Qamshi Complete Hausa Novel

Qamshi 1-5

Sponsored Links

 

*✨QAMSHI* 1-5✨

 

 

✍🏿Rashow

 

BISIMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM.

 

 

 

KHUBRA! KHUBRA !! KE KHUBRA !!!

 

“Wai ni khubra bakya gidan nan ne naketa faman Kiran ki kina Jina kin yi banza da ni ?

 

Wata dattijuwace tayi maganar matar ta dan manyan ta.

 

Wata kyakkyawan yarinya na hango zaune akan gado wacce shekarun ta ba zasu wuce shekaru sha bakwai ba (17 years), farace sosai farin ta irin mai yellow ne,tana da round face se manyan idanuwan da take dashi wanda suka Kara ma fuskar nata kyau,ga dan karamin bakin ta wanda yayi pink irin me duhu nan gwanin burgewa.

 

motsa karamin bakin ta naga takeyi amma jin Kiran ta da akayi ne yasa ta turo karamin bakin nata gaba tare da sakko da qafafuwar ta qasa daga kan gadon katakon da take.

 

tana daga cikin dakin ba tare data daina abunda ta keyi ba kuma bata motsa daga gurin ba,ta bude dan micilin bakin ta tace.

 

” Allah Hajiya Diddy kin cika Kira kamar wata tsohuwar makauniya.

 

seki jira na kammala abunda nakeyi nazo,duk da nasan yanzu haka wani abun zan miqo miki shiyasa kike ta kwalamin kira,yanzu haka ma abun yana kusa dake amma sabida son jiki irin naki bazaki tashi ki dauka ba,ke dai kullum kinfi son kiga mutum ya kare rayuwan shi a miko dauko”.

 

Gyara zaman ta tayi tare da cigaba da abunda takeyi ba tare da ta tashi taje taji Kiran da tsohuwar take mata ba.

 

“shin Khubra zaki fito a cikin d’akin nan kuwa ko sena shigo na gamu dake?

 

rai bace kyakkyawan matashiyar da aka kira da khubra ta bar abun da takeyi ta nufi kofar futa falo fuskarta Sam babu annuri,harta Kai bakin k’ofa zata futa se kuma ta juyo tare da dawowa da sauri ta tattare duk kudin da ta baza akan gadon,ta nemi guri mai kyau ta boye.

Seda ta tabbatar sun samu gurin boyo me kyau sannan tafito falo don jin Kiran da tsohuwar take mata.

 

“Hajiya Diddy gani nafito seki fadi abun da zan miki don sauri na keyi ”

 

Da ido dattijuwar ta bi Khubra tana duban ta.

 

kauda kanta gefe Khubra tayi tare da Kara hade fuskar ta.

 

kama baki Diddy tayi tace.

 

“Oh ni Abu! yanzu khubra akan Kiran da nake miki ne shine kike ta faman wannan 6ata fuskar haka?

 

duk da ba’a cikin dakin nan nake ba na tabbata babu abunda kike tsina nawa acikin dakin in banda lissafin karya d……

 

karyafa kikace Diddy?

 

kubra tayi saurin katse hajiya Diddy daga maganar da take fada sannan batare data jirata ta karasa maganar  da take shirin karasa wa bama.

 

ran khubra ne ya Kuma baci kamar zatayi kuka tace.

 

” yanzu tsakani da Allah Diddy lissafin kudaden da zanyi sarin da sune zakice kudin karya?

 

Gyada Kai Khubra tayi tace.

 

” Ehhhh lallai! tabbas ba laifin ki bane hajiya Diddy,laifi nane amma babu komai da Sannu zamu gauraya ni dake.

 

kuma kadan ya rage miki na dakatar da duk wata hidimar da nakeyi a gidan nan.

 

” in banda ma abunki Hajiya Diddy hala so kikeyi na dauki kudin nawa na kaima masu abincin kaji ba tare dana kirga ba,salon na basu kudin yayi yawa.

 

sororo Diddy tayi daga kan kujeran da take zaune a Kai tana kallon Kbubra,sannan ta mele baki tace.

 

“yanzu Khubra inba son bata ma Kai lokaci ba har kya dauki dogon lokaci kina qirga naira dubu uku? tun sanyin safiya fa kiketa wannan lissafin qirge qirgen da yaqi Karewa,kin bata tsawon awanni kina abu daya.

