TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 32

Sponsored Links

 

 

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/5, 3:35 PM] +234 816 362 6370: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

 3️⃣2️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Baka jin komai a motar sai kidan gurmi da irin wasu
dirobobin nan kan saka a mota idan wanan ya kare wani kalan zai dauka su ukune
a cikin motan daga driver sai tsohon nan guda sai ko kayan daya dauko a bayan
motan nasa.

    Don haka motan
yayi shiru sai kida ke tashi a ciki kawai yayin da Amadi ke faman sauraron
fatawan malam daurawa ta hanyar saka earpiece dinshi a kunne a yar karaman
wayan shi a lokacin .

   Idan malam din yaba
da wani adduan da bai gane ba zaiyi ta faman nanata adduan yana bi a haka har
barci ya dan daukeshi na dan lokaci.

   Mafalki yayi da har
ya manta da cewa a mota yake lokacin ba a gida ba komai yake mafalki a kai ba
sai farin cikin rayuwan shi watau zahra.

    Zahra din ya gani
zaune a cikin damuwa ya karaso inda take zaune yana tambayanta ko lafiya ya
ganta haka a cikin damuwa.

    Kai ta dago ta
kalleshi da fararen idanunta ta dan yi murmushin yake gareshi tana fadin sun
sakani a gaba brother sai kace ni kadaine diya a gidan mu.

  Why zasuce saini ni
kadai why da suke min hakan zasu rabani dakai su waye zahra ya tambaya bakin
shi na rawa ta dago kai cikin yanayin kuka ga hawaye ya bata mata fuska ta ko
ina ta nuna tana fadin sune sune suke son ganin bayan mu.

   Juyawan da yayi
yaga inda take nuna mashi din ne ya falka ya ganshi a cikin mota ana faman
sharara gudu sai tsohon nan abokin tafiyan shi daga gefen shi zaune sai
daya  mutumin dake tare da driver a gaba.

    Dan gyara zama
yayi yana fadin sannu baba jin haka yasa tsohon dan dagowa yana amsawa tare da
fadin amma yaro kai daga nahiyan sokoto kake ko naji hausan ka ta mutanen
wajajencan na sokoto.

    Eh baba amma ni
daga zamfara nake ba sokoto ba zani neman mahaifina ne a nan garin ysohon ya
amsa da na,am anan Manbila yake da zama yace eh to bandai sani ba amma yace shi
mutumin mambila ne saidai kuma in anzo mambila din anfi sanin su da chedawa.

   Chedawa tsohon ya
maimaita sunan yace anya kuwa a nan cikin mambilan zaka sameshi tunda naji kace
chedawa sai wajajen tasanma su gurojje.

  Jin hakan yasa
Amadin jin gaban shi ya fadi sai ya kasa daurewa yace baba ina ne hakan kuma ?

   Duk a cikin
bangaren mambilawa yake saidai ba gari daya bane don akwai dan tafiya tsakanin
shi da garin mambila din.

   Au bakone a wanan
nan nahiyar namu ke nan drivern ya fadi daga gaban motan tsohon yace bakone bai
taba zuwa wanan kasan ba.

  Yace wai ya fito
yawon neman mahaifin shine daga zamfara dattijon ya fada jin hakan yasa drivern
dan juyowa yana fadin daga zamfara fa kace kake yaro ?

   Wallahi daga can
nake ya kara fadi yace kace kasha hanya da tafiya mai nisa ke nan, amma kayi
kokori sosai wurin wanan tafiyan haka ?

  Drivern ya fada yana
mamakin yaron kafin ya kara fadin da fatan kasan inda zaka sameshi dai ya
tambayi Amadin ?

   Idan bai sani ba ai
baya zuwa har nan da sunan neman shi duk yadda akayi yana da kwatancen inda zai
sameshi dayan mutumin dake zaune tare da drivern gaban mota ya fada.

