Hausa NovelsM SHAKUR NovelsMatan Ko Mazan Hausa Novel

Matan Ko Mazan 37

Sponsored Links

💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 3️⃣7️⃣

CHAPTER ONE IS COMING TO AN END😫 Labarin Nura da Hadiza yasoma karewa have you subscribe for chapter two?? Is just 1k, zamuyi magana akan Matan aure da Mazan aure masu biye biye, no judgement but I will teach you something you never knew about cheating and I will help you overcome it.
Kome kikeyi don’t miss this chapter 2!!
Chat me up today and make payment.
wa.me/+2347012181461

37
Juyoda kanshi Baba yayi a tsanake ya kalleta dudda ta bashi tausayi but ya danne, yakalli Mama yanda take kuka da Anty Jams dama Amadu ya nuna Hadiza yace “duk sabida yarinyar nan kuke kuka?” Saikuma yayi shiru dan yanda Hadiza tafadi abubuwan datayi da bakinta sai zuciyan Baba yasake sosuwa ya nuna Hadiza up and down da hannu yace “kin dauka wannan borin da hayagagan nan dakikeyi shine zaisa nakira Nura namai magana?” Baba yadanyi murmushi mai ciwo yace “Hadiza yanzu haka ki fadi awajen nan ki mutu ni nasan cewa lokacin ki ne yayi bawai damuwan Nura ko wani abu bane yakasheki ba, cuta ba shine mutuwa, shi mutuwa lokaci ne kinsan mutane nawa har wankan gawa aka musu daga baya suka farfado why? Because lokacinsu baiyiba, idan lokacin mu yayi, ko yanzu, ko anjima, ko gobe, ko jibi ko gata, ko citta ko badin badadan zamu mutu Hadiza” yanuna kanshi da hannu yace “kin ganni nan dattijon arziki ne sabida ke bazan zubar da kimata a idanun Nura ba, bazan taba mishi magana yakomar dake dakinki ba idan yanaso yayi yayi idan bayaso duka daya awajena abu daya zan fada miki ki kama Allah ki rike addu’a kuma, sannan ki nemi gafarar wayanda kuka kuntata mawa Allah yasa mudace tashi Amadu muje” tashi Adamu yayi suka fice Hadiza tai kuka tai kuka har saida Mama tai ihu tace “wai bazakima mutane shiru ba kashe kanki zakiyi da kuka, kima mutane shiru dalla” tashi Anty Jams tayi tawuce inda Hadiza take kama hannunta tayi tadagata tace “muje daki” da kyar Hadiza ta iya tabi Anty Jams daki.

Sunyi nisa sosai, Nura yana tuki yana kallon hanya ahankali Aman dake gefenshi yana kallonshi yace “Dady” dan juyowa Nura yayi yakalli yaron yace “yes Son menene?” Dan shiru Aman yayi sai chan yace “you don’t want to make Mommy come back home with us”? Dan kallon yaron Nura yayi sometimes tambayoyin Aman nabashi mamaki kaman wani babba, dan shiru yayi baice komiba ahankali Aman yace “Dady is it because Momy na zaginka”? Dasauri Nura ya kalli yaron kafin yace wani abu Amal ta taso da gudu tana leko da kanta ta wajen takalli Aman tana zaro idanu kaman wacce zatai gulma cikin whispering but kana iyajinta sarai tace “Ya Aman Momy use to call Dady munafuki…….” “Amal!” Nura yakira sunanta da tsawa saida yarinyar ta firgice tace “Dady sorryy ai bantaba fadi ba ko Ya Aman”? Gangarawa Nura yayi yay parking motan gefen hanya, yasan yaran sunsan suna fada but baitaba sani har zagin sun sani ba, dasauri yajuyo yakalli Amali daduk ta rude strictly yace “kika kara fadin something like this I will be very angry with you kinason Dadyn ki yayi fushi dake?” Girgiza mai kai tayi tafashe da kuka tace “Dady sorry” dan shiru yayi yana kallon yanda take kuka saikuma yace “come here” dasauri tazo hannunshi yasa ya share mata fuska yace “stop crying okay babu kyau yana suna sauraron fadan Momy and Dady is a bad habit” gyadamai kai tayi tace “sorry Dady” peck yamata a goshi yakalli Aman dake kallonshi yace “I dont want this discussion ever again am I clear”? Gyadamai kai yaron yayi yace “yes Dady” zaunar da Amali yayi, yatada motan tareda dan sauke ijiyan zuciya yawuce.

