Hamshakiya 14
*🌸HAMSHAƘIYA*🌸
Na
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 14*
“Zama tayi akan sofa ta dafe kanta tana tunani ta yaya zata gane wanene umar? domin Umar ne ya aikata laifi shine saurayin teema, kamansu ɗaya komansu ɗaya babu ta yadda zata gane.
ɗago kai tayi tace “ta hanyan aikinsu, zan ganesu ta hanyan aikinsu Umar shine doctor Faruk kuma shine soja, abinda zanyi shine zan nemo asibitin da umar yake aiki daga nan zan ganeshi idan yana zuwa aiki.
murmushi tayi tunda ta gano hanyan da zatabi ta ganeshi, lumshe ido tayi tana addu’a Allah ya bata sa’a ta gano wanene me laifi a cikinsu.
tashi tayi saida tayi wanka ta sauya kaya kafin ta koma gida, da tunanin gobe da safe zataje na nemo Information.
*washe gari*
Yayi shiri tsaf cikin kayan soja yau fuskarshi ba annuri ba kamar kullum ba yana cikin fara’a da dariya, Ammi ta kalleshi nan take ta tuno Faruk wanda bai fiye fara’a ba saide idan abin dariya ya faru yayi murmushi kawai, hawayene ya cika mata ido, umar ya girgiza mata kai alaman kada tayi kuka, lumshe ido tayi tace “umar ka kula sosai kada a samu matsala”
“Faruk dai Ammi”
“Faruk ka kula sosai”
murmushi yayi sannan yace “Ammi ba abinda zai faru ki kwantar da hankalinki”
“hankalina ba zai taɓa kwanaciya ba sai naga ɗana, kaje Allah ya bada sa’a”
“Ameen ya faɗa yana yiwa Elham peck a kumatu”
tace “yah Faruk?”
“na’am Elham”
fita yayi daga ɗakin ya ɗagawa driver hannu kamar yadda yaga faruk yana yi, fuska ba annuri ya shiga motan aka tada sai barack, taku yake bayan an ajiyeshi yana tafiya yana kallon cikin barack ɗin, sai sara mishi suke yana ɗaga musu hannu kawai, bai tsaya ko ina ba sai office ɗin faruk, zama yayi akan kujera yana binciken files da suke jibge akan kujeran faruk ɗin, saide ya kasa fahimtan komai.
knocking yaji anyi yace “yes”
shigowa tayi tana yanga tana farfar da ido, hannunta rike da cup na tea ta ajiye a gabanshi tace “gashi sir”
Murmushi yayi yana kallonta ba shakka tanada hips ga breast Allah ya bata, kallonshi tayi yau ya mata murmushi taji daɗi cikin karya murya tace “zan iya zama sir?”
jijiga mata kai yayi, tayi mamakin yau da kanshi ya amince ta zauna? zama tayi a gefe tace “meyasa baka fitowa 3days”
“wallahi bana jin daɗi ne”
“oh sorry”
cigaba yayi da duba files ɗin yana son kasancewa da mace amma baya mood me daɗi ganin yayi shiru ta mike tace “to zan tafi”
bin bayanta yayi da kallo, lumshe ido yayi a ranshi yace “kodai faruk ma yana ɗan taɓa neman mata ne?”
kawar da abin yayi dan ya shaida Faruk ba zai taɓa bin mata ba.
*Amrish*
da motarta taje har kofan gidansu ta gaida me gadi yau taga abin mamaki ba baba megadi bane wani soja ne yake tsaye yana gadin gidan, da tsoro ta gaisheshi sanann tace “Faruk yana ciki?”
“wacece ke da kike nemanshi?”
“budurwarshi ce kwana biyu baya zuwa kuma wayarshi a kashe nace ko wani abin ne ya faru?”
tunawa yayi da gargaɗin da akayi musu na cewar kada suce faruk ne ya ɓata suce umar ne, kallonta yayi yasan mafi yawan lokuta mata dasu ake haɗa baki a cuci mutum, yace “ai Faruk yana wajen aiki a barack Umar kuma shine ya ɓata kwana biyar daya wuce”
Dafe kirji tayi kaman bata sani ba tace “Innalillahi wa inna ilaihiraji’un Umar ya ɓata kuma? kenan ya daina zuwa aikin a asibiti?”
