Qamshi 21-25
Please share and repost
Zaku iya sharing
Keep sharing
https://chat.whatsapp.com/KTlVcjaVxhk1Ab6j5wxRDi
Ina matukar jin dadin sharhin ku masoya na.
*✨QAMSHI 21-25✨*
✍🏿RASHOW
Kimanin kwana uku kenan da dawowar mu gidan da aka bama Baba Alhaji,gidan babba ne don yafi gidan da muka baro girma, Shima yana da sashi sashi kamar gidan mu kowacce ta dauki sashi daya kamar yanda Baba Alhaji ya tsara ma kowa.
tunda mukazo gidan yaune rana ta farko da muka shigo gidan ogan Alhajin mu wanda katangar gidan yana hade da namu se akayi wata qofa wanda yake haraban sashin da Hajiya Diddy ta zaba, idan ka futa ta kofar zai sadaka da qaton haraban gidan ogan Alhajin mu don haka Diddy tace mu shiga tanan ita bata son wannan doguwar tafiya ace wai seta zagayo ta bakin gate.
da ido mukabi qawattacen haraban gidan me matuqar kyau da d’aukar hankali,ko Ina na gidan abun burgewa ne da daukar ido shi kanshi interlock din dake haraban gidan daukar ido yakeyi ga wani titin dayake malale da kwalta,daga gefe kuma an qawata haraban gurin da fulawoyi tako Ina gwanin burgewa, sosai gidan ya burgeni baza idon mu mukayi nida Diddy muna Kallo har muka Kai wani sashin da yake kusa da kofar da muka futo duk da Shima sashin sekayi tafiya me dan nisa amma tafiyar bai kai wanda zakayi kafin ka qarasa wani qaton sashin da muke hangowa daga nesa damu ba,hakan nema yasa Diddy tace mu shiga wannan da yake kusa mugani ko nan ne gurin masu gidan don ita bazata Iya jiran Baba Alhaji ba wanda yace su jirashi zai shiga damu dukan mu a gaisa amma tunda mukazo aiki yayi mishi yawa idan ya futa tun farar safiya se goma na dare yake dawowa.
Sosai Karan wayar shi dake kan durowan dake gefen gadon barcin shi ya takura ma barcin da yakeyi,zuro hannun shi dake cikin bargo Hatim yayi ya lalubi wayar da ake ta kira tsawon lokaci.
Daga Kiran yayi ba tare daya bude idonshi me cike da Zallan barci ba ya Kara wayar a kan kunnan shi ba tare dayace komai ba sanin hakan da wacce ta kira wayar tayi ne yasa ta sauke numfashi na godiyan samun sa’ar yau ya daga mata Kiran ta da tayi mishi,don ba karamin wuya takeci ba kafin ta samu magana dashi,kasa tayi da muryan ta cikin kirsa irin na gogaggun mata tace.
“Kayi hutawar ka Sadauki na,ga dukkan alamu barci kakeyi?
Banza yayi da ita kamar wanda baiji me tace ba jin hakan da tayi ne yasa ta kara narkar da muryanta tace.
shine zaka yi barci a irin wannan lokacin baka nemeni na tayaka ba?
baki Hatim ya mele kamar tana gaban shi ya bude baki murya a sanyaye yace.
” Hmmmm kamar da gaske?
murmushi wacce ta kira wayar tayi tare da Kara lankwashe murya jin ya amsata tace.
” karka ce haka Hatim kaima kasan babu macen da zaka mata tayin kwanciya da Kai taqi amsar wannan babbar tayin naka, inkuwa kaga mace taqi amsar wannan gayyata naka toka qaddara cewa matar ta kasance mara rabo ne.
“kina daga cikin marasa rabon kenan?
yayi maganar cikin dan jin zafi amma idan ba nutsuwa kayiba ko daman ka San waye Hatim ba bazaka lura cewan ranshi ya baci ba don Kai tsaye yayi maganar,kara sassauta murya tayi da alamun lallashi tace.