   Murmushi Ahmed ya
sauke a fuskan shi yana girgiza kai cikin bacin rai yace ko sanin sa ban taba
yi ba asalima dai tun ina goye ya tafi ya barni nida mahaifiyata.

    Na daizo ne ko
Allah zaisa na gano inda zan sameshi amma bansan sunan garin da zan sameshi ba
din a yanzu yaji drivern motan yana fadin.

   Kai mutanen mu
akwai daukarwa kai nauyi zaka tafi kabar danka daka haifa da zufan ka babu ko
waiwaye wanan ai yiwa kai zaluncine don duk abinda ya shafi jinin ka ya
shafeka.

   Drivern motan nasu
ke fadin haka yaci gaba da fadin kayi dabara yaro don haka shine gatan ka da
cikar kimar ka a idon mutane don duk da mutane sunsan ta hanyar sunna akai
haifeka wanan ba zai hana su soke dashi ba.

   Ai wasu mutanen
suna yin abu a cikin duhun kai da jahilci ta yaya kasan kana da da a wani wajen
zaka gudo ka barsu tsawon wanan shekarun mutumin dake zaune gaban mota tare da
driver yake fadin haka.

    Wani lokaci kadara
da nisan wuri ke jawo hakan saidai wasu suna irin haka da son ransune Allah ya
kyauta tsohon dake tare dake tare da Ahmed din a bayan mota zaune ya fada.

   Duk Ahmed din yana
jin zafin maganganun nasu a zuciyan shi saidai baida zabin hakan don bai sani
ba ko ta sanadiyan hakan zai samu mafita ga tafiyan nasa.

    Haka sukai ta
zancen su daya shafi irin matsalan nan yana sauraren duk abinda suke fadi duk
yana jin zafin hakan amma bai saka masu baki a zancen ba.

  Kasancewa tafiyan
nasu yayi yamma da yawa don haka duhun dare ya riskesu sosai a hanyan baida
wani zabi sai wasiwasin yadda zaiyi idan sun sauka wani gari.

    Wayan drivern ne
yayi kara ya dauka hakan ya saka motan yin shiru lokaci guda da alaman tambayan
shi ake ko yana ina a lokacin don cewa yayi munashiga taraba yanzu.

    Nan Ahmed din
yasan inda suke ya gyara zamanshi yana bin hanyar da kallo ba tare da ya furta komai
nan zaka gane irin misikilancin shi na rashin son yin magana sosai da baiyi.

   Ina zaune falo tare
da mommy data dawo tasa Tabitha ta kirani a dakina tana tambayana abinda ke
damuna nace ba komai kaina kawaine yake dan min ciwo nasha magani kuma ya daina
yanzu.

   Idan bai daina ba
muje asibiti zaifi su duba idan wani abune yake damun ki na danyi murmushi ina
fadin ba komai mommy naji sauki.

   Fada min dai idan
kewa hjy kika farayi tun yanzu na sani nace a a mommy ba gaki ba tace nasani
amma tun zuwan ki nima nasan ban samu lokacin zama dake ba gidan nan daughter.

   Kiyi hakkuri
wallahi aiyukane sukai min yawa ga zancen bukin auren autan hamisu ga kuma aiki
daya taso muna a office wanan duk ya dauke min hankalina.

   Wallahi har fita
nake sonyi dake muje ki dan zabo wasu abubuwan bukatan ki a nan don kada ki
takura don naga bakizo da wasu kaya masu yawa ba don kada ki dade ko ?

   Murmushi nayi ina
fadin lah mommy wallahi ba hakana bane naga dai ba inda zanine yasa ban dauko
kaya masu yawa ba dama ban fada maki har kano zamu tafi buki tare dake ba.

   Za,ayi bukin autan
mu namiji zaiyi aure kinsan maman mu mu bakwai ta haifa mu uku mata da wanan da
kika ga dayan maman mu daya da ita itace yar wanda zaiyi auren a yanzu ita kuma
dayan yar kanwar maman muce ita.