 

“ Hmm Diddy kenan !

 

kefa bazaki taba ganewa ba,Wai kin manta cewar marashi idan ya samu naira dari (100naira) jin kansa yakeyi kamar Wanda ya samu dubu dari ne?

 

To Ina gani nida nake da naira har dubu uku?

 

Khubra tayi tambayar tana kallon Diddy,ganin Diddy ta kasa cewa komai se binta da ido takeyi hakan ne yasa Khubra cewa.

 

“No Diddy bama se kince komai ba ni barin baki amsa.

 

” Wallahi Diddy a yanzu Jina nake yi kamar wacce nake da Naira million uku, shiyasa ma kikaga na kasa daina lissafin kudin nan.

 

Kuma kin san dole na nutsu nayi lissafin abunda zai fissheni,don idan take ne da nayi lissafi da Kar nayi lissafi duk daya suke agurin ki tunda bake kike sayan komai na gidan nan ba shiyasa bakisan yaya duniyar take cikiba na tsadar rayuwan da muka tsinci kan mu aciki ba.

 

Please Diddy barin miki yar Karamar tambaya.

 

” shin kin kuwa San nawane kudin mudun masara da shinkafa a kasuwa yanzu kuwa?

 

To wallahi tun wuri gara ki farka daga dogon barcin da kikeyi don yanzu shekaran yin tattali ne ya kama,kuma da kike maganar cewa  ina ta qirga kudi na kasa gamawa ai ni naga amfanin sake kirgawan da nayi gashi dana sake qirgawan nasamu naira talatin ya hau kan kudin ni dai don Allah Diddy in kinga Ina lissafi kiringa barina nagama Kar ki ringa kira na kina rudani,yanzu dai gayamin Kiran me kike min ne? nabar kudi na acikin daki gara naje na zauna kusa da abuna.

 

” mtssss in kin gama fitsarar naki seki futa Kofar gida ki basu kwai(egg),in kuma sun gaji da jiran ki sun tafi to kinyima kanki,don kamar muryan isiya me shago naj…..

 

Da mugun sauri Khubra ta nufi kofar falon su ba tare da ta jira Diddy ta qarasa maganar taba tana cewa.

 

“a gaskiya Diddy kibar yin haka wallahi yanzu daman ashe arziki ne ya zomin har gida amma fisabilillahi seki zauna timmm akan kujera ki rikeni da maganar da bazai amfaneni  da komai ba fisabilillahi.

 

tana maganar tana karasa futowa tsakar gidan, hakan yayi dai-dai da sake sallamar isiya me shago.

 

“wa’alaikassalam! dan Allah isiya yi hakuri dan jirani gani nan zuwa.

 

da sauri ta juya cikin falon su bata tsaya jin maganar da Diddy takeyi ba ta nufi cikin dakinta ta dauko hijab dinta daga cikin wardrobe, hijab din yasha guga se qamshin turaren Kaya wanda ta Sanya a cikin wardrobe dinta yakeyi, da sauri ta Sanya ta fito ta nufi kofar gidan su.

 

Isiya me shago yana ganin futowar Khubra ya washe bakin sa don Yana tsananin son Khubra duk da yasan a bune me wahala Khubra ta kulashi da sunan soyayya duba da yanda bata kula duk wani saurayin da zaizo mata da suna soyayya, takance anata Kai wake wani soyayya kana nan kana fama da talauci amma kana batun wani soyayya to wallahi gara mutum ya koma yaje yayi Sana’a shi ya nemi kudin sa, idan ka samu kudin ka ko mata hudu kakeso a rana daya zaka samu.

 

“Allah yataimaki hajiya Khubra qamshin Duniya, kina tafe qamshi na binki.

 

Dan yamutsa fuska khubra tayi tare da dan murmusa wa tana wani dan basarwa murmushin da tayi mishin ma don ya ambaci qamshi ne, don ita arayuwan ta tanason qamshi,tana kumason intasa tatawo guri asan lallai taci sunanta khubra qamshin Duniya.

 

A yangan ce kamar yanda ya zamo kamar dabi’ar ta ne hakan tace.

