Sakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 1

Sponsored Links

 

📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️

 

بسم لله الر حمن الر حيم…

2:03 Pm.

Friday 4 February 2022.

 

*SAKAYYAH*

*GARKUWA SABON SALO*

Book One, page 1

NA

*AYSHA ALIYU GARKUWA*

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

*FREE PAGE*

 

*Komai na rayuwa sai Allah ya nufa, kugafa  Time and Date din da na fara rubata littafin nan amman sai Allah ya bani ikon fara sakinshi.*

 

 

Wannan littafin nawa mai suna FATTANAH kirkirerren labarine, Amman akwai wasu abubuwan dama da sun faru da gasken gaske, banyi da wata ko waniba, Hakkin mallakarsa nawane AYSHA ALIYU GARKUWA, ban aminceba! ban lamunceba!! ban yardaba!!! ayimin amfani da labarin littafina tako wacce sigaba, har sai in an nemi izinina an samu sahalewata, sabida haka ga number ta 09097853276 kafin ayi komai a nemi sahalewata, komai yafi daɗi cikin mutuntaka zama lfy yafi zama ɗan Sarki!!!..

 

*Yah Allah ka bani ikon rubuta al’khairai da abinda zai amfani al’ummar fiyeyyen halinta, Ya Allah kayi riƙo da hannayena, tunanina, idona, yatsuna, nazarina, ka hanani samun damar rubuta duk wani abin ƙi da zai zamewa al’ummar musulman masifa ko ƙazanta ko bata tarbiyya, ya Allah ka bani ikon tunasarwa da jan kunne da jan hankali ih zuwa ga nasarar mai tawakkali da imani da riƙo da ibada, Ya Allah ka nuna min ƙarshen littafin nan lfy kamar yadda ka nuna min forkonsa Lfy dani da iyayena ƴaƴana, yayuna, ƙannena, da maƙota makaranta na masu biyana kafin su karanta da masu karanta na sata da dukkan musulmai ya Allah ka nuna mana forkonsa da ƙarshensa lfy kayiwa rayuwarmu data ƴaƴan mu al’barka ka shirya mana ahlinmu ka bawa yayanmu mata maza na gari, mazan ka basu mata na gari, aurarru ka basu zaman lfy da zuri’a ta gari ka tsare mana tarbiyar yaranmu bisa tafarkin dai-dai.  Ya Allah kayi mana rufin asiri duniya da ƙiyama, ya rabbil izzati ka dubi bayinka masu buƙatan haihuwa da aure da idanunka masu rahama ka basu masu albarka, marasa lfy Allah ka basu lfy masu juna biyu Rabbi ka sauƙesu lfy masu fama da matsar babu da bashi ya Allah ka yalwata masu ka basu arziƙi mai albarka la basu ikon biyan bashi, Ya Allah ƴaƴan musulmai da tatbiyarsu ke a gurɓace Allah ka shiryesu. Ya Allah ka kawo mana sauƙin wannan zadar rayuwar, ka magance mana fitintinun dake damun ƙasarmu, mahajjatsnmu kasa sunyi hajji Mabruk. al’farmar Annabi da al’ƙur’ani, ya Ubangijin talikai ka jiƙanmu ka yafe mana kurarenmu kayi mana Kekkyawar ƙarshe kasa mucika da kalmar shahada yayin barinmu duniya ka sadamu da mala’ikun rahama masu zaran rai salamun salaman. Yah hayyu ya ƙayyum birahamatika astaƙisu ka jiƙan mahaifiyata Fatima (Deddena) ka sanyaya mata makwanci ta ka haskaka mata ƙabarinta ka yelwata matashi  ya Allah kasa tana cikin dausayin jannatul firdausi ya ubangijin kasa can yafi mata nan, ya Allah ka bamu haƙurin da juriyan rashinta. Ya Allah kai mata rahama al’farmar Annabi da al’ƙur’ani🙏🏻😭😭😭*

 

~Aisha Alto, Mom Bobo, kune wanɗa nake ganin kamar kunsan ciwon da nakeji a raina a duk sanda na tuna banda mahaifiya, domin kusan lokaci daya muka rasa iyayenmu. Allah yayi musu rahama yasa sun huta, ina tunawa a lokacin nafi son yin mgn daku fiye da kowa a social media, domin gani nake kun san yadda nakeji a zuciyata, Aisha Alto addu’o’in da kikeyi min dani da mahaifiyata yasa nakejin ke ta dabance mom bobo kuwa munsha kokawa tare, mu rasa mai lallashi wani tsakaninmu~

 

 

*Littafin SAKAYYAH na kuɗine 1k ne kacal wannan Free page, yar uwata ki biya ki karanta abinki cikin Salamah 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. In baki da account zaki iya bada a P.O.S ki Basu 100 na su turo 900 wasuma 50 suke amsa, ko kuma ki sayi katin Mtn sai ki copy number’s ɗin katin ki turo min ta WHATSAPP. Banda V.T.U. dan Allah.*

 

 

A hankali ta turo ƙofar ɗakin nata, cike da jin nitsuwa da salamar, sanin ta yanke baccinta ne ta tashi cikin talatainin daren, domin neman aminci da yardar ubangijinta daya halincceta ya bata rai da lfy, cikin rashin tsoron da ko yaushe in ta tashi tsakiyar dare, Allah ke yaye matashi, duk da kasancewar makaken gidane bila haddin wanda ke kewaye da tsirrai, kana ga wutsiyar kogin Gembulan na jihar Taraba da yayiwa gidan zanen harafi C, yayinda kuwa su biyu ne rak suke rayuwa a cikin ƙaton gidan.

Koda yake tazarar dake tsakanin ɗakinta da sade ɗin jikanta Modibbo tazarace mai yawan gaske, sai dai suna raya gidan da Ambaton Allah a koda yaushe, shiyasa ubangiji yake saukar musu da cikekkiyar nitsuwa salama.

 

Numfashin ta fesar a hankali tare da gyara ɗaurin zaninta,  kana ta gyara riƙon da tayiwa yar butar dake hannunta.

 

Ido ta lumshe tare da buɗe su a hankali, sabida wani irin sassayan iska mai masifar daɗi da ratsa jiki da taji yana ratsata da sakar mata wani irin nitsuwa, salama, da farin ciki.

Juyowa tayi ta kalli yamma sabida ganin wata ta faɗi alamun dare ya tsala, domin watan tayi kwana goma sha ɗaya ne, faɗawanta ke nuni da biyun dare ko ɗaya da rabine.

Kai ta ɗan juyo gabas ta kalli ƙofar safe ɗin Moddibo wanda yake can nesa da ita sosai, yayinda wasu sassayan fulawowi yayiwa ko ina na gidan ƙawanya.

 

Tsarin ginin gidan tsarine, wanda ko a ƙasashen turawa na musamman ne,

Ƙaton gidane mai yalwar fili.

Daga can bakin gate ɗin gidan filine mai girma wanda zai iya ɗaukar motoci shida ba tare da wata ta gogi wata ba, ko matsi wataba, ɗakine mai ɗan girma a bakin gate ɗin wanda ke haɗe da bayi a ciki, da yar baranda alamun ɗakin mai gadi, saidai babu kowa a ciki.

Daga gefe kuwa watsu tsala-tsalan bishiyoyin na mijin gwanɗa ne masu masifar tsawo da ganye mai duhu a can sama sune suke jere reras a jikin katangar gidan baki ɗaya, daga ƙasansu kuma, wasu tsirran fulawowi ne masu masifar kyau da sanyi masu collor’s blue,  red, and yellow.

Tsakanin farfajiyar gidan da can cikin gidan kuma, akwai wani katanga a tsakiyar da kuma ɗan madaidacin gate shima ɗin mota zai iya wucewa ta nan,

Cikin katangar shima zagaye yake da bishiyoyin dabino ta wajen ta cikin kuma in bishiyoyin mangoro ne guda biyu sai daya gefen kuma na goiba,  ne da kuma cabɓulle (Tsada) akwai fili ta gefen hagu, inda motoci biyu zasu iya tsayawa a wurin.

