Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 28

Sponsored Links

028
___________________
Yareema Abbad yau bai fita ko’ina ba,don haka ya zauna ƙarƙashin rumfar da yike shaƙatawa can garden ɗin part ɗinsa, Jabeer na hannun damanshi yana can gefe yana gadinsa ,an shaƙe masa fruit a wani tangamemen tasa na sarauta ,sai ruwan matsatsun kayan itace …Jarida yake karantawa as usual Amma deep inside ba jaridar yake karantawa ba face wani irin tunani mai zurfin gaske wanda har ya hardasa masa ciwon kai ɓari guda (Migraine) jin Yana jin juwa² yasa ya ɗauki ruwa ya ɗan sha kaɗan ,ya maida ya ajiye ,ya ɗauki jar tuffan da suke cikin kayan marmarin ya fara gartsa yanaci majestically .

ATHEELAH budurwar shi,and his wife to be ,a sanyaye ta shigo cikin garden ɗin ,bayanta kuyangi ne su biyu suna dafe mata baya ,ɗaya tana mata firfita da faskeken mahucin sarauta ɗaya kuma ta riƙo mata Lema a saman kanta ,Suna shigowa garden ɗin tun daga nesa ta ɗaga masu hannu ,cak sukaja suka tsaya ,kana ta cigaba da takawa ita kaɗai har ƙarƙashin rumfar da yike ,ɗan nesa kaɗan dashi ta tsaya
“Assalamu Alaik” a ciki ya amsa,ya ma amsa ne saboda darajar sallama ,amma hardly in taji .

A sanyaye ta sunkuya tasa gwuiwoyinta a ƙarƙashin turɓayan wajen,bata damu da tsadajjen supern da ta saka na doguwar riga ba.

“Ina neman afwan Shugabana….Yareemana nayi nadama ka yafe mun ,Babbar kuskure ne ƙin russuna maka yayin da kake tsaye…kazalika babbar kuskure ne , Nuna fushina da hukuncin da kayi mun ……

Miƙa hannu yayi ya ɗauki ruwa ya sake kurɓa yana hura hanci.

….Don Allah ka yafemun..nayi Alƙawarin hakan bazata sake faruwa ba”

Saida haka numfashi na wucin gadi kana ya soma magana cike da gadara
“Nasan zaki dawo…Saidai kin taimaki kanki da kika ƙasƙantar da kanki,Da wannan ɗan ƙaramin abun da kikayi na saki kin zama amintaciyyar mata a gareni ,nan da sati ɗaya zaki zama matata, uwargidana kuma sarauniya ta 😊” haukacewa tayi da murna ta juya tana waige² tana neman wanda zai tayata farinciki ,Jabeer na tsaya kansu sai Murmushi yake ,saboda murnar yau yaga walwala da fara’a a fuskar ubangidanshi…yau yareemansa ya nuna affections ɗin sa akan wata mace har ya furta mata magana mai daɗi

“Zoki zauna kusa dani”

Da gudu ta miƙe taje gabansa ta lanƙwashe ƙafa sai ta ɗago ta kallesa sai ta saki dariya tasa tafukan hannunta ta rufe ido ,kamar sabbin ango da amarya.

“Nagode Yareemana ,kuma Sarkin gobe…Na gode daka zaɓeni matsayin mata a gareka ,Nagode mijina I’m so glad to have you a rayuwa na”

Ɗaukan tuffa yayi ya gatsa ya ɗanci kaɗan ,kana ya miƙa mata sauran “Oya muci fruit tare ,Ci sauran 🍎 ɗin Yarima Abbad ”

Amsa tayi tasa bakinta a daidai inda yaci ,ta gatsa tanajin wani garɗi kamar ya sirka apple din da madara

“uhmm yumm yummm,Nagode mijina”

Yanda take zuba masa Surutu cikin nishaɗi ,yasa ya tsura mata ido full of excitement ,Ashe hira da mata akwai dadi

 

 

Oum Aphnan
#BAD BOYS
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_
_Ya haƙurin Abunda ya faru da sayyida?😔To adai ƙara haƙuri guys ,this is bad boys for you guys_

Leave a Reply

Back to top button