 

“Isiya kiret nawa zan baka?

 

tayi maganar tana duban isiya daya zuba mata ido se washe baki yakeyi.

 

“Kiret uku ma zaki bani, da yake Ina da sauran kwai din a shago.

 

” OK,yanzu dai zan baka kiret biyu da rabi don kwai din bazai kai kiret ukun da kakeso ba,maybe ko zuwa anjima idan kajin sunyi kwai din Sena turo maka da ragowar sauran.

 

Jiki na rawa Isiya ya miko ma Khubra kiret din hannun shi wanda zata zuba mishi kwai (egg)din aciki yace.

 

“ah haba ai wannan ba matsala bane ,ni da Kaina ma zanzo na karba basekin aiko min dashi ba qamshin duniya.

 

amsar roban zuba egg din Qamshi tayi da muryan ta me sanyi tace.

 

” ammafa Isiya yanzu kudin yakaru ba kamar yanda aka Saba bayar wa bane don komai an Kara mishi kudi,abincin kajin ne aka samu Karin kudi.

 

” ikon Allah to allah yasa mudace akawo min haka ai ko nawa kikace haka zan saya allah dai yakaro yawan qamshi.

 

” ameen tafurta tare da shiga gida domin kawo masa kwai din.

 

“Aikin banza a haka dai za’a kare kullum a bulbula qamshi babu mashin shini.

 

mama Tabawa tayi maganar tare da tsayuwa daga shanyar kayan ta da takeyi a igiya.

 

 

Hakan kuma yayi dai-dai da futowar Maam Saratu daga sashen ta tana neman Yaron da zaije mata aika.

 

Kallon Maam Tabawa tayi tare da yamutsa fuska tace.

 

“kekuma dawa kike surutu haka kamar wacce sanyi ya taba ta?

 

mele baki Maam Tabawa tayi tare da juyowa tana kallon Maam Saratun tace.

 

” in banda abun ki dawa kika ga magana ta tayi kama?

inba wancan me kama da Karan raken ba.

 

qan qance ido Maam Saratu tayi da alama itama tana da haushin wacce ake maganar a kanta ne tace.

 

” hmmm kedai bari kawai Tabawa, samun waje tayi shiyasa bata ganin kowa da mutumci a gidan nan,ita game Sana’a tafi kowa kudi gidan nan ko? da sannu zanyi maganin ta, ina me tabbatar miki da cewar matukar Ina numfashi to a haka Khubra zata yita zama ita da sana’ar ta babu cigaba fitsararriya kawai.

 

murmushi Maam Tabawa tayi najin wannan zance daya futo daga bakin mama Saratu.

da harara dukan su biyun suka bi bayan Khubra wanda bata masan sunayi ba,don gaba daya hankalin ta yayi nisa a jera kwai din ta se nishadin ta takeyi,  ita Inka ga tana nishadi to anzo sayan kayan sana’ar tane,sam bata da lokacin su mama saratu takance basuda abun yi ne shiyasa suke wahal da kansu a tunanin wani.

 

 

***********

 

 

yau take juma’atu babbar rana.

 

Baba me zuma baya futa ko Ina a wannan rana na juma’a inba masallacin juma’a ba, se kuma in wani muhimmin abu idan ya taso.

 

kowa nagidan mu yana kasan cewa a sashin su tare da yin wankan juma’a aci ado da sabbin kaya don har sabon abinci akeyi sabida wannan aranar kamar dai ranar sallah.

 

Kuma kowa zai nutsu a gida babu batun futa gurin Sana’a a ranar se dai kowa yayi hidomominsa a cikin gida.

 

ranar yazo a girkin mama Saratu don ita ta karbi girki a yammacin alhamis ta kwana a d’akin Baba me zuma.

 

futowa mama Saratu tayi haraban gidan don takira  yaro ya siyo mata kwai (egg) futowar ta kenan ta hangi Yaron ta yana tawowa zai shiga sashin su tace.

 

“yauwa Rabe zo kaje min gurin wancan Yar gadaran ka karbomin  kwai rabin kiret,kace idan Baban ku ya tashi za’a kawo kudin.

 

da murnar sa ya juya ya nufi sashen Hajiya Diddy don yasan yau zasu dan maida miyau.