Sai gefen dama kuma, wani ɗan siririn hanya ne, wanda fulawowi ne yazama kamar katangar wurin, tafiya kaɗan zakayi ka riski part din Moddibo, irin ginin nanne mai tudu, duk da bawai bene bane amman ginin a sama sosai yake, forko daga wurin baranɗace mai girma, da tudu wacce ke malale da tayis mai masifar sheƙi, a  bakin barandar anyi wasu steps guda bakwai masu faɗi, kafin hawa barandar,

A gefen dama da hagunsa kuwa wasu fararen ƙarafun silver ne masu kyau sukayiwa barandar garkuwa, a ƙasansu kuwa, wasu. Tukwanen ƙasane masu tsirran fulawowi masu masifar kyau da ƙamshi, kana a kan ko wanne step akwai tukanen a gefen hagu da daman a jere, guda bakwai-bakwai kenan.

 

In ka gama haurawa saman barandar kuwa ka juyo ka kalli bayanka ras zaka hango tekun Gembilan kwance a can, da tsirran bakin Kogin.

A can bayan Part ɗin nashi kuwa wani tamfatsetsen garding ne mai masifar kyau da ƙamshi, sai wani tabkin wanka mai kyau kujeru guda bibbiyu a kusurwowin alƙibila, sai kuma gado a gefen dama da hagunsa,

Cikin Part ɗin nasa kuwa, wani tamfatsetsen parlour ne mai kyan tsarin ƙasaitattun kujeru da labulaye da kayan wuta, komai na ciki farine tas,

tambarin shaidar tsananin  tsabtar ma-mallakin wurin kenan, sai ɗan ratsin sky blue, wanda hakan yasa in ka shiga falo sai kayi zaton a sararin samaniya kake shawagi.

Sai dinning area, da kuma kitchen, sai wani yalwataccen corridor’n wanda ke gefen dama da hagu ko wanne bedroom ɗaya ne a ciki, sai can mashigar falon nanma akwai wani ɗan madaidaicin bedroom.

 

Hatta cikin falon kuwa kewaye yake da fulawowi, shaidar ma-mallakin wurin masoyin sirraine da sanyi da kamshi window palon irin manyan nanne har kusan ƙasa, haka yasa yana iya hango bakin tekun daga cikin palonshi.

 

Daga Part ɗin nashi kuwa gefen hagu akwai wata hanyar mai kewaye da tsirrai, wacce ke sadashi da can cikin gidan.

inda ɗaki ɗaya ne rak, na kakarsa Innayi wacce tace ya isheta rayuwar duniya.

Sai kuma kitchen nata a gefe mai tsarin gargajiya, kana da bayan gidanta can gefe, domin sam taƙi yarda ayi mata bathroom a cikin ɗaki, acewarta kada santsin tayis ya ƙaryata, dole haka Modibbo ya haƙura da tsarinta komai na gargajiya, hatta gadonta taƙi a sauya mata.

Sai dai ta amince da tsarinsa na zageyesu da tsirran shuke-shukensa da zuba mata tattausan Turkey carpet mai masifar taushi, tsarin dakin nata komai ya fito kamar na gidan sarakai shuke-shiku kuwa ba dama.

Daga can gefen hagun side nashi, wani wurine mai ɗan tudu wanda akayiwa rumfa irin ta gargajiya rumfar bunu, gefenta zagaye, da tsirran, cikinta kuwa wasu tsala-tsalan kujerune masu masifar kyau guda hudu da table a tsakiyar su, sai ɗan dandamali na al’adar mutanen Gembilan wanda suke hura wuta a ciki sabida rage tsananin sanyin da ake tsula musu.

 

ALLAH kuma ya yelwata hannunsa da al’barka duk abinda ya shuka sai ya tsiro a yalwace.

(Moddibo kenan)

 

Numfashi Innayin ta sauƙe lokacin da ta gama ƙarewa farfajiyar gidan da lukkunan gidan kallo,

duk da ba hasken farin wata, babu kuma na taurari sosai, sakamakon hadarin gajumaren da yayiwa sararin samaniya ƙawanya.

 

Juyawa tayi ta nufi, ɗan bayan gidanta dake, nan gefenta kaɗan, tana maiyin taku cikin yanayin tsufar da ya cinmata, tare kuma da taka tsantsan gudun kada santsin simintin dake malale a farfajiyar sashin nata ya kadata.

 

 

A bakin ƙofar bayin ta ɗan tsaya tare da yin, addu’a shiga bayin.

“Allahumma inni’aauzubika minal kuɓsi wal kaba ihsi”.

Kamar yadda Moddibo ke nusar da ita mahimmancin addu’a ako wanne lokacin.

 

Bayan ta fito ne, da addu’a a bakinta, ta zauna bisa, wani dutse mai kyau dake bakin barandar ɗakinta, ta fuskanci gabas.

Tare da fara al’wala.

 

A can side ɗin Moddibo kuwa, kwance yake, harshensa jiƙe da ambaton Allah, duk da cikin bacci yake.

Saidai baccin, ba baccine kamar na kowa ba, domin bacci yake cikin wani irin yanayin daya gaza tantancewa, shi ba bacci ba, kuma ba ido biyu ba, ba kuma mafarkiba ba kuma zahiri ba, ba kuma a sumeba wasu abubuwan da lokuta da dama yana riskarsu cikin bancinsa yake fuskantar su.

 

Ita kuwa Innayi a hankali ta gyara zamanta, tare da juyowa ta kalli bayanta, da sauri sabida wani irin haske da taga ya gilmawa ganinta, sai kuma tayi saurin juyowa gabanta ta, kalli gabas saitin ɗakin Moddibo domin a zatonta ko an dawo da wutar nepa ne.

Ga mamakinta kuwa, babu alamun hasken wutan nefan sai wani irin sanyi mai ratsa jiki.

Haka nan taji wani yanayi na rufeta,

wanda yafi kama da tsoro abinda bata taɓa fuskarta sa acikin gidanba duk duhun dare.

 

Hakan yasa tayi saurin sunkuyar da kanta taci, gaba da yin al’wa’ar, hannunta ta wonken, kana ta ciko tafin hannunta na dama da ruwa, zata kai bakinta domin kuskuran baki kenan.

Wani irin saurin ɗago kanta tayi ta kalli gabanta, sabida ganin wani irin masifeffen haske mai firgitarwa da taga ya haska illahirin duniyar har hasken yana haska cikin ruwan dake tafin hannunta.

Cike da tsoro ta zubda ruwan tare, da juyawa ta kalli.

Gabas da yamma Kudu da Arewa.

Babu mutun ba dalilinsa, babu kuma alamun ta inda hasken ke fitowa.

Kana kuma ga kuma hasken dake tsananta.

 

Da wata sassayan iska mai ratsa jiki da sanyaya zuciya.

Wacce tasa Moddibo gyara kwanciyarsa tare da ci gaba da wani irin bacci mai mayataccen daɗi da yaji ya dannesa da kuma shigo masa da wasu sabbin ababen gani a idanniyansa, yayinda harshensa kuwa ke nanata addu’o’in masu tarin yawa.

 

Yayinda ita kuwa Innayi, wani irin tsuma jikinta ya farayi lokacin da taga gaba ɗaya duniyar ta ɗauki wani irin mashahurin haske mai kyan gani.

Wanda ta rasa ta ina yake fitowa.

“Innalillahi wa innailaihi raji’un hasbunallahiwani’imanwakil”.

Ta fara maimaita cikin firgici lokacin da ta ɗago kanta, ta kalli sararin samaniya.

Wani irin kerma da makerketa  mai cike da tsananin tashin hankali, firgici, tsoro, da karkarwa jikinta ya farayi, sabida yadda taga ubangijin talikai, yana wanzar da ikonsa da buwayarsa a sararin samaniya.

