Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 13

Sponsored Links

Volume:13 Jalilah
ZINNIEE’s SECRET
(One stop shop for a new sensation)

Kina Neman kamshi mai sanyaya zuciya❓
Shin kina Neman kamshi da dada❓
Ko kuwa kamshi mai ratsa zuciya kikeso❓ko Kayan gyaran jiki kike nema dry skin ne dake ko hard skin tabbas kinzo inda za’a share maki kukan ki

Tabbas Zinniee’s secret ya gama da damuwarku Ina mata masu aji mace mai aji ai Sai da gyara .tabbas Zinniee’s secret sun gama da damuwarki Hajiya ta.

Zinniee’s secret sun tanadar muku Kaya kamar……
Room freshener
Toilet spray
Bed spray
Dish wash
Mopping mist
Kai har ma da
Feminine wash
Akwai
Glowing soup dinmu mai kyau da inganci.
Glowing cream
Face cream da kuma body scrub

domin samun dadadan Kayan kamshi.da Kayan gyaran jiki maza garzayo Zinniee’s secret
Zinniee’s secret DUNIYA ne !!

Zaku iya yi mata magana a wadannan kafafan sadarwar kamar su—IG-@Zinniee’s secret
TIKTOK@ Zinniee’s secret
Ko ku tuntube su a wannan number 08080840567 za kuma ku iya mata magana ta hanyar Watsapp da wannan number.
Zinniee’s secret suna nan a kano Hadeaja road Kano state.

Zinniee’s secret one stop shop for a new sensation.

Zinniee’s secret got u covered,a trial will convince you.
_________________________
Zuba mata idanu yayi yana kallon ikon Allah, domin bai zaci haka daga gare ta ba. “Kika ce Malik ya zo nan ya aure ki? Kika ce Malik ya zo nan? Lallai Jalilah baki san Malik ba. Ganin shi kike yi, akan wannan yarinyar wallahi sai kin mutu ba tare da kin shirya ba, Malik bai tab’a rashin nasara ba, shi nasara ya sani.”
“Shatima kenan, ai shi yasa na yi amfani da yarinyar domin ita ce kwarin gwiwarshi. Kuma da kake ta min ihu ka fita ka bani wuri.”
Daga haka ya mike ya bar falorn yana kallonta. Duk rashin mutuncinta babu wanda zai iyawa. Lokacin da ya isa Asibitin ganin yadda aka hana kowa shiga inda yake yasa shi komawa gefe, ya zauna yana kallon shige da ficcen shi, ganin Elbashir yana waya da Malik yasa shi mikewa ya nufi bayan Elbashir ya fauce wayar ya saka a kunnen shi. “Mata nawa kake son su mutu domin ka? Malik itama yarinyar da babu ruwanta ka janyota cikin wannan masifar kenan? A duk inda kake ka kawo ko kazo ka samu gawarta.”

Kashe wayar yayi ya wurgawa Elbashir, sake kira Malik din yayi ya ce mishi..”me ya same ta?”. Hadiye yawu Elbashir yayi ya ce masa. “Bamu san me ya faru ba, kawai tun da ta fara Barci ata farka ba, sai fatarta yayi wani irin haske.”
“Jalilah!! Gani nan zuwa.” “Malik amma”
“Kada ka damu, rayuwarta yana da muhimmanci!” “Saboda kana sonta!” Kashe wayar yayi.
A gaskiya jikinta yayi laushi, don haka ko awa biyu ba ayi ba, wani likita dan kasar China ya iso asibitin daga gista Malik ya gayyato shi, tare da wasu kwararrun yan team suka iso akan lokaci.
A wannan karon abin ya dami kowa na Al’umma charity House, domin har ga Allah basu tab’a ganin lukutar masifa irin wannan ba sai yanzu, zuwan likitocin ya taimaka sosai, musamman shi Dr Xingi Wung. Tare da yan team dinsa suka fara shawo kan laluran.