Ummi na zaune dakin Hajiya tana matsa mata kafa basu dade da dawowa daga kesson ba itada Meena taga yaran sun shigo da gudu abin ya bala’in bata mamaki da Nura yayi sallama yashigo falon sai mamakin ya idasa kasheta batasa ran ganinshi ba yau danta dauka awajen Anty zai kwana yau, gaisawa yayi da Hajiya Ummi ta kalleshi akunyace sabida Hajiya dake wajen tace “sannu da zuwa Baban Amali” dan kallonta yayi yasakin mata good smile yace “me kika dafamin am hungry?” Tashi tayi tawuce kitchen din Hajiya, Hajiya dake kallonshi tace “yamai jikin?” Ahankali yace “dasauki gobe zansa driver ki yakaisu suje su kwana jibi su dawo, gata dasafe zamu wuce Abuja dukanmu” gyadamaikai Hajiya tayi tace “Allah kaimu, shima yaron nan dake neman auren Meena ai katuna gobe zaizo yaganka ko”? Anatse yace “natuna Hajiya Allah kaimu” abinci Ummi takawomai yaci yayi damm sannan yawuce masallaci bai dawo gidanba sai around 9, dakin Hajiya yawuce yamata saida safe sannan yawuce side dinshi Ummi na zaune tana duba wasu books yashigo da sauri tasaki books din ta tashi dagudu tai wajenshi murmushi yayi yace “ammata na” ahankali tace “an samari na” murmushi yayi yadagata suka wuce kujera suka zube lamo tayi ajikinshi ahankali tace “na dauka awajen Anty zaka kwana”? Remote yadauka yashiga kunna tv irin wanda bayason maganan nan yace “anan zan kwana” lurada yanayinshi datayi yasa bata kara cewa komiba daura idanunshi yayi cikin nata yace “kallon fa wawatsula kikeso?” Wani irin murmushi Ummi tayi tun ranan data gayamai kalman yarike gam yake fadi, kannemai idanu tayi tana lashe baki ahankali tace “ni gwaguyanka nakeso nayi” ohhh shi baimasan yanda zai misalta abinba but kobaiso dazaran Ummi tamai batsa sai jikinshi yatashi bakinta ya shafa idanunshi na kankancewa yace “menene kuma gwaguya baby” sauka tayi daga kan jikinshi takai hannunta kan idanunshi tace “rufe idanunka kagani” kulle idanunshi yayi kawai tai kneeling agabanshi tasa hannunta ta daga riganshi sama tana kwance mazariyan wandon yadin jikinshi hmmmmm…
Saida Ummi takusan sakashi sakin mata fitsari abaki anan falo suka watsewan su.
**
Washe gari around 11 nasafe Nura yasa driver Hajiya yakai yaran gidansu Hadiza.
Jibin daya fadi jibin akaje daukosu suka dawo da tsaraba sosai washe gari suka wuce Abuja.
Ummi kusan mutuwan tsaye tayi ganin durmemen gidan dasuka koma manya manyan flat daban daban guda uku ne komi iri daya, saida yafara shiga da ita ko’ina sannan yakaita second flat din inda yazuba mata furnitures naban mamaki a akwati saiti 16 jere a tsakiyan babban falon sai kawai Ummi tahau kuka dasauri yaran sukahau tambayanta menene shima Nura ma haka dago rinanun idanunta tayi takalleshi tace “ko amafarki bantaba tunanin zanyi rayuwa a irin wannan gidanba, kamin komi kuma, ga akwatina kaman wata yar sarki” murmushi yamata yace “kına kuka agaban su Amali, Amalili look at Anty Ummi is crying let’s make her smile” sai kawai yama Ummi chakulkuli suma yaran sukahau mata tahau dariya sosai daganan suka wuce sama 4rooms ne asama ga masters bedroom nashi ga nata ga wasu dakuna biyu dayace anan su Amal zasu zauna daganan shida Aman suka wuce mosque dudda baya nuna mata komi but shigowanta gidan nan yakara tabbatar mata da Anty batanan duksai taji tadamu hankalinta yaki natsuwa sauka tayi itada Amali suka tafi kitchen kunga kitchen Ummi kawai tasaki baki suka kara fitowa waje wow gidan yahadu babban gaske yayi wani karamin kauye girma.

