Qamshi Complete Hausa Novel

Qamshi 31-35

Sponsored Links

*✨QAMSHI  31-32✨*

 

 

✍🏿RASHOW

 

Yau kimanin wata biyu da sati biyu kenan da Jiddy ta damkamin gidan gonar ta Ina kular mata dashi kuma Alhamdulillah ansamu cigaba sosai don kullum se Jiddy tayimin godiya ga wani irin sabo da mukayi da yaran gidan mun hade kamar daman haka muke tuntuni,sosai Ammy take nunamin soyayya sabida Allah yayita macece maison yara son da takemin har mamaki nakeyi sedai idan Ka lura ta wani bangaren hakan kamar rashin diya mace da bata dashi ne da kuma halinta na son kyautatawa,wani lokacin ma a bangaren ta nake kwana tunda inada part dina a sama,Ammy tasa an gyaramin daki guda daya dayake sama an zubamin duk wani kayan jin dadi da more rayuwa aka sanyamin shi a dakina idan ka kalli falo na dayake Saman shi kanshi abun burgewa ne,kyan danayi ni kaina har mamaki nakeyi domin idan ka Kallen seka qara kallona,a kankanin lokaci skin dina ya goge yayi tas hasken fatana ya Kara futowa tamkar ka latsa jini ya futo,don Ammy da kanta take Kara koyamin wasu abubuwan ga wani irin sangartani da Ammy takeyi hakan seya karamin wani shagwaba sama da yanda nakeyi ma Diddy,lallaba ni Ammy takeyi kamar ni kadai ta haifa.

 

Rai a bace Baba Alhaji ya Kalleni yace.

 

“shin Khubra zaki wuce ki bude kofar muje ko kuwa sekin bari Hajiya ta futo ne?

 

Jikina na rawa na sanya hannu na bude kofar da zai sadamu da haraban BABBAN GIDA,dake tunda muka dawo haka muke Kiran gidan,muna shiga haraban gidan yayi dai-dai da futowar Jiddy kamar wacce take neman wani abun,ganin Jiddy ne ya sanyani a shagwabe Ina matsar kwalla na tafi gurin ta da sauri na buya a bayanta Ina kuka a hankali,kamani Jiddy tayi ta qara sanyani a bayanta tana kallon Baba Alhaji wanda ya sunkuyar da kanshi da alamar girmamawa yace.

 

“barka da safiya Jidd….. bai Kai ga qarasa gaisuwar nashiba Jiddy ta daga mishi hannu tare da cewa.

 

” Rike gaisuwarka Mu’azu bana buqatar ta, muhimmin abun buqata na anan shine ka gayamin abunda Jikata tayi maka da sanyin asubar nan harka sanya take kuka?

 

Kai Baba Alhaji ya girgiza don qara tabbatar ma Kashi halin Jiddy irin na Diddy ne rikicinsu sesu.

 

Karasowa Abby yayi wanda dawowar shi kenan daga masallaci sallah asuba, da yake shi yakan tsaya sauraran wa’azin da akeyi bayan kammala sallar asuba shiyasa se yanzu da gari yayi haske ya dawo.

 

Da mamaki ya kalli Jiddy wacce tacika tayi fam ga kuma khubra a bayanta tana kuka kamar wacce ake zarema rai,hannu Abby ya ware yana dawo da kallonshi ga Baba Alhaji yace.

 

” Mu’azu lafiya kuwa  naganku a tsastsaye.?

 

da sauri Jiddy tace.

 

” Inakuwa kaga lafiya anan nima shi nake jira naji abunda Jikata tayi mishi da asubar nan ya sanyo ta agaba se kurma kururuwa takeyi ga dukkan alamu wani bun yayi mata,nikam Mu’azu shin bakusan Allah yana kallon ku bane da Zaku rinqa irin haka?

 

sake gyara tsayuwa Jiddy tayi tana Kara kanne ido tace.

 

“zan iya rantsewa Sato jikin ka kayi ka taso marainiyar Allah ba tare da sanin Yar uwata ba don na tabbata da qawata tasan zaka sa mana jika kuka da asuban nan ni nasan bazata barka ba,amma hakan ma duk ba Faduwa bane tunda nayi caraf na cafke ka seka gayamin Ina daman zaka kaita daka sakota agaba tana kuka kamar Wanda zuciyar ka babu tausayi.

 

Sosai Baba Alhaji yake Kara girmama rikicin Jiddy ya tankwashe Kai tare da sassauta murya yace.

 

“ki gafarceni Hajiya daman bako Ina zan kaitaba illah gurin Alhaji don na bashi hakurin rashin hankalin da khubran tayi wanda ta samu jagorancin Diddy.

 

Sake gyara tsayuwa Abby yayi yana sauraron Baba Alhaji, ganin hakane yasa Baba Alhaji cigaba da magana.

 

“Alhaji kamar yanda na fara fada yanzu hakuri nazo baka wallahi duk abunda Khubra tayi bansani ba se jiya da daddare me dakina take Sanar dani duk rashin hankali da tayi.

 

kankance ido Jiddy tayi tana kallon Baba Alhaji, kan Abby ne ya kulle don Sam bai fahimci akan me Baba Alhji yake magana ba don hakane ma ya sashi cewa.

 

“Mu’azu ban fahimci akan me Kake magana bafa.

 

kallon khubra Baba Alhaji yayi sannan ya kuma kallon Jiddy wacce itama shidin take Kallo yace.