” Hatim ka karamin lokaci saura qiris komai ya Kammala zan dawo bada jimawa ba kuma dawowar da zanyi zanyi kokari na goge duk wasu laifukan danayi don zan jiyar dakai dad’in da babu wata diya macen da zata iya jiyar dakai bayan ni,domin banison Ko Yaya ne Kayi tunanin dad’in wata macen idan bani ba,Sadauki Ina nan Ina kular maka da abubuwan dakafiso ka wuta dasu gasu nan duk sun qara girma suna kewarka.
Wani irin sassanyar numfashi Hatim ya sauke a hankali wanda ba lallai bane taji, muryanshi a kasalance hakan yasa maganar bata futa sosai don ya kunnu,kalamanta da tayi masa ne ya saukar mishi da wannan kasalar ya sake lumshe idonshi yace.
“Hmmm haka kika iya ke kullum kina da excuse amma ki sani Safeena daga yau bazan sake daga wayarki ba,don bazan sake jin wasu Kalamai daga gareki ba matukar ba kawomin kanki kika yi ba,ke kullum na daga wayarki Kara jefani a damuwa kikeyi bayan wanda nake ciki kuma kinsan me hakan zai haifar min daga karshe,se kin gama sani a wani hali seki kashe Wayanki ki barni da matse qafa babu abunda ya dameki ko? to ki sani matukar kinason kanki da lafiya ki dawo, karki bari ki quremin hakuri na nakai iya yanda bazan iya jurewa ba,ke ko tausayamin bakiyi?
Safeena kina da imani kuwa?
Dan dakatawa da maganar yayi yana sauke numfashi kamar me cutar asthma, Seda ya huta sannan yace.
“Safeena ke kadai kike sani dogon magana wanda kinsan hakan ciwo yake janyomin amma magana ta qarshe shine ki tattaro ki dawo kuma bance kibi ko Ina ba I mean ko gidan ku ban amince ki fara zuwa ba, idan kin iso ki fara sauka a daya daga cikin gidana idan na ganki daga baya seki tafi gidan naku wannan umurni na ne kuma kwana biyu na baki idan kika tsallake hakan tabbas zakisha mamaki na awannan Karan.
Wani irin shu’umin murmushi Safeena tayi ba karamin dadi takeji ba idan taga Hatim ya haukace akan son tazo su hadu wannan abu yana faranta mata rai hakan ne yasa akoda yaushe idan sunyi waya take mishi kalaman da zasu tayar mishi da hankali sanin irin karfin sha’awar da tasan Hatim yake dashi,kuma wannan alqawari ta dauka bazata bari su haduba har seta ga Hatim yayi kamar zai zauce.
sosai muka sake a sashin Jiddy idan ka gammu seka dauka tuntuni tare muke, danbun nama Jiddy tace in Karo a kitchen idan wanda naci bai isheni ba na mike na Karo na dawo na zauna na kalli Jiddy nace.
“Jiddy amma kajin nan basu girma sosai ba aka yanka ko?
mele baki Jiddy tayi don qamshi ta Sosa mata yanda yake mata qaiqayi fuska a sake kamar wacce zatayi mata kuka tace.
” kema khubra da bakisan kaji ba kya fada, nidai jarabawa Kam Allah ya aikomin dashi se fatan Allah ya bani ikon cinyewa banda asara babu abunda nakeyi a gidan gonar nan shiyasa kullum nake zuwa na kamo kaji sama da guda a shirin na yanka naci ma raina don da raina da lafiya ta bazan zuba ido naga kajin nan suna mutuwa min ba niba da mora ba, ga dan Karan cin abincin da sukeyi kuma gashi sam basa girma kullum nice bada kudi a siyo abinci.
baki Diddy ta bude kawai tana kallon Jiddy harta Kai karshen maganar ta sannan tace.
“yau kajimin wani batu kuma, yo Allah na tuba wani irin kaza ne a duniyar nan wacce qamshin Alkhairi bata sani ba? to bari kiji na gaya miki gidan gona koya Kai girman garin nan a girma ne qamshi zata iya kula dashi, kuma a dan Karamin lokaci kajin zasu girma asayar a samu riba naban mamaki, nidai shawara zan baki kinsan dai bazan cuceki ba don yanzu mun zama yan uwa inaso ki kori duk masu kula da kajin,ki bama diyar albarka ragamar komai kiga yanda kajinki zasu girma suyi bulbul gwanin ban sha’awa zakiga kowa yana sha’awar su wanda ko kallon su Kayi sesun sace maka zuciya kaji kanason ka siyesu ka yanka.
