Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 4

Sponsored Links

Volume 4: Al’umma Charity House.

“May I have the sit?” Ta tambaye shi, murmushi yayi ya ce mata. “why not!” Zama tayi tana kallon yadda yan mata da samari suke yawo cikin shakuwa, tare da Romantic moments.
“Wani mataki kika tsaya na karatu?” “Degree a medical Lab!” “Masha Allah! Zaki cigaba da ne ko zaki yi aure?” A kunyance ta ce. “Duk abin da ya samu zan yi.” “Kina da boyfriend ne?” “Na’am! What? Boyfriend?” Sai kuma tayi kasa da kanta tana girgiza kai. “But why are you dressing like that?” Hadiye yawu tayi. “Ba kin san haramun bane? Dukkan mu da security babu muharraminki a cikin mu, but why you dress like whore? Kada ki kuma domin ko Nadrah bata tab’a irin wannan shigar ba, ina miki magana ne a matsayin abokin Mahaifayarki, not babansu Wahida kada na kuma ganinki da irin wannan shigar, idan kuma don ni ne kada na kuma ganinki a guest house dina, kin ji ko?” Idanunta cike da kwalla da mamaki ta ce mishi. “But ya aka yi ka gane ni ce?”
“DKNY Golden delicious, ni ne mutum na farko da na bata shi, tun bai kai matsayin da yake kai ba, so ina sane da duk motsin mutum musamman idan akwai abin da na sani a tare da shi.” DKNY Golden delicious turare ne me masifar kamshi da dadi, musamman mata sun amfani da shi. Malik yana da dabi’ar kyauta turare. Tashi tayi zata tafi ya ce mata. “Thank you.” Gyada kai tayi ta bar wurin, har kusan magriba suna wurin kafin dare yayi suka bar wurin.

★★★
KJK MANSION…..
Duk wanda yake ilahirin gidan, yaji yadda yake farfasa kayanshi. “Wallahi sai naga bayan Malik!, Sai na kashe Malik ni zai nakasawa arzikina.” Yadda yake masifa kamar zai kashe wani yasa babu wanda ya iya mishi magana. “Kai ya kuka yi da Elbashir?” Cikin tsannanin tsoro ya ce mishi. “Malik he refused!”
“Kace me?” Hadiye yawu yayi ya ce mishi. “Ka haɗa min zama da CM yau.”

“CM yana Demark zasu bude sabon kamfanin sadarwan hadin gwiwa da Malik a can!” “Babban bura uban bala’i har za a ci amanata? Ina yarinyar da ta yaudare shi tana iya?”
“Ya rjgada ya saka a farauci rayuwarta, daga mutanen shi har yan sanda duk wanda ya ganta ya kawo mishi ita a raye!”
“Ni kuma mace duk wanda ya kashe ta, zan bashi miliyan ashirin nasan zai bukaci ganinta a raye, tow a kashe ta.”

“Amma haka ba zai kuma rura wutar.” “Uban uban wutar fitinar! Nace fitinar taci kaniyarta.” Gyada kai yayi, sannan ya binciko hoton Zeenobia, aka turawa mutanen KJK, su fara farautar rayuwar Zeeno.
>
Sai dare likis suka koma gida, “yau ina kuka je?” “Gudun ceton rai!” Gyada kai Ammy tayi, tana faɗin. “Ba damuwa!” Daga haka ta wuce dakin ta rufe, zama tayi tana cire takalminta. Maganar Asp Zulfa yake dawo mata, “bana zo nan don kamaki bane, nazo ne na gaya miki. Rayuwar mutanen da suke kewaye dake suna cikin hatsari, ko yayya kika matsa daga gare su, za a iya farmaki. Ya rage naki ki mika kanki ga hukuma domin ta haka ne masu bibiyar ki zasu hakura babu wanda ya isa farautar rayuwarki tunda kina hannun yan sanda.”

