Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 21

Sponsored Links

Volume:21 Villains
Malik ya kware a iya jan makiyanshi jikinshi, ya kuma basu abinci yana tatsar gubansu. Domin yasan matuƙar suka shiga jikinshi, definitely zai san kansu. Kuma ya samu. Tun kafin Amjad Fahad su shiga jikin Zeeno ya fara nimanta, ya kuma san cewa dole ita zata iya shiga aikinsu shi yasa da tazo kai tsaye ya amshe ta, ya kuma saka mata sharadin aure a tsakaninsu. Daga Lalla Salmah da Shatima yasan cewa idan ya nime Auren Yaransu, aka yi kudirin su shine yaransu kwana ɗaya a gidanshi ranar na biyu su maka shi a kotu.
Shi kuma sai yayi musu wayon kin yarda da auren Yaran, na farko Nadrah wacce lokacin da ya ganta yana da interesting akanta, lokacin bai sake ya bar ta ba, sai da yasa mata wayar wani pen dinsa a jakarta wanda lokacin da ta isa gidan ya ji, yadda Shatima yake son ya shammace shi, ana auren ko kwana uku ba ayi ba, ya mallaki rabin dukiyarsa.

A bisa tsarin kasar, matukar mace ta ce ba zata zauna da kai, dolenka idan zaka saketa ka raba dukiyarka biyu, a bata rabi shi Malik ba fitar dukiyar ba ce matsalarshi, hannun wanda zata faɗa ne baya fatan haka, shi yasa ya ki maganar auren a tsakaninsu da yaransu, koda Zeeno tazo yasan tabbas zata zo domin ya jima yana nimanta. Ba iya shi ba hatta Zulfa da Yasir Aswad Al Yemini.

Tun bayan rasuwar iyayensu, yayi kokarin niman Zeeno amma bai zame ta ba, Yasir da Zulfa ya samu ya mai da su wurin danginsu, amma Yaran suka ki zama dole ya dawo dasu Keivroto tare yi musu alkawarin nimo musu Zeeno.

