TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 6

Sponsored Links

 

 

  Washegari  ummah na tana
kitchen tana hada breakfast  na
sameta a tana tsaye tana fere arish daga bayanta nake fadin ina kwana ummah ?

   Da sauri ta dan
juyo zuwa inda nake a kofan tana fadin fuska ba walwala a cikinsa maamah kin
tashi yaya kan da sauki ta fada tana kallon yanayi na a lokacin.

   Nace eh ummah ina
kwana yau kece ke girkin da kanki kafin Tani tazo tace nice kinsan Alh na gari
dan anjima nan kadan jama,a basu barin ya zauna karshe ma ya fita.

   Abba ya dawone na
tambaya a cikin mamaki jin haka yasa ta juyo dakyau tana fuskantana tare da
fadin yadawo mana jiya ai har nan yake wurin ki shida malam bawa ai.

    Cikin mamaki na
dago kai na kalleta nace malam bawa waye haka ummah tace wanan malamin dake
kasan layin nan shi ya dauko a cikin dare yazo ya ganki.

   Jikinane yayi sanyi
na karasa inda take ina karban yunkan data dauka a hannunta tana shirin fere
dankali don ta nufi inda dankali yake na tako ina mika hannu zan karba.

    Baki da lafiya ki
koma ki zauna ta fada ummah naji sauki zan iya na fada ki barshi ai ba wani
abin mai yawa zanyi ba dankalin nan ne kawai da kwai zan soya sai ruwa tea gaya
na dora a kattile.

    Hakan baisa na
fasa amsan yukan a hannunta ba ta miko min kafin ta juya ta duka tana debo min
adadin  dankalin da zan fere din a
lokacin.

    Tsaye nake ina
fira naji muryan ummah tana fadin waini Maamah ina kika hadu da iskane haka har
suka shafeki ?

   Wani irin juyowa
nayi wanda ya fitgita ummah har ta kalli yukan dake hannuna danayi setin inda
take dashi da sauri na sauke hannuna kasa tare da fadin iska kuma ummah ?

   Aiba shiganki
sukayi ba shafanki kawai sukayi malam yace ki kula da addu,a maamah ko banza
kinsan yadda muke a cikin mutanen nan bawai sun daukemu da daraja bane.

    Don gani suke har
gobe mu bamu cancanci rabar Alh ba matsayin mu baikai ace muna cikin ahalin Alh
ba a yanzu don kasancewar iyayyena tallakawa ko don na zama bare a cikin su
yasa har ku suke kallon ku a matsayin da bankai ga tantanceshi a zuciyana ba.

   Kallon Ummah nake
cikin mamakin zancenta gareni wanda ban gama na iskan data fada sun shefeni ba
ga wani zance ta dauko min a yanzun kuma wanda na kasa  tantance inda zancen nata ya dosa a lokacin.

    Taci gaba da fadin
sai jiya na kara fahintan cewa har yanzu maman ku bata dauke mu da muhinmanci ba
a gidan nan don irin maganganun data fada min a jiya kan kawai wai Alh ya dawo
gidan nan a ranan girkina ta rufe ido ta fada min magana na kaskanci lokaci
guda.

     Nayi duk kokarin
da zanyi wajen tausan zuciyana a zauna lafiya amma a kwanakin nan tun dawowan
mu garin nan yanzu ina ganin wasu halaiyan da hjy maimuna take tsiro min dasu
na daban dake nuna ni banda daraja ko kima a wurin Alh da kowa.

     Ummah meta fada
maki haka haka har kika kasa hakuri dashi ranki ya baci haka don nasan a zaman
ku kece mai hakkuri da kawar da ido akan komai da akeyi a cikin gidan nan.

   Nishin ciki ummah
tayi lokaci guda tana fadin yi sauri muyi aikin nan kada mu makara rana ya fito
bamu gama ba naci gaba da fere dankalin
gabana a hankali zuciyana tab da tunane.

   Allah ya taimaka
anyi angama har ankai falo an jera duk lokacin ba wannda ya fito ummah ta koma
tayi wanka ta shirya cikin wasu simple lace masu taushi dinkin zani da riga sai
turare mai taushe data goga a jikinta.

    Part din Abba ta
nufa sai ta samu mama a cikjn zaune tare dashi suna magana da ace can bayane
fita zatayi daga dakin da sauri amma wanan karon ga mamakin mama sai taga tayi
sallama ta shigo.