Shiru tayi tana nazarin al’amarin, zuwa yanzu ta fahimci girman Allah da buwayarshi, duk inda zata shiga dole ta shiga ita ɗaya. Kamar tayi ta kuka domin yau da ita daya ce, barin kasar zata yi amma al’ummar da suka yi imani da ita fa? Mutanen da suka yarda da ita fa, ya zata yi da rayukansu? Kawai zata zauna kawai a kasheta.
Tun daga wannan ranar, bata kuma barin gida na. Har ya kasance ana ta zuwa nimanta amma babu labarinta, domin sai da ta share kwanaki goma a cikin gida a dakinta.
Ranar juma’a da da dare, suka fita bakin ruwa shan iska. Ko waye ya gaya musu ta fita, kawai tana zaune taga mutane sun fara fara kewayeta dauke da makamai.

“Kece wannan?” Kallon hotonta tayi . Kallonsu tayi ta ce musu, “Kanwar Babarku ce!” A fusace daya kai.mata duka ta kwauce. “an biya mu, mu kashe ki don haka, ki zabi irin kisar da zamu miki!” Gyara zama tayi tana faɗin. “Ai shi kenan idan kuka kama ni zan tsaya har na gaya muku yadda zaku min na mutu, idan kuma baku da rabo kudin ya tafi a banza.” Aikuwa suka nufeta baki daya, dake tafisu danyen kai, yashi ta watsa musu a fuskarsu, baki daya sannan ta dauki wani katako, ta shiga mukka musu ta ko ina, bata gama lillsasu ba. Mutanen Malik da yan sanda suka nufo wurin.
“Kai waye ya gayyato min waɗannan awakan.” Da gudu ta juya tare da ɗaukar motar mutanen KJK, suka shiga wasan tsare a cikin garin Keivroto city. Wani shu’imin gudu suke ita da su, a tunaninka zaka dauka namiji suke bi, a’a sam mace ce da ta isa mace. Yar gaggara, uwar masara jin magana da taurin kai.

Sai da tayi wata irin gudu, kafin ta isa wani wurin shagali, ta tsayar da motar. Sannan ta kutsa cikin mutane ta saje da su. Tana hango mutanen Malik. A cikin mutane, wani sanda ta samu tana zuwa ta bayanka, zata make ka dashi ta wuce.

Abun sai ya zame mata abin Tsokana da zolaya, duk wanda ya gani sai ta baje shi, kafin wani lokaci ta musu illa. Sannan ta wuce abin ta. A hanyar da zata wuce ta hango Elbashir zaune yana zukar hayakin taba. Kallonshi tayi yana tsaye. “Kin gama gudunki?” Murmushi tayi ta ce “happy to see tail din Malik, idan ka isa wurin shi, kace naci banza!” Ta falla a guje, take da kai mishi wani irin bugu da karfen hannunta. Kaucewa yayi ya bata hanya, ta tsalleke shi tana dariya, “Waw ka gayawa Malik, ya fito farauta na da kanshi. Shine zan yarda ya cika namiji.” Tana fadar haka, ta haura wani katanga ta fara tsalleke gidajen mutane. Cikin fun babu daren da ya kai wannan daren dadi da armashi. Ciro wayar shi yayi ya shiga niman Malik.
“Malik ! Yarinyar nan akwai Evil spirit a tare da ita, wallahi ta bani tsoro” “Elbashir da fatan baka yi fitsari ba?”
“Eh ban yi ba!”
“Me ya faru?”
“Malik KJ ya saka mutanenshi su kashe ta, duk inda take!”
“Tow su kashe ta mana!”
“Malik su kashe ta kuma?”
“Eh su kashe ta!”
“Ok shi kenan Malik!”
★★★
Kwanakin shi goma da zuwa, kuma har ya gama abin da ya kawo shi, yana son isa South Africa duba wani ginin da yake na kasuwancinshi. A hankali ya bi wayar da idanu. Kafin ya shiga duba cantact din mutane, KJK ya gani a sanyayye ya danna kira. Kamar ba za a dauka ba ya dauka.
“Waye ne?”
“Mikawa dan kwaikwayon karen.” Ya fada da kwarin gwiwar shi. “Waye kai?” “Dodonka ne bisa layi, shudin riga, farin dokin tsare, bakin wando kaftani doki me jiki brown. Ƙwayar idanu zaiba, fari kyakyawar matashi dan kimanin shekaru ashirin da bakwai. Bindiga kirar Germany, snippier, wanda karfin gudunta ya zarce dari tara da digo daya. Garin Abhu Dabi, kasar Dubai. Kalma daya tak akan Yarinyar da kuka nakasa mata rayuwa, yau kuke bibiyar rayuwarta, zan tashi Matashin da yake bisa dokin nan!”