Wasu irin masifaffun hawaye masu zafi wanda irinsu kan tsinkowa ɗan Adam lokacin da yaga tsananin abin tsoro da shiga firgici da ƙudurar Allah.

Kar-kar haka jikinta yake rawa, ganin yadda taurari.

Suke fizgowa sunayin wani irin haske mai kashe idanun ɗan adam, wanda sune take ganin duk sun cika sararin samaniya da haske tamkar rana.

“Ya hayyu ya ƙayyum birahamatika astaƙisu, ya Salam, innalillahi wa innailaihi raji’un, la haulawa ƙuwta illabillahil aliyul azeem”.

Sune tasbihai da furucan da ubangijin ya bata ikon furtawa, lokacin da ta fara ganin taurarin sunayin ƙasa tamkar zasu faɗo, ƙasa domin gani take kamar sai sunzo har ƙasa sosai kamar zasu taɓo rufin kwanon ɗakin Modibbo, sai kuma taga ubangijin ya janyesu sun koma sama da azaban sauri tare da tartsatsin haske mai kyan gani.

 

Fadin halin tsoro ko tashin hankali ko firgici da ɗimuwar da take ciki ya zarta zaton mai zato, ya wuce tunanin mai tunani ya shallake nazarin mai nazari, wasu irin wahaye ne ke kwaranyo mata.

Yayinda ta koma baya ta jingina bayanta da jikin filan barandar ɗakinta dake bayanta, ta jingina kanta tana kallon sama.

Tare da fara nanata kalmar shahada.

Domin ta gama sallamarwa cewa, lokacin ta yayi, ma’ana mutuwa zatayi.

“La hailahaillahu Muhammadu Rasulullahi sallahu alaihi Wasallama”.

Shi ta fara maimaitawa can ƙasan maƙoshinta domin.

Komai na jikinta ya fara tsayawa, sabida azabebben tsoron daya rufeta da cikekken imanin kaɗaita rabbissamawati wal ardi zuwa yanzu tama fara ɗimautan shin anyama kuwa a raye take?.

 

A ƙalla 30 minute ubangijin talikai na wanzar da ikonsa! Da kuma, buwayarsa!! Can kuma sai ta fara ganin gaba ɗaya duhu na meye hasken.

Duhu mai cike da sassayan iska.

Wani irin tsorone ya kuma rufeta wanda ya diro mata da zazzafan zazzaɓi mai haɗe da masifeffen ciwon kai.

Wanda ya tilasta mata kife kanta bisa guiwowinta tare da rumtse idanunta tamkar zata liƙesu da juna.

 

A can cikin masarautar Gembilan   kuwa, Gimbiya Dadu ce, ke kwance bisa tsakiyar gadon ta, wani irin masifeffen mafarki mai tada hankali takeyi.

Wanda yasata ihun neman ceto, wanda bata saninba har ya fito fili.

Fitarsan ne, yasa hadimarta saurin shigowa tare, da tadata. Ai kuwa cikin tsananin firgici da tsoro ta farka tana mai karkarwa, lokaci guda kuma zazzafan zazzaɓi ya rufeta.

 

A nan gidansu Moddibo kuwa.

A hankali ya fara buɗe idanunsa tare da ambaton Allah.

Hannunsa yasa bisa  bed side drawer ya jawo wayarsa.

Gefen wayar ya ɗan taɓa da yatsarsa manuniya, wanda hakan yasata kawo haske har ya haska Kekkyawar fuskarsa mai cike da yalwataccen saje mai sulɓi da ɗan madaidaicin gemun da bazai uwace kamu ɗaya ba yayiwa siraran jajjayen leɓɓansa masu sheƙi ƙawanya.

 

A hankali ya ziro ƙafafunsa ƙasa, sabida ganin, ƙarfe huɗu saura kwata.

Bathroom ɗinsa ya nufa.

 

Yana shiga yayi brush da wonka tare da yin al’wala, kana ya fito.

Durowarsa ya buɗe yayinda yake amfani da wayar hannunsa wurin haska abin nemansa domin har yanzu babu wuta kasan cewar yanayin garin Gembilan garin mai masifar sanyi mai daɗi, yasa basu cika damuwa da rashin wutar da ƙasartamu ke fama dashi ba.

Wata tattausar jallabiya fara ya zira kan ƙananan kayan dake cikinsa, tare da jawo farin hula taɓa kaji hadis a kansa, turaren Oud bakhur mai masifar ƙamshi ya fesa, tare da sa hannunsa na dama, ya zaro carbinsa kana ya fito, falonsa, tare da sassarfa ya buɗe ƙofar falon ya fito.

 

Can cikin gidan ya nufa kamar kullum domin tabbatar da cewa kakartasa ta tashi daga bacci duda yasan kullum bisa sallaya zai sameta to amman hakan baya hanasa zuwa.

 

Ɗan tsayawa yayi tare da kallon inda Innayi ke zaune har yanzu, yadda kanta ke kife bisa guiwarta sai yayi kamar tana sunkuyene irin zata wonke fuskartan nan.

Da ɗan sauri ya juya ya nufi bakin gate nasu yana mai tasbihi.

 

 

Ƙarami ƙofar dake manne jikin gate ɗin ya tura ya fita asalin farfajiyar babban gate din nasu,

A hankali yake motsa laɓɓan bakinsa, yana taibihai, tare da shaƙar sassayar iskar,

A hankali ya kuma buɗe ƙaramar kafar  kana ya nufi masallacin jumma’a dake layin nasu wanda yana kallo tamfatsetsen gate din gidan tsohon gidan Alhaji Abubakar Mafindi mahaifi ga Amininsa M Jamil kenan.

 

Ita kuwa Innayi ƙamshin turarensa ne, da kuma motsinsa ya tabbatar mata shine, so take ta ɗago kanta amman ta gaza, sabida wani irin sarawa da kanta yakeyi.

Har yanzu sunan Allah take kira, a ƙalla mintuna 20 da fitarsan kafin Allah ya bata ikon motsawa,

Cikin ƙarfin hali ta ɗago kan nata, lokacin da taji sautin murya Jamil yana kiran assalatu.

 

Wasu irin zafafan hawaye ne suka tsilalo mata wanda tsananin ciwon kan ne  ya jaza mata su,

Cikin ƙarfin hali tayi, al’wala tare da yunƙurawa ta mike tsaye tana mai dafe kanta, ta koma, cikin ɗakinta, dai-dai lokacin kuma aka dawo da wuta, yayinda ko ina ya gauraye da haske, sallaya ta shimfiɗa kana ta zira hijabinta, ta fara nafila, jiki na rawan zazzaɓi da kyarman tsoro tanayi tana mamakin shin wai ashe a raye take?…

 

Ƙarfe bakwai dai-dai na safe.

Ya shigo gidan, maida ƙofar yayi ya rufe, tare da ɗan tsayawa, tsakiyar gidan, yana mai kallon ƙofar kitchen ɗin, Innayi yana mai nufar cikin gidan.

Agogon hannunsa ya kalla, tare da ɗan jinjina kai sai kuma ya juya, ya nufi, side ɗinsa, yana shiga bathroom ya wuce, ƙofar ya maida, ya rufe, tare dasa hannunsa ya jawo, tattausan towel, ya ɗaurasa a ƙugunsa bayan ya zare, jallabiyar, da vest, yana ɗauke da towel, sassayan numfashin ya fesar kana ya shiga cikin jaccuzie ɗin.

 

Cikin nitsuwa yayi wonka fes, ya fito.

Yana wani irin masifeffen ƙamshi yayinda gargasan jikinsa ya kwanta lib a tattausar farar fatarsa da damshin ruwa,

 

Wani towel ɗin ya jawo ya ɗaura, kana ya zare na ƙasan, matseshi yayi tare da shanyasa.

Sannan ya fito yana mai tsane tattausan sumar kansa da ƙaramin towel ɗin.