Damuwa tama Hadiza yawa taki kwaso kayanta daga Abuja tasake dagewa da addu’a da sallan dare, tanason taje tasami Hajiya but batasan taya zata mata magana ba yau ne the second time datake kara nadaman rashin shirinta da kannen mijinta, ijiyan zuciya ta sauke ta dauki wayanta tareda dialing number Ya Aisha amman harya katse bata daga ba sauran biyu takira basu dagaba, saikuma kaman bazata iyaba taciro number Meena tai dialing shima harya katse bata dagaba kawai saitaji hawaye sun zubomata dasauri ta sharesu ta ijiye wayan ta buga tagumi tai shiruuuu tafara tunani zaka iya kai downgrading yan uwan mijinka kana ganinsu kaman bakomi ba sabida mijinki na sonka but the truth is kowa nada rananshi arayuwan nan always respect kowa ijiyan zuciya ta sauke kafin ahankali ta kwanta akasa kaman marainiya Mama tadade tsaye agaban dakin tasaga labule tana kallonta amman bata sani ba, tsakanin uwa da d’a sai Allah, Uwace aduniyan nan duk lalacewan danta tanason abinta haka, tafi kowa tausayin Hadiza da damuwa da damuwanta, shigowa dakin tayi ahankali ta zauna gece ta hakan yasa Hadiza ta dan dago kanta saikuma ta tashi zaune da wuri takalli Mama, hannu Mama takai takama kuncinta tace “Hadiza na kin ganki kuwa? Kaman bake ba kashe kanki zakiyi ne dukkin rame saikace wacce kanjamau ki kama kinyi duhu, baki iyacin abinci, menene Hadiza? Ki hakura da Nura mana tunda shi ya hakura dake? Allah zai baki wani mijin daya fi zama miki Alkhairi” dan lumshe idanu Hadiza tayi cikin sansanyan murya tace “Mamaa” saikuma kawai tafashe da kuka Mama tadade tana kallonta kafin kawai ta mike hijabin Hadizan ta dauka da car key dinta da aka kawo mata daga abujan dan dama a plazan shagonta tai parking motan tadauki wayanta duka tamika mata dasauri Hadiza dake kallon Mama tana kuka tace “Mama mezanyi dasu?” Ahankali Mama tace “tashi kije wajen Hajiya go and amend mistakes naki Hadiza” Shiru Hadiza tayi tana kallon Mama saikuma cikin wani kalan muryan ban tausayi tace “idan takoreni fa” ahankali Mama tace “tashi kije kozata koreki bakomi ta isa ne but ki sauke nauyin dakikejin nan azuciyanki and asked her for sincere forgiveness ba irin wanda kikayi a asibiti ba, kinji don’t be scared tashi kije Allah zai dauraki akanta zan miki addu’a” Hadiza kaman tayi mutuwan zaune saikuma ta tashi ta karbi Hijabin tasaka ta karbi wayanta tawuce tafita.
Parking Hadiza tayi awajen gidan tadade zaune cikin mota sannan tabude kofa tafito jikinta duk yay sanyi kaman kankara dan batasan mezataje ta tarar ba tawuce tashiga gidan, matan datagani tsakar gida ta gaida tana tambayan ko Hajiya na nan aka cemata eh tawuce ciki sallama tayi agaban dakin daga ciki muryan wata mata ta amsa tace “shigo” ahankali Hadiza tacire takalmi tashiga ciki Hajiya tagani zaune kan kujera tareda wata mata wacce ita ta amsa sallaman tana nunama Hajiya wasu kaya da aka kawo ido cikin ido Hadiza tayi da Hajiya da sauri ta sauke kanta kasa matan tace “bismillah zoki zauna” wucewa Hadiza tayi tasami waje ta sauna akasa matan tace “bari naje Hajiya” Hajiya tace “to Salamatu ayi amfanida rabi kada ki manta” matan tace “to” tawuce tafita dakin yarage daga Hadiza sai Hajiya, ahankali Hadiza da kanta ke kasa tace “ina yini Hajiya” Kai tsaye Hajiya tace “lafiya lau Hadiza ya jikin naki? Naso zuwa dubaki amman kinsan kafan nawa maneji ne saisa, Allah yasa mai ceton ku ne sannu sannu”.

Leave a Reply

Back to top button