Cinikin Rai Book 1Hausa Novels

Cinikin Rai Book 1 Page 11

Sponsored Links

CINIKIN RAI….11
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
A yadda yake maganar ya masifar bata haushi, don haka bata san da ta daki table É—inshi ba, sai da ya razana. Takowa tayi gabanshi ta riko necktie É—inshi ta shiga gyara mishi a hankali tana me kara zuge mishi sai da ta shake wuyarshi. Bude baki ya fara. “lalacewar bata kai wanda zaka min barazana ba, baka isa ka min barazana ba wallahi. Kasuwanci muke da kai da kai ba bauta nake maka ba, banza irinka zaka shigo da al’umma charity House!” Ta kuma tamke wuyar. D’aga hannu sama yayi yana faÉ—in. “Ya isa haka, kyale ni zan gaya miki yadda zaki yi, da tausassawa. ” Kara matse wuyar tayi ainun har sai da ya fara kakari ta ce mishi. “Koda wasa kada ka tab’a martabar al’umma charity House, yadda na matse wuyarka haka zan tsinke ta.” Daga haka ta wuce waje. “kayi kokarin niman wacce zata maka aikin ba dai ni ba.” Ware idanu yayi yana tari, ina ba zata sabu ba, Ita ce ta dace da aikinshi. Sosai abin ya d’aga mishi hankali, don haka ya nufi hanyar waje. Ko da ya fito ya samu har ta fito daga dakin sauya kaya. Zubewa yayi a kan gwiwarshi. “Allah ya ya huci zuciyarki, na tuba nabi Allah na bi ki.” Ganin yadda a gaban ma’aikanta kamfanin ya iya sauke girmansa ita wace ce da ba zata hakura ba?
“Shi kenan kome ya wuce.” Ta fada tana, me dauke kanta. Abin sai ya zama Gulma sosai a cikin kamfanin Chairman ya durkusa yana bawa ma’aikaciyarshi hakuri kafin kace kwabo al’amarin ya zaga ko ina har ya fada manhajar social media. Sake wasu sun yi video din abin. Haka yasa shi Mr Amjad ya dakatar da ita, kuma daman haka yana cikin shirinsu.

Kwana biyu a tsakanin, Salim ya zo ya dauke ta, suka je aka mata international passport. Saboda fitarta USA.
<<<|=|>>>
Waterfall island.
Tsibiri ne da yake kan dutse, inda ruwa yake sauka izuwa babban tekun Keivroto sabuwa. Tsuni ce da babu wanda yake da ikon ya isa wurin sai ka isa ka kai, ka kuma gawurta. Yanki ne me dauke da manyan manyan jami’an tsaro ko ta kwana. Wadanda suke aiki na tsawon awa ashirin da hudu a sati. Sannan kullum sauya su ake babu wanda zai kuma dawowa, sannan wani abin da zai kuma daure kai, shi ne masu aiki a ilahirin tsibirin maza ne va mata ba, asalima babu mace ko daya.

Fili ne fallau a saman dutse aka fasa shi, sannan aka mishi wani irin stone house, aka yi wani ƙasaitacciyar Mansion a tsakiyar dutsen, aka zagaye shi da wasu irin duwatsu wanda aka yi katangar da ya zagaye gidan, na musamman ne domin ba daga asalin duwatsun aka yi su ba, wasu irin duwatsu ne aka zo da shi, idan aka ce za ayi bayanin yadda gidan yake bata lokaci ne.
Malik Menk Jordan, Mansion kenan me dauke da abubuwan ban al’ajabi da mamaki. Gidan da babu wata mace da ta tab’a zama cikinsa, sannan ko a cikin gidan shirye yake da kayan alatu da more rayuwa, domin kome da yake cikin expensive ne daga Æ™asashen waje. Babu abin da babu a gidan, daga masu kula da Flowers, bangaren abinci da sauransu babu wani ma’aikaci da yake permined dukkan su temperary ne, kullum sauya su ake.
Cikin gidan me dauke da dakuna shiga, kasa uku dama uku. Sai wani katon zanen hoto irin na da can, domin zana shi aka yi. Ba hoton aka dauka ba, wasu dattijai ne guda biyu. Mace da namiji sai wani yaro a tsakiyarsu. Gefe wani zane ne me Black and white. Bayansu babu wani abu na azo a gani, sai domin duk wani abin da yake cikin gidan ba bakon me karatu ba ne.

