TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 20

Sponsored Links

 

 

Kamar yadda mukai zaton Abba zai koma ranan monday sai gashi
monday din tayi duk Abba yana gari na dawo daga school na samu basu wuce ba ke
nan ranan ummah zata basu abincin dare.

   Don haka na samu
suna aiki amma kuma ga abubuwan rabanan na azumi   an kakasa a ko ina na gidan da gani damasu
shi na wuce zuwa ciki na kwabe kayan jikina na fito.

     A kitchen na samu
su umma suna aiki nasa hannu akayi girkin tare dani har aka hada komai muka
fito falo nida Tani lokaci guda don ummah ta barmu muna karasa kulin tuwo a
leda fara.

   A galabaice na
zauna kan two seater din mu na falon Tani ta kalleni ta kwashe da dariya tare
da fadin yau kan mutumiyar tasha aiki ko ta fada cikin zolaya.

  Ummah ta kalleni
tace har wani aiki tayi bayan ta samemu mun hada aikin muko kafin tazo nace hai
ummah nimafa nayi aikin nan sosai fa.

  Tsuki ummah tayi
tana fadin kina ji Tani ki dauki wanan kayan sadakan azumin guda goma kije ki
raba ga duk wanda ya dace a bangareki amma fa ba naki ciki don haka ki bayar a
sadakan yadda na fada.

    Na kai kallona gun
kayan tare da fadin ummah nima a ban na rabawa kawayena mana a school har sun
fara tambayana abin azumin su fa ?

   Wani kallo ummah
tayi min tare da fadin ji mun yar nan da zance kayan magidanta zaki kaiwa yan
mata kuma ?

   Hjy ai yan matan
suna da iyayye a gida sabasu ai ko tunda ta tambaya in akwai sai a bata irin
nasu Tani ta fada  gashi can ki diba gobe
idan zaki fita don ni duk bayarwa zanyi ga mabukata.

    Sukaci gaba da
maganan su ina bin kayan da kallo don ganin meye a cikin leda din dana gani
ummah ce ta juyo take tambayana har nawa zaki dauka ?

    Lokacin hankalina
bai garesu Tani tace dani mamangida dake aike magana fa na juyo idon ummah yana
kaina lokacin take kara tambayana mutum nawa zaki baiwa ?

   Ummah zasu kai goma
fa amma dai a binda aka ban sauran sai na basu wani abu ba zaki samu goma ba
nace toh ummah ko nawane a ban na bayar.

   Ki dauki shidda don
ina son in bayar nan bayan layin mu don akwai masu bukata sosai a wanan layin
ummah ko a barshine ki basu tunda kince suna da bukata suma.

    Washegari har na
manta da zancen na fita saigashi Tani ta biyoni da kayan  a ciki katon buhu tana fadin ga kayan nan zan
koma na dauko maki sauran.

   But na bude ta zuba
saura muka saka a bayan mota tayi min sallama nace ida  na dawo zan ganta tashige tana min godiya.

   Na isa school din
na samu ba a shiga ba don har na rigasu hannatu shigowa ajin ina zaune suka
sameni tana fadin gobe ne kawai ba zamu tashi da azumi ba don shi na tsaya na
dankari abinci na cika cikina.

    Ke kan kinji kunya
yanzu duk shekara dayan da kikayi kina cin abinci sai yaune zakiyi na kankat ta
kwashe da dariya muna haka malami ya shigo class muka natsu.

    Bayan mun fito ne
break na nufi wurin motana don i  dan
karya da ruwan zafin da aka hada min sai kwai dana zo dashi wanda Tani ke
asubancin zuwa ta dafa muna don yaran dake zuwa makarantan.

   A nan su hannatu
suka sameni don tare muka fito ta tsaya magana da wasu na wuta bayan ta bude da
niyar zama sai tayi tozali da kayan dake baya din aje.

   Wanan kuma fa kayan
meye zarah ta tambayeni na juyo na kalla tare da fadin sorry fa na manta in
fada maki dazun su madam Asma nazowa dasu na azumi.