 

Gaban dreesin meeror’nsa ya tsaya, ya fara kimtsawa, cikin yanayin nitsuwarsa da rashin yin abu da gaggawa…

 

Bayan ya gamane ya fito fes yana baza ƙamshi mai masifar daɗin shaƙa, sai wani irin kyalli sajensa keyi, yayinda jajayen lips ɗinsa suke wani irin sheƙi tamkar dai irin yadda lips ɗin jarirai yake sheƙi in sun ɗan laso lips ɗin.

Wata tattausar jallabiya blue color mai ɗan karen taushi da kyau ne, a jikinsa, tayi cib-cib da ɗan madaidaicin jikinsa, sai kuma fararen takalma half cover masu taushi da ya zira tattausan sawayensa da suke farare ƙal, yayinda dun-duniyar sawun nasa ke sarari.

Farin hirami ya naɗa a kansa, irin naɗin nan na zamani wanda matasan larabawa keyi,

Sai wayarshi daya zira a ajihun gaban jallabiyar tasa, wani irin sassayan ƙamshi mai ɗan karen daɗin shaƙa yake zubawa,

Taku yakeyi cike da kamala, yayinda hannunsa na dama ke riƙe da jakar system nasa.

 

Cikin yanayinsa na nitsuwa ya ƙara so bakin kitchen ɗin.

Siraran Idanunsa ya ɗan jujjuya ya kalli tsakiyar gidan baki ɗaya, sai ya kuma ɗan leƙa cikin kitchen din, nan ma babu alamun Innayi.

Cikin nitsuwa ya kuma juyowa ya nufi ɗakin nata, ganin takalmanta a bakin ƙofar.

“Assalamu alaikum”. Yayi sallama cikin wata iriyar sassayar muryar mai cike da haiba nitsuwa da kamala.

Sai kuma yayi saurin shigowa cikin ɗakin.

 

Ganin Innayi na kwance bisa sallaya babu ko pillown ga kuma karkarwa da jikinta keyi.

A hankali ya rusuna tare da takwara ƙafarsa ta dama ya zauna kanta ta hagu kuma ya tsaidata, cikin kulawa da tarin so tausayi, ya motsa lips ɗinshi a hankali yace.

“Yah Salam.

Innayi! Innayi!! Innayi!!!”. Ya kirata sau uku, ganin bata amsa bane, yasashi manna  tafin hannunsa kan goshinta, wanda hakan ne yasata buɗe kwayar idanunta da sukayi ja.

Sai kuma ta medasu ta rufesu, sai ga wasu hawayen masu zafi sun kwaranyo mata.

Jiki na rawa tasa hannunta, ta kamo hannunsa, murya a raunace tace.

“Aliyu”. Da sauri ya zuba mata idanun tare da tsareta dasu, domin zai iya cewa, wannan shine karo na biyu a rayuwarsa da yaji ta kirasa da asalin sunansa na yanka.

A hankali yace.

“Na’am Innayi meke damunki? Meyasa baki kirani kin gaya min baki da lfy ba? Tashi mu tafi asibiti”.

Ya ƙare mgnar yana mai tallabota ya zaunar da ita.

Wani dogon numfashi Innayin taja cikin rawan murya tace.

“Aliyu ka zauna, kaji abinda zan gaya maka”.

cikin yanayin kulawa a sanyaye yace.

“A’a muje asibiti tukuna, sai mun dawo”.

Cikin ɗan ɗaga murya tace.

“Aliyu ka bari kaji abinda baka saniba.

Bana son in mutu in barka a nahiyar maraici, bana son in mutu da abinda ni kaɗaice na sani kuma nakeda dama da ikon sanar da kai, idan na mutu a haka ban sanar da kai abinda ke bibiye da muba, nayi maka cuta mafi muni a rayuwarka.

Aliyu ka bari in sanar da kai abinda Allah ya nuna min a daren jiya”.

A hankali ya fesar da nannauyan numfashi, sai kuma ya juyo ya kalli ƙofar ɗakin, jiyo Muryar Amininsa mafi ɗan uwa, wato M Jamil yanayin sallama, a hankali yace.

“Wa alaikassalam J”.

Ya ƙira Aminin nasa da sunan da duk duniya shi kadai ke kiransa da hakan,

Ido ya zubawa M Jamil ɗin a hankali tare dayi masa alamun ya shigo da kwayar idanunsa,

Cikin yanayin sauƙin kai sakin fuska faram-faram Jamil ya sako kansa cikin ɗakin yana mai cewa.

“Iya innare yau me kika dafa mana ne, dan tun jiya da na dawo ƙasar nan banci komai ba, nace sai abincinki zanci ko na Ummina”.

Sai kuma yayi shiru tare da matsowa kusa da ita…

 

Cikin Masarautar Gembilan kuwa.

Wata Kekkyawar matace yar duma-duma mai kyan shiga da haiba, ke zaune bisa kujera, yayinda System ke gabanta bisa ɗan madaidaicin stool yayinda fuskarta ke manne da wani ɗan farin glass siriri.

Da alamu typing takeyi.

 

Kai ta ɗan jinjina tare da juyowa ta kalli dinning area inda hayaniyar yaranta ke tashi.

Kai ta ɗan jinjina tare da kallon wata yar narkekkiyar matashiya da bazata wuce 14 year’s ba.

Ido ta zuba mata ganin ta nufota da sauri.

Hannunta ɗaya.

Riƙe da school bag da  takalmin sinika da kuma ɗan madaidacin hijabin Uniform ɗin ta.

 

Da sauri ta rusuna gaban Matar tare da juya mata baya tana cewa.

“Ayya Momy tubke min kaina, nayi-nayi yaƙi sai na ƙulleshi sai ya sule”.

Kwaffa tayi tare da cewa.

“To wai ke kam Khausar yaushe ne zaki iya, tubke gashin kanki”.

Ta ƙare mgnar tana tattaro suman Khausar din yana mai zamewa,

Sai kuma ta ɗago kanta ta kalli Ɗan matashin yaron da yanzu ya fito cikin Uniform ɗinsa. Wanda yake iri ɗaya dana jikin wacce aka kira da Khausar.

Da alamun ya gama shirinsa tsab.

Cikin tsuke fuska ya watsawa Khausar din harara tare da cewa.

“Gsky ni zan tafi Ramadan Raudat zomu tafi, kullum ita ke jaza mana yin letting muje aita zanemu kamar bayi.

Ni wlh da zan samu a rabamun hanya da ita inaso, muna shiga school kamar wasu shaidanu zakaji an fara cewa.

FATTANAH kuka biyewa ko, duk sai an gama shiga aji  kafin ku iso.”

Cikin yanayin tsiwa da son girma ta miƙe tsaye tana ɗaure ɗan kwalinta harara ta watsa mishi tare da cewa.

“Wallahi ka shiga hankalinka dani Haydar in baka dena cemin FATTANAH ba zan fasa maka baki”.

Dogon tsaki yaja tare da juyawa ya nufi ƙofar falon, yana gyara zaman  net ɗin sa. Tare da cewa.

“Sai ki gayawa wanda yasa miki sunan, ko kuma ki nitsu ki dena rashin kunya da rawan kai”.

Cikin ɗan ɗaga murya Momyn nasu tace.

“Gsky Babana bana son wannan sunan da aka liƙawa Mamana sam bafana son sunan”.

Da sauri yace.

“Toh Momy ai ita ta jawa kanta fitinenneyar ce ta gasken gaske,  in dai kinji faɗa to da ita a ciki, in kuma babu ita to zakiji ance ai gulma akayi ta maidawa maishi, wai ita ba’a gulma da ita, itafa tana iya zuwa zuwa ta samu ana faɗa ta shiga tayi kane-kane sai an gama tace wai me dalilin faɗan”.

Ya ƙare mgnar yana fita.