Diddy ta karasa magana tana murmushi.
Zaraff Jiddy tayi tana gyara daurin zanin jikinta wanda ya kunce tace.
“tashi kiga,yanzu ma kuwa zani ku tashi muje gidan gonar yau babu me kwana da aikin gidan kaji na a hannunsa,duk sallamar su zanyi kedai na gode miki da wannan shawara naki.
baki Diddy ta bude tace.
“waaaaa? gaskiya ba zamu biki gurin ba don haushin suma nakeji na Salwantar miki da kaji da sukayi, in banda abun ki idan mukaje tare ai zasuce mune muka zugoki duk da ni dai bani tsoron kowa ato.
Shiru Jiddy tayi kamar me Nazari sannan tace.
” kuma fa hakane yanzu dai ki barmin komai ni nasan yanda zanyi dasu barinje na hadu dasu kowa ya watse ya barmin gidan kaji horon da suke min ya isa haka, yo Allah na tuba ai wannan horo ne tunda gashinan na gani qiri-qiri su dinga kashemin kaji.
tare dukan mu muka fito daga sashin Jiddy wacce zatayi mana rakiya zuwa sashin matar gidan.
Seda muka futo bakin sashin ne Jiddy ta Kalli Diddy tace.
“Aminiya ta kawai kibar shiga gurin Hajaran se zuwa bayan la’asar lokacin na kori wadancan mugaye masu kashemin kaji don kinsan halin mutane yanzu idan taji zan koresu zata iya bani hakuri Kota hadani da basamuden danta yace a bar su tunda ba kajin su bane ake asara, yanzu dai zanyi gum da baki na ne sedai suji na saka sabuwar me kula dasu.
Kai Diddy ta daga tace.
“kema kin kawo shawara yo Allah na tuba nikam tunda na same ki Ina zanje gurin wata Hajara,daman qamshi ne tace aje yanzu zamu bari Seda la’asar din tunda kinga yanzu ma ankusa Kiran sallar yanzu mu bari mu wuce.
juyawa mu kayi muka nufi gida ita kuma Jiddy ta nufi bayan d’akin ta zuwa gidan gonar ta.
Diddy da Khubra suna daf da qarasawa kofar da zai sa dasu da kofar sashin su Hatim ya futo daga cikin falon su yana sanye da black jeans da white t-shirt me gajeran hannu tana da adon wasu stars masu kalan red da black agaban rigan ya daura shirt me dogon hannu a samar white t-shirt din amma bai hada maballan gaban rigan samar ba, hannun shi yana daure da agogo red kala kalan kambas din kafar shi, gashin kanshi se kyalli yakeyi wanda yasha gyara se zuba qamshi yakeyi.
bin bayan Khubra yayi da Kallo tun daga Saman kanta wanda yake rufe da dan siririn mayafi wanda kake iya hango dogon gashin kanta da ya sauko har kusa da mazaunan ta hakan ne yasa mayafin ya tsaya mata iya Saman kanta zuwa wuyan ta, bin kayan jikinta Hatim yayi da Kallo tana sanye da dogon riga dark yellow me adon fulawoyi red and black,rigan tana da dan fadi shiyasa bai kamata ba kuma bai kai har qasa ba,ya tsaya iya kafafuwar ta bai Kai idon sawun ta ba,duk da rigan bai kamata ba hakan baya hana bayyanuwan tudun mazaunan ta sosai manyan hips dinta suke rawa aciki.
farar kafar ta wanda yake cikin wani red slipers yabi da Kallo yana mamakin su waye wadan nan wanda suke kokarin bin hànyar da ba’a bi?
Yana tsaye agurin har su Khubra suka bude kofar suka shiga ciki suka rufo kofar yabar ganin su sannan ya nufi bakin gate don zuwa masallaci.
*Rashow*
07052100719 chat me up.