“wallahi ya daina oga faruk yana iya bakin kokari dan ganin ya samoshi amma har yanzu shiru”
“Innalillahi ubangiji ya bayyana shi zan samu faruk ɗin acan wurin aiki nagode”
shiga motarta tayi tasa glass a idonta tana murmushi ta gode Allah umar ne a hannunta ba faruk ba, jan motan tayi tabar wurin, bata tsaya ko ina ba sai gidanta, ajiye motan tayi ta shiga ciki, kallon rainin hankali tayi mishi tace “malam faruk nasan kaine Faruk ba Umar ba, ka sani umar saiya karɓi hukunci a wajen kawar fatima ranta na zai tafi a banza ba”
so take ta kara tabbatar da shine Umar ko shine Faruk, murmushi yayi yace “na gaya miki nine umar idan baki yadda ba kiyi duk abinda zakiyi”.
zama tayi a kasa gefenshi tace “bazan bar wancan yayi yawo a gari yana shawagi ba, dole saina yimishi hukunci”
bata san yadda akayi ba taji ya shaƙo wuyanta ya haɗata da jikin bango, waro ido tayi waje tana shaƙuwa jin yadda ya shaƙeta da karfi, kwatan kanta ta fara da karfi ta bugi cikinshi da kafarta, sakinta yayi ya rike ciki ya kwanta a wurin, wani sandan mopping ta ɗaga ta kwala mishi a gadon baya, hannu yasa ya danna wurin yana runtse ido dan ba karamin azaba taji ba.
ganin zata kara kwaɗa mishi ya janyo kafarta ta faɗo kanshi, danneta yayi a jikinshi ya kwace sandan da take shirin dukanshi dashi, saida ya wurga sandan gefe kafin ya damƙe hannunta ya maida baya ya riketa da karfi, ihu tayi ta fara birgima a jikinshi tana kwatan kanta.
wani gigitaccen mari ya wanke kyakkyawar fuskanta dashi, wani ihun ta kumayi tana kiran masu gadi, hannu yasa ya toshe bakinta a kunnenta ya raɗa mata “ki daina tunanin cutar da ɗan uwana ki kasheni idan kinaso amma ko kuda ya taɓamin ɗan uwa da sunanki saina kasheki”
sakinta yayi ya wurgata gefe, hannunta ne ya bugu da jikin bango.
da sauri ta dafe wurin tana kallo ta fara kuka cikin ihu tace “na rantse da Allah saina taɓa shi inada tabbacin ba kai bane umar kaine faruk domin soja ne kaɗai zai iya yiwa mace wannan riƙon da kayimin, duk wani ɓoye ɓoye da zakayi saina gano gaskiya, kuma ka sani hatta Elham da Ammi bazan barsu ba idan ban gano gaskiya ba”
cikin zafin rai yazo wurin ya haɗa kanta da jikin bango, rike kai tayi tana cije baki tace “mugu azzalumi familynku duk azzalumai ne”
mari ya ɗauketa dashi yace “kada ki kara magana akan family ɗina”
ganin idan ta zagi family ɗin shi yana jin zafi kamar yadda take jin zafi a jikinta yasa ta ɗago jajayen idanunta tace “mugaye da kai da ɗayanka bakuda imani baku ɗauki mace a bakin komai ba, kuma macece ta haifeku kazo kana dukana ɗan uwanka kuma ya cuci rayuwar ƙawata har saida ta kashe kanta, kaima sai nasa an yiwa kanwarka Elham…” bai bari ta karasa maganan ba ya ciro socket daga jikin Tv ya rinƙa watsa mata a jiki, kuka ta fara bakinta yaki yin shiru wuka ta ciro zata daɓa mishi da karfi ya danne hannunta ya kwace, haukace mishi tayi tana dukanshi tako ina, rungumeta yayi da iya karfinshi ganin tanada karfi ya ciro mayafin data ɗaura akanta ya ɗaure hannunta ta baya.
kasan riganta ya yaga sannan ya ɗaure kafafunta dashi, tana fizge fizge har ya gama ya ɗaureta tamau ya ɗagata sama ya kaita ɗakin da yaga tana yawan shiga.
akan gado ya kwantar da ita, yana ji tana cewa “faruk ka kwanceni”
dawowa yayi ya samu tissue ya yagi dayawa yazo ya cusa mata a baki, hawaye ya sauka daga idonta tana kallonshi har ya fita, akan kujera ya zauna ya dafe goshinshi yana tuna abinda ya faro, baiso yayi mata haka ba, amma bazai iya juran a zagan mishi ƴan uwa ba, lumshe ido yayi yana jin zafi a inda ta cijeshi yasan ɗan uwanshi ya aikata laifi amma ai ya ɗau hukuncin yace tayi mishi duk abinda zatayi, to meyasa bazata kyale Umar ba kuma?
