Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 10

Sponsored Links

Volume:10 rumors
Al’amarin ya ta’azara Wanda ya shiga kunnen kowa da kowa, musamman alummar gidansu Zenobia, sakata suka yi a gaba da tambaya.
“Yar nan me muke a gari?”
Tun safe ake tambayarta har yanzu kalaman Malik yana yawo kunnuwarta. *Dole ki dauke kai kamar baki gani ba, dole wasu zantuttuka zasu yawaita, Amma magana daya zan gaya miki. Ki toshe kunnenki! Ina da darkside, alumma charity house yana hannunki think before take action!* Juya kanta tayi tana fadin. “Kunga ina da banbanci da ita, sannan matsalar Malik daban, alaΖ™ar mu daban, don haka babu abinda ya dame ni da matsalarshi, kuma babu abinda ya dame ku da matsalarshi da fatan Kun fahimta.”
…”Amma magana daya ne, taya zamu zuba miki idanu ai Allah ya tambaye mu! Kina jin yan mata uku ya lalata, kice muyi shiru!”
“Inna indai Zainab tana sonshi ai ba aibu bane matsalar idan bata sonshi shine matsalar ko Zeey!” Gyada kai tayi tana sauke ajiyar zuciya. Domin Ammy ta kawo mata dauki lokacin da ya dace. “Amma dai, kin san illar abin da kike shirin turata?” Girgiza kai Ammy tayi sannan ta ce mata. “Bana jin zanyi na danama Alan zabin Zainab, ko akwai wani abu ne Zeey?” Girgiza kai tayi a karo na biyu, “Tow tashi ko wuce daki!” Mikewa tayi ta haura sama.

Tun da ta haura sama take safa da marwa, ita ba wai matsalarta da shi ba ne, a’a yadda al’amarin yake shirin juyowa, tana tsaye har yanzu Malik be kirata ba, which means abin da ake ta yayyatawa gaskiya ce, “tow me yasa bai kira ni ba?”
Ta kurawa wayar idanu. Kafin ta cillar da shi. Me yasa ake kiranta da Yar getto area? Bayan bata ga wani laifin haka ba, ai ita abin a jajjanta mata ne zata auri tsoho kuma nakasasshe. “Ya Allah! Sam baya tafia fa?” Ta fada kamar zata fasa ihu. “Taya na biyewa Amjad muka tabo abinda ya dame ni? Nima na cika shegen zakewa da iyayi mtsew !” Taja tsaki. Turo kofar dakin aka yi, juyawa tayi ta zubawa hafsy idanu. “Eh lafiyarta lau! Ok” ta katse kiran.
“An ce na duba kina lafiya?” Tsaki ta ja ta koma ta zauna. “Idan ya matso yazo da kafashi kuma wallahi fita zan yi!”

Daga haka ta wuce tare da daukar simple coat dinta ta saka tana fadin. “Haka kawai ya shiga rayuwata zai hana ni sakat!” Ta fuce tana mita amma maganar gaskiya rashin kiranta ya wanke kanshi yafi kome mata zafi.
β˜…β˜…β˜…
Whiter town
Harkan gabanshi yake, kamar abin da yake faruwa baya cizon zuciyar shi, kokari yake ya forgot everything else, amma Ina abu daya yake yawo a ranshi Zeeno. Taya zata amshi thi situations? Taya zata amshi wannan al’amarin he thought da al’amarin bai kai haka ba, tow zai iya kare kanshi. Duk da Meeting yake tare da bayani amma Babu yadda zaka gane yana cikin damuwa sai Elbashir. Yana yawan lura yadda yake bayani, yana yana keeping heavy breathing, rabon da yaga Malik cikin irin wannan yanayin tun rasuwar Nuratu. Bai tsammanin haduwar Zeeno da shi zai kai matakin haka ba, da har zai boye damuwar a ranshi. Yana kallonshi har ya fita tare da kiran Hafsat ta duba mishi ita, kuma ta ce lafiyarta lau, sauke ajiyar yayi ya amso ruwa me sanyi, ya ajiye mishi.
“Thanks!” Malik ya fada.
“Ba kome!”
Yana tsaye, aka kira shi ya kalli Malik, Shima Malik din kallonshi yayi, a hankali ya fita daga dakin meeting din. Bayan ya gama wayar ya koma dakin. Lokaci zuwa lokaci yana kallon Malik. Har aka gama meeting din, bakin suka fita.
“Me ya faru da ita!” “Wai ta tafi bakin ruwa ne.”
“A motsa!”
“Zamu fita da Yara ne?”
“A’a ni da kai ai mun wadatar ko?”
Gyada kai yayi yana fadin. “Eh Malik amma naga kamar kana bukatar hutu!”
“Ka da ka damu, muje kawai.” Ya fada yana kallon agogon hannunshi. “Muje naga six tayi ma!” “Eh!” Haka suka fita har wurin mota, ya shiga tare da kwantar da kanshi, Elbashir shima ya shiga. Haka suka bar gidan, kwantar da kai yayi yana sauke deep breath, yana jin wani abu na mishi yawo a zuciyarshi.

