Furar Danko Book 2Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 45

Sponsored Links

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣5️⃣

…….Da kallo kawai ta bishi zuciyarta na wani irin rawa da mamakinsa. Gaba ɗaya ya juye mata a kammanin da ta sanshi tun farko na dakewa da rashin son ɗaukar raini. Gaba ɗaya sai taji ma shakkarsa ta shigeta. Kusan minti uku tunaninta ya fara zurfi sai kuma ta miƙe, dan ganin ɓacin rai a tare da shi kuma duk sai take jin itama nata zuciyar babu daɗi. Bedroom ɗin ta shiga da sallama ƙasa-ƙasa, inda yake tsaye yana saka bathrobe a jikinsa ta nufa, dan har ya cire kayansa. Sallamar kawai ya amsa mata batare da ko kallonta yayi ba harta iso gabansa. Fuskarsa da ke kicin-kicin ta zubama ido, ganin bazai kalletan ba yasata kai yatsanta manuniya ta ɗan takaleshi a kafaɗa. Kautar da jikinsa yay, ta ƙara lakatoshi a hannu, ya sake kaucewa kamar wani ƙaramin yaro, sai kawai ta matsa ta rungumeshi ta baya ta ɗora kanta a saman bayansa tare da zagayo hannayenta saman cikinsa tana wasa da igiyar bathrobe ɗin kamar zata kwance. Idanunsa da ya lumshe saboda jinta a jikinsa ya ɗan ƙanƙame jin ta zagayo hannunta saman cikinsa, a hankali ya firzar da iska yana cije lip ɗin sa na ƙasa kaɗan da ƙoƙarin yana ƙoƙarin zame hannun nata amma sai ta sake ƙanƙamesa.
       “Fushi kayi?”.
    Ta faɗa a hankali. Shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya ɗan sake sauke numfashi da kama hannun nata ya zagayo da ita gabanshi. Mayatattun idanunsa ya zuba mata kamar yanda itama take kallonsa cikin tsakkiyar ido. Gira ta ɗan ɗaga masa tare da kanta, “Fushin dai?” ta faɗa tana kai yatsarta ƙirjinsa a saitin zuciyarsa ta shiga zagayawa da faɗin, “To ki huce hajiya zuciya”.
Harararta yay da buge mata hannu yana sake ɓata fuska kamar wani AA. Sai kawai ta ƙyalƙyale da dariya da faɗawa jikinsa ta sake rungumesa.
         “ALLAH in kana shagwaɓa kamar AA najin yunwa fa”.
    Duk yanda yaso cigaba da riƙe kansa ya kasa. Murshi yayi yana ɗan lumshe ido da dungure mata kai, sai dai baice komai ba. Dan haka ta fara masa cakulkule. Dole ya fara dariya da ƙoƙarin janye jikinsa amma taƙi barinsa, sai ma baya yake tana binsa har suka faɗa saman sofar ɗakin. Bata daina ba duk rokon da yake mata sai da ta tabbatar ya jigata sannan ta barshi tare da faɗawa kansa suna dariya su duka.
        “ALLAH ke muguwa ce”.
    Ya faɗa yana ja mata hanci. Amsa ta bashi da “Ai kai ka koya min dan kaine malamin koya mugunta ma”. itama tana dungure masa kai. Sai suka sake ƙyalkyalewa da dariya.
            “Kin fara nauyi ALLAH, ɗaga ni karki fasa min ciki”.
