Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 32

Sponsored Links

032
___________________
Mai Babbar ɗaki A kashingiɗe take akan tumtum cikin kwalliyarta na dindindin tana kallon Yareema da ke zaune a gabanta ya lanƙwashe ƙafa sai wasa da zoben azurfan hannunsa yake
An ajiye masu tarin kayan marmari wanda ya raba tsakaninsu.

“Naji abunda kayi ma su waziri…Yarima mutanen da nan da kwana uku zasu ƙaddamar dakai a matsayin Sarki su ka tozarta kayi masu barazana da mutuwa!…Yarima wannan fa abu Al’ada ne baa ƙwacen mulki ta ƙarfin soji…In suka hanaka mulkin nan ba wanda ya isa ya baka….(Numfasawa tayi gamida caɓe baki ta kautar da kai ,kana ta ƙara ke maganarta da cewa) …A saboda haka naje na roƙesu gafara a maimakon ka…” ta ɗan motsa hannunta ta ɗauki ayaba tana ɓarewa cikin sanyin jiki.

Cikin rashin damuwa ko nadamar abinda yayi ya fara magana dakyar kamar an sashi dole sai yayi maganar “Kinci mutuncin sarauta Mama!!”

A harzuƙe ta ɗago ta kalleshi “Ban gane ba?🤨” ta tambayeshi a ƙagauce ,still Fuskarsa na nan yanda yake kuma bai kalli inda take zaune ba ya ƙara da cewa
“Kinci Mutuncin Shugabanci kuma…”

“Kai Yareema saurareni,kaifa ba ɗan kanka bane da zamu cigaba da zura maka ido kana duk abinda kaso ba…You must not do anything that will jeopardize our royalty…Da ace bakai kadai bane ɗana,bazan damu ba nasan in an ƙwace sarautar akwai subtitute ,to yanzu kai kadai ne dole in saita maka hanya,Don koda kai baka son sarautar nan ,Ni ban shirya barin gidan nan ba…” Lumshe Ido tayi tana maida numfashi sakamakon hassalar da tayi ,Amma still baisa yarima ya tanka ba.
Ko ya nuna ɗar a jikinsa.

“…Gobe Su waziri da Sarkin Musulmi da sauran tawaga zasuzo don ƙaddamar dakai a matsayin Sarki ,abunda kawai ake nema shine cancantarka idan har ka cancanta gobe sunanka SARKI ABBAD!!”

A tsorace ya ɗago yana kallonta

“So calm down,Idan zaka ci ubansu ne ka bari sai ka ɗare gadon mulkin mana ,why this craving?”

***
Washekari
Fada ta ɗauki haske jama’a ta taru ,amma na iya cikin gida ,don tantance cancantar yarima matsayin Sarki ko akasin hakan. Idan ya tabbata sarki bayan sati ɗaya zaayi gagarumin shagalin rantsar dashi,kazalika idan ya faɗi ,bayan sati ɗaya dai babu fashi za ayi gagarumin shagalin rantsar da Waninsa.

Yareema Abbad,Queen,Auta,su waziri da duk wani mai faɗa aji suna zazzaune a royal cushions din da ya kewaye tangamemen kujerar sarautar mai martaba ,kowa ya hallara Tsohon Sarkine kadai ,baya cikinsu yana can kwance akan gadonsa rai ga hannun Allah.

Sarkin Malamai ,daƙyar ya taƙarƙaro yana tafiya daƙyar cikin tsananin ciwon girma ,shekaru sun tura haka ya shigo fadan.

Tsura ma kujeran mai martaba ido yayi ,kawai sai ya fara ɗauke hawaye da hannunsa.
Tsit ɗakin akayi kowa damuwa ya cunkushe masa zuciya ,saboda kowa yasan kukan tuna tsohon sarki ne da ya kamata a ganshi zaune akan stage ɗin nan .
Saida ya gama sharɓensa saura na tayashi sannan yaje gaban Yareema ,ya ciro Wani zoben Sihiri wanda ake zura ma kowani sarki da zaa naɗa ya kama hannunshi zai saƙala masa ,saidai jikin shi karkarkar ya dauki rawa…yef !!! Zoben ya faɗi ƙasa .

Duk ɗakin daukan salati sukayi “Subhanallahi!”

Bai dandaraba ya sake duƙawa ya ɗauko zoben zai saka ma yarima ,amma dai still jikinsa yana ƙaƙƙarwa ne irin na tsofaffi haka zoben ya sake faɗuwa.