Kusan kwana suka yi, yayinda Ammy ta kwana tana gayawa Allah samuwar Zeeno. Ba karya wani irin kauna take nunawa Zeeno, domin kuwa kamar yadda take yiwa Abbas addu’a haka take mata ba dare ba rana, kwana likitocin nan suka yi tsakanin lab da dakin Zeeno. Har washi gari abu daya suke, shigowar Malik cikin asibitin ya kara saka hankalin mutane shiga jikinsu, domin baki daya aka shiga kama tun daga leburorri har masu shara da Nurses a cikin asibitin. Umarni daya bada, sannan aka wuce can inda ake zubar da shara, aka fara binciken kwalbar alluran.
Wasa wasa kafin karfe biyu, Dr Xingi Wung ya fito yana share goshinsa, “Dr ya take?” “Da sauki, za a iya farkawa kowani lokaci.” Sannan suka shiga takawa da Malik wanda yake kan keke. “Kasan me duk wanda ya haɗa mata wannan maganin ba yana nufin ta mutu ba ne, sai dai kuma akwai hatsari sosai. Domin zai iya shafar ƙwayoyin halittar jikinta, kama daga ƙwaƙwalwa, hanta, huhu, ko koda, na gaya maka haka ne domin ka fahimci girman lamarin, gashi nan samfurin jininta,mun tura can cibiyar hada maganinka da take Desa sun ce nan da kwana uku zasu turo!”
. “Me yasa sai kwana uku zata farka, me yasa ba zata farka yau ba!” “Ba zai yiwu ba, koda ta farka, zata iya samun tab’in hankali ka ga kenan an yi bq ayi ba.” Sabon jinya ya kuma samuwa, gara a barta ayi hakuri!” Gyada kai yayi yana jin babu dad’i. Bayan sun gama magana da shi, ta wuce dakinta. Dama yasan haka zai iya faru a koda yaushe. Amma bai zaci farmakin zai kai haka ba.
A lokacin da aka kamo masu aiki a asibitin, kawo mishi su aka yi ya zuba musu idanu, rike camera yayi yana kallon su. ” Na saka wannan abin a cikin dakin domin nasan tabbas haka zai faru, amma ba san daga ina za a farmake ta ba, idan kuka dake naga fuskar ɗaya daga cikin ku, abin da zai faru ba zai muku kyau ba!” “Munji
Shigowar Ammy da mutanen gidansu. Yasa shi juyawa yana me jin babu dad’i. Shiga dakin suka yi Ammy ta tsaya suka yi magana, wanda jikinshi yayi masifar sanyi. “Ayi hakuri haka ba zai kuma faruwa ba, a gafarce ni da sakacin da nayi da rayuwarta.” Girgiza kai tayi tana me wucewa dakin. Kiran Elbashir yayi ya mika mishi camera din, “A duba min.” “An gama!” Daga haka ya koma dakin, kallonta yake kamar ya cire ciwon ya mai da shi jikinshi. Juya kekenshi yayi ya bar dakin, a bakin kofar ya hadu da Shatima.
Bayan awa guda, Elbashir ya dawo dauke da laptop, ya saka masa video matar da suka shigo da Jalilah, har ta mata allurar tare da duk hiran da suka yi da Jalilah. Akan lokaci aka fara niman matar, a cikin asibitin bata nan, ya kuma bada umarnin a nimota a duk inda ta shiga. Jalilah kuwa, Malik bai kuma bin ta kanta ba. Ya ajiye mata