    Abbah tafara
gaidawa tayi mai ya gajiyan hanya kafin ta juyo inda mama take tana fadin hjy
antashi lafiya ya kwanan su Aisha dacewa yan matan dakin mama din a yanzu su
biyu.

    Ciki ciki mama ta
amsata ba yabo ba fallasa ta mike daga inda take zaune zuwa bandakin Abba din
ta hada mai ruwan zafi ta kara gyara wurin ta fito.

   Lokacin ne Abba ke
fadin mamana ta tashi kuwa ko har yanzu bai sake ta ba tace tashi tare ma mukai
aikin breakfast da ita ai.

   Ya jikin nata yanzu
ummah tace Alhamdullahi don ta dan watsake masha Allah ya fada barin yi wanka
na lekota sai wayanshi dake gefe ya dauki kara lokaci guda ya kalli wayan kafin
yace jiya saidai muka dauko malam bawa wa mamana lokacin kin rufe part dinki.

     Umm, ummmm ta
fada kawai tana mikewa tsaye tare da fadin yanzu ni ai uwarta ta nuna bani na
haifeta ba don ta nuna min hakan kaima gashi kuma ka fada yanzu da bakinka ai.

    Da inada
muhinmanci ko iko da ita aikona rufe kofa zaku tayar dani mudai zuba daku inga
iya gudunku inda zaku da wanan sallon da kuka dauko min a yanzu.

    Dukkan su kallon
mamaki sukai mata lokaci guda ta juya ta fice daga dakin ta gaban ummah tayi saurin
jada baya da sauri kada su kai ga hada jiki abinda ba a so ke nan kishiya da
kishiya su hada jikin su yana jawo tsiya a gida koga mijinsu inji manya.

    Na rasa meye
matsalan maimuna a kwanakin nan murmushi ummah tayi ba tare datace mashi komai
ba tabarmashi dakin itama ya bita da kallo yana gyada kai.

    Mikewa yayi ya
shiga wanka ya fito ya ya shirya bai zauna cin abinci ba ya nufi part din ummah
tana zaune da kannena a falo su uku ya shigo part din.

  Gaidashi suka farayi
ta hanyar tasowa daga inda suke zaune suna mashi sannu da zuwa tana amsa masu
tare da tambayan su karatunsu a lokacin naji muryan shi a falon mu yasa na nufo
falo da sauri.

   Daga kofa da zaka
fito daga dakunan kwanan mu nace Abba you are welcome ya dago inda yake yana
kallona fuskanshi cike da murmushi yake fadin mama kece nan haka yau ya fada a
cikin kulawa.

   Karasowa nayi zuwa
tsakiyan falon namu na sameshi kasa nakai yadda muka saba gaidashi ina fadin
ina kwana Abba ka dawo lafiya yace Alhamdullahi mama yaya jikin naki da sauki
dai yanzu ko ?

   Kan ya daina ciwo
ko jiya nazo mun dade dake baki san lokacin da haka ya faru ba dake hankalina
ya tashi jiyan sosai yadda na ganki din sai nake tunanen ina kika hadu da iska
haka.

   Da sauri na dago
kai na kalleshi  kafin nayi kasa da kaina
da sauri ba tare dana bashi amsa ba ganin hakan yasa yace to ki kula don Allah
mama don malam ya fada muna gamo dasu kikayi a wani wajen.

   Nan ma na sake dago
kai a cikin mamaki sosai ina ksllon su Abba din nace  dasu Abba ban hadu da kowa ba hakani bansan
zancen kaba Abba.

   Kallon ummah yayi
kafin ya juyo inda nake gurfane yana fadin ki kula da kanki watarana inyi
lfahari dake uwata yawan jin kida da kallace kallace a cikin dare ko shiga
bandaki kai tsaye ba tare da yadda musulunci ya koyar damu ba duk ki daina
uwara don tsaron lafiyan ki.

    Na amsa da toh
Abba nagode ina mikewa hannu yasa ga aljihun riganshi ya ciro kudi masu ya miko
min lokacin har na juya zan tafi tafi kanena daya ke fadin anty maamahb Abba
yana mika maki ya nuna min Abban da hannu.

    Juwowa nayi inda
Abban ya ya zaune ya rike kanin mu
karami a jikinshi wanan sallon na Abban namu mun dade rabon mu da muga
irinsa a garemu tun dowowan mu garin zamfara Abban ya daina bamu irin kulawan
da muka taso yana bamu.

    Lokacin da muke
zaune Abuja kula muke samu wanda duk wani uba zaibawa iyalanshi irin wanda ke
kawo shakuwa ga iyali amma muna dawowa sai sallon rayuwan ya canza a wurin mu
gaba daya har Abban namu din a yanzu.

