Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 40

Sponsored Links

40- Rungumeta yayi yana me sumbatar wuyarta. Zata kuma magana ya ce mata. “shiiiii! Ya isa haka, a yanzu babu ra’ayin aure amma idan aka cigaba da da barin waɗannan yan matan suna irin wannan shigar, tow zan haukace na karo aure, babu shiri.” Sake Rungumeta yayi yana dariya, yadda take kuka cike da sakalci da shagwaba. Duk hayaniyar da ake Malik yana jin su, ina zai iya da damuwarsu.
Nadrah da taga Malik bai wani dauki mataki ba, sai ta kyale su, ta kuma tsoro yawon dare. Kafin Elbashir su bar Keivroto Malik shima ya shirya visar kai ta wurin dangin Mahaifinta, tare da nuna mata shi maganar aurensu ne a gabanshi ,a tunaninta haka ne, har su Elbashir suka bar kasar, sannan shima ya sakata a gaba suka nufi kasar iyayen Shatima Dan kasar Gabon, domin su fulanin can ne, koda suka isa wani abun mamaki sun samu kyakkyawar tarb’a daga wurin dangin mahaifinta.

Duk da sai yamma suka sauka, basu samu zama ba. Sai Washi gari da safe bayan sun karya. Ana ya tara su baki daya. Ya saka Nadrah a tsakiyarsu, sannan yayi shiru ya ce musu. “Kune yan uwan Khamis, Ni bani da matsala da kowa amma a gefe guda, Khamis yana takun saka da ni da nayi kokarin magance matsalar amma ya kuma sako yarshi, idan ma ba shi bane. Hmmm ku mata fada, domin ni uba ne a gare ta kada ta kuma yunkurin shiga rigimar mu;”
“Dama an gaya min, ka kware a cikin amana da yaudara, me yasa ba zaka fadi exactly abin da yake ranka ba, sai ka buge da min alqawarin ka aure ni?”
“Ko da can baya ban yi miki alkawarin zan aure ba, ki gane ina da matar da nake so. Ina son Zainab sosai, koda zan aure ki ba zan iya nutsuwa naci ko na sha daga gare ki ba, saboda kin sha yunkurin kashe ni, daga ranar da na kai ki inda nake, sau nawa kika zuba min magani a cikin abin sha? Kin san me? Koda na ke zaune da Khamis ban tab’a yunkarin kashe shi ba, amma burinshi ya ga baya, ban san me yasa ba.”
“Ina sonka”
“Baki sona,wani abu kike nima daga kin samu zaki rabu da ni” daga haka ya kalli dangin mahaifinta ya ce musu. “Gata nan, ba zata gaya min wanda yake sakata tana wasu abubuwan ba, amma nayi imani da Allah, daga ranar da gaskiya tafito, zan hukunta har ita ba zan bari ba wallahi!” Ya mike yana kallon agogon hannun shi, ya ajiye mug din hannunshi yana faɗin. “ban yarda da cin kome a hannun kowa ba, ga tea dinku. ” Ya ajiye ya kalleta tana kallonshi. “Tow cikinka na jikina ya zanyi da shi?!”
Idan bata yi haka ba, ai ba jinin Khamis ba ce. “Ki zubda ko ko barshi ya rayu, matsalarki ce!”
“Dole ka aure ni, domin na riga da na turawa Yar gwal dinka. Matar da ta ƙasa yarda da kai, a karon farko kayi nazarin taya zata yarda da kai a karo na biyu. Ba zaka aure ba, haka kuma nayi alqawarin ba zata zauna da kai ba.”
“Kin kyauta, na san hanyar da zan ganar da ita.” Yana gama fadar haka, ta juya ya fita yana jin kamar yayi ya tarwatse ya huta, yarinyar ta shayar da shi mamaki. Haka ya bar gabon babu wani ci-gaba domin dai yasan akwai wanda yake behind din ta.
Idan da yasan tarkon Nadrah da ya faɗa, toh kuwa da ba zai tab’a barin garin ba, sai ya tisata a gaba har Maiduguri.
Amma ina baki daya, kome ya wuce tunaninshi, bai tab’a sanin haka zai faru ba, kuma koda ta gaya mishi abin da tayi bai yarda zata yi ba, domin dauka yayi tana mishi barazana ne, bai san zata aikata ba.
★★★
Maiduguri.
Kusan kwana biyu kenan da Zulfah ta gaya mata, gasu nan zuwa da Elbashir. Ita tasan iya shi da Zulfah zasu zo. Bata kawo a ranta zasu zo da Hafcy ba. Sai da suka iso.