A saman can harabar gidan, fili ne na tashin helicopter na daidai mutane biyu zuwa uku. Sai dan gefen can da aka ajiye expensive cars, irin wanda ake yayinsu. A ilahirin mansion akwai yar karamar drum da yake tashi irin na wasan Yara, sai dai wannan an sake shi ne, saboda tsaro da kwantar da tarzoma. Sannan akwai wasu irin tsuntsaye Eagle manya da suke shawagi a gidan, dauke da Camera a cikin gidan.

Akwai wasu manyan lion dogs da aka kewaye su, sai zuwa dare aka sake su, duk da a cikin gidan inda ake kwana akwai wani daki da aka ajiye tiger, wanda girmansa yafi na irin raguna udawa, a batun gaskiya masu kula da tsaron gidan kawai, abin tsoro ne domin tun daga tsibirin har zuwa inda aka saka iyaka da tsuburin. Domin sai an ketare ruwa kafin a iso, idan ta jirgin ruwa ne. Koda yake mutum daya ne yake amfani da jirgin Elbashir Jamal Arab, saboda kusancin shi da Malik.a bakin gabbar tsibirin akwai masu kula da ruwan suma 24/7 a cikin sati. Motoci kusan guda bakwai suka iso bakin ruwan, masu É—auke da Shatima01 har zuwa 6, a tsakiyar motoci shida nan ya fito daga cikin wata phantom. Wacce ake bude ta ta gefe daya, rike yake da wata irin sanda, yana dogarawa sanye yake da normal shigar hausawa, kanshi dauke da zanna bukar. Wacce ta kara fito da dattijuwar fuskarshi. Amma hutu da jin dadin rayuwa yasa baka iya hango dattijantaka da take tattare da shi. Lalla Salmah ta tawo a cikin motarta a tsakiya itama, sai masu tsaron lafiyarta kasancewar ta Assamblywoman. Bude mata motar aka yi, ta fito rike da yar karamar jakar Charles Keith , sanye take da turkiyya plan gown minti colour. Hade da hularsa, sai ya tafi da jakarta da takalminshi. Murmushi yayi mata sannan ya ce mata. “Yar majalisa ya kwana biyu?” Kallonshi tayi kamar ba zata yi magana ba, kafin ta ce mishi. “Lau!” Da wani irin yake, ta dauke kanta, sannan suka nufi inda jirgin da yake jiransu, shiga cikin jirgin suka yi kowa yana jin wani abu na daban akan dan uwansa, ko da jirgin ya fara tafiya, mika musu wani karamin akwati wani jami’in tsaro yayi, suka zazzage kayansu baki daya, ya ja ya rufe suka cigaba da tafiya, koda suka tsallaka ruwan. Jami’an tsaron suka karbe su, takowa suka yi aka fara screening dinsu, bakiÉ—aya a duk lokacin da zasu tafi ganawa da Malik sai ayi musu screening kamar masu zuwa lahira, sun san da Elbashir ne babu me mishi wannan binciken kwafkwaf din. Babu abin da ba karbe ba, domin kuwa babu yarda a cikin lamarin Malik. Karban kome da aka yi yayiwa Lalla Salmah ciwo. Haka yayi fuska sannan suma da mitarsu ba sabon abu ba ne a wurinsu. Domin ba yau aka fara bincikar su ba, shi kan Shatima bai wani ki dar ba, ai dama ba sabon abu bane a wurinshi.
Daga nan baki ruwan mota suka shiga da zai kai su, cikin Mansion É—in. Lokacin da suka isa kamar waÉ—anda suka fito sansanin cutar coronavirus, domin sai da aka musu feshi da magani sannan suka wuce shingen farko. Tsaki Lalla Salmah tayi tana dauke kanta, kafin suka isa wurin aka saka su, suka cire takalmarsu. Aka basu wasu, karshe sai da aka kai su wani daki na musamman suka sauya kayansu, sannan aka mika musu wani kati.

Sannan duk wannan abin da ake musu, babu wanda ya ce uffan domin aikin kawai ake a aikace, babu magana kai kanka ka kasan cewa kome sa ake yi da ilimi ake yinsa. Sai aka gama kome sannan suka wuce wani falon da ya dace kafin su samu kira daga Malik, Elbashir ne ya fito dauke da cup na wine. “Hi! Ya kuke?” Ya isa wurinsu, waiter ne ya iso dauke da tire na ruwa da wine. Ya mika musu, dauka Shatima yayi yana faÉ—in. “Yaushe Malik zai daina mana haka, wallahi kunya da jin babu dad’i nake, tsawon shekaru ashirin da biyar muna tare!” Murmusawa yayi ya mika mishi kofin suka dan buge kwalbar.

