Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 12

Sponsored Links

******
Sauran ruwan zafin lipton da Ababa yasha shayi aka basu babu bread haka suka shanye zallar ruwan zafin da ko sugar baijiba sukai shirin makaranta suka fice.

Suna fita yauma tafiya kadan sukai motar Bilal daya kwana dasu a ransa baida sukuni ta tsaida mashin dinsu a kunyace suka sauko sbd overload dinsu ba kyan gani itace a tsakiya sun matsu iya matsuwa suda mai mashin dayake jin tudun kirjinta wanda kusan hakan suke zuwa makarantar kullum babu ranar da har akai makaranta ba cikin baqin ciki da quncin yanda jikinsu ke manne dana mai mashin din ba.

Shi kansa Bilal dake cikin motarsa qarewa yanayinsu dana mai mashin dain yayi yaji wani irin abu ya tokare kirjinsa musamman yanda kowaccensu dazata sauko kusan daida jikinta dana mai acaban ya hadu.

Rufe idanuwansa yayi ahankali tareda dauke kai daga kallon gurin glass ya aka sauke drivernsa ya miqawa mai mashin din 2k yace ya wuce kawai.

Drivern da kansa ya fito ya bude musu bayan motar suka shiga sbd Sir bilal din yana seat din gaba.

Suna shiga aka bar anguwar dasu babu wanda ya iya magana acikinsu bayan gaisuwar da sukai masa cikin girmamawa da nutsuwarsu dake sake samar musu da gurbi a zuciyarsa.

Hanyar asibiti suka nufa kai tsaye
Yau babu bata lokaci dubata akai aka canja dressing din qafar wanda suna kama hanyar gida suke ciresa su yar sbd kada a gani.

Ana gama dressing gurin aka bata magani tasha suka fito ya ajiyesu makaranta bayan yasa akawo musu abinci daga restaurant dinsu na Kaante hotel and suites.
Suna fitowa first lectures dinsu aka kawo musu abincin har kofar hall dinsu sumayyah din sbd Sir bilal ya sanar dashi hall din dazai sameta tinda ba waya ne dasu ba.

Sumayyah ganin mutane dakuma tsoron jawa kai attention yasa ta karba da sauri tabar gabansa ta nufi gurin Benazir da itama tsoron ganin abincin yasata jan sumayyah suka bar cikin mutane.

Nesa da mutane suka boye suka zauna tareda zubawa ledojin ido hankalinsu tashe sbd zuwa lokacin har ga Allah taimakon ya ishesu tinda sumayyah din tasamu sauki ba laifi.

Har aka tashi basu ci abincin ba suka fito saiga driver yana jiransu a gate suka dauke kai suna shigewa mutane sbd kada ya gansu amma haka ya ringa binsu yana sanar dasu Sir bilal yace kada abari su hau mashin.

Benazir kaman zatai masa sujjada ta ringa rokonsa ya dena binsu shima kaman zai musu sujjadar ya ringa rokonsu akan umarnin mai gidansa ne.

Sumayyah datafi shiga tsoro tana kalle kalle tace su shiga kada wani yagani tinda ba tafiyar zaiyi ba.

Haka suka iso anguwarsu kaman zasuyi zawon kayan cikinsu sbd tsoro.
Yana ajiyesu suka fito qafafu na rawa suka nufi hanyar gidansu suna waiwaye sbd ledan dake cikin hijabansu.

Yauma cikin saa Hande bata tsakar gida sukai saurin isa daki.

Na yau basu ci ba sbd yanada qamshi zaa iya jinsu dan haka suka boye cikin kayansu sai tsakar dare suka tashi yunwa na neman kashesu suka hau ci kaman wainda sukai shekaru ba abinci.

Suna gama ci ko ruwa kasa fitowa su sha sikai sbd fargaba dan haka a hakan suka kwana yauma ledojin a cikin jikinsu suka kwana dasu.

Anne da sukaiwa bayanin Abinda yake faruwa tsorone yafara shigarta sbd ranar ra zaa ganesu take tsoro dan kuwa ranar ruwan masifar fa zaayi a gidan hakama shi kansa mutumin dake taimaka musun Ababan ba barinsa zaiyiba da balainsa dan haka ta ringa musu nasiha da gargadin su kiyaye su nesanta kansu da abinda zai qarasa kashe musu dan kwanciyar hankalin dasuke samu wasu lokutan idan masifar Ababa da hande ta kwanta.

