Qamshi Complete Hausa Novel

Qamshi 6-10

Sponsored Links

*✨QAMSHI  6-10 ✨*

 

 

*✍️Rashow*

 

Wani irin kallo Baba me zuma yabi mama saratu dashi irin kallon baki da hankalin nan,sannan ya kad’a kanshi yayi wucewar sa cikin dakin shi ba tare daya tsaya sauraran shirmen taba.

 

sororo mama saratu ta tsaya tana bin bayan Baba me zuma da kallon mamaki.

 

tafa hannun ta tayi tace.

 

“oh ni saratu! Tabbas malam yau zama bai ganka ba, don futowa zakayi ka sayomin kwai a duk inda ake siyarwa don tunda nasa rai na akan zanci kwai tofa yau senaci tukun na hankali na zai kwanta.

 

Rabe dake tsaye a gaban rijiya zai dibi ruwa a ciki ne ya ajiye gugar hannun shi ya matso kusa da mama Saratu yace.

 

“Mama tunda adda khubra bata bayar da kwan ba,to ke me zai hana kikawo kudin ki kawai nasiyo Miki a gun Isiya me shago.

 

Wani irin muguwar Kallo mama Saratu tayi ma Rabe tana jin kamar ta Kai mishi bugu a bakin daya ambaci ta bada kudin.

 

a fadace mama Saratu ta watsa mishi harara tace.

 

” Nabi kudin da gudu na takeshi babu takalmi.

 

lallai Rabe yau ka dad’a tabbatar min da cewar sunana saratu sarkin asara.

 

Yo inba hakaba Kai har kace na bada kudi na sayama kartin banza kwai suci su lashe baki,to wllh kowama ya hakura inbe karbo kwan agun yar gadaran ba to nima bazan cire sisi na na siyaba don ko Ina da kudin to Ina da abun yin da zanyi da kudin .

 

A fusace ta juya zuwa d’akin ta tana cigaba da surutai.

 

Shigowar kamal kenan daga sashin mama Tabawa ya tarar da mahaifiyar shi tana wannan jidalin ya kalli kanin shi Rabe yace.

 

“Rabe wai yau waya tabo mana mamar mu ne da sanyin safiyar nan haka ?

 

Seda Rabe yaja numfashi sannan yace.

 

” wallahi ya Kamal yau mama ce ta dage wai setaci kwai kuma bata da ko Kwan dala kuma kasan halin Adda khubra bata bada bashin kwai din ta,shine fa mama taji haushin hana ta kwai da Adda khubra tayi taketa fada.

 

” Allah ya kyauta to.

 

Cewar Kamal yana me qarasa shigowa cikin sashin nasu shikuma Rabe ya cigaba da dibar ruwan shi.

 

*****************

 

Numfasawa Alhaji Mansur yayi tare da kallon babban danshi yace.

 

“tun dazu fa nake maka  magana *HATIM* amma Kayi shiru ka barni se magana nakeyi ni kad’ai na.

 

Wata irin qaya tacciyar murmushi kyakkyawan matashin da aka kira da suna Hatim yayi har Seda kyawawan hakoran shi wanda suke Jere reras a bakin shi suka bayyana,murmushin da bama kowa yake yima irin taba se wa mutum biyu ko zuwa uku,Shima sei ta kama ne don yana jimawa kafun kaga yayi murmushin da hakoran shi zasu bayyana gaba daya,hakan ma iya ma alhalin shi yakeyi wato Ammee da Aby se kuma Jiddy wato kakar shi mahaifiyar baban shi wacce suke zaune gida daya da ita se dai kowa da sashin sa.

 

Numfasawa Hatim yayi tare da dago narkakken idon shi wanda akoda yaushe zaka ganshi kamar me jin barci ya kalli Alhaji Mansur koshe,Seda ya dan dauki lokaci kafun ya bude bakin shi da kyar kamar Wanda aka mishi dole yace.

 

“Aby yanzu ni me Kake so nace anan?..

