Nihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 2

Sponsored Links

💖💖 *NIHAAD*💖💖

 

By _Khaleesat Haiydar_📖✍🏻

Related Articles

 

~~

 

Dumbin gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga iyayen gidan Khaleesat’s Palace, my die hard fans🥰😍 Su Hajjaju Chamo me gwala-gwalai duk da jarin ya karye amma take ta bobboye mana, Hajiya Aunty Zahra mai siyar da harawa, Hajiya Nafisa Mom twins, Su Hajiya Aunty Maryam, Uwar Nabeela, Mrs Jay, Hajiya Inna, Hajiya Deejah, Hajiya Zeenaru, Nanisa Zero Zero, Hajiya Bilkisu, Hajiya Rabia, Damsel, Uwar Yusrah, Ummu Zainab, Uwar gidan Barrister wato Khaleesat me siyar da tayoyi, kai duk wanda bai ga sunansa a nan ba ya biyo ni da sunan xai gansa a next page😜 amma fa ko kun ki ko kun so sai nayi sharing link dinku, ku tanadar ma sabbin fans ruwa da cin cin ehe.🤓

 

Da daddare Abba na xaune parlonsa tare da Yayansa Alhaji Abubakar…. Alhaji Abubakar yace “Ae duk ba sai ka sanar masu komai ba, kawai gobe idan an daura auren kowa ma sai ya sani, i don’t think u owe anybody explanation to this” Abba ya numfasa yace “Toh shikenan” Alhaji Abubakar yace “Yea i think that’s okay ba sai kace ma kowa komai ba for now, a ina kace xa su xauna? I mean which of ur houses are they staying?” Abba yace “I don’t think i can keep her where she will in any way feel comfy, i wish xai koma can karkarar tasu su xauna in basa enough jari, idan noma xai yi ma yayi employing workers su yi masa a can ko ni xan dinga biya, cause i want her to learn a bitter lesson of her life, ina son ta san wata rayuwar bayan rayuwa cikin daula” Alhaji Abubakar ya girgiza kai yace “No… There is no need for all that, duk abinda ya kamata kayi kar ka fasa, ka basu inda xa su xauna comfortably” Bayan Alhaji Abubakar ya bar gidan, Umma ta shigo parlon Abba, ganin basu ta6a abincin da ta ajiye masu ba tace “Haba yallabai, ko abincin baka ci ba har yanxu?” Abba yace “Kawai ayi min black tea” Umma tace “Toh shkkn” Tashi tayi ta dau abincin ta fita, ba a dau lkci da fitarta ba Farooq ya shigo parlon, waya ya tadda Abbansa ke yi, wanda da jin yanda yake amsa wayar kasan magana ce aka kirasa a kan Nihad kuma abokinsa ne me kiran nasa, Farooq ya sunkuyar da kansa duk jikinsa yayi sanyi, har Abba ya gama wayar ya jinginar da kai da kujera bai ce masa komai ba, a hankali Farooq ya dago yace “Barka da dare Abba” Abba ya amsa, Farooq yace “Throughout ina ta kiranka but couldn’t reach u on phone” Abba yace “Ehh wata er tafiya nayi, is there any problem?” Farooq yace “Ya gajiyan hanya” Abba yace “Alhamdulillah” Farooq yayi kasa da murya yace “Abba magana ce dama a kan Nihad?” Dai dai nan Umma ta shigo da mug din black tea dake ta kamshi, Da hannu Abba yayi masa alamar ya aka yi, Farooq yayi shiru, Abba yace “Maganar me a kan Nihad Umar?” Farooq ya d’an fara kame kame, sai kuma dai kawai yace “Abba a kan auren nan da aka ce ne, is it not better a yi hakuri a janye, idan ya so…” Dakatar da shi Abba yayi yace “Idan wannan maganar ce ta kawo ka, ka je kawai i need rest Umar, kaga ban dade da shigowa gidan ba” Umma dai na xaune kan one sitter, pleadingly Farooq yace “Pls ka saurareni Abba” Abba yace “I said i need rest….” Umma tace “ka je yace xai huta ko kuwa?” Mikewa Farooq yayi ya