Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 5

Sponsored Links

Volume:5 Mrs Mayor
Cikin dattako da nunawa bai wani damu da abin take ganin ya mata ya ce mata, “Kin ga taimakon juna zamu yi, idan ba don ina da hakuri da mutunci ba, waye zai dauki abin da kika mishi? Har gida kika biyo ni ki tsaya ki sauraren ni kika k’i ya kike so na Miki? Sannnan kudin da na biya bai ci a ce an tausaya min ba, kawai sai ki shiga gaya min magana son ranki?”

Idanunta cike da kwalla ta ce mishi..”ban gane kana da hakuri da mutunci ba? Ni kaga bani da su ne?” Kallonta yayi sama da kasa ya ce mata.
“Kin ga auren nan, taimakon juna zamu yi. Sannan idan kin ga ba zaki iya ba. Tow biya ni kudina!” Kura mishi idanu tayi, wato kalmar nan ne kwalelen kare da hantar kura. Duk yadda taso ya kawo wata mafitar sai zuba mishi idanu tayi ta ce mishi.
“Malik! Babu wata mafita ne sai aurenka?”
“Mafita yana hannunki, idan kina sha’awar rayuwar iyalan nan suyi shi kan titi ba damuwa lokacin damina muke shirin fuskanta.” Ya fadi haka yana me juya kekenshi zai bar falon. “Na amince! Na Amince amma bisa nawa sharadin.”
Juya kekenshi yayi yana fuskartatta.
“Idan na aure ka, babu wani abin da zai shiga tsakanin mu!” D’aga kafad’arshi yayi alamar duk ɗaya. “Babu kai babu al’umma charity House. Sannan batun zan haifa maka yara babu shi, domin idan na samu mijin da ya bai kai ka ba, zan aure shi kuma dole ka sake ni!”

…. “Taya zan sake ki bayan aurenmu baki daya na shekara ɗaya ce!” Ya fada yana kallon fuskarta. “Ba zan iya auren shekara guda ne, kin ga daga wannan lokacin zaki iya auren kowa ma kai ko jinjirin da aka haifa yau zaki iya aura. Maganar gaskiya babu saki sai lokacin ya cika.”
“Malik kayi min alkawarin ko bayan mun rabu ba zaka tab’a al’umma charity House ba?”
“Wannan alƙawari nayi miki, ba al’umma charity House ba, rayuwar duk wanda yake cikin gidan abin karewata ne, domin na auri Yarsu.”
Takawa tayi tare da sunkuyawa ta ce mishi.
“Daga ranar da ka gaza kare rayuwarsu, da tawa rayuwar zan barka kuma zan farmake ka da yaki har sai na kai ka kasa. Malik ina jin wani abu a raina wanda ban san meye shi ba, sai dai daga ranar da na samu kaci amanata. Wuka zan dauka sai na huta nan” ta tab’a daidai bugun zuciyar shi.”

Lumshe idanun yayi ya zuba mata, sannan ya ce mata. “Ni bana cin amana, shekaru goma sha uku baya ma,na kare rayuwar mutanen da suka yarda da ni, na dauki amanar da aka bar min kuma ina fatar na cika shi. Gaya min bayan wannan me kike so!”
“Bayan shi kada ka sake kace zaka fara soyayya da ni, domin ba iyawa zan yi ba.” Murmushi yayi ya ce mata. “Xnoo yar kunama, me zai saka na fara soyayya da ke? Ai soyayya ta yara ce, masu jini a jika ni kuma ɗan gurgu ina zan kai soyayyar zukekiyar budurwa irinki!”
Hararanshi tayi tana faɗin. “Budurwan zuciya irin taka ya saka maka sha’awar auren yarinya karama”
“Ai gani nayi yarunyar kwaila ce, babu kome a kirjinta sai kirgan dangi!” Da sauri ta kare kirjinta. “Allah ya kiyaye, ni ba yar iska ba ce” “tow Allah ya baki hakuri!”
Kiran sallah farko yasa shi, kallon agogon da yake daure a hannunshi, ya ce mata.
“Mrs Mayor, zan shiga sallah zaki fara duty dinki ne ko sai an kawo min ke?”

Kamar ta rufe shi da duka, gashi ita ba gwanar kuka ba. “Wallahi ka fita idanuna ko na zage ka;” “tow Allah ya baki hakuri, ga daki nan ki shiga ki jira kafin gari ya waye, hakkina ne bawa rayuwarki kariya daga yanzu har ranar da zamu rabu!”