A hanyar tafiyar ne, ya saka Elbashir su tsaya su karba mishi yar kamar scart, a wata yar karamar kwali aka nade shi. Aka saka a paper bag, Elbashir ya fito da shi, ya shiga motar. “Thanks!” Juyawa yayi ya ce mishi. “Malik babu godiya a tskanin mu!”
“Na fada dai!” A haka suka Isa har bakin ruwan, anan suka same ta zaune tana kallon ruwa, like she missed wani abu na daban, special for her only life. A can nesa da itama Zulfa ce zaune tana kallonta, ita Dake tana da raunanniyar zuciya kuka take. Har ga Allah tana son kanwarta sama da yadda take son kanta, sai dai a halin da Zenobia take gara su boye mata, akan su gaya mata wacece ita.
A hankali ya matsa kusa da ita sosai ya zauna. “Zainab i’m I hurt you?” Juyawa tayi ta zuba mishi fararen idanunta. Kafin ta janye saboda nauyin da idanunshi ya mata. “I’m i hurt you?” Murmushi tayi sannan ta ce mishi. “Waye ya gaya maka zaka iya cutar dani? Ni nazo nan ne domin shan iska shima iskar ba zan shaka cikin salama ba ne?”
“Waye ya Isa?” Juyar da kanta tayi tana fadin. “Zaka iya tafiyar ka.” A hankali idanunshi ya sauka akan kayan jikinta. Kasa kasa yayi maganar da dole sai da ta zabura tare da cewa. ” Anya kasan Allah kuwa?” Ta fada tana kare jikinta. “Eh mana, taya zaki fito daga ke sai riga da wando, sun kamaki. Sannan kin dauki wani rigar sanyi mara kauri kinsa. Salon ki saka dan tsoho aika-aika!” “Don Allah me yasa make zantuttukar da suka girme shekaru na ne?” Kai tsaye kamar ita ya ce mata. ” Ai naga hannu hagu ba bakon wanke duwawu ba ne, kuma nasan irin wannan maganar ai ba bakonki bane!” Tabbas Malik ya hasalata kuma yana son lallai yayi magana ne, amma taki cewa kome. Murmushi tayi ta ce mishi. “Hmmmmm!” Ta ja harufar.
“Zainab!” Kallonshi tayi for same seconds ta amsa mishi. “Na’am!” A hankali ya kai hannunshi Kan nata, “Nasan kin ji abinda ya faru!” “Sai aka yi me?” “I like your style!” Tab’e baki tayi tare da murgud’a shi ta ce. “Na tsani turancin nan Malik!” “Ina laifin ki kira ni da Mayor!” Juyar da kai tayi tana fadin. “Ban kira ba, wanna karon wani lokaci na tuna na kira.” Kallonta yake bai San yadda zai fara fadar ga yadda yake jinta ba, but she take everything from him.
“Za…!” “Malam Mayor! Idan da hali kayi….!” Kasa karasa maganar tayi, sakammakon yadda ya dauki ya daura mata abin a wuyarta yasata kallonshi. “Ki kula da sanyi, kuma idan da hali ki zo na sauke ki a gidan!” Hadiye yawu tayi tana sunkuyar da kanta. She never expect from him. Ganin yadda ta mutu da mamaki yasa shi. Murmushi ya ce mata. “Muje Mrs Mayor” jiki a mace ta mike, tana tafiyar kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki,ya ce mata.
“Kin ga da Ina da kafa, daukarki zan yi Babu abinda ya dame ni da wannan tafiyar naki.!”
Shiru tayi bata iya magana ba, ita fa wallahi Malik yanzu Allah na tuba tsoro yake bata, ya koma wani irin mutum, abinda Zeeno bata gane ba, yanayin da take ciki Malik ya fita shiga, sai dai dukkansu gwanaye ne wurin hadiye damuwarsu a zauna lafiya. “Hmmm! Ba zaki gaya min maganar gaskiya ba” murmushi tayi sannan ta Isa wurin motat zata bude Elbashir ya bude mata, ta shiga sannan ya budewa Malik ma ya shiga ya dauki keken ya kai baya. “Muje kici abinci a gidana!”
“Na koshi!”
“Ni yunwa nake ji, muje ki dafa min abinci!” A hankali ta kalle shi, sannan ta ce mishi. “Ban iya girki ba” “hmmm! Malik ya gaji da cin abincin karti ya za ayi kenan?” “Sai yayi ai!”
“Okay muje!” Da sauri ta kalle shi zata yo magana ya ce mata. “Elbashir zai turawa Hafsat Muna tare.”
“Wani ya gaya maka wani abu ne?” “Sai dai yanzu zan ji a bakinki!”
“Hmm!”
Ita Zeeno lallai so take Malik ya fada mata abin da yake faruwa, shi kuma yaki yana son ganin reaction dinta, itama me shegen wayo taki nuna damuwarta. Haka yasa take ta ce mishi hmmm, Malik baya cikin irin mazan da zasu zauna ya ce zai gaya mata kome don kare kanshi, yafi son ta fara magantuwa shi kuma ya fahimtar da ita. Amma sai taki tayi shiru. Asalin shiru mara dadi.

