Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 45

Sponsored Links

45- Dariya yayi yana faɗin, “Allah ya baƙi wanda zai saka ki farincikin!” “Amin Ya Allah!” Ta faɗa tana d’aga hannunta sama, ta fita ta bar gidan, sauran yan matan da Zeeno wacce hankalinta yake can waje, suka zubawa kofar da zata shigo da shi cikin falon idanu, hadiye abincin bakinta tayi, tana kallonshi. Yana isowa wurinta sumbatar wuyarta yayi a gaban jama’a, kunya ya kamata, shi ko a jikinshi. “Kin san me? Ni babu abinda ya dame ni, kulawa nake bukata!” Ya faɗa mata kasa-kasa, kafin su ankara ai baki daya yan uwanshi sun watse, mikewa yayi ya dauki sauran kayan abincin ya shiga da su kitchen, yana shiga ya fito yana me sumbatar goshinta. “Kin kore mana baki!”
“Ni ban kore su ba, kai ne ka kore su.”
Zama yayi ya saka hannu ya fara cin abincin. Suna hira har ya gama. “Ban ga su Hassan ba?” “Sun bi matarsu sun gudu, me zasu miki?”
“Kawai na tambaya ne!” “Gulma ko? Gaya min gaskiya ko kina son su zo ne, ke da kike ce a cire cikinsu.” Tura baki tayi tana faɗin. “abin har da yar sharri ne? A dai ji tsoron Allah.”
Bakinshi ya kai kan nata, yana tsotsa. “Tsoron Allah ne yasa na fadi Gaskiya, da ba zan fara faɗa ba. Gaya min me kika min da na ka sa boye wacece ke a gare ni?”. Rufe idanunta tayi, tana dariya ta kai bakinta kunnenshi ta ce mishi. “Abin da kake bani kullum a cikin daki a rufe ” “sure?” “Yeap!” “Lallai ma, kin kore min Rahmah kin bar ni a matsayin Yayan gwauro!” Wayar shi ce tayi kara, ya zaro yana dubawa, kashe kiran yayi yana tsaki ya ce. “Elbashir lafiya kuwa?” Bin kiran yayi, ya saka a kunnenshi. “Ya dai Bashir?”
“Malik Hafsah ta sauka, an samu Y’a mace!”
“Kai Masha Allah, Ubangiji ya raya tafarkin addinin Muslunci, cikin satin nan muna hanya. A gaisheta.”
“Allah ya nufa ”
Kashe wayar yayi, yana faɗin. “Kin ji jaruman mata suna ta abin arziki, ke kuma sai sharewa kike?” “Ban san meye matsalarka da karin haihuwa ba, amma ni Alhamdulillahi, uku ma Allah ya musu albarka, a ka’idar likita sai na shekara uku na kuma haihuwa zaka addabi rayuwata da maganar karin haihuwa, sai kace kai zaka dauke min.nauyin cikin.”
“Tow Allah ya baƙi hakuri!” Ya fada yana dariya, itama dariyar tayi. A cikin satin suka bar Kano, zuwa Demark..kafin nan sai da suka tafi Hadejia da Maiduguri, Ummi, sai da ta roke shi ya saka baki a dawo da ita wurin Aunty Zeeno, kuma wani ikon Allah, Ubanta ya yarda aka batawa Zeeno ita, bayan Malik ya saka wani ya nima mata transfer. Zuwa Keivroto.

Abin gwanin dad’i, haka suka tafi cike da kewar juna. A lokacin da suka isa Demark domin har da ita Ummin, suna isa sai da ta ga kanta kamar bakauyiyya, ranar da suka isa tare da Malik suka tafi gidan Hafsy, ba laifi yarinyar tana da kyau domin ta dauko hasken fatar ubanta, basu wani jima ba suka bar gidan, har lokacin babu wani ƙawancen da suke da Hafsah, kowa harkan gabanshi yake, ranar suna kuwa don Elbashir tazo tare Ummi da Wahida, domin Wahiba bata cika shiga mutane ba.