  Dukkan su a wurina
suke tuntasowan su danayi auren farko nake zaune tare dasu mijina na farko mun
rabune dashi yarana suna can hannun shi biyu maza sai mace daya.

   Saidai nan gidan ku
kuma idan na samu indada karawa ta fada tana dariya nace Allah yasa mommy muma
mu samu kani ko kanwa don  Affarace
karama har yanzu su ummah da mama basu kara bamu baby ba kuma .

   Da alama taji dadin
zancen  nawa don yadda naga ta lumshe
idanun ta tace watau zahra kin gane wanan halin naku yasa nake son ku keda mahaifiyar
ku.

  Don idan kuna zama
da mutum da zuciya daya kuke zama da kowa ba tare da wata manufa ba kinsan
maman ku maimuna ido da ido ta kalleni tace dani ba daina haihu da daddyn ku ba
saidai na saka a masai ?

    Wanan yasa nake
son haihuwa yanzu sosai zahra ko don in nuna mata iyakarta ta gane ba aiwa
Allah shishigi ga lamarin shi da sam banda ra,ayin kara haihuwa a rayuwata .

   Amma yanzu naji ina
son na haihu a gidan ku nima na saka nawa irin a cikin ku naga yadda zatayi
damu din a gidan lokaci daya duk muka juya don jin kamshin turaren Abba da
mukayi alama  ya shigo gidan ke nan ya
dawo lokacin.

    Fuskan Abba a
kanta yake fadin wai zama kikayi da yarki haka kuna hira kamar kin samu wata
babba sa,arki  kuna hira.

   Daddy ke nan idan
uwa bata zauna da yarta tayi hiraba a yanzu dawa zaka zauna hirana da zahra
naji dadinshi sosai don yarinyace mai hangen nisa sosai.

  Ni ki tashi da
wana  shirmen naki ki bani abinci Abba ya
fada kamar wani yaro mai jin yunwa ita kuma tana kokarin janshi da wasa har dai
ta mike ta wuce zuwa kitchen wurin masu aiki.

   Lokacin Abba ya
kalleni yace maamah ya labarin karatun kine da fatan kina mayar da hankali
sosai dai kuma ina fatan kin fita zancen wanan yaron mara asali ?

    Gabana ya fadi
amma haka na daure nace Abba lafiya kalau Alhamdullahi bana wasa da karatu in
sha Allahu shine amsan dana iya ba Abba din lokacin.

   Zanji dadi idan
hakan ya kasance gareki don ina da hope maikyau a gareki don hakane bana son ki
tsaya yin wasa ko kulawasu can idan kinyi hakan zamu shirya dake.

  A zuciya na bashi
amsa da sabanin hakan matsalane ke nan ko amma fili cewa nayi ban wasa Abba
kuma ban kula kowa yanzu duk ina da labarin komai Abba ya ban amsa.

   Shiru nayi na dan
lokaci kaina yana duke kasa kafin naji fitowan mommy daga kitchen hakan yasa na
daga daga wurin na nufi dakina don kada in tsaya idona ya gane min irin
soyayyan da sukeyi kamar yara ko a gaban kowa.

   Daki na nufa
zuciyana cike da maganganu kan zancen mu da Abba dana mommy din da mukayi watau
dai Abba har yanzu ya dauki zancen Ahmed da zafi a ranshi ?

    Ni banga wani illa
dake ga Ahmed din ba da ko yaushe Abba ke kiranshi da kaskantance kawai dai
rashin fahinta ne wani tambaya ne yazo min to ko Ahmed din baida ubane shegene
da Abba ke fadin baida asali ?

    Gabana ne ya fadin
yin wa kaina wanan tambayan to ko shegene meye laifin shi tunda shi yana da
natsuwa bashi ya aikata hakan ba ai.

   A take wani sashi
na zuciyana ya bani amsa da fadin inko hakan ya tabbata ko ummah ba zata yarda
ba balle Abba da yake na miji nima kaina duk da nasan za,aita aibantani kan
hakan ba yarda zanyi da hakan ba.