         Fuska ta ɓata da duban kanta, sai kuma ta hararesa da faɗin, “Ta ina na ƙara ɗin? Ni ALLAH bana son sharri”. Kallo ya bita da shi irin a ɗan ɗagen nan, sai kuma ya nuna mata yana gimtse dariya. Inda ya nuna ɗin ta kalla. Da sauri tace “ALLAH zai saka min” tana kai masa duka da filo. Ƙoƙarin riƙewa yake tana dariya da faɗin, “Daga faɗar gaskiya. To shikenan na yarda baki ƙaraba. Ƴar ƙanwata na nan yanda take ƴar sawalwala abinta cas-cas”. Sauka tai da ga jikin nasa ciki nuna irin nayi fushinnan, shima sai ya miƙe da sauri ya riƙota tare da ɗagata gaba ɗayanta suka fice a ɗakin. Tana zille-zille da faɗin ya sauketa bai kulata ba ya fita ta baya inda swimming pool ɗinsu yake. Direta yay a bakin ruwan ya cire bathrobe ɗin jikinsa yay hanging a kan ɗan ƙarfen da aka saka domin hakan kawai dama. Da sauri ta kauda idanunta da ga kallonsa, dan har yanzu ta kasa iya daina jin kunyarsa, duk da bawai haka nan yake ba akwai ƙaramin boxer jikinsa bazata iya jurar kallon nasa ba kai tsaye a haka. Shima komai baice mata ba sai murmushi da ya saki kawai, cike da kwarewa yay tsalle da sufa irin na masu wasa da ruwa cikin ruwan. Yanda ya fantsama ciki sai da ruwan ya tarwatso mata a jiki har a fuska. Fuskar ta kwaɓe tana kallonsa kamar zatai kuka, shi baima san tana yi ba sai da ya kai ƙarshe zai juyo ya kula. Dariyar mugunta ya kwashe da shi, sai kuma yay ƙasa cike da kwarewa ya sake dawowa gabanta ya miƙe tsaye yana dariyar da ɗibar ruwan a hannu ya sake watsa mata a fuskar. Lulu ba haƙuri idan akai saita rama. Hannu takai itama zata ɗibo danta rama ya fisgota ta faɗo ciki. Kokawa suka fara a ruwan yana kunnata da dariya, sai kuma yay mata gwalo yay ƙasa cikin ruwan. Itama da sauri ta nutse ciki ta bisa saikace wasu kifaye…
      Sun jima a cikin ruwan suna nishaɗin su kafin suka fito saboda tunawa da AA shi kaɗai a ɗaki. Bathrobe ɗin da yazo da ita ta saka, sannan taje ta ɗakko masa wata shima. Tun shigarta ɗakko masa rigar ta samu AA ya tashi, dan haka bata zauna jiransa ba ta juya ciki. A ɗakin ya sameta tana cirema AA kaya, yana ganin shi ya shiga miƙa masa hannu dan yanzu ya daina masa ƙiwa. Shima cikin farin ciki ya ɗauki abunsa yana mai sumbatarsa da faɗin, “Oh oh Baban Ammah ya tashi kowa ya ɓoye kayansa kafin a cika musu aiki”.
Cikin dariya Lulu tace, “Aikam dai, dan yanzu zai fara haɗa gwaramar tasa”.
“Ai ke ya gado, dan Uncle Yousuf ya cemin kema kina ƙarama hummm”.
A shagwaɓe ta ce, “Shi Uncle You ɗin ya faɗa, ni dai ALLAH babu ruwana salaha da ni, sai dai kai dan dama Ammah tace tasha rashin jin ka”.
Shima fuskar ya ɓata da faɗin, “Sharri ba haushi zanji ba ai” daga haka ya nufi bedroom da AA a kafaɗa domin yimasa wanka. Dan yanzu in har yana gida kusan komai shikema yaron, acewarsa yana koyane koda ta haifo ƴan uku basai sunje neman Nanny ba. Takan hararesa kawai idan yace hakan…..