“Idan baka manta ba, rashin tsaurarra tsaro yasa aka samu matsalar da har yau yake jinya, idan har Malik bai kiyayye rayuwarsa ba, me kuke so yayi?” Shiru suka yi, suna kallon juna. “Yaushe ka dawo?” Lalla Salmah ta tambayi Elbashir, tab’e baki yayi ya ce mata. “satin da ya wuce, ina Maidah?” “Tana lafiya, next up week zata tafi Demark, akwai course É—in da zata tafi tayi akan karatunta na wata shida.” Gyada kai yayi, sannan ya cigaba da kallon jaridar da yake gabansu. Kallonta Shatima yayi ya ce mata. “Gashi kusan lokaci guda Nadrah zata gama karatu da su Wahiba da Wahida. ” Murmushi tayi ta ce. “Eh wallahi, Yaran Nuratu sun girma! Har yau ba a samu danginsu ba ko?” “Ki tambayi Malik shi yake da masaniya akan zuriarsu.” Tabe baki tayi tana faÉ—in. “Naga ai kafi mu kusa da Malik, kai zaka riga mu sanin kome.” “Nima bani da ikon sanin kome, sai abin da Malik ya gaya min, ba zaku gane cewa Malik Menk Jordan ba kome yake sanarwar ba, sai abin da ya zama dole Ppl dinsa ba kowa ya sani ba, sai shi kaÉ—an shi.”
Kallon agogon hannunshi yayi ya ce. “Oopss… Sorry ashe yau ba zaku samu ganawa da shi ba, sai nan da wata sati.” Ya mike yana murmushi, “what!!?” Lalla Salmah ta zare idanu, kamar zata fasa ihu. “Yanzu don Allah meye haka? Duk wannan wahalar ace ba zamu samu ganinshi ba?”

“Akwai matsala ne idan baki ganshi ba? Ko akwai wani abu ne rashin ganin Malik din?” Yadda ya tsare ta da idanu,yasa ta sunkuyar da kanta, ta ce. “Ko É—aya.” Ta mike tana faÉ—in. “Allah ya kai mu.” Inji Shatima dama shi bai wani damu ba, harka ce ta siyasa, kuma suna fitowa yake gayawa Elbashir abin da ya kawo shi, ita kuma ba haka ba ne, kudirinta akan dole sai tayiwa Malik tallar Maidah ne.

Haka suka fito daga tsibirin ranta a bace, shi kan Shatima bai yi wani mamaki ba, domin yasan darajar Malik kafin ya yarda a ganshi tow sai kayi kamar kana yi, don haka ya sakawa ransa sallama, Indai Malik ne ko wancan watar da ake ta bala’in akan abin da ya faru suna tare a Green House. So shi bai wani damu ba.

—–
Lokacin da suka iso gida, maid dinta suka tare ta, bala’i da masifa ta tare su, sai fada kamar zata doke su, babu wanda ya kulata.
★★★
United States of America.
New York.
Anan suka sauka, a wani apartment me kyau na fita hankali, ba kowa yake zama a cikin apartment din ba, sai manyan mutane ko Celebrity da yan matan yan siyasa. Sai da aka yi sati biyu tana sauka span a kasar apartment din ana mata gyaran jiki. Kafin ranar da ta cika wata guda,aka fara kaita kamfanin Baazar ta dauki hoto tare da musu tallar wasu abubuwan, kamar kamfanin kayan kayan kwalliya, sai kamfanin sarrafa kayan sawa, D&G, sai na turaren explore. Watan ta biyu a US, suka wuce Dubai inda tayi tallar wasu abayas, tallar ya janyo aka gayyace ta bikin karrama Celebrity a London, tare da Vogur babban gidan mujallar Ingila, me cin gashin kasa, wanda yayi promote Halinta haded, Rawda Muhammad, da sauran hijabs girls, duk wannan tafiyar sun shi ne, da Salim duk inda ta saka kafarta yana biye da ita. Kayan da ta saka doguwar riga ne, shiffon material aka dinka mata, shi me shegen kyau, shara-shara me azazzben kyau da É—aukar idanu. Kanta wani turban ne, da aka yi like net, fuskarta an yi mata normal makeup, da kayan makeup na milan, daga takalmin kafarta zuwa jakarta, abin dubawa ne domin ta nutsu tana abu gwanin ban sha’awa.
A lokacin da suka shiga hall din, hankalin kowa ya koma kanta, musamman kamfanonin da suke buƙatar sabuwar fuskar da zata musu talla, kuma abin da Mr Amjad yake bukata kenan, ta zama wacce duniya zata yayyata da zuzzutatta. Kowa ya santa duniya ta san wace ce ita, kowa ya gane ita wace ce, kuma haka ya faru. Domin a cikin wurin taren mutane dayawa sun bukaci ganin Manager ɗinta, da suke yi sponsored ɗinta, babban burinshi ne.
Kafin wani lokaci gidajen tv da na radion, Gista da Keivroto ya dauki labarin ana yayyatawa ana kara zuzzuta Zeenobia, yarinya daga getto area, ta zama shaharariyar da ba a zata ba. Dakyar ya yarda ta saka hannu a kan wasu kamfanoni guda biyu, zata yi aiki da su na wata biyar biyar, domin baki daya baya son sharararta ya wuce haka.