   Ke nan taraiyana da
Ahmed din dai akwai matsala ke nan don haka dole in tambayeshi inji gaskiyan
abin daga bakin shi don ban taba kawo wanan tunane a kwakwalwana ba.

   Haka na ajewa raina zan tambayeshi labarin
mahaifinshi dana yan uwanshi inji daga bakin shi don komai nason tambaya asan
gaskiya tunda Abba ya nace da maimaita kalma daya haka a gareshi .

   Nasan talauci ba
zai hana auren mutum ba tunda Allah shikeyin mai arziki jikin matalauci haka
yayo matsiyaci jikin mai arziki don ba a san mai gobe zata zamawa mutum ba ai a
rayuwa.

    Ni kadai a daki
nake faman kullawa in warware  don banda
abokin magana a gidan daga mommy sai yan aikin ta da mukan dayi hira kuma akan
abinda ya shafi girkine haka.

    Don kanen mommy
dake gidan zan iya kirga ganina dasu a gidan don basu zama  gida ko suna gidan ma ba ruwan su dani nima
haka ba ruwana dasu don naga suna da gadara da jin kai sosai a yanayin su.

    Sallah nayi na
koma gado don sam ban jin yunwa a ranan na kwanta a lokacin zancena da mommy ya
fado min a raina nace watau ita mommy haihuwa take so a hakan da girman ta
gashi ummah ma data haifi Affara mama tana fadin ta tsufa tana haihuwa balle
mommy da zata girmewa ummah din nake gani.

   Ina nan ina mirgina
saman gadon naji mommy ta shigo dakina wuta dake kashe ta kunna ta ganni kwance
take fadin badai yarinyar nan barci tayi bataci abincin dare ba ?

   Kara lafewa naji
kamar ina barcin gaske naji ta gyara min rufin bargo ta kawar min da rigana
dana aje a gefen gadon ta kashe wutan dakin taja kofa ta fita.

   Ajiyan zuciya na
sauke ina bude idona kallon lokaci nayi a wayana karfe goma sha daya na dare
saura naga lokacin yayi saurin yi a ranan duk ban sani ba.

    Wayata din na
kalla naji kawai in kira Ahmed mu danyi hira na danna kiran layin shi ya shiga
yana ta ringing bai daga da wuri yadda ya saba dagawa ba idan na kirashi din.

   Sai can wayan na
batun tsikewa naji ya daga yana sallama yanayin da nake jin muryan shi din yasa
nake jin kamar a mota yake tafiya don karan iska da nake ji a lokacin.

   Ina kake haka nake
jin wata kara kamar kana cikin mota yace muryan shi da nake ji can kamar yana
yawo a iska yana fadin gani taraba zahra zanje wurin mahaifina ne.

   Na ambata Taraba fa
kace Brother yace eh ina cikin mota yanzu idan mun sauka zan kiraki idan baki
barci ba Allah ya tsare hanya nayi mai ina lumshe idanuwana a hankali daga inda
nake kwance din.

   Baya  mun gama wayan ne  na ambata Allah mai tsarki da daukaka na godewa
Allah da banyiwa Ahmed wanan tambayan ba har na samu amsa a wurin shi haka a
cikin sauki.

  Da nayi masa
tambayan dani zan rage da kunyar hakan shiyasa ake cewa komai yana son tunane
da nazari kafin mutum ya aikata shi a rayuwan shi ashe .

   Hakan yasa naji
wani natsuwa da dadi a zuciyana kamar an cire min lakkan jikina a lokacin yadda
nake jin kaina a lokacin har wani nauyayyen barci ya saceni lokaci daya ban
sani ba.