 

Baki na bude na gyara tsayuwa kawai Ina Kallon ikon god,sabida tsananin dadin muryan Hatim, muryan nashi tana dauke da izza da kuma qasaita ga wani irin kwarjinin da take qara mishi idan yana maganar.

 

gyara zama Aby yayi yana fuskantar Hatim yace.

 

“Hatim wani irin magana ne zaka ce ba kasan me zaka ceba.?

 

” Please mana Aby! tun fa last zaman da mukayi da Kai na baka shawarar ku canza manajojin ma’aikatan ku kaida Jiddy amma kukayi buruss da magana ta tun abun bai Kai haka jagulewa ba.

 

Sosai Aby yake kallon Hatim wanda yake sauke numfashi da kyar da kyar, dan yayi Yar wannan maganar kamar Wanda yayi gudu.

 

“yanzu Hatim kana ganin sauya manager kowani kamfani na shine samun maslaha na lalacewar da kamfanin nan tayi? Kuma hakan kana ga kamfanonin zasu samu cigaban da aka rasa?

 

Kai Hatim ya gyada ma Aby tare da lumshe idon shi ya furta.

 

” In sha Allahu hakan muke fata da kuma sa rai.

 

Girgiza kai Aby yayi sannan yace.

 

” har yanzu dai Hatim kana nan akan bakan ka naqin amsar kamfanonin nan a hannun ka kaja ragamar su ko?ka tattare a naka kamfanin abun ka.

 

Murmushi Hatim yayi yace.

 

“Aby bazan iya hada aiyuka dayawa a kaina ba, wannan ma da kyar nakeyi Jin kaina nakeyi kamar aiyukan sun min yawa.

 

Murmushi Aby yayi tare da daga kafada ya mike yace.

 

” ni zan tafi, zanyi kokari zuwa gobe naga mun zauna da ma’aikatan kamfanin duka semu ga abunda zai yiyu.

 

Ya mika ma Hatim dake zaune akan kujeranshi hannu su kayi musabuha kafun Hatim din ya taso suka futo yana ma Aby rakiya har bakin motar shi,Seda Aby ya shiga motar da aka kawo shi direba ya shiga yaja motar suka bar haraban ma’aikatan  abincin kaji dasu kifi da duk dai wata dabba, wannan kamfanin ba kamfanin kowa bane illah na Hatim,bama wannan ne ka dai kamfanin Shiba yana da Kamfanoni da dama a qasar waje.a hankali Hatim ya sauke numfashi tare da juyawa ya nufi sama yanda office d’inshi yake.

 

Bai Cika zama a Nigeria ba, amma duk lokacin da yake Nigeria to yakan zauna a office d’inshi na nan Nigeria yayi aiki sosai.

 

Hadaddiyar agogon diamond din dake daure a hannun shi ya kalla ya sauke numfashi sannan ya tattare wayoyin shi ya danna wani abu dake ajiye asaman tabur din dake gaban shi kamar bell haka abun yake, zuwa can Sega wani matashi ya tawo yana zuwa bakin kofar office din yaci burki tare da Sanya hannu a jikin kofar office din yayi nokin,bai shigo ba har Seda Hatim ya bashi izinin shigowa sannan ya shigo, bai tsaya tambayar komai ba ya fara tattare Kayayyakin da yake kan tubur wanda Hatim din yazo dasu yayi amfani dasu irin laptop da wasu takardu, Seda ya tattare duk abunda ya kamata sannan ya dan risina yace.

 

“ranka shi dade angama hada komai.

 

Ido Hatim ya lumshe tare da sake jingina jikin shi da kujeran da yake Kai.

Seda ya dauki tsawon minti goma a haka sannan ya mike suka futo daga office din wannan matashin shine ya rufe office din sannan ya biyo bayan Hatim din da sauri suka Jera har zuwa wajen elevator suka shiga ya saukar dasu zuwa kasa yanda motacin sa suke.