      ★ Zaune suke a wajen cin abinci yana cin abincin da tai masan idanunsa a lumshe alamar dai yana jin daɗin sa, itako sai murmushin farin ciki takeyi. Dan a yanzu babu abinda ke sakata a farin ciki sama data gansa cikin farin ciki. Batai zaton zaici abincin haka da yawa ba, sai gashi ko yaci sosai har yana faɗin jikinsa yay masa nauyi. Bayan ya kammala ta gyara wajen suka koma falo. Zama yay yana wasa da AA ita kuma ta kwashe kayan da ya shigo da su zuwa ciki, na kitchen kuma takai kitchen. Sosai taji farin cikin ganin kayan sakawa ne ya siya mata, sai turarruka na mata masu daɗin ƙamshi duk da tazo da su khumra da turarrukanta abinta. Sai kayan kwalliya da batazo da su ba, shima AA an saya masa nasa. Tana cikin kwashe kayan taci karo da camara. Tsai tai tana kallo da jujjuyata a hannu, sai kuma ta ajiye cikin taɓe baki ta cigaba da gyara kayan. Sai da ta kammala tsaff ta ɗauka camara ɗin ta koma falo da ita. Kwance yake a ƙasan carpet yana waya da Ahmad, AA na gefensa yana wasa da kayan wasansa, yanda ya nutsu sosai ya tabbatar mata da magana suke mai muhimmanci, dan haka ta kai zaune Camara ɗin a hannunta tana kallonsa shi da AA ɗin cike da jin farin cikin su ɗin duk nata ne fa. Abinda ya ɗan fara jan hankalinta ga wayar tasa shine kalmar daya ambata cikin yanayin ɗan ƙaraji har yana tashi zaune. Sosai ta zuba masa idanu, yayinda shi kuma ya cigaba da faɗin, “Kaga Ahmad relax please. Karka ruɗar da kanka, ni dama nasan dolene wannan binciken ya tono mutane da yawa a ciki, aiba abin mamaki bane ba hakan karma ka tada hankalinka a banza. Yanzu abinda zamuyi shine dole mu tafi mataki na biyu, wato plan B.”
        Cikin matsanancin ruɗani da ga can Ahmad ya ce, “Dole ne hankalina ya tashi Aliyu. Mahaifin aunty Khadijah fa! Kasan kuwa yanda nake ganin mutunci da kimar mutumin nan, amma ace har da shi a cikin mutanen nan. Kasan kuwa irin muggan miyagun kwayoyin da yaron nan ya sanar min ana saidawa a pharmacy ɗin nan! Ban taɓa sanin haka ƙasar nan tamu ta lalace da rashin doka da bin ƙa’ida ba sai yau. Innalillahi wa-inna ilaihiraji’un”.
        “Humm Ahmad kenan kana wasa da mutanenmu. Abinda yasa kake ganin irin waɗan nan abubuwan abin mamaki saboda rayuwar daka tashi ne. Amma mu da aka haifa a getto eria muka rayu a ciki munsan irin waɗan nan abubuwan fiye da yanda kake zato, kawai dai mutum dan baida ƙarfin ɗaukar matakine shiyyasa. Ni dai abinda nake so da kai yanzu dolene fa ka sake ƙara ɓoye kanka, dan ko Yaya Hameed da Uncle Yousuf ban san susan da hannunka a ciki, shiyyasa ma kaga nace Uncle Yousuf ɗin yabar komai a hannuna shima saboda suma suna huɗɗa da mafi yawan manyan ƙasar, zamu iya zuwa gaɓar da al’amarin wani zai girgizasu su buɗe mana aiki”.
        “Hakane Smart na fahimceka yanzu, kuma in sha ALLAHU zamu basu mamaki, tabbas mune matasa ya dace muyi hanƙoran gyara ƙasar nan tamu akan wannan mummunar safarar dake cigaba da yaɗuwar gurɓatamu tamkar wutar jeji a kasarmu, in ba haka ba sai anzo lokacin da babu wani matashi da zai iya amfanar kansa balle wani ko ƙasar, zasu cigaba da mana illa ta hanyar dafe madafin iko su barmu da raɗaɗin shan miyagun ƙwayoyin da suke mana safara mu kuma muna sha da tunanin rage raɗaɗi, wlhy Smart naji na tsanesu, natsanesu, su azzalumai ne…..” Kukan da ya tahoma Ahmad ya hanashi ƙarasawa, shiru kawai Smart yay yana saurarensa shima zuciyarsa na ƙuna. Tuni idanunsa sun gashe zuwa jajur. Yana jin raɗaɗi fiye da wanda Ahmad yake ji, tun yana yaronsa ya tsani shaye-shaye, baya son yaga anayi, yana jin ciwo matuƙa idan yaga matashi ya lalata rayuwarsa da shaye-shaye, shiyyasa cikin ƙanƙanin lokaci al’amarin Lulu yay tasiri a zuciyarsa. Da ƙyar ya iya furta, “It’s okay Ahmad. Kuka bashi ne magani ba, aiki tuƙuru domin ganin mun karya su. Sannan inaga dolene zamuyi amfani da ƙungiyar Mawaddat a wannan gaɓar domin tattarro hankalin matasa dan wannan aikin yana son taron dangi ne. In ba hakaba zaƙulosu da muka ɗauka ɗammarar yi bazai magance mana matsalar ba tunda zasu iya sayen hukumomi da kuɗi kasancewar wasu a cikinsu suma ruɓaɓɓune”.
        “Tabbas haka ne nima nayi wannan tunani, kuma na yarda da shawarar nan naka. Sai dai yanzu ban san yaya zamuyi ba tunda kaga ita tana nan”.
    Cikin ɗan ɓata fuska da kallon Lulu ta gefen ido ya ce,,……✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Leave a Reply

Back to top button