Yarima fusata ya kamayi ,ya fara hura hanci cikin fushi .

Ɗago kai Sarkin Malamai yayi yana sharce zufa idonsa suka kaɗa sukayi jaaa
“Innalillahi wainnailaihir rajiun” tuni cikin kowa ya ɗura ruwa .
Bismillah sarkin malaman yayi ,ya duka ya dauki zoben a karo na uku ,yaje saitin Yarima ,saidai kafin ya kai ga ƙarasawa aka kaɓe masa hannu da ƙarfi ,zoben taje ta daki kujerar sarautar ,danjan da akayi adon zoben dashi na Alharir ya doki ƙasa ya dagargaje ya bar tsuran ƙarfen Azurfan.

Sarkin fada na ganin haka ya juyo yakalli duk mutanen fadan ,suma shi suke kallo cikin tashin hankali da neman karin bayani ,waigawa yayi ya kalli Yarima fuskarsa Neutral ba yabo ba fallasa. Kawai sai ya juya ya fara takawa zuwa hanyar ƙofa yana faman girgiza kai cikin tashin Hankali.

Yarima Abbad da yaga zai fice a gidan ba tare da ya rantsar dashi a matsayin Sarki ba ya ɗebi fushin zuciya ,a harzuƙe ya wani daka masa tsawa

“Kai!!!….” Ya kira shi a gadarance.
Sarkin Malamai bai waigo ba ya cigaba da tafiya

“Kai Sarkin Malamai Zonan…Ashe ba dakai nike yi ba? Zonan!”
Ko waigowa Sarkin Malamai beyi ba ya buɗe ƙofa ya fice

Wani mugun tsaki yaja “Banza!!,Tsohon banza mara Amfani… Irresponsible nonentity…” Auta diddulo Ido tayi cikin tashin hankali ,mai babbar ɗaki kuwa hannayen ta biyu ta haɗe ta doki ƙirjinta. Kamar zatayi hauka ,shikuwa ya cigaba da zarya yana tijara

“In banda Iskanci a tara manyan mutane kamar mutanen da suka taru a nan ,wai sai ace baza a iya kaddamar da naɗin sarauta ba ,sai tsohon Aladen nan yayi mana tsubbace tsubbace da bokanci?…Wannan ai jahilci ne ,mulki irin na jahiliyya…
A kaina komai zai sauya babu sauran bokanci a masarauta na ,don haka na soke sarautar Sarkin Malamai! Kuma na Koreshi a masarauta ta….Daga yau na soke duk wasu surkulle da bokanci a fada na duk wanda ya kuskura ya kawo mun shirme a fada na sai na yanka kanshi wallahi…,sabon Sarki!! Sabon shugabanci!!!Dukkanku ku fita ku bani waje ,Mamana dake da waziri Ku tsaya” yaje da sauri cikin zafin nama ya tattare riga ya zauna jirif akan tangamemen kujeran mulkin wanda akayi ma samansa ado da kan zaki.
Yana zama ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya

Cikin hargagin balai ya cigaba da gargadinsu da cewa
“Zan iya zama sarki koda karagar nan ko babu shi…,Daga Yanzu kuma Nine sarkin ku….!” yasa hannu ya daki hannun kujerar da ƙarfi.

Yana dukan kujerar da hannunsa ,kamar ya ƙyatta ma fetur ashana kawai wuta ta tashi bal akan kujerar ,ta cafkar mai ɗuwawu.

Wani gantsarewa yayi ya fasa magigicin Ihu yayi Zumbur ya mike ya riƙe ɗuwaiwukanshi gam cikin azaban zogin wuta.

Ƴan fadan da suka juya zasu fita a tsorace suka juyo,gilmawar jan wuta suka gani ,ya tashi daga jikin kujeran ya fita ta window ,kujerar tana nan daram ba alamun ƙonewa sai yarima da ya ɓalle da kururuwa…..!”

Mai babban ɗaki a firgice ta nufi inda yake ita da auta ,suna kururuwan kiran sunanshi ,tsit ya daina kukan halshensa ya karye ,idanuwarsa suka kakkafe ,Mai babbar ɗaki tana damkarsa ya tafi jikinta gaba-daya suka zube a ƙasa tare ,babu rai babu dalilinsa..

Rai baƙon duniya!😭
Allah ya jiƙanka Abbad!!!

 

 

Oum Aphnan
#Bad boys

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button