fice daga parlon, Umma ta kalli Abba tace “Kayi hakuri Yallabai, xan so ka cire wannan damuwar a ranka, in sha Allah everything will be alright, kar kaje ka sa ma kanka wani ciwon bayan hawan jinin da kake fama da” Abba yayi sigh yana girgiza kai yace “A kalla ba a kirani a rana ba xa a kirani sau goma a kan Nihad, the video is trending day by day…. Me yafi wannan bakin ciki Sumayyah? A reputable person like me, noo Nihad tayi tarnishing image din gida na” Da damuwa Umma tace “To ya xa ayi Yallabai haka Allah ya kaddaro mana, sai dai kawai mu rungumi kaddara, amma akwai wani malami bawan Allah, tun ranan da abun ya faru Hajiya Sukhaina tace ko shi xa ayi ma magana yayi addu’a Allah ya kawo karshen trending din abun, shiru xaka ji kamar ba ayi ba wllh, neman video din ma xa ayi a rasa” Abba ya mata wani kallo yace “Malami? Wani irin malami?” Umma ta gyara xama tace “Ba boka fa nace ba Alhaji, amma dai shkkn kawai, ina ce akwai malamai bayin Allah wa enda…” Mikewa Abba yayi bayan ya dau mug din black tea dinsa ya wuce daki ya kulle kofa. Washegari friday ana sauka sallan juma’a, Abba ya tafi tare da yayansa da cousins dinsa biyu xuwa garin da aka daura ma Nihad aure, a kan sadaki dubu hamsin wanda shi ya bayar. Sai kusan la’asar suka dawo gida, nan kuma ya sanar ma Umma su fara shirye shiryen kai ta, Umma tayi shiru cike da jimami, sai kuma ta sauke ajiyar xuciya tace “To wani gidan kenan xa a kai ta yallabai?” Abba yace “Wannan gidan da aka gama na Rijiyar zaki, it’s already furnished” Umma tace “Allah sarki, ina laifin wannan gidan na kusa da mu yallabai, ai xa su fi sakewa a nan…” Abba yace “Ban yi niyya ba” Umma tace “Rijiyar zakin ma yayi ai, Allah ya saka da alkhairi” mikewa tayi ta fita don xuwa sanar ma Mum din Nihad da Yan uwanta dake can bangarenta abinda Abba ya ce, nata side din ta fara shiga, first daughter dinta Kamila na xaune parlon sai second daughter dinta Amina, sannan kanninta mata biyu da suka xo daga Jigawa daxu, Umma tace “To duk ku shirya kai amarya an daura mata auren yau dai” Kamila ta riƙe ha6a tace “Har an daura?? yanxu Umma Abba bai fada maku da wa aka yi auren ba, ni kawai sai xuciyata ke bani Hamid ne ko Saif” Umma ta saki baki tace “Hamid? Ita uwar Hamid din karen hauka ya cijeta xata yarda a hada shi da Nihad? Ko kuma shi Hamid din mahaukaciya ne da zai amince da auren Nihad, Kai har shi Uban Hamid din da ya kirkiro auren ba yarda xai yi ayi auren da ɗan sa ba karewa kenan, haka ita ma Innar, wani can dai Abban naku ya samo a karkara, hakan kuma kadai ne rufin asirinta a dai abin nan da ya faru” Amina ta mika ma Umma wayarta dake ring, Umma ta amsa ganin autarta ce ke kira ta daga ta kai kunne da murmushi tace “Hello auta, duk yau kin ji ni shiru ko” lkci daya ta hade rai tace “Ki zo kiyi me kina karatun ki Nihal? A kan wani dalili xaki taho kuna tsaka da karatu? To wllh kar ki fara idan ba haka ba yanxun nan in kira Farooq in gaya masa, me xuwanki xai sa a fasa, bayan har an daura auren ma, duk sanda ku ka yi hutu idan kin dawo sai kije ki ga dakin er uwar taki ba shikenan ba, amma ki wani ce xaki kamo hanya kamar ana yaki” a kufule Umma da ta gama sauraronta tace “To wai uban meye na wannan kukan da kike, so kike ki ja ma kanki wani ciwo ne ko