Cinikin Rai Book 1Hausa Novels

Cinikin Rai Book 1 Page 16

Sponsored Links

CINIKIN RAI….16
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
Ai dama kome a shirye yake, don haka Jihad Khan ya fito, yana faÉ—in. “Yarona! Ina zaka a cikin wannan daren? Ina iyayenka?” Girgiza kai Malik yayi yana faÉ—in. “Babana ya rasu, Ummata tana asibiti, zata mutu don Allah baba ka bani kudi a duba ta!” Ya fada yana me rike kafar Jahid Khan.
“Ai kai Yarona ne, dole a kula da mahaifiyarka, muje na ganta.” Riko hannun shi yayi suka shiga motarshi, suka nufi asibitin, kallonta yayi in pitiful kafin ya ce. “Ina Director na asibitin nan?” Baki daya asibitin aka taru musamman Drs da nurses, “ku duba lafiyarta kafin na dawo!” “Ok Sir!” Suka fada, sannan ya rika hannun Malik suka fita. “Yarona zan baka wani aiki, kafin ka dawo za a kula da ita kaji.” Gyada kai yayi. Daukar shi yayi har wani kofar gida, ya mika mishi Æ™aramar bindiga. “Ka shiga gidan nan, akwai Hashim Zubair, ka harbe shi. Shine wanda ya kashe maka Babanka ya dauke maka dukiyarka. Ka tattara fushinka a zuciyarka, ka dauki fansarka!” Gyada kai yayi, sannan ya fita daga motar, ya nufi gidan ba tare da wani abu ba, ya buga ai kuwa lauyan babanshi ya bude mishi kofar, “A’a Malik kai….!” Sake mishi harbin yayi har sau uku. Faduwa Hashim Zubair yayi, a wurin bai shura ba. Shima kuma Malik ko da ya gudu, ya sami Jahid Khan yana jiranshi, don haka yana Isa wurin shi, Yan sanda suna cafke shi. “Shine ya kashe babban Lauyan nan ta fafutukar kwato hakkin talakawa, a tafi ea shi.” Sake baki yayi yana kallon Jahid Khan. Har aka saka shi a motar yan sanda. Haka suka tafi da shi, a hanya yayi ta dambe da su har suka yi hatsari. Ya fita dakyar, daga nan bai tsaya ko ina ba sai asibiti, koda ya isa ya samu Mahaifiyarshi ta rasu, tsayawa yayi akan gawar har aka zo aka tafi da shi, ba a taba kai mutum gidan yari babu shara’a ba, sai akan Malik, tunda aka kai shi, ake dukanshi da azabtar da shi, sai yayi wata shida a dakin da babu haske ko kaÉ—an, sannan aka fito da shi. A lokacin Jahid Khan yazo yake bashi labarin shi ya kashe iyayenshi, shima anan aka kawo shi, tow makabarta shi ce, Malik bai ce mishi kome ba, domin a zaman da yayi cikin gidan ya koya mishi shiru ko nace mutuwar Iyayenshi ya saka ya koyi hakuri da shiru, wasa wasa sai da Malik ya kwashe shekaru sama da goma sha biyar a gidan Yari, an manta da tarihinshi a lokacin muka hadu da shi, amma kafin mu haÉ—u Malik ya gawurta a cikin gidan Yari, domin sai da ya kwace duk wani matsayi da masu fada a ji a cikin gidan. Malik ya samu karfi tun a cikin gidan yarin, domin Yaran da yake dashi a cikin gidan suka fito tow kasuwanci suka fara mishi, misali fasa kori, sayar da kayan maye, shiga harkan siyasa, Yaranshi sun yi karfin suna..
A lokacin sai da ya kai babu wani ne tarin matasa irinsa, gashi a cikin gidan ya karasa makarantar shi na secondary, ya kuma hada da matakin diploma a cikin gidan Yarin. A lokacin da na shiga cikin tura ni aka yi na kashe shi, domin yana gidan wani dan siyasa ya bashi aiki aka yi kuma aka samu nasara, jam’iyyar adawa ta tura ni na kashe shi, amma ban kashe shi ba, an yanke min hannu.

Dawo labari.
Kallon hannun shi yayi dungulumi ya ce mata.
“Malik Menk Jordan, shi ya yanke min hannu. Yarinyar ban tab’a ganin fusataccen mutane irin Malik Menk Jordan ba, domin hatta gashin jikinshi a fusace take, a tsaye-tsaye haka suke. Lokacin da na dawo na samu an daina yayi na, dole na koma gefe da Yarana, muna tab’a Kasuwancinmu.