Shi yasa yayi dabarar tafiya ita gidanshi ko zata sake a can yayi maganar da ita, sai dai har suka dauki hanyar bata kuma magana ba, asalima tafiyar suke tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce taci kuka ta koshi, nan kuwa damuwa ce take dawainiyya da ita, tin daga maganar auren har zuwa yanzu, abin zuwa mata yake bazata. Har suka Isa gidanshi, sai da Elbashir ya bude mata ta fita sannan ya budewa Malik, suka shiga cikin gidan. “Malik dazu, Ramadan ya gaya min Jalilah tazo. Kuma tare da Lalla Salmah Amma ta tafi.” “Me yasa baka gaya min tuntuni ba? Me yasa baka gaya min Jalilah tana cikin gidan nan ba? Bashir kasan aikinka kuwa?”
“I’m sorry Malik!” Juyawa yayi ya kalleta, “muje!” Ganin yadda ya masifance Elbashir yasa ta kame kanta ina zata iya jarabar Malik. Idan ya fara masifa kamar Wanda ake Ingiza shi.
Haka suka shiga cikin gidan, Rai babu dadi. “Zo ki wuce dakina kiyi wanka da sallah kada ki sake ki fito kin ji ko?”
“Tow!” Ta fada tana wucewa hanyar d ya nuna mata, tunda ta shiga dakin. Ta sake baki. Domin kuwa abin da Malik ya guda shi ya faru, Jalilah ce a dakin. “Kece karuwar da kike bibiyar Malik?” Ita bata ce kome ba, sai ma juyawa da tayi zata fita ta ce mata. “Zo nan Dan ubanki, waye sa’arki Ina magana kina tafiya baki ji tsorona ba?”
“Ai ban San shi. Kin gane!” Daga haka ta saka kai zata fita, kwalbar turaren imperial majesty ta kwala mata, a baya daidai shigowar Malik dakin. “Ke wacce irin dakikiya ce?”
“Dakikai dai! Malik na ce dakikai dai! A shekaruna kamar ita, ka kwantar da ni karya na.maka? Waye yayiwa Nuratu ciki ba kai bane?” Wani irin kunya ce ta kama shi. Yayi fatan da yana iya tsayawa da kafarshi tabbas sai yayi kwallo da Jalilah. Abin karin takaicin yadda yake hango fushi a idanun Zainaba, “Koda na kwanta dake, ai sauran wasu na samu, ko karya ne!” “Karya ne! Na ce karya ne, blackmailed dina kayi, akan wani bukatarka, sake kallonshi Zeeno tayi, “amfani da ni kayi, domin biyar bukatarka kuma ai ka samu ko karya ne? Ai ka samu na maka karya ne? Malik ka zata ban sani ba ne? Ka zata ban san cewa tsafi kayi shi yasa ka kwanta da ni.” Kallon Zeeno tayi tare da fashewa da kuka ta ce mata. “Kin san ko ban haife ki ba, ni ba sa’arki ba ce ko? Ki gudu da kafarki domin kuwa sirrin dukiyar shi yana jikinki yana samun biyar bukatarka shi zai nimo hanyar da zai rabu dake, ba akaina ya fara ba.” Kallon shi Zeeno tayi, a hankali ya ja kafarta zata fita ya riko hannunta.
“Baki yarda dani ba ne?” A sanyayye ta ce mishi. “Me zance ce bayan abinda nake son ji daga bakinka, ta fada.” Sai tayi murmushi ta ce mishi. “Batun da yake tsakanin mu, yana nan wannan kuma tsakaninku ne zan tafi gida na gode da gayyatar!”

A hankali ta juya ta bar dakin, a zafaffe ya tura keken shi, ya bi bayanta. “Elbashir kaita gida!” Ya juya yana fuskatar Jalilah. “Ba zan miki kome ba, domin akwai lokacin da kunyar yarinyar zai hanaki sukuni har na karshrn rayuwarki!” Daga haka ya wuce ya barta nan. Har ga Allah ranshi yayi mugun baci bai San yadda zai yi ba, Amma ba damuwa bata da hankali zata gane bata da wayo lokaci na zuwa
*Ayi hakuri wayata ce ta lalace don Allah ayi hakuri πŸ₯³πŸ€©πŸ˜πŸ§*
500N
07035133148
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button