“Duk macen da ka haɗa hanya da ita, sai an nime kashe ta? Na kasa fahimtar shin tsafi kake ko kuma.” Kura mishi idanu Malik yayi ya ce masa. “duk yadda kace daya ne!” Daga haka, bai tab’a jin b’acin rai sama da yau ba, don haka ba tare da ya nuna musu haka ba, domin kuwa yana son Zeeno ta farka sai ya dauki matakin da sai ya girgiza su.
A cikin kwanaki uku, da a za a gwada jininshi ya haura ya kai dubu, Allah da ikonshi ranar da dare ta fara farkawa. Ammy tana zaune akan abin sallah. Shi kuma yana waje domin a cikin kwana uku nan barci baya iya runtsawa. Mikewa Ammy tayi tana kallonta.
“Zainaba?” Ta kira sunanta. Jin muryan Ammy ya shigo dakin. “Ta farka ne?” “Eh!” Daukar wayar dakin yayi ya kira likitan da yake aiki a daren, tare da Nurse suka zo aka fara bata agajin gaggawa. Tare da mata allurar barci, idanunta yana kan Malik ta lumshe.
“Sir in sha Allah, gobe zata farka da yardar Allah. A kula da masu shigo mata.” Ajiyar zuciya ya sauke yau kimanin kwana uku rabonshi da barci, juyawa yayi ya nufi daya daga cikin dakunan da suke ɓangaren vip aka gyara mishi. Ya shige ya kwanta. Ya samu Elbashir yana zaune yana ta famar aikinshi. “Mutanen tsibiri na ajiye ka, gobe ba sai ka kwana ba. Ta farka.” “Alhamdulillahi, Ubangiji ya bata lafiya. Juliet ta rayu, Romeo sai a a kula da ita, yanzu ya batun kasuwanci.” Shafa kansa yayi yana kallon kofar waje. “Ikon Allah! Jama’a kuzo yau Malik yana jin kunya.” Mikewa yayi daga kekenshi ya koma gadon, ya kalli Elbashir. “Bani wani abu me zafi ba sha, yunwa nake ji.” “Ikon Allah na zata soyayya zaka ci:” daga haka ya mike ya fara kokarin hada mishi coffee.