Ita kuwa Khausar zama tayi gefen Momynsu tana sa takalmanta da ɗan sassarfa domin yau din ranace ta musamman a wurinta tana cike da ɗokin zuwa makaranta kasancewar yau suka dawo hutu, kuma hutune na canjaza aji da JSS zata tafi SS 1 wanda takega matakin samun encinta ne kenan zata taka, tunda yanzu zata koma aji da matan aure, a islamiyar safe, sai kuma na bokone tacan anan ne babu enci sai randa ta gama sa takalmin ta saka, tana sakin yelwataccen murmushi.

Yayinda Ramadan da Raudat suke tsaye gefenta.

Hannu tasa ta kama hannun Raudat tare da cewa.

“Mu tafi”.

Da sauri ta juyo ta kalli Momyn nasu tare da kwaɓe fuska jin tana cewa.

“Ku biya sashin Gimbiya Dadu ku gaidata, bata da lfy”.

Cikin kwaɓe fuska tace.

“Momy zamuyi letti muje wannan mai sunan baban naki ya samu damar sawa a azabtar dani”.

Ta ƙare mgnar cikin son zillewa zuwa sashin Gimbiya Duda, ita kuwa Momy tsuke fuska tayi tare da cewa.

“Ku biya ku gaisheta da jiki nace ko”.

Cikin bin umarnin mahaifiyar tata badon tasowa tace.

“Toh Momy”.

Daga nan ta kada kan ƙannen nata Duk suka fito.

Sai kuma tayi sauri ta juyo tare da cewa.

“Momy mun tafi”.

Murmushi tayi sanin manufar ta yasa cikin lumshe idanu tace.

“Allah ya kaiku lfy ya baku Sa’a Allah yasa ki shiga SS 1 da ƙafar dama, Allah ya shirya min ku”.

Cike da jin daɗi tace.

“Amin Ya Allah”.

Kana suka fita.

Suna fitowa suka samu duk sauran yaran gidanma sun fito.

 

Kamar haɗin baki kab ɗin su sashin Gimbiya Dadu suka nufa.

Kai tsaye suka wuce har bedroom ɗin ta domin bata falon.

 

Su Asiya ce, a gaba ita da sauran ƙannenta,  sai kuma su Khausar din.

 

Zaune suka sameta bisa tsakiyar gadon mulkinta, mai martaba Lamido Gembilan yana zaune ƙasa bisa carpet, yana haɗa mata tea,

Cikin tarin biyayya, da sauri suka rusuna baki ɗayansu, kusa haɗa baki sukayi wurin cewa.

(“Allah saine Abba, noi nɓanɗu Dadu?) Allah ya faranta maka Abba ya jikin Dadu?”.

Cikin son ahlin nasa ya jinjina masu kai tare da cewa.

(“Yettore Allah nwodi dama) an godewa Allah da sauƙi”.

“Allah ntokkin dama”.

Suka faɗa a tare, cikin tankwashe sawunsa yace.

“Allah jabu”.

Amin suka faɗi  baki ɗayansu,

Yayinda Khausar kuma taketa jan hijabinta, tana mai sunkuyar da kanta ƙasa,

Allah ya sani bata ƙaunar abinda zai kawo ta gaban Gimbiya Dadu,

Domin jikinta da nitsuwarta duk rasasu takeyi, sabida wani irin mayataccen kallo mai bada tsoro da tsohuwar ke Binta dashi.

Kamar koda yaushe kuma hakane, duk da bata da lafiya, amman wani irin masifeffen kallo ta tsare Khausar ɗin dashi har bata jin gaisuwar da jikokin nata keyi mata,

Cikin taɓe baki Asiya tace.

“Dadu wannan wanne irin kallo ne? muna gaidaki kinyi shiru?”.

Jin hakanne yasa  Khausar ɗan ɗago kanta,

Ai kuwa ido cikin ido sukayi da Dadu.

Da sauri ta motsa lips ɗin ta a hankali tare da cewa.

“Innalillahi wa innailaihi raji’un”.

Sabida wani irin tashi da tsikar jikinta ya farayi, yam-yam.

Ita kuwa Dadu har lau bata cire idanunta a kantaba,

Haydar ne ya ɗan miƙa tsaye tare da kamo hannun Ramadan da Raudat yace.

“Dadu Allah ya sauwaƙa, zamu tafi school kada muyi letti Raudat muje”.

Abin mamaki har lau Dadu batama san anayi mata mgna ba, bare ta amsa musu, gaba ɗaya nitsuwarta da kallonta yana kan Khausar….!

 

Lamido kuwa ido ya zubawa maifiyar tasa, cike da mamakin lamarinta, ya zama  ana kallon kalo, ita tana kallon Khausar data kasa koda ƙwaƙƙwaran motsi shi kuwa yana kallonta.

Asiya kuwa itama miƙeqa tayi tare da kaɗa kan ƙannenta tayi gaba Amina ce ƙanwar Asiya mai binta ta ɗan miƙa tare da cewa,

“Uhum”. ta fice

Ya zama daga Dadu sai Lamido sai Khausar.

 

Cikin wani irin yanayi da Khausar din keji ta kuma kallon Dadu, wacce zuwa yanzu ta saki laɓen bakinta na ƙasa, wani irin  yawu mai cike da mayataccen kwaɗayi ne ya tsinko mata, har yana ɗan sauƙowa kan lips ɗin ta.

Cikin sauri Khausar ta miƙe jin Lamido yana cewa.

“Mamana tashi ku tafi”.

Ai kafin ma ya rufe bakinsa, tuni ta fita tana mai cewa.

“Toh Abba”.

Ita kuwa Dadu wani nannauyan numfashin ta sauƙe tare da juyowa takalli ɗan nata, dake miƙa mata cup ɗin tea.

Cikin diriricewa tace.

“A’a bana buƙatar abin zaƙi, a kawo min abu mai yaji-yaji”.

Cike da biyayya yace.

“Toh”.

Kana ya miƙe ya  fita.

 

Tuni su Khausar kuwa sun shiga school bos ɗinsu,

Amina ce ƙanwar Asiya mai binta ta kalli Ramadan dake cewa.

“Kalli fa 8:13 na tabbatar yauma zamu zanu”.

Cikin sanyi tace.

“Mu dai Allah ya rufa mana asiri daga SS 2 akwai matan aure da yawa a ciki, so ba batun duka a side ɗin mu.

Kuma ma duk bama saɓa doka cikin nitsuwa da tarbiyyar mu muke, ko nayi litting nasan za’ayi min uzuri.

Cike da jin daɗi, Khausar tace.

“Nima dai Allah ya yaye min masifa da cin zalin su Moddibo tunda yau dai  zan tafi Ss 1 ɗin, da ba duka ba zagi, wlh inci karena babu babbaka”.

Taɓe baki Haydar yayi tare da cewa.

“Mu gefen maza, babu manya, duk yarane, manyan da dare suke zuwa, shiyasa babu roggomi”.

Asiya ce ta kalli Khausar cikin yanayin son yarinyar tare da cewa.

“Ai wlh ke dai in baki nitsuwa ba ko jami’a kikaje in dai Moddibo na cikin malamanku, na tabbatar zai san matakin da zai ɗauka a kanki.

Sannan ma da kike batun  kin tafi Ss1 akwai matan aure, kin mance cewa, na safene, na islami.

Akwai na rana zuwa biyar bokone, kuma kuna tare da moddibo.”

Kwaffa tayi tare da cewa.

“Kai na shiga ukuna wlh”..

 

Anan gefen su Modibbo ku, fir innayi taki aje asibitin. Su kuna su kasa fahimtar ta, gani suke zafin zazzaɓin maleria ne yake son sata surutai shiyasa suke hanata mgn sukayi ta mata addu’o’i hardai ta ɗan fara samun nitsuwa har bacci ya ɗan sureta.

Gani  ta ɗan rumtsane yasa suka tafi wurin Ummin M Jameel suka ɗauko Ummin dan tazo ta ɗan kula da ita.