  Meye a ciki ta fada
tana kokarin budewa ta gananwa idon ta kwan ina tsiyaya ruwan shayin dake
tururi a kofi nace ban sani ba nima wallahi na dai dauko ne na rabo a falon
ummah nazo masu dashi.

    Kaji manya ke nan
ki dauko abu kice baki sani ba ruwan shayin na kurba kafin nace ban duba ciki
nasan  meye a ciki ba ta shiga budan
kayan kafin ta dago tana fadin wasu madam asma gamu ?

   Kaya  shayine fa a ciki sai shinkafa zaikai mudu
biyar nace OK kawai naci gaba da shan shayin da nakeyi abina ta zauna ta dauki
flask din shayin ta tsiyaya ta jawo kwai tana ci.

    Kamar sun sani
saiga su madam din su uku matan auren department din mu sun jero sun dawo daga
wurin sallah muka gaisa zasu tafi Hannatu ke fadin aiko mayana tana nema  ku fa .

    Suka juyo zuwa
inda muke  muka kara gaisawa dasu tace
wai abin azumi ta riko maku shine kuma take jin nauyin da zata baku din don
kada ku dauki hakan wani abu.

   Haba dai keko mukan
mun gode wallahi kaina yana kasa ban dago ba sai ku bari idan an tashi sai ku
dauka a, a ki bamu abin mu yanzu abu a hannu shine mutum.

    Hannatu ce ta mike ta dauko leda uku ta mika
masu suna godiya da addua suka tafi kafin mukai class har wanan zancen ya yadu
a class din muna shiga akayo min caaa wai ina nasu ban dai yi magana ba don ba
zan iyasu duka ba ai ajin.

     Wa yanda nayi
niyar bawa sauran mutum hudu na mika masu har hannatu muka shiga mota muka bar
school din saida muka dauki hanya na kalleta tare da fadin zaki gane gidan su
master kuwa ?

    Zan gane mana ai
nayi zama a unguwar wurin kakana kafin ya rasu saidai shi yana ta bayan su
kadan nace OK ki nuna mi  hanya muje.

   Akuyar nan fa tana
nan saboda Akuyar zanki zuwa mu kai masu wanan kayan su nayi niyar kawai da
wana  tsohon makwabcinsu daya shigo din
nan ok muje zan gane ta fada.

    Da kwatance har ta
kaimu gidan yana nan kamar yadda muka barshi mun dade a cikin mota muna
shawaran shiga kafin mu fito da addua a bakina muka nufi hanyar shiga gidan
tare da almajirai a bayan mu dauke da kayan.

   Munyi sallama ba
kowa a tsakar gida abin mamaki muna sallama idona na kan wanan akuyan ta mike
tsaye tsam a daidai lokacin da zata fara wanan kukan natane tsohuwar gudan ta
fito daga daki tana amsa sallaman mu.

   Daga inda muke
kamar matsorata muka gaida ita tare da tambayan ko Ahmed yana gida tace baya
nan kuwa kallona hannatu tayi sai nace ga wanan kaka idan yazo ki bashi meeeeh
har cikin raina naji wanan kukan akuyan mai daga min hankali.

   Haba uwargarke
bakin ma baki barsu bake nan bako fa rahamane a gida balle wa yan nan ai bakin
arzikine su a kullun suka zo gidan nan koba kune na ranan nan da kukazo ba ta
fada tana dawo da kanta ga kallon mu.

  Ganin yadda na rike
hannatu gam a jikina yasata dan murmushi tana fadin kai haba ai bata komai
itama tana maku godiyane kusan dabba da sabo da mutane ai.

   Hanne ko cewa tayi
ai akuya kamar mutum take da fahinta wani lokaci sai su dinga abu kamar mutane
don sabon su da zama ciki  mutane da
sukeyi ko yaushe.