Tamkar wanda aka wajabtawa haka Alh bilal kaman yanda su suke fada yafara sauya rayuwarsu daga wahalalliyar azababbiyar yunwa,
Kullum sai ankawo musu abinci a boye suke karba suna isa dashi gidan sunaci su da mahaifiyarsu wadda a yanxu ciwon yunwar daya gama cinye hanjinta yafara dan sakewa sbd a baya haka take kullum a mokade kaman ledar da aka jefa cikin tafasasshen ruwa.

Aduk sanda suke shigowa da cin abincin cikin masifaffen tashin hankali da firgici mai tsanani sike cinsa su gama dan kuwa sun sani na lahira sai yafisu jin dadi duk randa mummunan tsautsayi yasa kaddarar tonan asiri ya kamasu.

Shi kansa Alh bilal din daya sake fahimtar yanayin da suke ciki na ba qaramin taimakawa abincin ke musu ba daya fara fahimtar yunwar dake tareda sumayyah tafara sakinta kaman yanda likitan dake dubata yafada sai ya dage da ciyar dasu din a boye ta yanda shima nasa familyn basu san rayuwar daya jefa kansa ba.

A yanzu da ya zama kaman biyayyarsa shima kusan tilas ce garesu sbd kyautatawarsa garesu sai ya zama wani irin girma da darajarsa suke gani gashi shima din sai ya dena tinkararsu kai tsaye cikin mutane sbd fahimtar suka tsananin shiga firgici da tashin hankali idan yayi hakan dan haka haduwarsu sai ya zama a sirrance sukeyi.

Hawa Mashin din zuwansu makaranta daya tsana fiyeda komai sai ya siya musu napep kai tsaye sbd kaisu kawai da daukosu tinda basa son shiga motarsa koyaushe suka shiga cikin yanayi na mummuna suke dan haka wanda ya bawa napep din aikinsa kawai kaisu da dauko su.

Da farko tsoron hakan sukeji sosai sbd basu san yanda zasiyi da kudin mashin din da ake basu ba,
Basu iya boye kudi ba sbd ko sun boye basu san me zasiyi dashi ba tinda basu taba sakawa ransu tinanin guduwa subar gida ba bare su ringa boye kudin gashi idanma sun gwada boyewan tinda suka fara zuwa makaranta akai akai Ababa ke sawa hande tana bincikesu da kayansu dan haka basu taba tinanin boye wani abin ba ko ba kudi ba
Abincinmq dasuke shigowa dashi dan suna cinyewa ne a take dasun shigo dashi, dan haka kaman yanda Allah ya kawo musu mai taimakonsu a boye sai suma sike bawa wani tsoho makaho kudin a hanyarsu ta tafiya kullum sbd baida kowa shima yana cikin mawuyacin hali.

Tsohon daya gama wanyewa dasu kullum shima a duk lokacinda ya bude bakinsa Benazir yakewa addua sbd itace mai fitowa ta basa,
Adduarsa kullum Allah yakaita matsayinda bata taba tinanin zuwaba tareda rayuwa mai Albarka da kwanciyar hankali tareda zuria dayyaba.

Exams dinsu aka fara dan haka hankalinsu ya rabu sbd kowa karatunsa yake kokarin maida hankali akai musamman Benazir sbd lectures da dama data ringa rasawa a lokutan sbd sumayyah da ciwon datayi bayan nan dan haka idan suka shigo makaranta sumayyah bata sake ganinta sbd Sosai karatunta ya samu ci baya shiyasa ta dage sosai kafin ta fadi Ababa ya kusa kashesu su dukan gwara a samu mai taimakawa wani acikinsu.

Sumayyah da kanta ya daure matiqa sbd exam din farko da suka fara babu abinda ta gane sunanta kawai ta rubuta sai questions din data maimaita masa a booklet bayan question daya babu abinda ta amsa said ta fito idanuwanta cike da hawayen tausayin kanta da yanda rayuwa zatai mata idan ta gama shekarun nan biyu duka a fail,
Wane mataki Ababa zai dauka akanta?
Siyar da ita zaiyi ga ‘yan qwaya da gaske ko me?

Inda suke zama ta nufa ta zauna ahankali tana sauke kanta qasa dukkanin jikinta na mutuwa hakama tsoron dake mamaye zuciyarta na qara bayyanuwa a kan fuskarta.

Haka ta jima a gurin tana saqa da warwara cikin damuwa har lokaci yayi suka sake shiga wata exam din nan ma kusan biredi ne ke dukan fanke bata tsinano abin arziki ba dan haka wannan karon tashin hankalinta da tsoronta qaruwa yayi sbd azabar datasha wancan karon data fadi exams din a hannun Ababa.