Aka je aka dauko su, tana zaune a falo, suka shigo a tare da Zulfah, Hafcy tana bayansu. Mikewa tayi tana kallonta kafin ta ce.”Ki fita a gidan nan, kafin na baki mamaki.”
“Zeeno ki saurare ni don Allah!”
“Wallahi ba zan saurare ki ba, yanzu ma ban san da me kika zo ba, ki cutar min da Yarana. Ina tsoron Allah ina tsoron mutumin da na mishi rana, ya bini da masifa oya fita.”
“Zainaba! Malik yana raye.” inji Zulfah Dafe kirjinta tayi tana zare idanu, “Yana raye?”
“Eh yana raye, ki bar maganar Hafsah sai na kira shi kuyi magana ma ” ta cigaba da da gaya mata abubuwan da bata sani ba, a haka ya mantar da ita zancen Hafsah an aka shiga hira da Elbashir yaushe gamo.
Ba karamin hira suka yi ba, sannan aka basu yaran, ita kan sai da Hajja Yayye ta fito tayi ta mata fada, baki sun zo ba a basu abinci ba. Daga nan aka shiga jera musu abincin. Yara kuwa ana kawowa Elbashir yayi musu huduba. Sannan ya ce mata. “Wannan da yake babban su, sunan sa Muhammad Menk! Wannan kuma Muhammad Nasr, wannan kuma ya ce a saka mata sunan Maidah!” Kallonshi tayi tana me dauke kanshi. “Me ya samu maidah da aka sakawa Yarinyata?” “Allah ya mata rasu ne!” “Allah ya mata rahama!”

So take ta tambaye shi, amma baki daya bata san yadda zasu dauki Abinba, don haka ta mike tare da nufar saman gidan, ta zauna tare da fashewa da kuka. Wani irin kuka take me matukar cin rai, haka ta share awa guda tana kuka, Zulfah da Hafcy sun biyo bayanta, su kawo mata Yaran amma ganin halin da ke ciki yasa dole suka kyaleta. Kafin zuwansu tun da ta dawo gida, take fama da damuwa da yanayin gajiya. Ga Yaran Masha Allah, bata cika magana da kowa ba, sai Yaran shi yasa baki daya bata son shiga cikin mutanen, bayan dinbun damuwar da yake ranta. Haka bai hana ka ganta cikin yanayin sanyin halin da tsokanar Hajja Yayye ba..
Idan ta samu farinciki wuni guda, mantawa take da kome, har da wayarta yadda Malik ya turo musu kaya, yasa ta fita tana kallon kayan, ana saukewa.
“Ina zamu kai kayan nan?”.
“Ai na Yaranshi ne, don haka a kula mishi da Yaranshi da kyau!”
“Hmmm! Da ya damu da yaji halin da Yaran suke ciki da ya kira mu!”
“Amma ai ke kika ce ya jira kiranki sai ya zama laifi?”
“Ni nace ya kira ni tow!” Ta faɗa tana turawa Zulfah baki, ita bata son haka. Harara Zulfah ta watsa mata, suka komawa cikin gidan. Anan suka zube aka wuce aka yi sallah, bayan an idar aka shiga hiran abun da ya faru, watanin baya duk da bata fito ta nuna farincikinta ba, amma daga yanayin yadda ta zuba nutsuwa akan labarin da Elbashir yake bata,zaka gane she missing Malik lots.

Amma shegen halinta da zurfin ciki, yasa taki nunawa ta damu, akan kome har dare ya fara ja, can part din da aka warwa baki, suka nufa dama tun wurin magariba, Zulfah ta gaya musu part din, a can suka sauka. Ita kuma kasa barci tayi ita da Zulfah, tana bata labarin Malik. Har barci ya dauki Zulfah. A hankali tayi ta kuka mara sauti. Sai da kanta ya dame ta da ciwo, ya sha magani ya kwanta. Sai wurin karfe biyar na asuba ta farka, ta shiga ban daki tayi wanka da alola, tazo ta gabatar da sallah, har gari ya sha, sannan ta haura gadon ta kwanta tana jin wani irin gajiya na rashin barci. Tunda ya kwanta bata kuma sanin waye akanta ba, har aka gyara yaran aka kwantar da su. Don ma ana hada musu da Madara da nono, idan sun sha madara kafin suka samu awa guda sai su sha Nono.

Sai karfe daya na rana ta farka, sannan ta kuma wanka ta gyara jikinta, ta sauko kasa, ana ta hira yan’uwan Babansu fa basu samu zuwa ba ne, suka zo. Suka ga yaran. Kallon yadda ta sake kamar ba ita ba. “Zainab iyayen rikici!” Murmushi tayi, tana me zama ta gaishe su, tana kallon Hafcy da take ta kallon Maidah. “Yaya me yasa kika bata Yarinya?” “Wannan matsalarku ne, Ammyn sun futa da mijinta shi yasa take rike da Yaran gwal. ” Amsar yaranta tayi ta kwantar da su, tana me cigaba da hira duk yadda Hafcy taso danne zuciyarta amma ta kasa, sai da ta fashe da kuka. “Kiyi hakuri don Allah!”
“Ni kada ki tara min mutane, da kin san yadda rabuwa da miji yake, ba zaki gaya min magana akan Malik ba, kika gaya min tare da nuna min yadda zan tsane shi, ban tab’a mafarkin na cutar Dake ba amma ke me yasa kika yi mafarkin cutar da Ni? Ban da mugun nufi akan ki me yasa ke kika gaza gane haka? Ba ke ba wani wanda ya min halacci ya min haka, ba zan yafe mishi ba, ki kyale ni kiyi rayuwarki nayi nawa. Kada ki kuma kusantar inda nake na gaya miki!”
Baki daya kansu ya daure ban da Zulfah. “Dalla ya isa haka, san baki kirki, mai sonka shi yake bibiyarka, tayi kuskure kuma ta gane laifinta da ace ba a yafe mata ba? Ko kema ai kinyi wasu kuma haka zasu yafe miki. ….
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/27, 10:26 PM] Yan Mata:

 

Leave a Reply

Back to top button