“Ina Jalilah?” “Tana can na saka an rufe ta. “Ka nima mata ticket ta bar kasar nan, bana son na cutar da ita.” “In sha Allah! Ai halin da take ciki ma abin tausayawa ne domin yau kwanta uku ko ruwa bata sha ba. ” “Ka kyauta!” Ya amshi coffee din a babban mug, ya fara sha yana kallon Elbashir ɗin. “Duk da bana tsoronsu sai dai alaƙar da yake tsakaninmu yana bani tsoro, Bashir ka gaya min gaskiya kana kanta ko kaima dama kake jira ka kashe ni?” Murmushi yayi ya ce masa. “Lokacin da aka ce min Babanka ya kashe mahaifina, nayi fatan kafin na hadu da kai na kashe ka, amma yadda ka taimake ni bayan turo ni aka yi na kashe ka, karshe da aka ga ban iya samun nasara akanka ba, shi ne sune suka zo kashe ni, Malik a ranar da ka taimaka min na farfaɗo na ji zan iya kare ka da dukkan zuciyata na rantse da Allah ina masifar jin ciwon yadda kake nuna min baka yarda da ni ba ” yana kai aya ya mike zai fita. “Kada ka ga laifina yadda khamis ya sauya yasa nake ganin kamar kowa ma zai iya sauyawa!”
“A’a Malik ba kowa ba, ba zan tab’a sauyawa ba.” Yana gama fadar haka, ya dauki jacket dinsa zai fita domin yaji haushin Malik sosai. “Dawo ka zauna dan uwana, kada ka ga laifina nima abin da na ga yana faruwa ne!.”
“Don Allah ka daina zargina!”
“Na daina!” Ya faɗa, sai kuma ya fashe da dariya yo abun bai mishi dadin faɗa ba a bakinshi. Haka suka yi ta hira kafin Malik ya ce. “Idanuna akwai bashin barci, ina jin barci ne!” “Kwanta ka huta!”. Kwanciyar yayi shima, Elbashir ya zauna ya cigaba da kula da tsaronshi kamar yadda shima ya hana idanun shi barci ya kula da Elbashir ɗin, tow me zai yi mishi don ya cutar da shi bayan shi rayuwarsa ya sadaukar saboda shi. Ya kuma taimakawa danginshi da dan kanwarshi..
Sai da barcin Malik din yayi nisa, ya tashi ya rufa mishi bargo, sannan ya juya ya koma ya kwanta, barci ya dauke shi a saman kujerar.
5:15am
Malik ya ri ga Elbashir farkawa, don haka ya bar Elbashir ɗin ya rintsa, sai biyar da sha biyar ya farka yana kallon Malik!
“Me yasa baka tashi ne ni ba?”
“Saboda na ga kana bukatar hutawa ne!” Wucewa ban daki yayi, tare da alola ya fito, lokacin Malik ya koma saman keke ya zauna. Yana azkar duk da ibada, sai dai yadda yake niman kuɗinsa yasa ba a ganin yawan ibadanshi.
Sai da garin yayi haske Elbashir ya koma kujerar ya kwanta, ya koma domin cewa Malik. “Ni babu inda zan taka, ka kare yawon shigar da soyayyarka ni sai na gama barcina!”.
“Wai meye nufinka da Hafsah?”
“Gaskiya kake son na gaya maka, ko nayi shiru?”
“Kai dai ka zama ɗan iska!” “Na yarda kaho ne a kaina.” “Ina jin ka!” Malik ya ce masa. “gaskiya yarinyar tayi, amma kuma .”
“Amma kuma me?”
“Tayi kankanta, sannan bata da tsawo, ina da zaɓi a kan macen da nake so, da doguwa ko bata da fasali zan tafi da ita.”
“Allahu ya shirya ka.
“Allah ya kyauta, sai ka cigaba da dakon doguwa irin Zainaba!” Daga haka yayi kwanciyar shi.
★★
Tun da Elbashir ya dauke Jalilah ya kawo ta, wani gida ya rufe kome yayi tafiyar shi, bata kuma ganin shi ba, kusan bai wawayeta ba, har yau babu ruwa babu abinci, babu kome tun tana dauka yanzu zai zo, har ta daina saka ran da ta wuni da yunwa da ƙishirwa kamar zata mutu, haka ta kwana, washi gari ma haka, babu ruwan. Dole ta fara tunanin anya ba kashe ta za su yi ba, domin ba ruwa ba abinci.
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata: ZINNIEE’s SECRET
(One stop shop for a new sensation)

Kina Neman kamshi mai sanyaya zuciya❓
Shin kina Neman kamshi da dada❓
Ko kuwa kamshi mai ratsa zuciya kikeso❓ko Kayan gyaran jiki kike nema dry skin ne dake ko hard skin tabbas kinzo inda za’a share maki kukan ki

Tabbas Zinniee’s secret ya gama da damuwarku Ina mata masu aji mace mai aji ai Sai da gyara .tabbas Zinniee’s secret sun gama da damuwarki Hajiya ta.

Zinniee’s secret sun tanadar muku Kaya kamar……
Room freshener
Toilet spray
Bed spray
Dish wash
Mopping mist
Kai har ma da
Feminine wash
Akwai
Glowing soup dinmu mai kyau da inganci.
Glowing cream
Face cream da kuma body scrub

domin samun dadadan Kayan kamshi.da Kayan gyaran jiki maza garzayo Zinniee’s secret
Zinniee’s secret DUNIYA ne !!

Zaku iya yi mata magana a wadannan kafafan sadarwar kamar su—IG-@Zinniee’s secret
TIKTOK@ Zinniee’s secret
Ko ku tuntube su a wannan number 08080840567 za kuma ku iya mata magana ta hanyar Watsapp da wannan number.
Zinniee’s secret suna nan a kano Hadeaja road Kano state.

Zinniee’s secret one stop shop for a new sensation.

Zinniee’s secret got u covered,a trial will convince you.
_________________________

Leave a Reply

Back to top button