jingina yayi da jikin kujeran yana kallon saman ɗakin, sauke idonshi yayi ya kalli gefe inda ta tarwatsa cup ganin jini a wurin ya dudduba jikinshi yaga ba jini, to daga jikinta ya fito, a hankali ya mike yaje ɗakin daya kwantar da ita, ganin tayi bacci ya karasa yana kallon kafarta wanda yake fitar da jini, tissue ya ɗauko ya zauna a gefen gadon ya ɗago kafanta wanda yake fari sol yana shining ga maroon na lalle da tayi ya kara haska ƙafan sosai, ɗaura ƙafan yayi akan cinyarshi ya fara goge jinin da yake zuba kaɗan-kaɗan, saida ya goge tass kafin ya ɗaura mata wani kyalle fari yadda yaga Umar yana musu idan sunji ciwo, tashi yayi zai fita bayan ya maida kafanta inda ya ɗago, a hankali ya dawo ya cire tissue dake bakinta yasa a dustbeen, kwance kafanta yayi sannan ya kwance hannun ya tsinci kanshi da janyo mata blanket, kallon gashin kanta daya barbazu garin masifa, hannu yasa ya maida mata baya, gyara mata kwanciyan yayi ya rage Ac ya kashe fankan dake ɗakin ya kashe wutan, ya kunna mata dim light sannan ya juya ya fita.
akan kujera three seater ya kwanta, ta bashi tausayi tunawa da shatin bulala daya gani a jikinta yayi jajur abinka da farin fata, bai son yana dukan mace saide wannan ai itace ta janyo, marin kanshi yayi kaɗan “meyasa zaka mareta kuma marainiya ce”
Lumshe ido yayi a hankali yaji bacci yana shirin ɗaukanshi, saida ya tashi yayi raka’a biyu sannan ya kwanta a inda yake kwanaciya wato ƙasan tiles wannan shine hukuncin da take yanke mishi kuma zaici gaba da karban hukuncin har zuwa lokacin da ranta zaiyi sanyi ta daina zancen Umar.
bacci take sosai domin ta jima batayi bacci me kyau ba, kullum idan zata kwanta tana cikin tunani, rabi bacci rabi tunani takeyi, cikin bacci taji hannunta sakayau alaman ya kwanceta, murmushi tayi cikin gigin bacci ta janyo pillow ta rungume, taji daɗin baccin duk da tana jin ciwo a jikinta domin ya mata duka ba kaɗan ba.
*Asuba ta gari*
tashi tayi jin ana kiran salla dama sallan asuba baya wuceta cije baki tayi jin kafarta yana mata wani raɗaɗin ciwo, da ɗingishi ta shiga toilet alwala tayi sannan tazo ta shimfida sallaya ta tada salla, tayi raka’a biyu na fitowan alfijir sannan tayi sallan asuba, kur’ani ta ɗauko ta fara karatu kaman yadda ta saba da muryanta me zaƙi.
ganin bata fito ba abin ya bashi tsoro kodai yaji mata ciwo ne? addu’a yayi Allah yasa ba wani ciwon taji ba ameen, a hankali ya tura kofan zai shiga ya jiyo sautin zazaƙan muryanta tana raira karatun Alkur’ani tana karanta suratul qasas, jingina yayi da jikin kofan ya lumshe idanunshi yana sauraran karatun da takeyi, saida tayi karatu sosai kafin ta rufe kur’anin ta tashi da ɗingishi taje ta ajiye, shafa mai tayi tasa dogon riga da guntun hijabi ta fito, komawa yayi ya kwanta a inda ya saba kwanciya, tana fita ta hangoshi yana bacci akan tiles sai kame jiki yake alaman yana jin sanyi, zunguro baki tayi tana aika mishi harara sannan ta koma ɗaki ta ɗauko blanket tazo gabanshi, rufa mishi tayi ta juya zata tafi, har taje bakin kofa ta kuma dawowa ta janye bargon tace “shima yaji sanyi kamar yadda nima jiya ya dakeni mugu kawai”
ajiye bargon tayi a gefe tace “idan yaji sanyi ya ɗauka ya rufa jikinshi dashi, fita tayi daga ɗakin saida yaji ta rufe kofa ya buɗe idonshi yana murmushi, shikam bai taɓa ganin inda aka kama mutum kuma ake barinshi yana yin duk abinda yaso ba a cikin gida sai a wurin Amrish.
_hauwa shu’aibu jiddah 08144818849_