 

Seda yazo dab shiga sashin hajiya Diddy sannan ya dai-dai ta tafiyar sa sannan ya shiga sashin bakin shi dauke da sallama.

 

da yake ni agurin Diddy na nake da zama tun rasuwar mahaifiyata.

 

amsa sallamar nayi ba tare dana dago daga abun da nake yi ba.

 

karasowa yayi kusa dani ya rusuna yace.

 

“Adda khubra barka da safiya da fatan kin tashi lpia.

 

” Lafiya Lau na tashi.

 

 

“Adda Khubra daman wai inji mama nane ki bata kwai rabin kiret in baba ya tashi daga barci zata karba miki kudin k……

 

hannu Khubra ta daga mishi ba tare da ta bari ya qarasa ba, ta kada yatsar ta manuniya tace.

 

” ba wannan maganar.

 

 

“wa kake da suna! Rabi’u kake ko Rabe?

 

“kul ka yarda ka karasa wannan batu mara b’ullewa don kasan bana bada kwai dina bashi.

dama mama Saratu tace maka na bata bashin khumra ne,da senayi shahadar quda nabata shima don nasan in ta shafa ubana ne zaiji qamshin,amma batun na bada kwai na bashi sam hakan ma be faruwa bane,zaka iya tafiya na gama magana, maza tafi kayi hidimar gabanka nima kaga aiki nakeyi.

 

juyawa nayi na cigaba da zuba ruwa a robobin kaji don zan shigar musu dashi dakinsu ne daman.

 

tunda Maam Saratu ta hango hannun rabe Babu kwai, kuma taga yanayin fuskarsa tun daga nan tasan yau ma khubra tayi halin nata,Rabe ne ya karaso gun mama Saratu yana me cewa.

 

“ni wallahi mama ki daina turani gurin Adda khubra domin lamarin ta Sam babu sanayya, ya kwashe kaf yanda sukayi da khubra ya gaya ma mama Saratu.

 

batace komai ba ta juya cikin sashen ta rai a bace.

 

Kwafa mama Saratu tayi tana tafiya tana surutu tana cewa.

 

” Yarin ya dani kike maganar, yau tunda na sa a raina se naci kwai tofa tabbas se naci, ai yau uban ki yana gida yanzu zansa yafuto yaje shida kansa ya karbo min kwai na soya naci.

 

” malam!malam !!

 

miqa baba me zuma yayi tareda yin salati ya bude idonsa me Cike da barci ya zuba ma mama saratu, yana jin wani irin takaicin abunda tayi mishi yanzu, jinjina wannan rashin hankali na Saratu yayi, tsabar rashin hankali yana cikin barci me dadi ta katse mashi da wani irin mahaukacin tashi.

 

Kwafa baba me zuma yayi yace.

 

“Dan Allah Saratu yaushe zaki waye ne ke kam?

 

Wari irin tashin mijine haka Saratu ?

 

a mai makon da kikazo tashi na a barci ai kyamin tashin yan gayu,amma fisabilillahi ki dubi irin yanda kike ta dani daga barci.

 

Shin nace se yaushe ne zaki waye ne ke kam ?

 

ace Ina mijin ki kidubi yanda kike tashina abarci kamar wanda kike tashin kwarto.

 

Baki bude mama Saratu take kallon Baba me zuma tace.

 

“ahhh ! Kai kajimin malam, yo inban tasheka hakaba yaya kakeso na maka ?

 

kai kullum in anyi abu se kace mutum be iya tashin ka a barci ba.

 

” mtssss daman ai baki iyan ba,ke ko kunya bakiji kullum kizo kina cewa malam malam, to Allah yasa malum malum ne ba malam ba,mata fa yanda aka sanku an sanku da lallashin miji ne bawai zabura miji ba.

 

Barin baki shawara ko zai miki amfani,in zaki tashe mutum a barci kamar ni mijin ki,Kamata yayi kizo kusa dani kiringa shafani kina mannamin kiss agoshi ko akan bakina ,amma ku matan yanxu sekace matan zamanin da Sam baku iya lallashin miji ba se tsagoron rashin kunya kuka iya.

 

mtssss to waima tsaya! Shin me zan miki yanzun da kika zo kika min qerere akai.

