadar sai ubansu na nan, daga bayama ko uban nasu na gida sai basa zuwa, da tayi magana kuma za’ace makaranta ce ta ɓoye su. Kaɗaici da damuwa sunma Dada yawa, ga kewar mijinta da rashin ƴancin data saba dashi na tsawon shekaru, babu irin kalar kiran da bataima Baba Garko da tura masa saƙo ba amma tamkar ma baya ganinta. Abinci kuwa sai wanda aka gadama ake bata dan nata daban ake dafa mata garo-garo su kuma suci lafiyayye. Idan Uncle Manner ya gani kafin ma yace wani abu matarsa ta fara zayyana masa zancen Dada ce tace ai mata, sunyi-sunyi kuma ta kafe harda musu tsiya. Sanin halin mahaifiyar tasa da yayi da irin hantara da ƙyarar da takema matar tasa tunba yanzu ba saya baya maida hankali ko ƙin yarda. Idan kuma ta saka masa kuka da nuna son ita dai a canja mata gida ko’a roƙar mata mijinta sai zuciyarsa na bashi son komawa wajen baban nasu ke damunta kawai. Yakan zauna yay mata nasiha da nuna mata illar biyewa zuciya da ɗan uwan nasa da tayi, yanzu gashi nan ya barta a halin ƙaƙa nakayi, tunda ko Nigeria ya ƙi zuwa, hasalima yaji ƙishin-ƙishin tattare iyalinsa da yake shirin yi su bisa inda yake a ɓoyen saboda tsoron umarnin mahaifinsu akan duk randa ya diro ƙafarsa Nigeria tun a airport a kamashi. Ga kuma tashin hankalin rashin sanin ina Lulu take a yanzu. Dan zuwa yanzu ta gama tabbatar ɗan nata nada manufa akan al’amarin da nasa. Ga Baba yasa an cafke Tajuddeen da ya shigo Nigeria a watan daya gabata, saboda bakinta daya furta cewar tare da shi ake komai ai. Iya binciken Tajuddeen anyi amma ya rantse shi bai san ina ubansa ya kai Lulu ba, ya dai san da su ake komai da farko amma shima kansa bai farga akwai wata manufa a ziciyar mahaifin nasa ba sai bayan na son ya aura masa ita. Sai a randa ya rabosa da Canada ya kwashe su Lulun. Ya kuma rantse a yanzu bai san ina yake ba, dan ya ɓoye kansa ne. Amma sam Baba Garko yace bai yarda ba, ƴan sanda su cigaba da riƙe Tajuddeen ɗin har sai Alh. Sulaiman ya miƙa kansa koya sako Mawaddat. Baba Garko yayi hakane kuma dan ya jima da sanin Tajuddeen shine zuciyar ɗan nasa. Kamar kuma ya sani dan hankalin Alh. Sulaiman na can a tashe game da kama masa yaro, dan haka ya baza mutanensa suketa shige da ficin ganin an saki Tajuddeen ɗin amma hakan ya gagara. Dan Baba ma da babansa, duk ƙarfin ikon da suke jin suna da shi da alfarma a ƙasar Baba Garko ya taka su ya shanye. Wani lokacin ma da bazarsa yake rawa.
Waɗan nan abubuwa marasa daɗi sunka haɗu suka tararma Dada a zuciya dan haka sam ta kasa lafiya. Ga shi a lissafinta wannan watanne na haihuwar Lulu in har Alh. Sulaiman bai salwantar da cikin ba kamar yanda yay niyya tun farko, sannan iddarta ta kusa cika, tana cika kuma hakan na nufin sun rabu kenan, dan tasan irin kafiyar Nana garko, sai idan da rabon su koma ne ma sai an sake ɗaura mata aure da mijin nata na auren tun jajayen sawu. Kwanciyarta asibiti kusan uku a tsakanin nan, a yanzu hakan ma tana asibitin tun shekaran jiya ƙarƙashin umarnin likita, sai banka mata allurar barci suke dan ta samu nutsuwa…

★Tsaf Alhaji Garko na biye da al’amarin matar tasa, kuma ya maida aurensu tun a randa ya saketa kodan tausayin yaransu. Amma ya zaɓi yin biris da ita dan lamarin jikar tasa na ci masa zuciya. Ya kuma ɗauki alƙawarin hukunta ɗan nasa akan wannan al’amarin. A yanzu haka ya baza cid suna kan bincika masa inda yaje ya ɓoye kan nasa, dan yanaji a jikinsa a duk inda yake Mawaddat tana tare da shi….