 

Suna isa bakin gate, ba tare da sun shigaba, Ummin ta kalli M Jamil da yayi saurin fitowa bayan yayi parking marfin motar ya buɗe, mata cikin tsananin son mahaifiyar tasa, yace.

“Bismillah Ummi fito ki shiga  wurin Innayinki, domin mu dai yau mun gaza gane kanta, da alamun Ita dai dare ɗaya gigin tsufa ya sauƙo mata”.

Ɗan buge ƙeyarsa tayi tare da ciwa.

“Tsufa kan zai cimma taka uwar mafa, kawai dai inaga zafin zazzaɓine kusan wasu lokutan yanasa yara surutai, to ita kuma girma yazo dole in ciwon yayi zafi zatayi kamar na yara”.

 

Juyowa tayi ta kalli Moddibo daya jingina kansa jikin kujerar gaban motar gefen mai zaman banza,

Cikin sanyin murya yace.

“Uhmmmm Ummi waifa cewa tai taga taurari suna sauƙowa ƙasa har kamar zasu taɓa rufin side nan, anya kuwa Ummi wannan zazzaɓi ne?”.

Sai kuma ya ɗan fesar da numfashi tare da lumshe idanunsa cikin alamun nazari yace.

“Ina tsoron kada fa matsalar ƙwaƙwalwa ce, nayi nayi muje asibiti kuma taƙi.”

Ya dire mgn tare haɗa kan yatsun hannunsa.

Jamil ne yaci gaba da cewa.

“Saida fa Moddibo yayi ta mata tofi kafin muka samu tayi bacci har muka fito ɗin.”

Cikin kulawa Ummi tace.

“In sha Allah babu komai, bari in shiga, ku kuje”.

To Jamil yace kana ya shiga mota, ita kuma tayi cikin gidan.

 

A hankali ya miƙa dalleliyar motarsa ƙirar BMW kan shimfiɗeɗen titin,

Yana tafiyar hawainiya, murmushin yayi ganin kallon da Moddibo yake masa.

“Sanin yau za’a dawo makaranta ne, yasa nayi ƙoƙarin dawowa baro Marrocco, duk da akwai ayyukan da ban gama dasu a company’nba,”.

Cewar M Jamil shi kuwa Moddibo kai ya jinjina alamun yana jinsa, shi kuwa M Jamil gudu ya ɗan ƙara tare da ci gaba da mgn dan yasan ba lallai ne Moddibo ya amsa mishi da bakiba, inda sabo ya saba, kuma shi yasan cewa body language al’adane ko ɗabi’a koma yace halittar Moddibo ne.

Juyowa yayi ya kalleshi tare da cewa.

“Na zaƙu muje makarantar nan, dan nasan zaiyi kyau sosai a tsarin gyarashi da akayi”.

Cikin ɗan ƙwaɓe fuska yace.

“In an gama gyaran ba”.

Da sauri M Jamil yace.

“Kamar yaya za’a gama mana”.

Juyowa yayi ya ɗan kalli M Jamil ta gefen ido kana a takaice yace.

“Toh ba’a gaman ba”.

Cikin sauri M Jamil yace.

“A.S da gaske ba’a gama ba?”.

A.S shine sunan da yake kiran Moddibo dashi kuma su biyu kaɗai suka san ma’anar sai kuma abokan karatunsu.

Shi kuwa Modibbo littafin dake gaban motar ya ɗauka tare da buɗe wa kana yace.

“Dama tun lokacin da za’a bada hutun na faɗa bazai isa a gama gyaran school ɗin ba, musamman da ya zama an ƙara yawan class, kana ga gina hall din da akace za’ayi, kuma dole aikin bazaiyi guduba sabida Ramadan, tun lokacin nace a ƙara kwanakin hutun, sabida samun isasshen lokacin, wannan  Ba fulatanin yaƙi”.

Murmushin M Jamil yayi tare da cewa.

“Toh kai meyasa baka ƙara hutunba, ai da sai ka sanar”.

Juyowa yayi ya kalleshi bayan hannunsa yasa ya shafa tattausan sajensa tare da cewa.

“Uhmmmm”.

Ya san me wannan Uhmmm ɗin take nufi, kai ya jinjina tare da cewa, “Mu dai yan kallone,”.

Da sauri yace.

“Nima haka, dan na gaji ko yaushe sai ya kwaɓa abu yazo yana cemin ina mafita”.

Dai-dai lokacin aka buɗe musu gate din makarantar, Ya Salam.

Wani irin tsarine da zubi makarantar yake dashi, tsari mai burgewa, yayinda shima makarantar Moddibo ya ƙawatata da tsirrai na kyautata muhalli.

Tabbas gyara kam da saura ba’a gama shi ba.

Domin daga woje dai kam an kammala komai amman daga ciki, duk cikin ajujuwan a hargitse yake.

M Jamil nayin parking, wani kekkyawan dattijo bafulatani ya nufo matar tasu da sauri, bisa alamu dai shine shugaban makarantar domin duk malaman na miƙa gaisuwar garesa cikin mutuntawa.

“Moddibo! Moddibo!! Moddibo!!!.”

Jamil ne ya fito yana murmushin tare da cewa.

“Allah rene,”.

Da sauri yace.

“Ina Moddibo”.

Cikin motar Jamil ya nuna masa, da sauri ya sunkuyo,

Yayinda shi kuwa Moddibo meda bayansa yayi ya jingina tare da lumshe idanunsa, murmushi Dattijon yayi tare da cewa.

“Ga ɗalibai duk sun dawo makaranta ta cika maƙil ga sabbin ɗauka, kuma aiki baifi rabi ba, ya zamuyi?”.

Cikin taɓe baki yace.

“Allahu a’lamu!”.

Jamil ne ya juyo ya kalli Malam Ahmad da Malam  Habibullah da suma fitowar su kenan daga can cikin makarantar.

Shi kuwa Malam Arɗo Umaru mamallakin makarantar kuma .

Kai ya ɗan dafe tare da cewa.

“Dan Allah ka fito Moddibo kasan bayanin da zakayi musu, kana ka kara musu kwanakin hutun, tsawon lokacin da kakega za’a iya gama gyaran”.

Yadda ya dire mgnar da karya wuyane yasa Moddibo fitowa.

Murmushin sauran malaman sukayi, domin sosai tsufa ya fara cimma Mala Arɗo, zuwa yanzu ya kamata ragamar makarantar ya zama a hannun yara, domin badon Allah yasa Moddibo ke tsara komai na jadawalin abubuwan ciki da wajen makarantar ba, da tuni ta durƙushe, to amman sabida shi da sauran haziƙan malamai da suke da tsananin kula da tarbiyyar yara da sukeyi yasa har yau makarantar bata da na biyu a faɗin birnin Gembila.

Kusan a tare suka rakaya cikin makarantar.

 

Yayinda hayanin ɗalibai manya da yara maza da mata, ke tashi.

 

Juyowa yayi ya kalli Jamil tare da cewa.

“J kaje masallaci kayi mgn duk mu su haɗu a tsohon halla ɗin mu na sama.”.

To Jamil yace yana tunanin to me zaice musu,

Masallacin ya wuce tare da yin sanarwan.

Nan take kuwa, duk ɗaliban suka haura sama, suka shiga cikin babban hall ɗin nasu wanda yake ƙato sai dai duk da haka yanzu ya musu ƙaramin,.

 

A gafen mazama suma duk sun haɗu a halla nasu.

 

Shi kuwa Moddibo office nasa ya wuce.

Jim kaɗan ya fito, da Lapel Microphone a hannunsa yana saƙalasa a wuyan tattausan jallabiyar jikinsa Malam Ahmad ne ya matso kusa dashi tare da cewa.

“Zamu jirane ko an ƙara mana hutu”.

Ɗan murmushin gefen baki yayi tare da cewa.

“Hutu kuwa sosai ma har na tsawon mako uku za’a ƙara”.