Har zuwa hatsarinshi da yayi fatan da ya hadu da Zeeno, ya kaita wurin Yan uwanta. Dake Yasir ya fi Zulfa wayo. Ya taso da mugun tsanar Malik domin akan kunnenshi ya sha jin tashin hankali da iyayensu suka shiga. Sai da ya gama secondry school. Ya tafi jami’ar da Malik ne ya dauki nauyin shi, a lokacin ya shiga binciken motsin Malik, da abubuwan da yake faruwa, yana gama jami’a yayi joining Police academy. Inda ya fara nazartar abubuwan d suka shafi binciken. Ba karamin wahala yasha kafin ya iya gano wasu bakin zaren munakisar da aka yi na wani case din dan kasar China da Malik ba. A lokacin sai da aka yi wata biyar ana bincike kafin aka kama mutanen da suka kashe dan china da sunan Malik, wannan ya wanke zargin Malik wato rigar shi ake sakawa ana kashe mutane, kwarai a lokacin yayi aiki da Malik ba na wasa ba, domin yadda ya dinga bin didigin Malik da gayyatar shi, yasa Malik yayi ta saka shi yana haduwa da manyan har ya kai matsayin da yake na AIG a tsakanin shekaru Ashirin da tara a duniya.
Wannan kenan.
Yadda take ta juyi, tana jin wani irin bala’in tashin hankali yasa ta mikewa zata fita, wutar gidan daukewa. A hankali ta soma jin wani irin motsi me mugun rikitarwa. Duk wannan abin da ake baki daya Malik yana kallonsu ta cctv. Har dauke wutar, sai da ya kirga yawansu. Kuskuren da yaso aikatawa barin Zeeno ita ɗaya a cikin dakinta. Haka ya shiga bi ta wasu hanyoyin gidan, sai da suka shiga asalin falon gidan, sannan suka ji waka a bayan sun. Juyawa suka yi tare da kai harbi. Suka ga yar karamar Radio ce ta MP4.
“Sako ya shigo, Malam Malik Menk Jordan me kake bukata a wannan lokacin?” MP4 ya tambaye shi, daga bayansu ya ce mata. “Malam Rebecca wuta za a bude musu!” Juyawa suka yi, suka samu baya nan, sake juyawa wurin MP suka yi, suka samu yana tsaye. “Sako ya kammala!” Kafin kace kwabo an bude musu wuta, karar harbe – harben ne ya kidima Zeeno ta fadi can kasa, ashe wasu sun biyo ta window dakinta, suka fasa glass din window suka shigo.
Zare idanu tayi ganin yadda suka saka mata bindiga a kai, tare da riko gashin kanta, suka fito da ita, suna haska torch. ” Ka sake baka dakatar da Harbin nan ba, zamu kashe ta!” Hasken gidan ne ya kawo, tana tsaye suna rike da kanta, dukar kafarta suka yi, ta durkusa. “Ku kyaleta tafi, ni ku min abinda kuke so”
“Ai mu baki dayanku aka ce mu kashe ba zamu tab’a kyale ku ba.”
“Wannan shine kuskuren da zaku aikata, matata bata san kome ba.”
Ya faɗa yana kallonta yadda take kallonshi. “Ka mana shiru!” “Tow ku kyale ta”
“Munki kyaleta!”
“Kuskuren da kuke aikatawa fa ba zai kaiku ko ina ba?” “Dama ai mu akan kuskuren muke. “Malama Rebecca duba adadin fitar numfashinsu!”
“Sako ya amsu!”
Kafin su fahimci me yake faru, hayaki ya cika falon, a lokacin ya saka abin zukar iska a hancinshi. Ya mike a hankali ya daga kan keken, idanun Zeeno kamar zai fado kasa, tana mishi wani irin kallo. Kafin ta ankara daga ita har mutanen sun fadi sunammu. Koda yake ita kafin ta daina hango shi, ta ga yadda yake takawa, cikin Isa da jin kai irin na gogagun marasa mutunci. Yana isa wurin da mazukin iskar ya saka mata a hancinta. Sannan ya ɗauke ta suka bar gidan, daya daga cikin motar shi. Ya sakata a gaba, snnan ya bude motar y zauna.
Yana shiga ya danna bleutooth, a hankali ya ce. “Malama Rebecca. Ruftar da gidan. Kada a samu wata shaidar ina raye”
“Malam Malik Menk Jordan, sako ya amsu!”
ba tare da bata lokaci ba, ya bar gidan, Haka ya rubta cikin karkashin kasa, a daren ya wuce bakin taku, aka saka motar shi a cikin wata kwantena, ya dauki matarsa suka shiga wata jirgin, tare da barin ƙasar. Koda zai dawo sai ya gyara shirinsa da matarshi domin yadda zai ci amarcinsa a nutse.
Tunda ya kwantar da ita ya kira likitan jirgin, ya fara dubata tare da saka mata ruwa, sannan ya shiga yayi wanka ya fito sannan ya dawo ya kwanta a gefenta. Yana kallon yadda take barci Bayan saka mata ruwan da aka yi. Bata farka ba sai da gari ua waye, har haske rana yana lekawa ta dakin sannan ya bude idanu tana kallon cikin dakin. A hankali ta sauka a gadon, ta ga wani kofa, bude kofar tayi ta ga banɗaki, wanka yayi tana me lumshe idanun kafin abin da ya faru ya shiga dawo mata. A razane ta zauna dabas a kasa. Kafin ta mike tana me yin alola. Ta fito ganin abin sallah a shimfide yasa ta nufa, tayi sallah.
Tana idarwa Malik yana turo kofar dakin, hannunshi dauke da tiren, ja da baya tayi tana faɗin. “Innalillahi!” Murmushi yayi mata ya ce mata. “Kin razana ne?” Ya d’age mata gira biyu yana murmushi. Yana matsawa gabanta, ya ja da baya. “Wayyo Allah mugun ji mugun gani Allah ka kare ni da gani” ta faɗa tana ja da baya.
Ajiye mata abincin yayi yana faɗin. “Oya zoki ci!” “Na koshi!”
“Ok haka ma yayi amma ki sani, yau zan amshi hakkina!” Ware idanu tayi tana faɗin. “Wallahi ba zan iya ba! Ni dama tausayinka nake ji, yanzu kuwa na daina tausayinka tunda da lafiyarka.”
“Wallahi sai kin bani hakkina kaji wani wayon banza,” haka suka yi ta jajjyayya, har yayi nasarar cafketa. Saka ihu tayi tana faɗin. “Don Allah kada ka min haka wani, wallahi ƙaddara ta kawo ni rayuwarka,. Idan ka yafe min xan fita.”
“Na ji zaki fita sai kin bari na haihuwa da ni ko daya ne, baki ga na tsufa ba ne”
“Wayyo Allah na, wallahi ni yar karama ce ba xan iya haihuwa ba ” saka bakinshi yayi a kunnenta. “Idan kika haifa min yara masu irin idanunki sai ki tafi a binki”
“Ai ko masu kama. Da ni ba zaka samu ba”
“Ai kuwa nasan wacce tafiki kyau zaki haifa min”
“Don Allah ka kyale ni!” “Idan na ki fa?”
“Ni dai wallahi ba zan iya ba” abin dariya haka yayi ta zolayarta, dakyar ya samu ta ci abinci, sannan ya ciro mata wani kayanshi ya bata. “Ina zan kai wannan jamfar?” “Sakawa zaki yi.” Ya faɗa yana mata dariya, wato sai yanzu ta ƙara gane Malik yana da barkwace da zolaya sosai ga babu abinda ya dame shi kai tsaye yake magana, yana daga cikin mutanen da basu dauki kai da wani damuwa ba, shi dai idan zaja mutuntatta shi bai da matsala. A cikin kwanaki uku da suka yi ya kara musu shakuwa, tunda ya fahimci ita din matsoraciya ce ya gaske. Domin da zarar ya ce yana son wani abu zata fara zaro idanu. Shi yasa bai sake niman kome ba, yayi kokarin koya mata yadda zata shiga jikinshi,
*Kuyi hakuri bamu da wuta ne*
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*[9/23, 1:53 PM] Yan Mata: V

Leave a Reply

Back to top button