Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 26

Sponsored Links

026
___________________
A tsorace Adnan ya miƙe ya nufo shi tun kafin ya karasa
“Ina yini”
Maimakon ya amsa rike kugu yayi kamar mace “wane ma kace sunanka?”
A sanyaye yace “Adnan ”
“Eheeeen ,Adnan,Naga kyautan da ka baiwa mata na,Nada gode sosai….amma kasan kuwa matan aure ce😨” yana masa magana ya zazzare masa ido masifa_masifa.

“Oga izi…izi kaji Easy kana ta ɗaga murya ,in ma kayi magana a hankali ai zan jika…da Adnan kake magana ba da duk duniya ba”

“Naƙi inyi magana a hankalin ,tmbyr ka nike yi ,kakuwa san matar Aure ce?”.
Jinjina masa kai yayi with affirmation “Ƙwarai na sani ,kuma ina matuƙar Alfahari da saninta a rayuwa na…

Ras ! Gaban sheikh ya faɗi a harzuƙe ya nunoshi da yatsa ,kafin yayi magana ,Adnan ya maza ya tari numfashinsa a nutse

“Salima macece mai mutuntaka ,komai naka abun girmamawa ne a wajen ta ko a gaban kowa nunawa take kaine shugaban da ke jan ragamar rayuwarta ,such a wife material da kowani namiji ke fatan samu…na taya ka murna Bros…Allah ya Albarkaci auren ku”

Ya daki kafaɗarsa da ƙarfi ya juya zai koma ciki wani abu na masa tuƙuƙi a zuciya ji yake kamar ya shaƙe Sheikh ya mutu kowa ma ya huta

Sheikh tsayawa yayi kamar gaɓo ,jin ya taso zai masifa amma an fake da yabon matarshi a kanshi …. “Nagode sai anjima”

Ya ɗan ɗaga murya ,kana ya juya yana ƙoƙarin cire bolt ɗin saƙatar gate ɗin gidan ya fita ,Adnan jinjina masa kai yayi yana ƙoƙarin kanga waya a kunnensa ,baya so damuwa tayi tasiri a zuciyarsa ko kaɗan.

Wani ƙuuuuuuuuu🚗Yaji giftawar mota da gudu cikin tuƙin ganganci
“Wayyo ya Sheikh ɗinaaaaaa😔😭” fuyiiiiiii motar ta gifta ta gabansa…A tsorace yabi bayan motar da kallo ,Da ya tabbatar ya jiyo Muryar Salima ta ciki .

A plate number motar an rubuta BAD BOYS da manyan baƙi ba Number motar .
Saida motar suka gifta da kamar second goma ,wawan ya tafi duniyar tunani kafin kamar an gaura masa mari ya ƙwalla Kiran “Salimaaaaaa!!!” ya dirkaka da gudu yabi bayan motar .

Dam gaban Adnan ya faɗi yayi cilli da wayar hannunsa ,yabi bayan Sheikh da gudu

“Malam…Malam ,ka tsaya me ya faru da Salima ta ”

Jin Muryar Adnan a bayansa bayan ya shanye dogon layin nan har sun ɓace ma ganinsu yasa ya faɗi a ƙasa ,yana nuna masa hanya

“Shikenan sun sace mun mata….wlh Salima ta ce sun gudu da ita. ”

Adnan da ya gama ɗaukan ya sheikh Mai karamar ƙwaƙwalwa sam bai yarda da surutunsa ba don haka ya falla gidan Sheikh da gudu yana kwarara mata kira ,saida yaji tsit ,yana shiga lungu da ƙofa na gidan bata ba motsinta kana hankalinsa ya dawo jikinsa .

Ta tabbata sun sace mun ita…To suwaye wannan

“Salimaaaaaa” kawai ya rushe da wani irin gigitaccen Ihu,wanda yafi ka Sheikh ɗin ma

 

Oum Aphnan
#BAD BOYS
_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button