    Jinsu kawai nakeyi
don kiris ya rage min na sake fitsari a lokacin don tsoro da tashin hankaki
juyawa nayi da sauri tare da fadin sai anjima ai banyi nisa ba wanan akuyar ta
kucce ta biyoni a baya sai ji nayi ana fadin subbahanallahi.

  Juyowan nan da zanyi
akuyar ce a bayana tana zagayena kace ta saba danine dama idan nayi nan tayi
nan tana wani tsale tare da kuka kamar na rike tsaba a hannuna tagani.

   Yaran nan da muka
shigo dasu suka kama dariyata irin yadda na tsorace don akuya ikon Allah basu
kiwone a gidan su ina fa kaka wana kilama sai a ciki mota take hango akuya ai
don su din yan gidan masu garin nan ne ai.

   A ina Amadi ya hadu
da yar masu kudin nan tana fadi hankakinta na kanmu da akuya muna drama yaran
nan sai kwasan dariya sukeyi.

   Haba uwargarke ba
tsaba ta dauko ba ga tsaba can idan yunwa kikeji mana kai ku kamata ku daure
min ita a garken ta Dije ta fada jin hakan yasa akuyan ta kara matsowa kusa
dani sosai tana dago kanta gareni kamar tana sunsunan kamshin  jikina.

    A zatona dai
cizona akuyan nan zatayj amma sai naga sabanin hakan sai sun sunan jikina kawai
takeyi tana dan sake wani gumji a cikin wani sauti da ni kadai nake jin shi
wani iri.

    Zarah ya ambata a
bayan mu idona suna lumshe bansan lokacin dana budesu ba nanufi wurin shi da
sauri na tsaya a bayan shi ina sauke numfashin wahala lokaci guda.

   Haba uwar garke
kada ki kada itama tunda tana tsoron hakan don Allah ki tafi a daure ki abin
mamaki sai akuyan ta dago kai ta dan dubeshi kamar mutum ta dukar da kai kasa.

   Haba uwargarke kina
tsorata farar tumfafiya mai furen albarka baki baiyanan a wurin banza,  zuwanta
garemu alheri ya kawota wurin mu nasan kema farin ciki kike nunawa kan
shigowanta mazaunin mu.

    Dijece ke jera
wanan kirarin lokaci guda haka kai kuje ku daure ta Ahmed din ya fada cikin
bacin rai yaran sukaja akuyan ki suna turata tare da fadin ke ke ke yau sai
kinsha daure a hannun mu sosai.

   Zarah lafiya kukazo
gidan nan ya kara tambayana saidai ya fahinci cewa ba a cikin hankalina nake ba
lokacin don na gama tsorata ko lokacin.

  Ya juya wurin
hannatu yace hannatu ina kuka fitone kuka zo nan wallahi mun kawo wa  kaka abin azumi shine ka ganmu nan yanzu.

   Kaidai kaji yar
arziki abinda ya kawosu ke nan sukazo muna da abin arziki haka na azumi wanan
yar ta zamo silan alheri azumin bana zanyi shi da yar gwaunati ka kayan shayi
kuma duk an hado muna dasu.

   Sai washe baki
takeyi tana bayani shi kuma ya daure fuska ganin yanayinda nake ciki yasa hanne
fadin zamu tafi sai anjima kaka .

  Sannuku da kokari
yaran nan angode Allah kara arziki da nisan kwana Allah ya kade shedan da raban
rayuwanku  a kullun sai mun ga abin
sallah kuma in Allah yakai rayuwan mu lafiya ba matsala kaka tunda kinga wanan
ai kishi yana tafe in sha Allah hanne ta fada.

    Har lokacin jna
rakube a bayan shi cikin tsoro da tashin hankali ganin na kasa wuce yasa ya dan
juyo idona yana rufe shige man ku tafi zarah ke take jira ku tafi.

  Kamar wace ta
farfado na dan zabura ban tsaya mata ko sai anjima ba na bi bayan zarah muka
fita har ina hadawa da dan gudu kadan don sauri.