ko? Bata da waya yanxu a hannu, idan na fita yanxu xan bata sai ku yi magana, amma ta ina xaki baro Zaria da yamman nan ba hutu ku ka yi ba, kuma dama kin ta6a dawowa gida ke kadai ne banda gulma da daura ma kai wahala Nihal?? Ni dai sai anjima ban san shashanci” Katse wayar Umma tayi, Aunty Laraba tace “Wai tahowa xata yi daga Zarian?” Umma tace “Ehh wai, kinji wata gulma dai, ko uban me xata xo tayi oho” Aunty Laraba tace “To wai ita tace ma Abban nasu bata son Maryam Abatcan da er uwar ke xuwa ne?” Umma tayi murmushi tace “Aa haka dai yayi niyya ita ya turata federal dai dai ita, ita kuma Nihad dama Private ne dai dai da ita inji uban, wato Maryam Abatcha, option ma ya bata ta xabi Private uni da take so shine ta xabi Maryam Abatcha” Aunty Maimuna tace “Ai ko ga Maryam Abatcha ana ta gani a soshiyal media” Umma dai bata ce komai ba, sai kuma tace “Allah dai ya shirya mana zuri’a kawai” daga haka ta fita xuwa bangaren mum din Nihad, a corridor ta hadu da matan Alhaji Abubakar su biyu sun shigo gidan, suka gaisa da fara’a ana kara jajanta lamarin da ya faru, Hajiya fatima tace “Daxu Abbansu Hamid ya dawo gida yake sanar mana ai har an daura aure, nace shine babu labari ko daga gare ku Hajiya” Umma tace “Wllh abun ne ya xo a haka Hajajju, kinsan muna ta tunanin xa su hakura a fasa auren a nemo wani solution, to kin san halin mazan namu da kafiya, wllh sun ki, kawai fatan Allah ya basu xaman lafiya da ko ma waye mijin” Hajiya Zuwaira tace “Shikenan addu’ar, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi a gareta, Allah kuma ya duba yan baya” Duk suka amsa da Ameen, Umma tace “Mu je dama bangaren Maryam din xan je” a tare suka tafi part din Mumy, bayan an gaisa an kara jajantawa, Mumy dai bin su kawai take da kallo bata cewa komai, Umma ta sanar mata abinda Abba yace sannan ta fita daga dakin. Bayan magrib xa a kai Nihad, kafin Magrib din Abba ya tara gaba daya matan nasa da ‘ya yansa, Usman, Farooq, Kamila, Amina, Nihal ce kawai bata nan a yaran Umma, yaran Mumy kuwa Nihad da kanninta biyu wa enda duk maza ne, daya me shekara tara da kuma me shekara shidda duk basa parlon, Bayan duk sun hallara a parlon Abba ya nisa yace “Ina fatan duk kun ga abinda ya faru da yar uwarku Nihad, Nihad is nothing but a disappointment to the family, kar ku ga Nihad tayi wannan mummunan laifin na bada ita ga wanda nayi niyya without bothering ko ya cancanceta ko bai yi ba, to wllh wllh if anything of such should happen again in my family infact ko wanda bai yi kusa da hakan ba idan ya faru a family dina wllh i will prefer to shoot that person” Umma ta sauke ajiyar xuciya tace “Allah Ubangiji ya tsare, ya kare mana zuri’a Alhaji” Abba ya kalli Mumy da bata cewa komai tun faruwan abun, amma kana ganinta kasan she is heartbroken, her first child, habaa ko bacci bata iya yi tunda wannan lamari ya faru, da tasan Nihad xata girma ta yi irin wnn rashin jin da Allah bai raya mata ita ba, tun faruwan hakan ita ma ta kashe wayarta sbda kiran yan uwa da abokan arziki da suka san Nihad, Abba yayi gyaran murya yace “Ban ga laifinki ba Maryam don ni nasan kinyi iya bakin kokarin ki na ganin kin ba ma Nihad tarbiya yanda ya kamata, u tried ur best, matsalar kawai u didn’t make Nihad ur frnd aside mothering