Tana fitowa kasa riqe zuciyarta tayi taje maboyarsu ta zauna hawaye na tsiyayo mata ta saka fuskarta tafin hannuwanta tana sakin kuka mara sauti gashi bazata iya fadawa Benazir ba ta sakata damuwa nata karatun ya fita kanta,
Bazata so hakan ba sbd ko yayane tanason Benazir ta samu kammala karatun da sakamako mai kyau.

Tana gurin zaune har yamma Benazir ta gama suka tafi gida a napep gurin komawarsu Benazir ta lura da yanayin Sumayyah din ta tambayeta exams dinta.

Kasa magana Sumayyah tayi sbd hawayen dasuka cika idanuwanta kafin tayi wata magana Benazir ta fahimci komai cikin damuwa da tausayin yar uwarta tayi shiru ta kasa cewa komai sbd itama tasan suna dagewa ne suyi karatun sbd azaba da hukuncin Ababa,ita kanta idan ta tina da azabar da zata biyo bayan faduwa jarabawar tashi hankalinta keyi bare Sumayyah data dandana azabar hukuncinsa na faduwan.

Shirun Benazir yasa hawayen sumayyah saukowa tana rufe fuskarta da hannuwanta sbd kukan dayake zuwar mata zuciya a karye.

Har suka isa gida kuka sumayyah din keyi itama Benazir kukan zucin takeyi jikinta a mace,
Mai napep na jiyesu suka nufi hanyar gida sumayyah na goge hawayenta dan kada hande ta gani wani masifar ya biyo baya.

Sulaiman drivern napep dinsu na aje su wayarsa ya fidda ya nemo numbern Alh bilal ya saka kira sbd umarnin daya basa akan duk yaga matsala ko damuwarsu ya sanar masa.

Kai tsaye ya sanar masa suna cikin wata matsalar sbd Sumayyah nata kuka har suka isa.

Shiru Alh bilal din yayi sbd yana tareda Mahaifinsa a lokacin.

Dan numfashi ya sauke ahankali tareda bude baci yace

“Ok shikenan idan na samu time zan kira naji qarin bayani.”

Kashe wayar yayi tareda ajiyewa gefensa yana qin kallon mahaifinsa sbd zai iya tambayarsa daga ina ne kiran.

Kallonsa Alhaji DAUDA KAANTE yayi sbd yasan Bilal din da zurfin ciki yanzu haka wata matsalar ce dan haka kai tsaye ya gyara zamansa kan lafiyayyar luxury couch din dayake kai cikin babban palonsa dake Kaante Mansion yace

“Da matsala ne?”

Dagowa Alh Bilal yayi ya kalli Dad Kaante yana basar da tinaninsa akan zancen kukan sumayyah yace

” ba komai bane wani yaron dana sa aka dauka aiki ne ya kira.”

Basar da zancen Dad kaante yayi cikin manyanci irin na wanda tarin arziki yagama hudawa tako ina komai a hankali kwance ba sakawa hayaniya sai ciwon kai da ‘dayan ‘dansa yake sakar masa wanda idan ba DD kaante din ba babu wanda ya isa tayar masa da hankali ya sanyasa shiga tinani.

Kallan hoton DD din da shi kadaine hotonsa ya isa a maqala a palon Dad kaante din dana Oga kwata kwata wato kakansu shugaban family din gabaki daya wanda shine Asalin Kaante din wato Dalhat kante.

Shi kansa Alh bilal hoton DD din ya kalla kafin ya sauke ajiyar zuciya cikin nutsuwa yace

“Dad insha Allah zan gwada masa magana zai dawo ko zuwa qarshen watan nan ne”

Numfashi mai dumi Dad kaante din yakuma sakewa a karo na ba adadi sbd ya rasa tayaya DD yake iya sakar musu pressure,
Tayaya zai dauke mahaifiyarsa da qanwarsa sama da watanni Shida suna gurinsa Zurich,
Meyasa bazaiyi tinanin anan din yaya ake ji babu su din ba,
Ina matsayin mijin Mahaifiyar tasa kuma mahaifinsa dana qanwar tasa daga zuwar masa ziyara ya riqesu,
Sam baya duba bacin Raina dana DD babba akan hakan koyaushe mahaifiyarsa kawai ya sani.
#MAMUH#
#DD KAANTE#BILLONAIREROMANCE#Contrct
#BENAZIR#MARRIAGE#LIFE

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-FURAR DANKO
Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at
09033181070
09032345899

Zafafa🫶🔥🔥

Leave a Reply

Back to top button