“Kai… Kai….. kai…!! Malik ka da ka fara, kai gayawa Antoni su kyale yarinyar nan, Rayuwar Arif yana cikin hatsari maza a dakatar da su!”
“Hmmm! Kada ka damu, wanzamin ya gama maka gyaran fuskar? Ka shafa wuyarka ko ka ce a duba maka zuwa kunnenka. Ina tafiya ne bisa lissafi da hanya ta, ka sake gaba na kuma turo wani wanzami kayi tunanin abin da zai faru haka sauke kan dan banza irinka zan yi. Kuma na gaya maka, idanunka ya fita kan Yarinyar.”

Kashe wayar yayi, ya cigaba da tafiya da kekenshi. A kofar fita ya hango Jalilah ta ci kwalliya cikin Blue berry gown. Kafarta sanye yake da DG shoe, sai yar karamar pose..
Tayi kyau, dauke kai yayi ta nime wuri ta zauna. Wayarshi ce tayi kara ta dauka, “ina jin ka!” “Malik akan yarinyar nan ce, haka za a kyale KJK ya kashe ta.”
“Yaushe ka fara damuwa da rayuwar wasu?”
“Malik yarinyar babu ruwanta!”
“Yaudarata tayi ta ci min kudi, akan me zan kyaleta.”
“”Malik don Allah kayi hakuri, Yarinyar!”
“Elbashir idan kana son yarinyar ka gaya min kawai ayi muku aure ” ya kashe wayar. Ta cigaba da harkan gabanshi kamar babu halittar Mutum a falon. “Malik!” Ko kadan bai ji wani abu ba, sai ma cigaba da abin da yake. “Nazo na gaya maka gaskiya, ba nice na aikata.”
“Dude you keep quiet?” “Amma ya kamata ka saurare ni, nima lokacina yayi wallahi sai na zubda mutuncinka a idanun duniya.”
“Idan kinso ki zubda Kinji, I don care. Sannan da kike cewa zaki zubda shi, hala madara ce da zan ta riketa a kwarya kada ta zube, and ki fita ki bani wuri ”
Takaici yasa ta fita daga cikin dakin tana faɗin. “Sai na lalata maka suna!”
“Ki kara himma har abada zaki kare rayuwarki baki san asalinki ba. Jalilah Bulama Shuwa;”
Cak ta saya tana me juyawa a hankali, kamar wacce ruwa ya cinyeta. “Kasan asalina ne? A ina dangina suke?” Banza yayi mata, shima ya dauke kai kamar bai santa ba, duk magiyar da take mishi Malik mirsisi yayi yaki kulata da ta ishe shi, ya kira Adnan yayi mishi waje da ita.

Shi ba zai dake ka ko ya zage ka ba, amma zai daki inda sai ka kusan mutuwa kafin ya sarara maka. Washi gari ya wuce South African, inda ya sauka a Cape Town