her, amma dai babu komai, kawai dai kafin Nihad ta dauko mana abinda xuciyarmu xai kasa dauka nan gaba tun wuri ni da yayana da yan uwana mun mikata, kusan xance na bada sadakarta” Abba na fadin haka ya ciro sadakinta dake aljihunsa ya mika ma Umma yace “Sai ki damka mata ku da xa ku kai ta” Umma ta amsa cikin sanyin murya tace “Yanxu Yallabai mun yi deserving a bada er mu ba tare da mun san wanda aka ba ma ba? Ai hankalinmu baxai taba kwanciya ba, tun jiya nake bin ka kaki gaya min, ai yana da kyau a sanar mana mu sani don muna da hakkin sani, idan ma ni bani da hakkin in sani mahaifiyarta fa?” Abba ya ɗan yi shiru, sai kuma ya dau wayarsa yayi dialing number snn ya kai kunne, ana dagawa yace “Ka shigo nan parlor ka sameni yanzu” daga haka ya katse wayar, duk kowa yayi shiru ya xuba ido ya ga wanda xai shigo parlon barin Farooq da Umma. Da sallama ya bude kofar parlon, ganin su Umma ya dakata daga bakin kofar bai shigo ba, Abba na kallonsa yace “Karaso” ya karasa shiga cikin parlon kansa a kasa, duk occupant din parlon kallonsa suke with full shock, Abba ya nunasa yace “Shi na ba auren Nihad, shine mijinta” Mikewa Farooq yayi yana kallon Abba baki bude, Mumy ta hadiyi wani kullutu da taji ya tokareta a makogwaro, Umma kuwa sae kallonsa take daga sama har kasa babu ko kiftawa, ta ma rasa yanayin da take ciki ita, Kowa na parlon ya kasa cewa komai, tsabar silence din parlon da allura xai fadi xa a ji karar faduwarsa, shi kam dai yana ta tsaye ya sunkui da kai har sannan, Abba yayi breaking silent din yace “Je ka” Juyawa yayi ya fita daga parlon, Usman ya kalli Abba yace “Haba Dad? Yanxu shi ka aura ma Nihad?” Farooq yace “No Abba, u should have given her a choice, bata yi deserving ayi mata dole ba sbda wannan kaddarar tata, but Abba….” Kasa cewa komai yayi ya koma ya xauna, shi ma ya rasa yanayin da yake ciki, but he don’t think it’s still bad after all, just dat…. Girgiza kai kawai yayi, Umma tace “Haba Alhaji….” Abba ya mike yana bin kowa da kallo yace “No one have the right to query my authority” Yana fadin haka ya bar masu parlon ya shiga bedroom dinsa, suka dinga kallon kallo a tsakaninsu a parlon, Usman ne ya fara mikewa ya fice daga parlon, Mumy ta mike ta bi bayansa ita ma tana share idonta, Umma ta sauke ajiyar xuciya tana kallon Farooq, ita gaba daya ma kanta fa ya kulle, Abba really took them unaware, jinginar da kanta tayi da kujera Farooq ya mike ya fice daga parlon shi ma. Ana idar da magrib yan kai amarya suka fara shirye shiryen kai ta, Nihad bata ta6a shiga irin tashin hankalin da take ciki ba a wannan moment din, ko video dinta bai tada hankalinta kamar yanxu ba, gashi nobody is there to console her, Nihal na schl, Husnah kuma taki xuwa gidan sbda Farooq, gashi bata da numberta a kai balle ta amshi wayar wani ta kirata, su kamila da Amina tamkar ma farin ciki da abinda ya sameta suke don uban kwalliya suka ci har da kashe dauri Hajiya Zuwaira ce ta kai ta gun Mumy tayi mata fada ta sa mata albarka, sbda takaici da bakin ciki Mumy ta ki cewa komai daga karshe da aka tilastata sae cewa tayi Allah ya tsare, Alhaji Abubakar ne kawai yayi mata fada, Abba kuwa tun da aka idar da magrib ya ki shigowa gidan dama, a haka dai aka tattara ta da akwatunan kayanta uku