__________★

Kamar yanda bokanta ya sanar mata ta koma sai da tai yanda tayi wajen hillatar Abba ya sake barinta fita yau suka koma ita da Hajiya Naqiba. Sun gurfana a gabansa suka gama masa bayanin komai, cikin jinjina kai da bugun ƙasa ya ce, “Tabbas akwai ɓoyayyen al’amari kuma iyayensa sun sani, sai dai an gargaɗesu da sanar wa kowa shiyyasa sukaja bakinsu sukai shiru. Kamar yanda na sanar muku tun farko bawai yaron zai gagaremu bane, kawai dai tsaye yake da ƙafafunsa wajen bautama ALLAH tamkar mahaifiyarsa. Bata gajiya kuma da nusar da duka ƴaƴanta ta wannan fannin. Shiyyasa cin galaba a kansa kamar baya abune mai wahala. Amma zamu gwada sa’armu mu gani a yanzun ma sai dai akan matarsa duk da itama tana nata ƙoƙarin . Sai dai maganar gaskiya ban gano abinda zai iya tasirin rabashi da nasarar da ke tunkarosa ba game da abinda yake yi ɗin. Dan lokacin hakanne yayi. Kunsan ance mai laya kiyayi mai zamani. Abinda kawai zan iya muku aiki a kansa shine nisanta shi da al’amarin matarsa itama kuma a nisantata da duk abinda ya shafesa, wannan zai iya zauta masa zuciya ƙila har al’amarin ƙwallon nasa ma ya iya taɓarɓarewa duk da dai abune mai wahala hakan ta kasance. Sannan kuma ko akan wannan farraƙun tsakaninsa da matarsa in ma anci nasarar sake nisantasun fa na gano akwai haɗari a ciki, kuma haɗarin zai iya dawowa ne matsayin ƙaiƙayi koma kan masheƙiya gareki. Yaya kika gani ayi ɗin?”.
Ɗan jimmm Umma tayi yayinda Hajiya Naqiba ta zuba mata ido da mata signal ɗin ta yarda kawai babu abinda zai faru ai sune masu nasara. Wannan ƙarfin gwiwar data hanga a idanun aminayar tata ya sata jin jina ma malamin nasu kai da faɗin, “Babu ma abinda zai faru malam in sha ALLAHU. Ni in sansamu ne ma har uwarsa da uban ai musu kalar asirin nan dan na tsani buɗe ido naga Hafsatu a gidan nan wlhy, sauran sakarkarun basu daman ba, dan babu wacce tasha gabana sai ita. Na rasa wane shegen boka ke mata aiki haka”.
Murmushi malam yayi kawai. Sai kuma zuwa can ya nisa da cewa, “Maganar iyayensa gaskiya bamai yiwuwa bane kamar yanda na faɗa miki. Dan matar nan a tsaye take fa wajen bautama ALLAH. Ke dai kawai ai miki na yaran ma zai baki duk nasarar da kike buƙata in har ba’a samu kuskure ba”.
“Bama za’a samu ba malam ayi kawai.” Hajiya Naqiba ce mai maganar. Malam ya amsa musu da to, tare da gaya masu adadin kuɗun da aikin zaici, babu musu ta ajiye masa duk da da ƙyar ta ƙwaƙulesu a hannun Salim, sai da tasha ƙunƙunai ma da ƙananun magana sannan ya bata. Amma da yake tana so haka ta amsa tana sanya masa albarka……

Koda ta koma gida dukkan yanda akace mata ta aiwatar tayi cikin kulawa da taka tsan-tsan, daga haka ta koma gefen kallon yaya wasan zai fara kuma………✍️

_(Ni dai nace Hummm Ummah kenan🚴😵‍💫)._

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Leave a Reply

Back to top button