 

***********

 

Tunda naji futar Baba Alhaji daga sashin mu na dawo falon na zauna kusa da hajiya Diddy wacce take ta santin dankali da kwai d’in dana soya mata.

 

Kallon ta nayi na kada Kai na nace.

 

“hajiya ta irin wannan Santin dankali haka ?

 

Ko daga Kai Hajiya Diddy ba tayi ba bare ta kulani har sanda tagama santin ta tas sannan ta dubeni tace.

 

 

” daman so nakeyi nagama nakira ki don haka zauna da kyau inason muyi magana.

 

gyara zama na nayi a qasa kamar yanda tace.

 

“me kike ganin zakiyi da kudin da mahaifin ki yace zai baki?

 

Baki na bude Ina Kallon Diddy har Seda ta Kai karshen maganar ta nace.

 

” kai hajiya! wllh harkin razana ni, nafa zaci wani magana me girma zaki gayamin ni har kinsa gabana yana ta faduwa.

 

Ware hannu Diddy tayi ta nuna ni tace.

 

” kinci gidan ku! yanzu wannan ba magana me girma bane kike nufi a wajen ki?Kai amma dai kekam khubura Allah ya gyara min ke.

 

Baki na turo gaba nace.

 

” to inbanda abunki Hajiyata Ina kikaga an taba lissafin kudi mutum besan yawan kudin da za’a bashin ba?

ai kamata yayi mu jira muga idan yakawo kud’in se muga nawa ne idan yaso sena zauna na tsara abunda nakeso nayi dasu,daga baya idan nayi lissafi sena gaya miki abunda na tsara don jin shawarar ki a game da tsarin nawa, kedai yanzu kawai mu zuba mashi ido muga nawa zai bayar.

 

kanne ido kakus tayi tare da cewa.

 

“wai yaya naji kina cewan mujira mu zuba mishi ido mugani?

Ai ni na zaci yanzu zai tafi sashin sa ya dauko kudin ya bayar?

 

Diddy tayi maganar tana me qarasa mikewa tsaye daga kan kujeran da take zaune akai.

 

Binta da Kallo nayi nace.

 

” Ni dai a fahimta na gaskiya inaga ba yau yake nufiba amma bari dai mu jira mu gani.

 

“muga wa”?

 

Diddy tayi maganar tana gyara daurin zanin ta daya kunce tana wani zaro ido waje.

 

“cab din ai ni kam zama bata ganni ba,tabbas bakin daya furta zai bada kudi tofa bakin shi zaisa ya bamu kudin nan a yau, don bazan tsaya sanya har matan sa suji labarin nan ba kinfa San mutum da kudi se Allah mu muna nan zaune muna jiran zai kawo kudi shikuma suna can suna juya masa lissafi yazo ya hana kudin nan,don gaba daya na fahimci hidimar gidan nan kamar akwai has aciki,don nasan hakan ba k’aramar aikin su bane nikam kinga fucewa ta a gidan nan gara na taro kudin nan tunda zafin ta.

 

hanyar futa a falon Diddy ta nufa,se kuma naga taja ta tsaya cak tare da juyowa tace.

 

“khubra yi maza ki shiga d’akina a durowan dake kusa da gado na zaki ga wani durowa ki Jawo a hankali,zakiga laida viva bag maza ki dauko min.

 

Da sauri na shiga dakin na duba yanda tace na dauko na kawo mata.

 

Seda Diddy ta Kade ledar ta leka sannan tayi ajiyar zuciya tace.

 

“Alhamdulillah Kinga wannan laidar aciki zan zubo kudin idan ya bani, kinga laidar baqace maganin masu rufa ido kenan Allah dai ya dauramu akan duk wani me nufin mu da sharri, duk wanda kuma yake son ganin gazawar mu to Rabbi kasa seya biyo ta qasar takalmin mu kafun ya wuce,ni dai na tafi seki bini da addu’ar dacewa.