“Salon na shiga a yanke min kaina!” Murmusawa yayi ya ce mata. “har da bakinki zan saka a cire min!” Ya wuce ya barta nan, sai lokacin ta fara jin barci, ta nufi dakin, bude kofar tayi ta tura kanta da sallama, Idanunta ya dauka akan wani dream furniture’s na kasar South Korea, me masifar kyau. Royal blue me ratsi gold and gray. Hatta carpet din tsakar dakin gray and gold ne, juya kanta tayi tana kallon wardrobe din dakin wanda yake manne da bango, duk da na gadon ne yana hade da madubi, a hankali ta taka wurin dress mirror, da aka jera kome kamar da macen da take rayuwa a wurin. A hankali ta taka har gaban Mirror, tana d’aga kayan kan mirror din tana duba expensive costume’s, duba expire date dinsu tayi taga akwai lokaci sosai, wani kwalbar turare ne ya burgeta ta dauka, tare da duba sunanshi.
“Shumukh!” Ta furta a hankali, budewa tayi ta fesa a bayan hannunta, kamshin ya mata dad’i. Bata san lokacin da ta fara fesawa ba tana dariya. Jin shigar sallah asuba yasa ta ajiyewa ta nufi ban dakin, hadiye yawu tai tana kallon ban dakin da kaɗan dakin ya fishi girma. Har inda zaka yi alwala akwai, wurin ta nufa ta zauna tai shiru.
Mikewa tayi ta bude wasu drower din banɗakin ta dauko rigar wanka, sakawa kofar key tai, sannan ta gabatar da wanka sosai, tana me amfani da lady Gaga shower gel. Tana gama wankar ta fito ta gabatar da alwala sannan ta fito daure da rigar. Kayan jikinta kuma, ta jefa shi a Wash Machine. Ta nufi drower din, doguwar rigar abaya ta samu, sannan ta saka hankali kwance. Sai wani hijab da tasaka da shi tayi sallah, tana idarwa ta zauna sai tayi azkar har gari ya waye.
Sannan ta je ta cire kayanta ta busar da shi, a lokacin barci ne a Idanunta sosai, shanyawa tayi a banɗakin, ta fito a daddafe ta fada gado, rub da ciki.
Tund barci yayi gaba da ita, shima Malik barci ne yayi gaban dashi, bayan dawo masallacin gidanshi.

*09:30*
Ya farka yayi wanka, sannan ya shirya cikin jallabiya. Sannan ya fito a hankali yana kallon falon wayarta ya hango inda ta zauna jiya.
Dauka yayi ya shiga kallon wayar infiinix ce da taci ubanta, murmushi yayi ya zaro wayarshi da take charge a falon ya kira Elbashir.
“Lafiya lau, idan zaka zo ka biya ta Menk Jordan system world ka tawo min da Sumsung babbarsu baki ɗaya ina jiranka.”
Bude da sakon yayi, wato saboda bata dauki duniya da zafi ba, wayarta babu ko yar security code.
*Zeenobia kina ina ne?*
*Don Allah kiyi magana, mutanen sun tafi*
*Zeeno ba zan iya barci ba ne*
“*Allah ya tsare ki a duk inda kike*
*Daughter ina kike? Muna cikin tashin hankalin rashin dawowarki.*
Murmusawa yayi yana shafa kanshi, wato su din sune duniyarta, ita kuma rayuwarsu.
10:16am
Elbashir ya shigo gidan, kallon shi yayi yana faɗin. “Malik me zaka yi da waya?”
“Zan bawa Mrs Mayor ce!” Gyara zama yayi ya ce mishi. “Good morning Malik!”
“Morning Elbashir!”
“Wace ce ka samu haka?”
“Zaka ka dai jira zuwa an jima!” Suna zaune har sha daya, kunna tv Elbashir yayi. Malik ya ce mishi. “Dan rage sautin tv nan, zai tashe ta!”
“Malik wace ce haka ka samu?” Domin shi ya manta batun Zeenobia.
“Ai jiya mun daidaita kanmu, aure zamu yi.”
“Auren lafiya? Kodai asiri ta maka!”
“Ban sani ba” ya fada yana kallon labaran, har Elbashir ya tashi ya nufi inda aka shirya mishi abin karyawa ya ce. “Me za a zubo maka!”
“. “Bar shi sai ta tashi!” Zama yayi ya fara cin abincin, domin ba zai iya da sabon halin Malik ba. Ko Zeenobia yake tsammanin, bai san lokacin da abincin ya haura mishi kai ba, ya juya yana kallon Malik, shima shi yake kallo. “Sannu kaci a hankali.”
“Malik yarinyar nan ce zaka aura?”
Dauke kai yayi yana kallon tv, ana nuna matattan man fetur Khuldu Jahid Khan, “da fatan gwamnati ta kwace wannan wurin.”
“Ai babban abin shi ne tuhumar shi da ake yi, kuma ya tabbatar da nashi ne. Gaskiya Malik ka iya dukan mutum ba fada ba zagi”