A Nelson Mandella streets ya sayi filin ana mishi, wani hadadden apartment y hadu iya haduwa, ga injiniyoyin da suke aikin. Kwananshi uku ya tattara ya dawo Keivroto city da safe ya sauka, ranar juma’a. Bayan sallan juma’a ya tura Elbashir da Lauyanshi akan suje su rufe mishi gidan. Ko kuma su sako Zeeno a gaba a duk inda take.
—. Dake kwana biyu daga ita sai yan sanda da mutanen Malik suke wasan tsare-tsarensu. Tana can inda take boyarta Black ya kirata a waya.
“Zeeno an kore mu, hadu nan suna mana watsi da kaya.”
“Shit!” Juya kanta tayi tare da fitowa daga gidan da take zaune, ta nufi office din yan sanda.
“Nazo shigar da kara ne?”
“Karar waye?”
“Malik Menk Jordan!” A yadda tayi maganar da fully confident yasa baki daya yan sanda suka juya suna kallonta. “Me ya miki?”
“Yaje yana koran mutane daga gidansu!” “Ok bari a kira kansilar birni ya haɗa ku da shi.”
Haka aka yi kuwa, can sai ga Elbashir da Lauyan Malik. “ta kawo karar Malik Menk Jordan!” “Gaya musu bayan niman kashe ni da suke son yi bai ishe su ba, sai sun d’aga mu ba bisa ka’ida ba!”
“Shi kenan, mun yarda da laifin mu Asp ko zaa bamu damar mu sassanta kanmu a gida!”. “sassantawa na kalau ban yarda ba a kai mu kotu kawai!”
“Hmm! Zeeno ku tafi ku sassanta!” Bata san dalilin da ya sa ta bi shawarar. Suka fita kai tsaye gidan Malik suka nufa. Yana zaune a hankalinshi yana kan Tv.
“Barka da zuwa yar gudun hijira!”
Zama tayi, ya juya ya kalleta sannan ya tura mata takardan gabanta. “An gama biyan kowa kuɗinshi!” Daukar takardan yayi ya ce mata. “kika ce kinci kudina kin ci banza?” Kallon Elbashir tayi ta zabga mishi harara. ” Ku bani wuri!”

Ya kuma tura mata wasu takardu, “wannan takardun a hannun dan uwanki Abbas ba samu, ya saka gidanshi a kasuwa. Kuma na sayar domin ya fashin rayuwarki!” Mikewa tayi jikinta yana rawa. “Me na maka da zafi!!?”
“Kudina!” Ya gaya mata hankali kwance, “me kake bukata?” “Filin gidan Al’umma Charity House!” “A’a Malik Menk Jordan, ka nime wani abu. Ban da wannan gidan na haɗaka da Allah!”
“A’a ni gidan nake so!” “A’a shi abin da ya rage mishi taya zan barka ka raba shi da ita?” “Kin san wannan wurin itace rauninki, me yasa kika ci amanarmu?”
“Malik ban ci amanarka ba!”
“Idan baki ci ba, dawo min da kudina!”
Dafe kanta tayi, “Malik!” ” Ba zan kuma sauraron abun da zai fito bakinki ba, fita ki bani wuri!”

“Don Allah ka saurare ni!” “Security!” Ya d’aga muryanshi yayi tare da kwalawa jami’an tsaro kira, suka fita da ita a wannan karon bata da ra’ayin amfani da karfi domin fadar kawai ya dubi girman lamarin ya bar musu gidan, haka suka fitar da ita daga Mansion ɗin, ta tsaya tun farkon dare har dare ya raba. Malik yana cikin gidanshi, har Elbashir ya bar gidan tana wurin lauyarshi ya bar gidan tana tsaye bata bar kofar gidan ba.

Security suna zuwa suna gaya mishi, tana tsaye, duba Cctv yayi ya ganta tsaye tana kallon kofar gidan, har ya juya zai tafi yaga wani mota yazo da gudu ya wuce ta gabanta. “kai ku shigo da ita;” ya fada da dan sauri, haka kuwa aka yi. Security suka shigo da ita cikin gidan, a falo suka barta ta cigaba da tsayuwa.