 

tsabar mamakin Diddy ne ya hanani cewa komai harta bar sashin namu.

 

 

“Assalamu alaikum!yaaa Mu’azu gani nan tafe.

 

Hajiya Diddy kenan wacce ta wage muryan ta tana rafka sallama a kofar sashin Baba me zuma.

 

Mama tabawa dake kishin gide a d’akin ta tajiyo muryan hajiya Diddy,wuffff Maam Tabawa tayi ta futo daga dakin nata murmushi dauke asaman fuskar ta tace.

 

“Hajiya Diddy kene tafe”? maraba maraba

 

“Ina kwana Hajiya Diddy”

 

wani kallo Hajiya Diddy tabi mama Tabawa da dashi sannan ta kauda kanta gefe tana kare ma gidan Kallo tana yatsina fuska kamar me jin warin wani abun kafun ta maida kallon ta zuwa kan Tabawa da take tsugu ne daga gefe tace.

 

“Amma dai Tabawa ku Kam kun yi haddar gulma wallahi,tsabar haddan da kukayi kwararo kwararo an San da zaman ku,in banda jin tsegumi daga jin na kira sunan dana Mu’azu ke se kiyi wuff ki fito kamar wacce ki kaji nace ina Tabawa take?

waini tsayama tukum na tambaye ki, shin ko kin canza sunan ki ne kika Koma Mu’azatu ban sani ba?

 

kanta mama Tabawa ta girgiza alamar a’a.

 

” ai na zaci kin sauya sunane ban saniba?”

 

Kara sadda Kai qasa Maam Tabawa ta kuma yi don ta rasa abun cewa.

 

Ina tambayar ki nayi?.

 

nace kokin saki tabawa ne kika riqi Mu’azatu wato takwarar sunan Mu’azu kenan?

 

Kai mama Tabawa ta sake girgiza wa don babu bakin magana.

 

“inba gulmaba daga jin nace Mu’azu seke kiyi futt ki fito Salam Salam dake kamar wacce akayi ma kiranye,dama sunan ki Mu’azatu ne sekice yayi kusan kamar sunan na ki,to se naga Ina had’in tabawa da Mu’azu fisabilillahi in ba son gulma ba?yanzu nasan cewa zakiyi gaisheni kika futo kiyi.

 

Tayi maganar tana kwaikwayon muryan Tabawa tana binta da harara.

 

” to billahillazi karrr nake kallon mutum ehe, ai da In da gaske kina son ki gayar dani din ne ai kin San hanyar sashina,da tun asuba kinje can kin gaisheni, to bazan amsa gaisuwar ki anan ba tunda nan ba  gida na bane kuma nina tako takanas nazo har inda kike,maza tashi ki juya kiyi sashin ki hala  bakya rasa abun yi ba acan don ni banson iyayi,kuma ki bude kunne kiji ni da Kyau gurin Mu’azu d’ana nazo bagun Tabawa ba dukan ku kuma kusani duk abunda kukayi ma uwar wata tofa kushirya karb’an saka mako au badade au bajima,don kun haifi mace kun haifi namiji wataran duk abunda kuka yimin tasss se anrama min abunda kakumin akan ku,kuma tunda babu abunda na muku na cusgunawa se aikin alkhairi dana muku na haifa muku d’ana danayi a cikina har ya girma ya auro ku kuke rufa ma juna asiri kuda shi.

 

sim sim Mama Tabawa ta tashi tayi cikin sashin ta.

 

Maam saratu dake labe  daga bakin kofar da zai  hada sune ta kunshe bakin ta se Zabga dariya ta keyi tana Allah shi Kara.

Seda tayi me isar ta kafun tayi futttt tafito ta d’aya kofar da zai hadasu a tsakar gidan su,fuskarta a sake kamar ba taji komai ba ta dubi Maam Tabawa tace.

 

“Tabawa Ina zakije ne haka?”