 

” bayan wata biyun da suka wuce khubra da ita da Diddy ne suka zuga Jiddy ta Kori duk masu aikin gidan gonar Jiddy akan cewar Wai ita khubra setake kula dashi, to wallahi ni Sam bansan da hakan ba se jiya shine na dauko ta muzo na Sanar maka kuma na baka hakuri na rashin hankalin da tayi senaji a inda ma’aikatan Jiddy suke naje na basu hakuri suzo su cigaba da aikinsu.

tafa hannu Jiddy tayi tana  matsalar kwalla da muryan kuka tace.

 

“tabbas Mu’azu ka nunamin asalin kalan ka yau Allah ya nunamin wanda basu qaunar cigaban gidan gona ta, lahaula’walaquwata illabillah,Jiddy ta rafka uban salati tana me kallon Abby tace.

 

” Ni bazance ma Mu’azu komai ba illah nace Allah ya yafe shi sannan ka Sanar mishi yaje yayita istigifari kuma kafun ya tafi ku biyoni muje kuga gidan gonar.

 

Kallon Baba Alhaji Abby yayi yamishi alama da ido akan subi bayan Jiddy don karsu Kara ma kansu wani laifin.

Zagawa sukayi ta bayan dakin Jiddy wanda yake dauke da fulawoyi masu kawatarwa,ta qaramar kofar dake gurin suka bi suka shiga, police din dake zaune a gefe ne ta mike tare da Sara ma su Abby sannan ta rusuna ta gaida Jiddy take Jiddy ta washe baki tana amsawa kamar ba ita bace me kuka dazu.

da kallon mamaki Abby ya kalli police din nan don tabbas police ne na gaske bawai wasaba kanshi ne ya daure don shi dai yasan bai dauki wani police aiki ba illah police dinda suke mishi aikin bakin gate dinshi.

 

Kamar Jiddy tasan me yake nazari a  zuciyar shi tace.

 

“kun dai fara ganin aikin da Jikata tayi tun daga farkon shigowa.”

 

kai kawai suka iya gyada mata suna bin haraban filin gurin da Kallo wanda yaji interlock gurin tsaf dashi da alamar ba’a jima da share gurin ba,tafiya sukayi don gurin yana da girma na sosai,kallon gefe Abby da Baba Alhaji sukayi wani gini ne akayi shi kamar part an rubuta female part dayake shine a farko yasa Jiddy fara shigar dasu gurin,corridor ne a farko se kofa idan ka shiga ciki zaka samu falo wanda yaji kujeru kamar a cikin gida se wasu kofofi guda hudu daya dakin hutune harda gado da bayan gida, se daki na biyu shikuma dakin canza Kaya ne se na uku kitchen ne se na hudun kuma toilet ne kowani kofa an rubuta sunan shi daga Saman kofar ta waje sosai gurin yayi masu Abby kyau, futowa sukayi suka danyi tafiya ba mai nisaba anan suka tarar da wani block din Shima shiga sukayi suka gani nan kuma gurin da ake kyankyasan kifi ne wanda suka farayin kyankyasan sati biyun daya wuce,gurin yana dauke da gurin da suke tara abincin kaji da dakin abincin kifi se dakin tara egg idan kaji masu egg sunyi.

 

Jinjina Kai kawai Abby yakeyi shida Baba Alhaji, gurin kiwon kifi suka fara zuwa suka ga yayan kifin da suka kyankyasan pounds din da suke gaba kuma su irin kifin ta siyo ta zuba su gasu harsunyi wayo sun tasa se shawagi sukeyi acikin ruwa gwanin burgewa, murmushi Abby yayi don sunyi matukar bashi sha’awa harya gaza hakuri yace.

“lallai daughter kinsan kayan Jan hankalin mutum, ai nikam kinmin gurin zama ne anan.

 

Yayi maganar yana nuna kujerun da suke ajiye a rumfar da akayi daga gefe suna fuskantar kifayen wanda kana zaune akan kujerun kana kallon yanda kifayen suke wasan su a ruwa, Kara sawa dasu gurin dakunan kaji masu egg tayi suka duba su haka gurin kaji masu nama ma, se kuma wani part din da yake can kusa da gate shikuma ansa Male part idan ka shiga cikin part din irin na mata ne sak Sedaga jikin gate kuma dakin police ne wanda police din take zaune akan kujeran roba ganin su Abby ne ya sata tashi tana gaida su cikin girmamawa,bin gate din da baisan dashi ba Abby yayi da Kallo kasa hakuri Abby yayi yaje jikin kofar ya bude gate din tare da futa daga cikin gate din yana kallon ikon Allah.

 

Dawowa yayi ya kalli khubra yace.

 

“Sannu daughter da kokari Allah yayi miki albarka.”

 

“Amin” nace kaina a kasa Ina wasa da yatsun hannu na,kallon Baba Alhaji Abby yayi fuska cikeda murmushi yace.

 

“Mu’azu kaga aikin da diya ta tayi ko? tabbas ta cancanci tukwici tayi aikin da dukan mu bamu kawo hakan a ranmu ba yarin ya karama da iya tsara abu haka Kai masha Allah rabo na da shigowa nan na Kwan biyu Sam bansan da wannan gyara da akayi ba.

ya karasa maganar da dan dariya don abun yayi matukar yi mishi dadi.

 

 

 

*RASHOWS*

07052100719 chat me up

Leave a Reply

Back to top button