Cike da murmushi yace.

“Mu tafi kenan”.

Kai ya gyaɗa masa tare da cewa.

“Suma duk yanzu zan kaɗa kansu ko wacce tai gida sai dai muma muna da zama na musamman”.

Ai kuwa jin haka yasa duk malam suka zauna jiran.

 

Shi kuwa ya haura saman yana mgn da M Jamil a waya.

 

“Su maza basu da hayaniya, kawai J ka ɗanyi musu nasiha, kana kace sai bayan  mako uku zasu dawo kafin nan an gama gyara,

Sai dai masu zuwa hadda suci gaba da zuwa.”

Cike da gamsuwa M Jamil yace to.

Kana sukayi sallama.

 

Dai-dai lokacin kuma  su Khausar suka shiga cikin makarantar,

Da in ka gani kace a ƙasashen ƙetarene, domin makaranta ce mai zaman kanta, mai cike da haziƙan malamai, duk da sunyi makarar mintuna 20, an bar motarsu ta shiga ne, sabida magiyar da sukayi tayi da kuma girman gidan da suka fito, da bada uzurin motar ta ɗan lalacemusu a hanyane kana da kuma ganin ma yau ba karatun za’ayi ba, hutun za’a kuma ruɓanyawa.

 

Suna shiga kuwa, ga mamaki su  aka barsu suka shige ba hukuncin komai.

 

Kana ko wa ya nufi sashin da ajinsa yake.

 

Da sauri duk suka tsaya jin Malam Habibullah na cewa.

“Fattanah uwar yan letti yau makarar har ta 20 minute duk da yau aka dawo, duk kuyi sama ana taro a hall”.

Cikin ɗan tura baki tace.

“Toh Malam”.

Yayinda tuni su Asiya kam sun haura har sun shiga hall ɗin.

 

Da ɗan sassarfa ta fara take steps ɗin da zai sasanta, da hall da yake a sama ganin ita kaɗai ta rage.

 

Daga corridor’n steps ɗin, ta ɗan lumshe idanu ta, tare da gyara saƙala school bag ɗinta a kafaɗar dama.

Sabida ƙamshin turarensa ya shaida mata, tabbas tuni ya shiga hall ɗin.

 

A hankali ta sauƙe numfashin ta tare, da nemo dukkan nitsuwarta.

Lokacin da ta gama haurowa, sama, da sauri ta tsaya, jikin window dake gab da bakin ƙofar shiga, ido ta lumshe tare da buɗewa a hankali kana ta kutsa kai cikin hall din da a kalla mutane ciki sun kai ɗari da hamsin, duk da tasan bai taɓa barinta, ta shiga ajiba, muddin ya rigata shiga, to amman kullum sai ta gwada sa’anta musamman yau da yake a hall ne.

Taku ɗaya tayi ana biyu, ta tsaya, sabida, ganin ya ɗaga mata, tafin hannunsa.

Cikin yin mui-mui da bakinta tace.

“Afwan ya mu’allim sayyara…”.

Da sauri ta ɗan ja da baya ta koma jikin window ganin ya juya baya tare, da gyara ɗan masaƙalin Lapel Microphone dayake saƙale a wuyan jallabiyar jikinsa, sabida tsananin sanyin sautin muryarsa yasa dole sai dashi yake amfani a cikin class, domin ɗalibansa su samu damar jinsa sautinsa ras domin sam baya iya kware muryarsa yayi mgna da ƙarfi haka Allah ya haliccesa da nitsestsiyar sauti to bare a irin taron maƙil da hall ɗin yayi yau.

Cikin tattausar muryar sa mai cike da sanyi yace.

“Makfut?”. Cike da  jin daɗin nasihar da yakeyi musu suka amsa da “Na’am”.

Kai ya jinjina tare da cewa.

“Ɗeyib!”.

Sai kuma ya ɗan juyo ya fuskancesu, hakan ya zama, ya ɗan bawa Khausar baya, tattausan sumar ƙeyansa dake kwance lib-lib ta zubawa harara.

Numfashi mai sanyi taja tare da shaƙa daddaɗan ƙamshin turarensa mai sawa ɗan adam salama.

Sai kuma tayi ƙasa da kwayar idanunta dugadigin sawunsa, ta zubawa idanu tana ganin yadda sukeyin ja in ya taka sawun, in kuma ya ɗaga sai suyi fari, baki ta ɗan tura sama ta da liƙa ƙeyarshi wani sabon hararan.

 

Shi kuwa Moddibo a hankali yake taku a gaban ɗaliban nasa, masu biyayya da girmamawa a garesa, cikin tattausan lafazi yace.

“Falalar zikirai da karatun Alqur’ani , nakeso son in tunasar mana, sabida kididdigar manazarta, ta nuna mana Al’ummar wannan ƙarnin sun samu naƙasun zikiri da   karatun Alqur’ani mai girma, sun maida hankali akan sashin yanar Gizo-gizo fiye da yadda ya kamata,  mu maida hankali kan Al’ƙurani littafin Allah da hadisan Manzon Allah,  mu samman a wannan taki da muke ciki, na shuɗewar Ramadan wanda zaka samu da yawa mutane sun fuskanci aikin al’khairai da bautar ubangiji a cikin watan, da zaran watan ta gabata sai a koma gidan jiya aita sharholiyar duniya.”

Sai kuma yayi shiru, tare da fesar da numfashi a hankali, kana ya juyo a hankali yace.

“Mutane da yawa sun mance koma ince wasu basu san me Allah maɗaukakin sarki yace ba  A cikin Suratul Baqara, ayata 152.

Allah maɗaukakin sarki yace.

فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُوا لِي وَلَا تَكْفُرُونِ.

Ma’ana:

Ku  ambaceni zan ambaceku, ku godemin kada ku butulcemin.”.

Ya ƙare mgnar da rumtse tafin hannunsa alamun ƙarfafa mgnar, wanda kuma wannan ɗabi’arsace ko ace halittar sace.

Duk mgnar da yakeyi yana kamantata ko suffantata da tafukan hannunsa like dai yadda manyan sarakuna keyin mgn turawa kuma suka cewa hakan body language, Wanda mafi akasari ɗabi’ar yan jarida ne, in suna mgn.

Shiru hall ɗin yayi alamun suna fahimta sosai.

Shi kuwa Moddibo cikin girmama zancen Allah madaukakin sarki yaci gaba da cewa.

“A dai wannan ƙarni da muke ciki da yawa, suna butulcewa faɗin Allah madaukakin sarki, daga barin ambatonsa, gaba ɗaya shagala tayiwa al’ummar mu ƙawanya, shafukan sada zumunta na yanar Gizo-gizo ya maiye gurbin da yake muhallin Qura’ani ne a wurin wasu musul manmu, sai a wuni a kwana musulmi bai ɗauki Qura’an ya karanta ya duba kyan baƙin da yake haɗawaba,  amman sai ka sameshi awa 14 na awannin 24 na rana yana rungume da wayarsa, ana charting, a  Facebook a koma whatsApp, daga nan a tafi Instagram, sai kuma a murgina a koma twitter sai kuma a rarrafawa zuwa wannan lalataccen kuma kazamin dandalin Tiktok, ayi ta raye-raye da waƙe-waƙe, anaiwa juna cin zarafi, wasu su koma yiwa malamai isgilanci ana yaɗa fasadi da fajirci ana meda ashariya kamar ruwan sha.”

Ya dire ayar mgnar tare da haɗe kan yatsun hannunsa gaba ɗayansu wuri ɗaya alamun ya dunƙule mgnar kenan bawai ya gamata bane zai tafi sashi mafi muhimmanci ne.

 

A jikin window a waje kuwa, cikin jujjuya ido Khausar ta raɓa jikin window tare da maida hankalinta baki daya cikin.

Shi kuwa Moddibo a hankali ya ɗan juyo gefen damansa, jin inda sautin surutu yake ɗan tashi kaɗan.