 

Maam Tabawa bata kula Maam Saratu ba domin ta shaqa dayawa taji haushin kwafsa mata da Diddy tayi don taso jin dame hajiya Diddyn tazo don tasan bata xuwa sashin su haka kurin seda dalili.

 

wucewarta tayi tabar Maam saratu tana mata dariyar mugun ta a ranta.

 

**************

 

futar hajiya Diddy na mike na cigaba da gyaran sashin mu,nagama goge ko Ina se kyalli yakeyi na sauke labulaye tare da rufe kofar falon nashiga cikin gidan na dibo gaushin wuta nazo na kunna turaren wuta d’an borno me dad’in qamshi nan take dakin ya dau qamshi me sanyi ,sannan na nufi bayi (toilet) don nayi wanka .

 

***************

 

Qamshi ! Ke qamshi!!

Nifa tsiyana dake kenan ata kiranki kina nan kina wannan wahalallan lissafin naki,to yi maza ki fito ga babban lissafi ya samu.

 

Cak na ajiye biro da takardan da yake hannu na nafito daga cikin dakina Wanda yake acikin falon sashin Diddy,Ina ware ido na don naga wani lissafin ne hajiya Diddy take fadin yafi wanda nakeyi.

 

bakar laidan dake hannun ta ta mikomin,kallon miye wannan na mata Ina me bin laidar da kallo.

 

“ke banson iya shege miye hakan Ina baki abu kamar Ina baki Kashi bazaki sa hannu ki karba ba,to kidai tsaya iyayi kiyi ma kanki don kudin da alhajin ku yace zai baki ne naje nayi yaqe-yaqe da qone-qone na karbo miki kinsan ni banison jir……….

 

ai ban tsaya naji ka rashin maganar Diddy ba na wafce laidar har sanda hajiya Diddy ta furgita ta kurma salati.

 

” innalillahi! khubra kinada lafiya kuwa zaki karyamin hannu na, yanzu khubra sakayyar da zaki min kenan? takanas na tashi naje na titsiye dan marayan allah nan na karbo miki kudin wai don karki rasa shine zaki zubar dani agefe?to kidai gyara halinki nikam bazan iya miki ba inkin isheni tsaf zaki barmin sashi na ki koma can gun matan ubanki suyi yanda sukeso dake.

 

dariya nayi Ina me rungume Diddy nace.

 

“Afwan sweet Diddy na wllh babu me rabani dake se Allah kuma in banda abunki Diddy ai kinsan murna ne tamin yawa har na rasa yanda zanyi.

 

Da sauri na sake Diddy na shige cikin daki na, hannu na yana dauke da jakar kudin da Diddy ta bani.

 

ban wani dauki lokaci ba nafito nasake fadawa jikinta Ina murna don Sam murmushi yakasa barin fuskata.

 

Kallo na Diddy tayi da mamaki tace.

 

“ina kuma kika Kai kudin.

 

” shiiiiiii kiyi shiru Diddy ki daina ambatar kudin nan da qarfi kinsan ance kudi al’aura to don haka kiyi qasa qasa da muryar ki,ke in banda abun ki Diddy taya zamu bude kud’i irin wannan da rana tsaka?

salon kiga manyan garada akan mu,to nikam ba dani za’ayi haka ba, dole mu jira se dare ya raba shine lokacin da naji a kace ana lissafin kudi irin wannan,shin Diddy bakiji mutane suna cewa masu kudi basu barcin dare ba? to don haka kema ki jira se zuwa jibi ko cikin dare zamu bude mu k’irga.

 

au bama daren yau za’a bude kudin ba?

Diddy tayi tambayar tana bud’e baki.

 

“A’a ba haka nake aikina ba Diddy,dole ne kibi tsari na zuwa gobe na tara yara na musu sadaka, sannan nayi istihara mu roki alkhairi game da abunda zamu fara da kudin ……

 

*Rashow*

Allah ya jikan iyayen mu.

 

07052100719 chat me up if you want.

Leave a Reply

Back to top button