Haka suka je awan su biyu suka bar gidan sunan, Elbashir da Malik sun so lallai su daidaita matansu, amma Zeeno ta hau muƙamin naki, haka yasa dole Malik ya kyaleta. Haka kwanakin suka tafi, watansu guda suka bar Demark suka wuce Keivroto.
Sun iso lafiya, har da ita maijegon da Wahida da Wahiba, haka suka iso. Motar da tazo daukarsu ta kamfanin Malik ne, tun kafin su iso an sanar Malik zai dawo. Don hakan garin ya tashi da wani sabon biki, ga tashin ganguna da yake karade garin. Lokacin da suka isa whiter town, da aka gyara shi a nan Zeeno ta ga Ammyn, cikin farin ciki, ta isa wurinta. “Da alamu yarinyar Ammyn ta girma, ko kefe? Dubi yadda kika koma don Allah?” Dariya tayi aka shiga kawo abinci. Kafin wani lokaci sun huta, Elbashir ya dauke matarshi da Yarshi suka bar gidan, Ammyn ta dauke yan uku, da su Wahiba suka bar gidan suka wuce can bangarensu. A matukar gajiye ta nufi Malik tana faɗin. “Daadi na gaji jikina ciwo yake min!”
Cak ya dauke ta, yana faɗin. “Muje nayi miki wanka da tausa!” Kwantar da kai tayi tana sauke ajiyar zuciya.

Murmushi yayi yana faɗin. “Me yasa kika matso mu dawo, gashi kin kore min yan hira na” “dama ai ba zaman nan zasu ba, wurin Ammyn zasu koma ni nan da mijina ne, idan da mutane ba zan sake nayi abinda nake so ba, a bar ni da tsohona lafiya.”
“Allah ya taro min ke!” Ya fada bayan ya kwantar da ita a gado, ya nufi ban daki ya haɗa ruwan zafi, ya dawo ya dauketa. “Ban cire kayan ba!”
“Zaki cire ai idan kika ji ki a ruwa!”
“A’a Abu Hussain, don Allah taimaka na cire kaya.” Murmushi yayi, sai da ya kaita ban dakin ra cire kaya, suka shiga wankar. Basu fito ba, sai dab magariba, sallah suka yi, suka koma cin abincin. Suka kara fitowa falo.
Bayan sallah isha, dakyar Zeeno ta kai tara. Barci da gajiya yayi gaba da ita. Sai wurin Asuba, ta farka ta ga babu Malik. Ban daki ta shiga ta same shi, a cikin ruwa yana wanka, shiga ruwan tayi, tana me daura kanta a kirjinshi, bata damu da jikar da tayi ba, ta ce mishi. “Shi ne zaka bar ni daki ni ɗaya!”
“Saboda kin san zan iya damunki, shi yasa na dawo cikin ruwan zafi na rage zafi.”
“Ba gani ba, kawai kayi kome da kake so.”
“Ji kamar da gaske dake kin ga asuba tai ba.”
Dariya tayi tana kwanciya a jikinshi. Haka suka gama wankar suka fito, kafin wani lokaci. Sun shiga ya tafi masallaci. Ita kuma tayi sallah, tana idarwa ta zauna azkar har ya shigo. Kur ya mata da idanun tasan halin abinda, sallamewa tayi ta mike, tana cire hijab a hankali. “Don Allah a daina ja min class!” Ya faɗa yana amsar hijab din.