   Ahmed kuwa yana
kashe wayan ya nisa ya lumshe idanun shi yana sauke ajiyan zuciya zakace yasan
abinda ke a ran zahra ne a lokacin muryan tsohon nan dake kusa dashi zaune yaji
yana fadin ai yanzu mun dan fita taraba bakaji yanayin ya canza maka ba.

   Yanzun zamu shiga
hawan Mambilane daga nan mun fara tasan ma nahiyar mu na mambila ke nan daga
nan ya  zakaji yanayin garin ya sauya ma
daga nan .

    Saidai tsohon bai
gama rufe baki ba yaji driver na fadin banga mota nabi hanyar nan ba idan mun
kai nan ga kadan mu tambaya muji lafiyan hanyan yaya yake.

     Nan yaga yan
cikin motan a tsorace suna fadawa driver cewa ya dakata kawai su kwana a dan
kauyen gaba zaifi da asuba sai mu kama hanya na gaban motan ya fada.

  Bari dai mugani
malam idan hanyar zata biyu sai mu mike zaifi inji drivern shidai yana jin su
yana zaune a bayan mota yayi shiru yana addua.

   Ummah ce zaune a
falonta da safiya Tani maiyiwa ummah din aiki ta shigo ta sameta suka gaisa
take tambayan ummah din ko anji mata motsin uwardakinta anyi waya ko da ita ?

    Ta kira jiya mun
gaisa kin santa da shiririta ko sakarcine wai tayi mafalki ta falka da safe duk
jikinta ya mutu ita tana jin tsoro ko waya fada mata mafalki gaskiyane oho ?

   Da sauri Tani din
ta kalli ummah tace hjy kune dai baku daukan abu da muhinmanci a yanzu ai bai
kamata ko kice haka ba da sau ki tambayeta kiji akan me tayi mafalkin aji ?

  Duk da dai ba duka
mafalki yake zama gaskiya ba amma da haka dan karamin abu yake zama babba
watarana saidai sakaci irin namu na mutanen yanzu ke hana mu dauki mataki kan
abu sai yazo ya girma yadda bamu iya dauka muce muna neman sauki a kan abin.

    Yarki ta girma
yanzu ba za,asata a sahun marasa wayau ba don tasan ciwon kanta yanzu kama yayi
kiji irin mafalkin kinga in na sadakane sai ai mata sadaka a nan Allah ya tsare
zaifi.

    Wanan ne kuma
Allah bai ban ikon yi ba ko ince zan mata sadakan banyi ba gaskiya ummah ta
fada a dan damuwan hakan don maganan Tani din yayi tasiri a zuciyar ta.

   Tasani cewa tun
tana karama wani lokaci manya kance sunyi mafalki bari suyi sadaka don Allah ya
mayar da abinda sukai mafalkin alheri garesu.

    Amma gashi ita
bata bada daman hakan ba ga yarta sai binta da tayi da fada tana kira mata
sakarci komai sai ta saka arai ya dameta don mafalki zatace tana jin ciwon
jiki.

    Iyayye mu farga da
wanan maganan a yanzu a kan yayan mu don a yanzu zamani na tafiya ne da nau,i
biyu wayewa da jahilci don har yanzu akwai masu
jahilci dake sihiri akan mutum kuma Allah zai iya nunama a mafalki wanan
baiwane da yawancin mutane da yawa kedashi a cikin rashin sanin hakan garesu.

  Mata mu farga da
yawaita yin sadaka ga yayan mu don min sadaka riga kafin masifa ne ga bawa
sadaka baya tafiya a banza inji masana addini komai kankanta abin sadakan zaiyi
amfani ga maishi.

  Musan man sadakan
abinci, kudi, tuffafi kosai sugar kuli,kuli alewa naira darin ki sai yai maki
riga kafin rayuwan ki dana yayan ki duniya da lahira.

  Amma yanzu wata ana
sati daya ko fiyema da hakan bata mika wani abin ba da sunan sadaka saboda
Allah da Annabi Allah ya kare ya tsare ya bada ikon yin hakan Amin.

Leave a Reply

Back to top button