Ganin yana kallon sune kuwa yasa,

Samira Sani yin shiru.

Cikin nitsu ya kuma cewa.

“A wata ayar kuwa a cikin suratul Ahzab ayata 41, me Allah maɗaukakin sarki yace mana!???”.

Ya ƙare mgnar da alamun ayar tambaya, hakan na nufin su ja mishi baƙi yake so, sanin mafiya akasarinsu yan haddansa ne,

Ji kakeyi, hall din sit kowacce tayi ƙasa da kai, gudun kada ya nuna ta kaɗan daga cikinsu kuma bawai basu sani bane diricewa ne da kwarjininsa ke sasu yin ƙasa da kai.

Cikin sanyi yace.

“Na’am Samira Sani”. Da sauri tace.

“Malam ni?”. Fuskarsa ya  tsuke tare da juyowa ya kalli Asma’u Ahmad dayi mata alama da hannu, tsilli-tsilli tayi da idanu.

Samira Sani kuwa ganin ya cire ido a kanta ne yasa tayi saurin buɗe Qura’an ɗin ta.

Dan dubo ayar,

sai kuma duk suka ɗago kansu suka zuwa Khausar dake jikin  window  idanu,

jin ta uzi shaitan tare da yin basmalla kana  taja numfashinta tare da lumshe idanu murya cike da tajwed ta fara jan ayar.

Surah Al-Ahzab aya ta 41:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا

Murmushin mai cike da jin dadin Asma’u Ahmad tayi tare da sauƙe numfashin, FATTANAH ta ɗauki belinsu kamar yadda aka saba, domin in dai batun jane na ƙwaƙwalwa to kwanyar Khausar ta musamman ce.

Mata da yawa kuma cikin manyan mata kallonta sukeyi cike da sha’awa da jin daɗin zazzaƙar muryarta na kuma ratsa musu kunnuwa.

 

Shi kuwa Moddibo ba tare da ya juyo ya kalle taba.

Ya fara kawo musu fassarar ayar.

“Allah madaukakin sarki yana cewa:

Yaku waɗanda suka yi imani, ku ambaci Allah ambato mai yawa.

Ammato kuma na haƙiƙa bawai kawai kije kiyi karatun Qura’an kara zube ko gatsa-gatsa ba, kuyi karatu kwatankwacin yadda tayi inma kunce juyawa ih zuwa irin nawa da wuya.”

Cikin sanyi Asma’u Ahmad tace.

“Malam ai karatun Khausar irin nakane, ba banbanci kawai dai, ita muryar mata kai muryar maza muna son mu koya irin ƙira’ar sosai.”

Kai ya ɗan juya ya ɗan basu baya tare cewa.

“In sha Allah zaku iya”.

 

Samira Sani kuwa, tattausar sajensa ta zubawa idanu cikin wani irin salo dake cikin jiki da zuciyarta.

Shi kuwa Moddibo a hankali ya kuma yin gyaran murya tare da  cewa.

“A wata ayar kuwa cikin suratul A’araf aya ta 205. Allah maɗaukakin sarki na cewa…

Sai kuma yayi musu alamun suja ƙira’arar.

Cikin kauda kai Khausar ta lumshe idanu ganin wani irin masifeffen kallon daya watsa mata, wanda saida taji hantar cikinta ta kaɗa.

Cike da dagiya a fagen neman ilinta dan bata wasa kuma bata barin tsoronsa ya hanata fahimta, cikin nitsuwar da take samu in zatayi karatu  tayi bismilla tare da fara jan ayar.

“Surah Al-Araf, aya ta 205:

وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ

Ta dire ayar da sauƙe nannauyan numfashi  sabida tagib da taja, wanda dole ta ɗan riƙe numfashinta na kusan second 32.

 

Samira kuwa, wani irin malolon bakin cikine, ya tokare mata maƙoshi, sabida masifar kishi da takaicin yadda ko yaushe Khausar ke gaba dasu.

Asma’u kuwa sai murmushi takeyi,

Yayinda da yawa suke fatan Allah ya buɗa musu kwakwalensu kamar na Khausar.

 

Shi kuwa Moddibo a hankali ya fara fassara musu ayar.

“Abinda Allah madaukakin sarki yake cewa.

(Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin zuciyarka, kana mai ƙanƙan da kai,  da tsoro, ba da ɗaukaka murya a, tsaka-tsaki tsakanin asirtawa da bayyanawa da safe da kuma maraici, kuma kada ka zamo cikin falaki,.

A wata ayar kuwa, Allah madaukakin sarki na cewa.

(Da masu ambaton Allah,  maza,  da masu ambaton sa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai  girma)”.

Sai ya kuma ɗan tsagaita wa tare da kallonsu yana cewa.

“Makfut?”.

 

“Na’am”. Suka amsa baki ɗaya,

“Ɗayyit”. Yace tare da kallon agogon hannunsa, ganin saura 9 minute lokacin da ya kamata ya sallamesu yacika ne, yasashi ci gaba da cewa

“Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

(Misalin wanda yake ambaton Allah da wanda baya ambaton Ubangijinsa kamar misalin rayayya ne da matacce.

A wani wurin kuma yace.

(Shin bana baku labarin mafi al’khairin ayyuka ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Sarkin da yake mallakarku,  kuma mafi ɗaukakarsu, ga darajojinku,  kuma mafi al’khairi gareku daga ciyar da  zinariya da azurfa, kuma mafi al’khairi gareku daku haɗu da  abokan gabanku ku riƙe dukkan wuyoyinsu kuna dukan wuyoyin suba?)

 

Duba Sahihul Bukhari, tare da sharhinsa Fathul Bari (11/208)  Muslim ya ruwaito da lafazin:

Misalin gidan da ake ambaton Allah a cikinsa da wanda ba’a ambaton Allah a cikinsa kamar misalin rayayya ne da matacce, (1/539)

Sai Sahabbai Sukace ka bamu labari.

Sai yace musu.

(Ambaton Allah madaukaki sarki)

Kuma yace:

Allah madaukaki yana cewa:

(Ni ina tare da zaton bawana dani,

Kuma ina tare dashi idan ya ambaceni, cikin ransa, zan ambaceshi a cikin raina,

Idan kuma ya ambaceni a cikin jama’a zan ambaceshi a cikin jama’ar da ta fisu al’khairi, in ya kusanceni taƙi ɗaya, zan kusancesa kamu guda, in ya kusanceni kamu guda, zan kusancesa  tsawon gaɓa guda, in yazo min yana tafiya zan zo masa ina gaggawa)”.

Sai kuma ya fesar da sassayan numfashi a hankali tare dasa tafin hannunsa ya shafa tattausan sajensa, yana mai lumshe idanunsa alamun cikekkiyar nitsuwarsa buɗe idanun yayi a hankali tare da cewa.

Tirmizi (5/459). da Ibn Majah, (2/1245). duba Sahih Ibn Majah (2/316). da kuma Sahihul Tirmizi  (3/139). Bukhari (8/171). Da Muslim (4/2061) lafazin riwayar na Bukhari ne.

Cikin nitsuwa ya kuma juyowa ya fuskacesu, murya cike da kamala, da tashin lafazi yace….!

 

 

 

*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

 

_Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma na dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi Gumbar Ukku al’khairi, Dukansu  garukan da gumbunan akan  dubu uku uku ne sai gumbar Riɗi da uku khairi su dubu biyar biyar ne ! Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace ta koma tamkar budurwa 7k, kana masin Daɗi har Maɗigan mai masifar kyau da kwaranyo da ni’ina 5k

Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa 8k, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi duka a dubu uku-uku ne ƙananan robobinfa, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, set dinsa dubu goma in kuma komai rabi-razi zan sa miki 5k ne butar sirri da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai duba littafin (Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci ga kuma account no 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, kina iya tura kuɗinki kafin ma ke min mgn duk abinda na irga akwaisu Available…._

 

 

 

🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

 

 

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button