 

yayi maganar yana me kallon Maam saratu da take sake da baki tana kallon shi.

 

cikin gajiya da halin mijin nata Wanda shi kullum yana jin kanshi kamar yaro.

 

kullum shi burin shi a zauna a kusa dashi a ringa shafashi sekace wani mage(cat).

 

mtssss mama Saratu taja karamar tsaki aranta tare da kumbura fuskarta tace.

 

nidai duk ba wannan bane a gaba na don na riga da na hardacce wadan nan zantukan naka, yanzu dai tashi zaka yi kaje kama fitsararriyan yarka magana tabani kwai,na aika a siyomin amma  da yake taga bani na haifeta ba shiyasa ta raina ni ta hanani kwai din, wata qila idan Kai tagan ka ta bayar, kuma wallahi bazan lamunci rashin kunyarta ba.

 

Da mamaki baba me zuma ya Kalle ta yace.

 

“wace yar tawa ne kam kike magana ban gane ba ?

 

 

” kaji Malam da wani Magana.

 

“waye kuwa kaga duk fadin gidan nan zatayi min rashin mutumci batare da tayi shakkaba inba khubra ba, ita kasan ta samu goyon baya a gidan nan shiyasa takeyin yanda taso.

 

 

fuska hade Baba me zuma yace.

 

Ke kuma meya hadaki da Khubra da farar safiyan nan?

 

Baki mama Saratu ta mele tace.

 

“ni kuwa malam me zai hadani da ita? kasan a kullum nakan gujema shiga harkan ta saboda gudun rashin kunyan ta shiyasa inba ta kamaba bani shiga damuwar ta,yanzu ma na aiki Rabe ne na bashi kudi nace yaje gurinta ya sayomin kwai domin insamu in soya maka kafin katashi daga barci don bana son ka tashi ban gama abun karya wa ba, sannan ga hajiya Diddy be kamata ace abun Kari yana kaiwa rana ba bata karya ba, amma budar bakin yarinyar nan setace ita Sam bazata bayarba duk salon mu karya mata Jari,ita ma ta dawo ta tsugunna kamar yaran mu wanda se abun da aka basu Sannan zasu samu .

 

Shiru baba me zuma yayi sannan ya sauko daga Saman gadon ya nufi sashin mahaifiyar nashi.

Tunda ga bakin sashin mu Baba me zuma ya fara sallama.

 

Dajin sallamarsa hajiya Diddy tace yau kuma mu’azu ne nakeji haka da sassaafe?

 

“Assalamu alaikum.

 

baba me zuma ya sake sallama tareda shiga cikin falon yana me zama kan daya daga cikin kujerun falon.

 

“Hajiya barka da safiya.

 

barni kawai Kai dai mu’azu,ka fito fili kawai ka gayamin shin wanene Allah yayi masa cikawa da farar safiyan nan?

 

daga ganima mutuwar keso yayi aka kaishi yanzu.

 

” mutuwa kuma Hajiya?

 

Baba me zuma yayi tambayar yana kallon hajiya Diddy da mamaki .

 

“to Mu’azu inba mutuwa akayi ba Ina kafito da farar safiyar nan haka?

 

naga baka saba shigowa nan sashin da sanyi safiya bane shiyasa nace hala mutuwa akayi.

 

dukar dakai Baba me zuma yayi qasa yana me sake gaishe da hajiya kaka.

 

” antashi lpia hajiya yaya sanyi da gajiyar ayyuka ?

 

” Alhamdulillah ayyuka kam wannan sedai atambayi yar albarka na.

 

tayi maganar tana nuna khubra lokacin da ta fito daga kitchen din da yake cikin falon, hannun ta yana dauke da babban ture wanda ta sanya tea flas akai,gefe kuma plate din soyayyar dankali ne a ciki se gefen sa kuma soyayyar kwai ne.

 

karasowa cikin falon tayi anutse ta ajiye tiren agaban hajiya Diddy sannan ta rusuna tace.

 

“Alhaji Baba barka da safiya antashi lpia.

 

 

murmushi baba me zuma yayi sannan ya amsa mata gaisuwar da take mishi.

 

” lpia lw khubra Yaya hidiman kaji?

 

Caraf Hajiya Diddy tayi tace.