A hankali ya turo kekenshi, yana kallonta. “Dame zaki kare Al’umma Charity House?” “Da kare rayuwata ina me bin umarninka!” “Ok zauna mu sake tattaunawa akan cantract marriage!” Wani irin kallo ta mishi. “Idan baki shirya ba, Jeki amma ki sani gobe zan saka a make min gidan nayi gidan shakatawa!” Zama tayi da kyau, tana hadiye yawu ta ce mishi.
“Ina jinka!”
“Ina jikimar?” Shiru tayi yau bata da bakin magana duk abin da Malik yayi daya ne.
“Ok gashi nan ki duba abin da bai miki ba, dai a gyara a saka sabon tsari!”
Ɗaukar takardan tayi tana karantawa.
*{One Year Cantract Marriage}*
Malik Menk Jordan and Zainab Nasr Hadejia.
1-Babu jagaliyanci.
2-Babu taurin kai
3-Dole ayi min biyayya
4-Kwana daki ɗaya
D’ago kai tayi ta kalle shi, kafin ta ce mishi.
“Na yarda da sharuddan amma ban yarda da kwana daki daya ba! Sannan auren wata shida zamu yi”
“Cigaba da dubawa dai! Kafin kiyo korafin ki!”
5-Dole ki tayani Mijinki kula da abin da yake nashi!
“Kace kawai baiwa ka dauko saboda miliyan dari huɗu zaka mai dani baiwa!”
“Cigaba dai!”
7- Dole ki kilace kanki as matar aure.
“Ba saba yawo babu me daure ni a gida! Wallahi kuwa” ta fada tana bata rai.
“Cigaba da dai”
8- Dole ki sauya shigar da kike.
9- A auren shekara guda, zaki haifa min Yaro ko Yarinya.
Jikinta daukar wani azazzben rawa ya ɗauka, ta ce mishi. “Na rantse da Allah ba zan tab’a hada jiki da kai ba, dube ka tsoho da kai, duk ka tsufa da gashi buya-buya.!”
Murmushi yai ya ce mata, “duba last number!”
10- Idan baki yarda ba, na baki nan da awa ashirin da hudu ki dawo min da kudina har da wanda na bawa mutane sai kin biya ni.
D’ago kai tayi jikinta ya jike jagwab da zufa. Muryanta yana rawa ta ce mishi.
“Kana da imani kuwa?”
“Ki ajiye a ranki ba ni da shi!”

“Yanzu wannan dokokin duk zan bi?”
“Idan basu miki ba, sai a sauya na me da daukar zafi!”
“Zan bi dokokin amma ban da kwana daki daya, babu batun haihuwa, sannan zan tafi duk inda nake so, sannan batun saka kaya na yarda amma kilacewa ne ba zai samu ba. Sannan a auren mu babu body cantact, babu!”
“Na ji amma ki kawo sharudan ki, sai na ga wanene zan iya bi.”
“Bani da sharuddan da zan gindaya maka, amma kiji a ranka budurwa kama ta ta kare a auren tsoho, ban san dan abubuwa da ake yi a soyayyan ba, sannan ka auna kanka mana, sannan ace kawai don nayi laifi sai a hukunta ni da aurenka, ka duba wace ce ni? Ni ma ina son soyayya kamar kowa, ina son kulawa kamar kowa, duk yadda kaso kayi da ni, ai ni ce na kawo kaina.” Tana gama fadar haka ta mike zata fita.
“”Koda auren Cantract ne xan yi treath dinki,kamar masoya i give you my words. Ki saka idanu ki gani, zan kuma baki damar kiyi rayuwarki yadda kike so.”
“Kana son amfani da ni ne, domin biyar bukatarka, idan ka gama ka wullar dani.”

“Kawai ka tsaya ne akan auren yarjejeniyar amma da a tawa ra’ayin ne ba zan amince da wannan auren ba, domin baya cikin sharuddan Muslunci.”
“Eh amfani da ke zan yi kina da ta cewa ne?”
“Bani da shi, kuma bana fatar nayi amma ka sani Allah zai saka min ne lokacin da baka da tsime baka da dabara, idan kaso ka cinye ni, daya ne!”
Murmushi yayi yace mata. “Ai bana cinye mutane, sannan bana hadama abin da n sani nake yi! Idan kin ga ba zaki iya ba, ki tafi babu dole amma ko yanzu haka na saka bolldoza a kofar gidan al’umma charity House, kin san aikin buldoza ai ” ya fada yana wani murmushin mugunta. Zaro wayarta tayi tana kiran Black. “Ya ake ciki?”
“Zeeno ga shi an kawo kayan aiki za su rushe Al’umma Charity House!”
“Ok Ina zuwa!” Kashe wayar tayi tana faɗin. “Ka kashe ni ga ni a gabanka me ya rage?”
“Bana kashe mutane,abin da na sani ina cinye duk wanda ya tab’a min kudina!”
“Ka zama mashani ka kashe ni ka huta….
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/10, 9:17 PM]

Leave a Reply

Back to top button