Haka kuwa aka yi kamfanin farko daga Gista take na sadarwa ne, ita zata na musu talla akan wasu abubuwan su. Sai na biyu kamfanin kayan kwalliyar mata ne, sai da ta kai manyan gidajen jarida masu zaman kansu, sun sayi hoton fuskartar. A wannan tafiyar sai da ta kwashe wata hudu cur kafin ta dawo gida, tsabar ta gaji, sai da ta kwana uku bata iya ko lekowa, sai ranar na hudu ta fito ta shiga cikin gari, a nan ta samu garin ya cika da poster dinta, murmushi tayi har ta. Wani shagon cin abinci, dake dare ne kuma ta saka riga me hula da facecap. Haka ta fita ta sayi abin da zata saya, a hanyar dawowarta ne, suka yi kicibis da Asp Zulfa suna patrol. Dauke kanta tayi zata wuce da motarta suka tsayar da ita. Ko a cikin dubu ta sauya shiga zata gane ta, balle a ita daya kaya kawai ta sauya. “Miss Zeenobia, ba a taba sauyawa tuwo suna ba, tun duniya na kwance balle yanzu sa take zaune da gindinta.” Cire facecap din tayi tana lashe dark red lips dinta ta ce mata. “Kina bukatar selfi ne?” Murmushi Zulfa tayi tana faÉ—in. “Ina selfi amma ba da watsassun mutane ba.” “Keee yar sanda!” Tayi wani karkata baki irin na samu na yan daba, ta ce mata. “Ki iya bakinki!” Ta juya zata shiga motarta, rike rigarta ta bata Zulfa tayi tana faÉ—in. “jagaliyarcin ya motsa ne?” “Na rantse da Sarkin da yake busa numfashi idan, kika dame ni sai na kaddamar miki, na gaya miki.” Tayi tsaki tana shiga motarta, “Na kama mutane biyu da suka lokacin da kika kashe Ayuba da Wasim.” Cak tayi ta tsaya tana kallon Zulfa in confidence ta dauka a motar tana me nufar Zulfa. “I’m glad da abin da kika yi, sai dai ki sani ni naci dubu sai ceto, idan har kina da zarra tow ki kwamushe ni, Zeenobia nake Xnoo, yar kunama karamar su Babbar su.” Ta wuce tana me barin motar, sai da ta tashi motar sannan ta bud’a musu hayaki. Tayi gaba abinsu.
★★★
2weeks.
Mika mata file yayi, ya ce mata.
“Zaki musu tallar sati daya, kamfanin abin sha, ture file din tayi tana faÉ—in. “Ina son kudi zan tafi Ofishin haraji ne.” Murmushi yayi ya dauki wayar shi yayi kira. “Hello bani takardar harajin nan!” Can sai ga Salim ya shigo, mika mishi takardan yayi, ya mika mata. “Zeeno gashi nan” sake bude drower dinsa. Ciro wani kwali yayi ya ce mata. “Gashi nan” murmushi yayi yana kallon yadda ta ruÉ—e. Kallonshi tayi na wani lokaci, kafin ta ce mishi “me zan yi da shi.” “Bude ki gani mana” a hankali ta bude kwalin tayi, zare idanu tayi kamar zata fasa ihu. “Kina tsammanin zaki yi aikin nan, babu wani abu ne sannan ki duba motarki, kina babban yarinyar babu mota na more rayuwa! Ga wannan katin ki tafi bankin golden bank a cire miki password É—in da kike so, sai a cigaba da sharholiya.” Murmusawa tayi tana faÉ—in. “Dole ayi sharholiya a al’umma charity House.” Ta fada tana kallonshi. “Kinsan me yasa na zuba miki kudinki ta golden bank? Domin mutanen Malik da Yaransu a wannan bankin suke amfani da shi”, ware idanu tayi tana faÉ—in. “Yaushe zamu fara nufar Malik din!” “Da sauran lokaci”
Gyada kai tayi ya dauke kome ta fita, murmusawa yayi tana fita, Salim da MD suka shigo. “Me ya rage Chairman?” Murmushi yayi ya ce mishi. “Ta fada komarmu! Ita ce abin harin mu, domin Malik ba zai kamu ta dadi ba, dole sai da tsananin hawa.” “Kenan Malik kifi ne da ba za a kama shi ba, sai an watsa mishi tanna da kwari!”
D’ago idanu yayi ya ce mishi. “ita ce tannar tawa!”
Murmushi yayi ya ce ” Musu, rayuwarta wadancan mutanen ne, idan kana son ganin farincikinta, ka yiwa mutanen hidima!” Gyada kai yayi suna masu jin dadi a ransu.