 

“ai ba kaji kadai take hidimaba harda ni tsohuwar ka take hidimtawa.

 

murmushi nayi wanda har Seda gefen fuskata ta lotsa nace.

 

” Baba alhaji  barin kawo maka abun karyawa.

 

Kitchen din na koma na fasa kwai (egg) guda uku na soya mishi sena juyo sauran dankalin dana bari a kula na zuba black tea a flas na kawo na ajiye a kasa na  tsiyaya masa tea a cup tareda mika masa,ya karba ya ajiye akan tebur din dayake gabansa Wanda na daura plate din chips da kwai akai ,yaduben cikin nutsuwa yace.

 

“hajiya khubra me kaji da kwai ,wato dadinku  kawai kukeji keda hajiyar ki shi yasa kuka yi jazur daku.

 

murmushi nayi Ina me sunkuyar da kaina,don nasan zolaya ta alhajinmu yakeyi .

 

” to Amma khubra meye ya hadaki da mamar taku ?

 

na dago kaina da alamar mamaki Ina girgizawa alamar a’a.

 

” to idan bake ba akwai wata bayan ke dakike gabana ne me suna Khubra ?

 

“Aa’uzzuki bikalimatullahi,aniyar kowa ya bishi, da ikon lillahi babu wanda ya isa yayi miki komai.

 

dukan mu Hajiya Diddy muke Kallo don jin abunda take cewa.

 

 

” eyy Kalleni da kyau Mu’azu!

 

” saratu dai ta gyara halinta,menene abun juya magana anan inbason shiga tsakanin ya da uban ta ba?

barin mayar maka da yanda akayi tinda abunda ta turoka kaji kenan idan yaso in na gama baka labarin daga baya seka hada dani da khubran karufe mu da duka.

 

“inace cewa tayi abata bashin kwai inta samu kudi zata biya daga baya,dake ita qamshi Yar albarka ne tace wa rabi’u.

 

“rabe kaga wannan kwai din duk dama su shi nariga da karbi kudin su akan zan tara musu,a hakan ma ban gama tarawaba saboda kajin basu dayawa guda 20 ne,kaga bazai yiyu na sayarba bayan nakarbi kudin mutane alqawari baice haka ba,ko zakaje mata shagon isiya ko zaka samo mata?

 

Kallon Baba me zuma  Hajiya Diddy tayi bayan ta gama bama baba me zuma labarin tace.

 

“duk Ina zaune agefe sukayi haka *(oh kaji tsohuwa da tsari)*

 

shikuma rabe da kake gani,da yake yaron zamani ne shi,da yaje gurin maman nashi seya gayama uwarsa karya da gaskiya,don su aikinsu kenan zaman gulma .

 

Shiru baba me zuma yayi tare da gyada Kai kawai yana mamakin hali irin na saratu don abunda ta gaya mishi daban da abunda yanzu yazo ya tarar.

 

cigaba da karyawan su sukayi tare da hira Jefi Jefi  har ya kammala karyawa ,sannan ya mike yashiga toilet din dayake cikin falon ,ya wanke hannunsa ya futo yana mai duban mahaifiyar tashi da mama ki akan fuskar shi yace.

 

“Hajiya me nake gani acikin bayan gidan ki haka kamar abun tafasa ruwa na zamani ?(water heater).

 

” yi maza Mu’azu ka cire Wai din da kasa a maganar ka.

 

don kuwa ba kama bane abun tafasa ruwanne da gaske.

 

“aini babu abunda zance ma wannan jika tawa sedai nace Allah yakara tsaremin ita ga mugun baki da duk wani abun ki, Allah yama rayuwar ta albarka, qamshi nikam ta zamomin qamshin alkhairi,dubi falona dubi jikina yanda na dawo kullum bakina acin mai dadi mai maiko yake.

ni dama zan gaya maka kayima matan ka bayani daga yau na sauke musu kwanona a gidan ka sedai in sunyi abun dadi sesu kawomin,don qamshi tanamin komai nidai Babu abunda zance sedai alhamdulillah duk yayan ka babu Wanda yayi koyin halin ka da kwazonka kamarta.

 

“amiin hajiya.