Wayar Zeenobia yayi haske, kurawa number idanu yayi. “Kenan Shatima bai rabu da ita ba?”
“Kamar Ya?”
“Na mishi iyaka da ita!”
“Kasan dai ya riga ka fara sonta, kuma akan me zaka shiga tsakaninsu gaskiya Malik akwai sonkai a lamarinka!”
“Me nayi na son kai?”
“Ka rabu da yarinyar ka bar shi da ita.”
“Kasan yar Nasr Hadejia ce, sannan ba zan barta hannun mutumin da bai da aiki sai mugunta da zalinci, kada ka manta Rahilah sakamakon zalincin shi ta rasu ta bar Nadrah, ka zata naki auren Nadrah ne domin kai na? Na ki aurenta ne domin amfani da ubanta zai yi da ita, ina tare da. Shi ne a matsayin wanda ya kula da ni lokacin muna gidan yari. Bayan nan hatta numfashina idan da xai san yadda zai datse min ita tow ba makawa Shatima zai yi don haka ka kula. Lalla Salmah itama nata haukar bai bata lissafi daidai ba.”
Shiru yayi ya cigaba kallon kofar da wutsiyar ido, har wurin karfe daya daura sannan ta bude kofar, fuskarta ya kumbura sakamakon barcin da ta sha ba na wasa ba.
“Shi ne ba a tashe ni ba?” Ta fada tana duba wayarta. “Me kike nima?” “Wayata mana, zan kira gida!” Mika mata yayi, ta fara Duba sakonnin mutane.
Kiran Hafsy tayi ta ce mata.
“Baby gani nan, ki cewa Ammy gani a hankali!”
Kashe kiran tayi ya kira Number Shatima.
“Boy ba ga kiranka?!”
“Jiya ina kika shiga hankalin kowa a tashe?”
Kallon fuskar Malik tayi, ba yabo ba fallasa ta ce mishi. “Ina Menk Jordan Mansion ne!”
“Innalillahi! Meye yayi Miki? Dan Luwadi ne fa, dudduniya tasan baya niman mata sai maza, ina bai miki kome ba?”
“Hmm-Hmmm!” Ta fada a sanyayye.
*Baby gani nan zuwa!”
Katse wayar tayi ta cewa Malik.
“Zan tafi”
“Wuce ki karya!” Yadda yayi maganar yasa ta wuce, domin a sharadin su babu gardama.
A hankali ta nufi wurin abincin, ta zauna shima da kekenshi ya iso wurin, ya ɗan mike tare da bawa hannunsa karfi ya zauna a kujeran table ɗin.
Kallonshi tayi na wani lokaci kafin ta ce mishi. “Yasa ba zaka mai da cin abincinka kasa ba? Idan a kasa ne zaka fi samun nutsu. Amma shi hannun da kake daukar karfin kafar ka bashi zai iya gajiya, idan aka yi al’akari da shekaru wasu abubuwan zasu faru marasa dadi.”
“Hmm! Na saba da saman kawai a bar ni nayi yadda nake so!” Daga haka ya buga wani dan karfe sai ga kukun ya fito.
Shi ya shiga server ɗinsu.
Kamar wanda aka cillo shi ya shigo falon,babu sallama.
Kura mata idanu yayi ya nufe ta.
“Taso muje!”
Kallon fuskar Malik tayi babu wani matsalar kome abincinshi yake ci. “Taso muje nace!” Zare hannunta tayi tana me cigaba da cin abincin. “Ke taso muje!” Duban farfesun kaza Malik yayi ya kara mata. “Ci ki kara weight! Ina son mace me kiba kaɗan!” “Ni bana son kiba!”
“Ok ci!” Fisgota Shatima yayi ya ce mata.
“Duk abin da zaki ci daga hannunshi haramun ne, muje na baki kome da kike bukata!” Zare hannunshi tayi daga nata, tana kallon Malik.
“Duk abinda zaka bani, ba zai kai wanda nake da shi anan ba, ka tafi Malik nake son zama da shi!”
Cikin fushi ya ce.
“Tirsassata kayi ta zauna da kai?”
“Bai tirsassani ba, ni ce na ga dacewa haka!”
“Zeenobia kada kiyi abin da zai saka ki danasani, baki dace da shi ba. Shi ba mutumin kirki bane, idan kika juya bayanki wuka zai dabb’a miki, idan kika juya gabanki ya jima da cilla cikin Ukubar rayuwa. Kizo muje KE RABONA CE!”
Girgiza kai tayi tana faɗin.
“Kayi hakuri, zan zauna da shi.” Dukar table din yayi yana faɗin.
“Waye kai da zaka tirsassa mata!”
“Juyawa yayi yana kallon Zeeno.
“Taso muje babu abin da zai miki!”
Ruwa Malik ya sha, sannan ya ce mata.
“Idan zai iya biya na kudina,.kuje abinku idan kuma ba zai iya ba, ki ce ya fita ya daina min hayaniya cikin gidan domin bana son hauka!”…..
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/10, 9:17 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button