A lokacin da aka kafa Jam’iyyar PKO Malik da kansa ya kafa ta a gidan Yari, sannan aka samu nasara, a take aka fitar da shi ta hanyar yan majalisunsa, yana fitowa ya saye duk wani kusan gwamnatin, kafin ya shirya tsaf, ranar cika Mayor Jahid Khan, a cikin Bainar nasi, Malik ya kashe shi da duk wani me taimaka mishi sai da Malik ya ga bayanshi, sannan ya shiga bibiyar makasan Iyayenshi, a lokacin da aka ce Malik ya kashe Mayor Jahid Khan, sai da ta kai kowa rufe gidan shi yake, domin kuwa garin Keivroto ya samu tashin hankalin da rikici, yadda suke kokarin zubda jini, yasa Malik shiryawa ya nufi cikin gari, aka yi ta bata kashi sa mutanen Jahid Khan, rigimar da ta janyo dole mahukunta suka dauke kansu, domin rigimar cikin gida ce, Malik sai da yayi ta bin manyan mutane yana kashe su a cikin gari, a gaban Jama’ar gari, haka yasa mutane suke mugun tsoronshi, da kace musu ga Malik gara mutuwarsu.

Sai da ya share Keivroto tass, sannan ya amso dukiyarshi, ya shiga harkan kasuwanci da siyasa kamar me, bayan shekara biyu, Khuldu Jahid Khan ya dawo domin fansa, a gaban jama’a Malik ya mishi dukar kawo wuka.

Wannan yasa shi daina fuskartar Malin gaba da gaba, ya shiga bibiyar shi ta baya, sai dai bai sha dadi ba, domin da Malik ya fahimci haka, sai da ya mishi illar da ya bar Keivroto da kafarshi. A hankali kome ya fara typing daidai,.kafin kuma Malik yayi hatsari bayan mutuwar wasu abokan Kasuwancinsu.”

Shiru tayi kafin ta ce mishi.
“Malik bai da rauni ne?”
Kura mata idanu yayi kafin ya ce mata.
“Rauninshi Nuratu ce, ita din Marainiya ce daga gidan Marayun Demark, kamar kanwa take mishi, a lokacin yana da Yarinyar da yake so, Jalilah karshe an ce Jalilah ta sayar da nuratu ga wani Bature ya lalata mata rayuwa inda ake daurawa Malik sharrin yayiwa Marainiya ciki, kuma a haka Malik ya amshi cikin sai dai basu kasar nan, suna Demark.”

“Kenan bai da Rauni?” Shiru yayi kafin yayi kasa kasa da murya ce mata. “Ai bai da shi, sai dai akwai wani Bad side É—inshi Dan Luwadi ne, abin da yake aikatawa kenan yasa bai yi aure ba, har yau!”
“Me yasa ba fitar da sanarwar haka ba?” Kasa yayi da murya ya ce Mata. “Babu wanda ya isa ya fada, domin mutuwa zai yi!”
“Kana nufin babu wanda isa ya fitar da zancen kashe shi za ayi?” “Eh yar nan!” Mikewa tayi tana faÉ—in. “Aikin Banza da ace akan wannan labarin zan bata lokaci haka da banzo ba,.” Ta saka kai ta wuce tana mita.
Karshe hudu na asuba ta isa gida, bata wani bata lokaci ba, ta wuce daki ta kwanta abinta, dakyar tayi sallah asuba. Karfe tara, ta shiga tare da nufar kamfanin Malik! Tana shiga ta wuce office din Elbashir.
Shiga tayi tana me faÉ—in. “Na dawo, ina son ganin Malik!” Sake baki yayi yana kallon ta.
“Ke wacce irin taurin kai ne dake? Baki ga ina waya ba ne? ” “Da sauki tunda kana raye!” Tayi kanshi da wani karamin wuka ta saka mishi a wuya. “Ina son ganawa da Malik!” Kallon wayar shi tayi taga An daka MMMJ, amsa tayi tana faÉ—in. “Mayor Malik Menk Jordan! Kana magana da Zeenobia Nasr Hadejia, ina son ganawa da kai na baka nan da kwana uku, ga number ta 0803032……. Idan ka shirya ka kira ni, ni kuma zan iso inda kake! Ka rike sunana Zeenobia Nasr Hadejia, ko Xnoo ko Yar kunama, Zeeno. Duk wanda ya maka kai ka sani. ” Katse wayar tayi ta cilla mishi. Tana me faÉ—in.
“Baka san halina ba ne, ba zaka min taurin kai ba.” Ta juya ta fita tana waka, ban da rashin mutuncin irin na Zeenobia an gaya mata waye Malik amma tayi biris tayi abin da take da niyya.
Daga nan kai tsaye kamfahinsu ta wuce, tana shiga office din Mr Amjad taja kujera ta zauna, sannan ta daura kafaffunta a saman teburin gabanshi.
“Me ke tafe dake?” Yadda ta bude kafar tana kallon shi ta ce mishi. “Daga yanzu zuwa wani lokaci, zan gana da Malik!” “What!” Ya mike tsaye, “Tantama kake?” Girgiza kai yayi yana faÉ—in. “Ban yi ba, amma taya haka ya faru?” “Ikon Allah, waye ya gaya maka, wayo da dabara ce?” Nan ta kwashe kome ta gaya masa, gyada kai yake yana mamakin yadda ta daki sa’a.
“Idan kuma yaÆ™i gayyatarki fa?” Murmushi tayi ta ce……. Me zata ce? Rigima tana gaba,
_Free pages ya kusan karewa! Saura nawa ma? Muje zuwa…._
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[29/08, 12:47 pm] usmanlauratu71

Leave a Reply

Back to top button