 

 

cewar alhaji Baba me zuma yana dan nazarin maganar da Diddy tayi yanzu.

 

Hajiya Diddy kallon baba me zuma tayi Wanda yake sake gyara zaman sa akan kujera tana sauraron jin abunda zaice.

 

” Hajiya tunda naga kajin sun karbeta zan bata wasu kudin seta Kara kajin yanda kasuwar zai dan dada bunkasa tunda dakin da kajin nata suke ciki naga yanada girma,kuma naga tana kula da kasuwancin ta babu shiririta aciki.

 

Baki Hajiya Diddy ta washe tace.

 

” in kayi hakan ma ka kyauta Allah yama albarka ya Kara arzuki da daukaka,amma wani hanzari ba guduba nidai bazance komaiba bazan ma yar albarka na shishshigi a harkan kasuwan cinta ba gara tazo kaji daga bakinta ,naga bata cika son karban kudin mutane tana hadawa dana kasuwancin ta ba *(kaji wani batu agun tsohuwar nan sekace kudin tsafi zai bata)*

 

“kina Ina jikar hajiya!?

 

Hajiya Diddy ta bude murya tana Kiran Khubra.

 

” yi maza ki fito mahaifinki nason magana dake.

 

futowa nayi na durkusa daga gefe nace.

 

” gani Baba.

 

gyaran murya baba me zuma yayi yace.

 

 

” khubra tunda naga kiwon kajin ya karbe ki to inaso zan karamiki wasu Yan kudi ki Kara siyo kajin don abun yadan fadada inaga zaki fijin dadin ana kiran ki da hajiya khubra qamshi me kaji da kwai.

 

 

dariya nayi na rufe fuskata nace.

 

 

” Baba alhaji nagode sosai Allah yakara budi yajikan mahaifa.

 

” amiin khubra Allah yamuku albarka.

 

Yanzu karfi da yaji nima kin makalamin sunan Alhaji,gashi suna ya bini har kasuwa da gurin aikina haka ake kira na dashi.

 

baba me zuma ya fada yana murmushi .

 

 

Murmushi Hajiya Diddy tayi tace.

 

” Nima ba gani ba, ni ko kano ban taba zuwa ba amma qamshi na ta samin suna Hajiya Diddy, gashi kuma suna ya bini har mutuwa allah dai yasa yanda kika samin sunan Hajiyar nan allah yasa ki biyamin kudin kujeran maka naje nasauke farali.

 

murmushi nayi nace.

 

” amiin hajiya ta.

 

namike nakoma daki don na karasa shirya wa.

 

Hajiya Diddy ne ta dubi Baba me zuma tace.

 

” to tunda allah yasa yar hajiya ta amsa zata karbi kudin to fa dole se ankaro mata ma’aikata don aiki zai mata yawa ,ni dama zaka yarda daka tura Rabe yaje neman aiki anan gidan gonar Yar hajiya ko za’a dace,

kaga shikenan ma ya huta da wannan yawon tazubar din da yakeyi agari .

 

murmusa wa alhaji yayi yana mai jinjina yanda hajiya da jikanta suka daukaki wannan sana’ar nasu,kwata kwata kaji guda 20 nefa amma har ake kiransa da gidan gona.

 

Baba me zuma Jan numfashinsa yayi yace.

 

“yanda kikace Hajiya hakan za’ayi,babu damuwa zan turo mata shi ko za’a dace yasamu gurbin aiki agunta.

 

sun dan jima suna tattaunawa kafin yayi mata sallama ya fita.

 

Mama saratu me jiran a kawo mata kwai ta soya ta cika tayi fam.

 

Lokacin da Baba me zuma ya shigo sashin ta ta dubeshi tayi mishi kallon shekeke kamar bazata tanka mishi ba se kuma wani qullutin baqin ciki ya taso mata adan hasale tace.

 

” yanzu malam

fisabilillahi tuntuni Ina zaune Ina jiranka ka kawomin kwai na soya amma se yanzu ka dawo daga sashin su, kuma daka dawo din ma seka dawo babu kwai.

 

shin ko kaima tafi karfinka ne?.

 

Kuma zaman me Kake yi a sashin nasu har tsawan wannan lokacin?

 

 

 

07052100719 only chat.

Leave a Reply

Back to top button