  Muryan shine a bayan
mu yake fadin kiyi hakkuri zarah akuyan na
bata komai haka take idan taga mutane don son mutane ne da takeyi aina
fada mata haka akuya take idan ta saba da mutane.

    Munkai bakin motan
lokacin yaran suka fito daga gidan da sauri suna fadi  mun daure ta hanne tace a, a kudai dan abinda
mukace zamu baku kuka biyo dai ga hamsin ku tafi jin haka yasa na bude baki da
kyar nace.

   Wani irin hamshin
kuma ku jira nazo zan sallameku na bude motana na zaro kudi daga cikin jakkata
dan dubu daya sabo kar na mika masu nace mungode kunji.

    Kai amma zarah kan
dan wanan abin zaki basu har dubu daya nace haba dai ai sunyi kokari sosai hjy
mungode Allah ya kara arziki da wadata na amsa da amin.

  Yana tsaye yana
kallo  mu kafin yace kin daiki jin
maganata zarah wanan dawainiyan haka ga kuma uwargarke data tsorata ki haka
kuma.

  Inbanda ke wa yake
tsoron akuya zarah a lokacin na zauna da kyau a cikin motar na dago kai na
kalleshi nace   ban taba zuwa inda ake
kiwon su bane kuma bana son kukan nan nata ina jinshi wani iri sosai har cikin
raina.

   Yayi murmushi yace
kardai tsoro gareki haka kai mata ke nan meke a cikin akuya kike tsoranta haka
sai anjima na fada ina tayar da motan nawa.

   Yana tsaye har muka
bar wajen muka fice daga unguwar nasu ya juya ya shiga gidan  ya samu Dije na bude kayan tana ganin ya
shigo ta fara washe baki tana fadin sun tafi ko ?

   Eh sun tafi ya samu
wuri yana kaiwa zaune tare da kallon abinda tsohuwar keyi tana fadin in Allah
yaso ka da arziki tsuntuwa yake baka.

   Haba Dije bai
kamata kina nuna hakan ba a gaban su gaskiya yarinyar nan Allah ne ya hadani da
ita kawai jinin mi yazo daya daga taimako abin ya koma muna zumunci a tsakanin
.

   Amma don kinga sun
kawo wanan kika kasa boye zumudin ki kan wanan abin don Allah me kuma nayi
yanzu akan hakan na zubar da mutunci Amadi ?

   Kudine ta jawo a
cikin ledan yasa ta juyo tana masa kallon tambaya a cikin mamaki yar nan da
abin arziki take har da wani kudi ta dora a kai bayan wanan wahalan.

   Kudi kuma ya
tambaya yana kallonta tace gasu kana gani kuwa nan ta shiga kirga kudin tana
gamawa tace a, a a dubu ashirin cif ikon Allah wanan yarinya lalai tumfafiyace
ita raban ta alheri ne a garemu gidan nan.

    Ashe uwargarke
taga abinda tagani take mata wanan godiyan haka har muna hanata hakan taga
abinda ta gani ashe a jiki  yarinyar ke
nan ?

    Mikewa yayi ya
ciro yar nokia din shi tsohuwa data sha dauri ya danna kira na sauke hanna ke
nan naga kiranshi ya shigo min a wayan na dauka.

   Bai jira mu gaisaba
ya fara fadin zarah don me zaki min hakan tun farko ina munyi wanan maganan
dake ba wanan a tsakanin zaman mu dake ko ?

   Wanan sai mutane su
dauka saboda irin hakan yasa nake tare dake dama sai su mace mutumcin da ke
tsakani na dake a dauka abin hannun ki yasa nake mutunci dake ashe ?

    Amma kasan bakai
na kawowa kaya  nan ba ko kuma ba gidan
ku kawai na bawa ba don Allah ka daina min irin haka idan nayiwa kaka Alheri.

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[1/15, 6:03 AM] +234 701 497 9567: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2️⃣1️⃣

Leave a Reply

Back to top button