Dariya ta mishi, sai da ta bari ya gama ninkewa ta zille ta fara bashi, wahala dafe goshi yayi ya ce mata. “idan na kama ki zaki sha wahala ne kawai.”
“Oho dai!” Ta faɗa yana juya mishi kugu. “Zainaba idan na kamaki zaki yi kuka kina rokon don Allah a kyale ki,amma ina ce no one more second round!”
“Dake ni tuwo ce ba” ta fada tana juya bom-bom.
“Hmmm Baby girl kada na kama ki fa!”
“Oya kamani mana”
Ai kuwa kafin ta san me tuni yayi sama da ita. “Ayya Daadi kayi hakuri ba zan kuma ba.” Ta faɗa da karfi tana dariya, ai bai bata amsa ba, ya shiga da ita Chinese royal bed dinsu, wanda yake zuwa da labilaye da net. Bawan Allah nan, ya rutsata sai da ta gane Allah da girma yake,domin ya nuna mata no mercy.

Sosai ya gurjeta kamar zai yagata, sannan ya kyaleta suka kama barci, me nauyi. Basu farka ba sai karfe daya, tow an jima ana cin uwar Sabada ina dalili. Sai da suka yi wanka suka huta, kafin ta fita ta dauko musu abinci, ta kawo dakin. Suka zauna suna ci, kallonta yayi ya ce mata.
“Mun dawo Keivroto! Ina son ki koyo dauke kai, wasu abubuwan zaki ji ko zaki gani don Allah ki xama adila a kaina. Ina ruwa ne akan makiya, idan na samu kwarin gwiwa a gare ki, ba zan tab’a nadama da jin tsoro ba, Zainab kece kwarin gwiwata. Don Allah ko text ko kira, kada wani ya turo ya baƙi mamaki, idan kika yi haka kin gama min kome. Wancan abin da ya faru don Allah kada ya kuma faruwa.

Ki tuna akwai Hassan da Hussaini da Maidah. Don Allah kada wani ya gaya miki abu, kiyi fushi fuuu ki same ni muyi magana . Zan saurare miki, Zainab ba sai na gaya miki waye ni, ke kanki kin san waye ni. Ki ɗauke kai daga kan duk wani a abinda zai bata miki rai please.”

Yadda yake bata hakuri da son ta fahimce shi, ya kara mata wani mahaukacin sonshi. Matsawa tayi ta sumbace shi. Sannan ta ce mishi. “Kome xaka yi ina tare da kai.” Rike wuyarta yayi ya shiga lallubar soft and smooth lip’s dinta, ya shiga grabbing ɗinshi crazy.

★★
Shatima.
Idanunshi yana kan Tv yadda aka nuno saukar su Malik da Matarshi da Beautiful kids ɗinshi. “Nadrah kina gani ko? Kice kada na kashe wancan tsinannen, sai na ga bayan shi, saboda shi aka yanke min kafa saboda shi na shiga gararin rayuwa. Dukiyata ta kare, kome nawa ya kare kije ki gayawa media press ki ce musu cikin da Malik ya miki sai ya amsa.”
“A’a wannan ba mafita ba ne, mu fara zuwa ga mahaukaciyar matarshi mu haukata yardan da yake tsakaninsu. Ina son gidanshi ya kama da wuta, kafin na kara bakanta mishi rai da batun aurena.”
Murmushi yayi yana faɗin.
“Yanzu na haifi yar halak!”
Nan suka yi ta shirya sharrinsu.

Bayan tafiyar da Shatima yayi nason ganin Bayan Malik, ya hadu da masifa da bala’in da sai da aka yake mishi kafa, a sannan ka kwashe kudin shi na cikin account dinshi, zuwa yanzu bai da kwanda na shi dai na hannun Nadrah. Ba karamin wahala ya sha, shi yasa ya kuma kullatar Malik a ranshi.
Sai da yayi jinya a gadon asibiti, sannan ya warke. Yanzu haka babu kafarshi na dama an yanke mishi ita. Sakamakon tetanus da suka shiga kafar har ya fara rubewa. Dakyar aka nimo Nadrah ta fara mishi magani, yanzu haka bai daina maganar Malik ba, shi bai gane Hassada ce ta kawo mishi haka….
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/29, 8:01 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button