wanda Umma da Kamila suka hada mata wasu kayayyakinta a ciki, kuka take kamar xata shide, har addu’a ta dinga yi Allah ya dau ranta kafin a karasa da ita gidan, tana ganin an shiga gidan ta kara sautin kukan da take a haka har aka shigar da ita daki, gida ne bungalow madaidaici me dakuna uku, ko wani daki da bandaki, sae bandakin dake parlor sai kitchen, anyi furnishing gidan babu laifi sai dai furnitures din ba masu tsada bane, Nihad ta dinga kuka tana cewa ta shiga uku, masu bata bakin ma har sun gaji sun daina, karfe tara saura suka fara shirin tafiya, Nihad ta rike hannun Kamila cikin kuka tace “Aunty ynxu tafiya xa ku yi ku bar ni, don Allah kar kuyi min haka…” Kamila tayi dariya tace “Ae ko dole xa mu yi maki haka tunda mun kawo ki gidan mijinki kinga ni ynxu sae na koma xan dau jakata inyi driving xuwa gida, kawai kiyi hakuri ki bi mijinki ku xauna lafiya ko hakan xai goge wannan ta6on da kika ma kanki” Daga haka ta fice daga dakin don dama ita ce karshen fita, Nihad ta silalo kasa ta xauna tana kukan takaici, tana jin duk suka fice daga gidan ta daina jin hayaniyar kowa, nan kuma tunanin ta ya tafi gun wanda xata gani a matsayin mijinta, tsoho ne, yaro ne, baki ne, fari ne, kato ne, siriri ne, mummuna ne, kyakkyawa ne, infact duk wannan tunanin ne suka baibaye ranta gabanta ya dinga faduwa hankalinta ya kara tashi, daga karshe ma daina kukan tayi banda bugawa babu abinda xuciyarta yake, ta fi minti ashirin a haka taji an bude gate, da sauri ta mike ta tafi gun window ta bude labule amma sai taga ba ta nan gate din ma yake ba balle taga me shigowa, komawa tayi ta xauna can karshen gado tana jin yanda kirjinta ke heaving, to waye wannan da ko mota ba shi da, bayan wasu mintuna taji an shigo parlor, daga karshe ta ji kamar an bude wani daki an shiga, mikewa tayi ta jingina da window with so much fear, har ta gaji da tsayuwa bata ga alamar xa a shigo dakin ba, komawa tayi ta xauna gefen gado, a kan idonta karfe sha daya tayi, bacci take ji amma taki kwanciya sbda fargaba, kafin sha biyu bacci barawo ya saceta. Ba ita ta bude ido ba sae da hasken rana ya sauka saman fuskarta washegari da safe, a firgice ta mike xaune, sae kuma ta sauka daga saman gadon ta shige bandaki da sauri, bayan ta idar da sallah ta mike a hankali ta nufi kofar dakin ta bude ta fita xuwa parlor, ta dinga bin ko ina da kallo xuciyarta na bugawa, kofar da take tunanin kitchen ne ta nufa ta bude kofar a hankali, wani kara ta saki ba tare da ta shirya ba ganin mutum a tsaye yayi backing kofar kitchen din ga ruwa ya daura saman gas, juyowa yayi suka yi ido hudu da ita, wani irin shock ne ya bayyana a fuskarta ta dinga komawa baya tana kallonsa bakinta ya kasa furta komai, can ta nunasa da yatsa nan ma words suka yi failing dinta, juyawa yayi ya kashe gas din don ruwan ya fara tafasa ya juye cikin mug sannan ya bi gefenta ya fice daga kitchen din ba tare da ya sake kallonta ba, makalkalewa tayi jikin kofa jikinta na 6ari tana ganin abun kamar a mafarki, sae a sannan bakinta ya bude ta fasa wani raxanannen ihu, sai kuma ta fara ganin kitchen din na juya mata lkci daya ta sulale kasa….

 

_8 months earlier_

Contact me directly via👇🏻 to gain access to the book

07087865788 ✍🏻

Leave a Reply

Back to top button