——– Zeenobia kuwa motar ta dauka ta nufi bankin, yayi duk abin da zata yi, lokacin da ta shiga bankin mutanen da suka ganta, sai ta zama celeb domin kuwa kowa rubibinta suke. Bayan sun gama mata kome da girmamawa,a hanyar fitar ne suka hadu da Mr Shatima, har ga Allah kallon da yayi mata, ta tafi da imaninshi. Kara kallonta yayi yaga yadda take taku a nutse yasa shi shagala da bin ta da idanun.
Gyada kai yayi, Hadi P.A din shatima ya ce mishi. “Yallabai baka san ta bace, ita ce yar tallar nan ta Baazar da Vogur.” “Hadi ayi wani abu a kanta, tayi min sannan a tura mata kyautar ban girma a account É—inta. Domin kuwa kaiwa Manager magana.” “An gama Yallabai!” Murmushi yayi yana imagine yadda zai sarrafa yarinyar, domin kuwa yana cikin mutanen malik masu mugun son mata, shi yasa tun rabuwarsu da uwar Nadrah bai wani kara aure ba, domin baya son damuwa, shi yasa ya bige da bin yan mata musamman yan kananun Celebrity, yana kashe musu kudi kamar yayi hauka.

Babu abin da yake tashin kanshi ya ga mazaunin mace, yana bala’in son ganin kugun mace tana juya shi, ga Kirjinta a cike, irin na yan matan da suke tashe da yan matancin su. Murmushi yayi yana ji tabbas zai more domin yasan yadda ta zama shaharariyar nan, ta goge na fitar hankali.
——
Daga fita ita kan gida ta wuce, a can aka cigaba da shagali sai saka yara take a mota. Tana nuna musu. Sarin na yan sanda yasa ta dakata, ta zubawa motar idanu. Shigowa Zulfa tayi tana kallon gidan. “Aunty Zeeno, wace ce ita?” “Aunty Yar sanda ce!” Gyada kai suka yi suna kallon su.
Takowa tayi tana shafa motar, tana faÉ—in. “Nawa nawa kike ka sa musu ne? Gaskiya labarin da nake ji ya bambanta da wanda idanuna yake gani,” ta fada tana shafa motar. “Zeenobia Nasr Hadejia, me kike basu suke rawan jiki akanki haka ne?” Dauke ta tayi da mari, tare da murde hannunta, ta haÉ—a ta da motar. “Tunda nake ban tab’a jin kwadayin bada kaina, ba kuma bana fatan na bawa wani dan iska kaina domin na burge su. Du inda na shiga ina girmama mutuncina sama da kome.”

“Zainabia!” Aka daka mata tsawa, daga sama. Inna ce, tana zuwa ta wanke ta da mari. Sai huci take. “Baki ga ta girme ki bane? Ko ance Miki sa’arki ce!” Cire hannunta tana huci ta ce mata. “Ta kuma jifar mutuncina sai na lahira yafi ta jin dadi.” Ta fada tana me barin Æ™asar. “Barka dai yar sanda.” Shiru Inna tayi kafin ta ce mata. “Idan tayi laifi ba kuskure bane a hukuntatta, amma kuskure ne a ci zarafinta……
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 2:22 AM] Maman Sadiq Da Khadija

Leave a Reply

Back to top button