Qamshi Complete Hausa Novel

Qamshi 26-30

Sponsored Links

 

*✨QAMSHI  26-30✨*

 

 

✍🏿RASHOW

 

 

Wannan page din naku ne.

 

MUMMY ANWAR .

MMN HAIDAR.

 

 

Hatim a Koda yaushe bazan gaji dayi maka tunin cewa shekaru Kara Ja sukeyi ba ya kamata kaima ka ajiye iyalin ka kona samu naga Yan jikoki na nima,amma Koda yaushe idan nayi maka maganar amsa daya kake bani na cewar na Kara maka lokaci, shin Hatim so ka keyi na koma ga Allah ba tare da naga jinin ka bane?

 

Abbi ya karasa maganar a sanyaye irin wanda zuciyar shi ta Karye,da hanzari Hatim ya dago kanshi wanda yake a sunkuye tun lokacin da Abbi ya fara magana muryan shi a tausashe yace.

“ba haka bane Abby kasan ra’ayina kuma kasan zabina Abby saura fa qiris.

 

Kai Abbi ya girgiza jin Hatim ya kuma furta kalmar dayafi tsana yaji amma se bai gajiya ba domin so yakeyi yau su cimma matsaya Sam baya kaunar ganin Hatim a haka babu mata duk da yasan yaron shi ciki da bai amma zaman nashi a haka Sam baiyi ba,sake kallon shi Abby yayi ya numfasa yace.

 

“why Hatim?

 

” meyasa se ita?

 

“shin kana ganin babu matan da zasu maye maka gurbin tane?

 

Shin ma me Kake nema agurin mace wanda wata matar bata dashi se ita wannan din?

 

Narkakkun idon shi Hatim ya dago ya dubi Abby kamar Wanda zaiyi kuka yace.

 

“Abby kasan banason macen da zata zamemin damuwa wacce komai se annuna mata,nafison mace tsayya wayayya wacce ta waye tasan rayuwa wacce ta mallaki komai ajikin ta takuma mallaki hankalin ta.

 

Kai Abby ya shiga girgizawa idon shi kuma yana kan Hatim wanda ya maida idon shi ya lumshe tamkar bashi yayi maganar ba.

 

Gyara zama Abby yayi yace.

 

“nagane kalan matan da kake sha’awan zama da ita, to amma inason na nusar dakai wani abunda inaga kai baka sani ba kokuma ka sani ka mance,ashawaran ce inason na baka shawara a matsayina na abokin shawaran ka wanda bama boye ma juna damuwar mu ko matsalar mu ina me baka shawara ni a ganina daka auri mace wacce ta waye gara ka auri wacce zaka wayar da ita da kanka domin zatafi lankwasuwa maka yanda kake so,itafa wacce ta waye zaiyi wuya ta biyu maka yanda kake so.

 

Kafada Hatim ya daga yace.

 

“please Abby Kayi min addu’a sannan ka dan bani nanda 2 days.

 

Sosai Abby ya zuba ma Hatim ido yana kallon shi kamar Wanda yake nazartan yanayin fuskar nashi,sannan yaja numfashi yace.

 

” 2 days kace na baka?

 

Hakan na nufin idan ka wuce kwana biyun na zartar da duk abunda naga ya dace kenan?

 

Kai Hatim ya daga batare daya kawo komai a ranshi game da maganar Abby ba.

 

 

Sorry kuyi manage

 

*Rashow*

 

 

07052100719 chat me up.

Leave a Reply

Back to top button