[Music] Dauda Kahutu Rarara – Jagaba Sai Ka Shiga Villa
Yo ita dai wagga Villa shigarta yin Allah ne ba yin waka ba, Shararren mawakin siyarsar nan, jami’a gonar waka, Dauda Kahutu Rarara, ya saki sabuwar wakarsa mai taken, “Jagaba Sai Ka Shiga Villa” (mp3 download).
Babu adawa in dai ta fannin waka ne, Rarara zakaran gwajin dafi ne na kasar Hausa wanda yanzu kam inda da yakinin babu tamkarsa.
Also Download: Dauda Kahutu Rarara – Dan Arewa Door to Door
Inama inama, ina ma da isashshen lokaci, lallai da na matukar cika ku da dan karen suturu game da wakar nan ta Jagaba Sai Ya Shiga Villa.
Bola Ahmed Tinubu dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar APC tare da mataimakinsa, tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima.
Za su fafata ne da Alhaji Atiku Abubakar, babban abokin hamayya wanda ke rike da tutar takara ta jam’iyar PDP.
Kazalika za kuma ku gwaru da dan takarar jam’iyyar NNPP, masu kayan gwari wato Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso.
Sai kuma Peter Obi wanda ke a jam’iyyar Labour Party (LP) shi ma ya fito neman takarar shugaban kasar Najeriya a kakar wannan zaben.
To, ko ma dai menene, zan so ku yi gaggawar sauke wakar nan domin ku saurareta cikin sauki.