  Don ko bu za a bamu
saidai mama ce zata sayo ita Abba zaibawa kudi ko kuma ta saya idan yazo ta
karbi kudinta a hannunshi.

  Irin abubuwan da dai
ke tauyewa dan adam hakkinsa da rashin

yanci a gida shi muke gani a zamam mu nan zamfaradin daga mu
har mahaifiyar mu muna a tauyene muna zama na rashin gata a cikin mama da
yaranta wanda muke ganin su suna komai nasu a cikin gata da walwala na jin
dadin nuna halin akwashi a gidan mu din.

    Don ko motan da
nake hawa yanzu wanda anty Aisha tayi amfani dashine mama tace ta barmin shi a
ka sayo mata wani na mata mai kyau na yayi ni kuma don zuwa school aka ban
wanan din don shima baiji jiki ba.

    Gyara akai ta kara
komawa sabuwa nake hawa har mutane na ganin aimu a cikin gata da jin dadi muke
koda yaushe don basu gane gaskiya idan ba wa yanda suka zamo na jikin mu ba
sunsan komai.

    Kaina girgizawa
Abba din alaman ya barshi murmushi naga ya sake a fuskanshi yana fadin uwata
idan ban bakiba wa zai baki ki karba karbi ki aje a wuri ki.

    Hannu bibiyu na
mika na karba ina godiya kafin na tashi na mike na bar falon saida ya dan jima
da yaran kafin ya fito yal nufi part din mama data riga ta samu labarin cewa
Abbn yana part din mu kusan minti ashirin a ciki tare da mu.

    Don haka yana
shigo tana zaune ta hakince saman kujera sai commad da take bayarwa daga inda
take zaune din don ita mama tana da yan aiki har uku part dinta.

    Bayan diyan yan
uwa maza da mata dake zaune tare da ita don har yan aikinta biyu a nan suke
kwana a gidan namu don aikin mama.

    Abba ya shigo da
sallaman shi fuska mama ta hade mai nan wanda suke falon suka shiga gaida Abba
din yana amsawa ya kai zaune a gefen mama din ta dan jaye tana gyara zama.

    Lafiya naga kin
hade rai haka ta kallo shi tana fadin duniya na hada haka kawai za a ce wai na
hade rai a kan me kan wa yancan banzan iyalin naka kome zan hade raina.

     Murmushi yayi
yana fadin sune kuma banza yau da bakin ki ke fadawa iyalina haka maimuna wai
meke damun kine haka wai ?

     Lokacin su Aymana
da Aisha suka fito daga dakunan su jin muryan Abba din a part din nasu suka
fara gaidashi kafin su fara zuba mai shagwaba yana biye masu.

    Daddy sai ka ban
kudin gaskiya don in katafi saidai muji cewa ka bar gari kila Aisha ta fada
tana wani shagwaba kamar karamar yarinya.

    Dole Abban yasa
hannunshi a aljihun shi ya ciro kudi masu yawa suma ya mika masu har lokacin
mama na zaune sai busan iska takeyi tana jan kamshi ita a dole an mata ba
daidai ba.

   Yayin da shikuma
Abban yake kokarin ganin cewa ya daidaita tsakanin shi da mama din ita kuma
tana bultsewa.

    Ranan ya kamata ya
juya don wayan daya samu amma dole ya daure ya kara kwana don mama suka
daidaita kansu suka koma daidai.

    Shi kanshi Abba
din a lokacin ba zaice ga dalilin dayasa yaji lokaci guda ummah ta tsaya mai a
rai haka ba har yake dan jin tausayinta ita da iyalanta a wanan zuwan.

   Don baibar gari ba
saida yayi dabaran ganin ya kyautatawa kowa don ya cikawa ummah account dinta
da kudi har saida tayi mamakin ganin hakan wanda da dane saidai mama ta bata
idan yatafi tace Alh ya basu su rike.

     Lokaci guda itama
ummah din tana jin wani son mijinta yana taso mata dan lokaci lokaci a ranta
wanda yasa Abba yana isa Abuja ummah ta kirashi tana mashi godiya tare da addua
mai inganci a gareshi wanda hakan yasa shi lumshe ido a cikin wani yanayi.

    Yau kwana biyu ke
nan yana zuwa school yana dawowa hannu sake ba kamar yadda ya saba rikowa Dije
dan ledan abinda ya samo a wurin aikin shi ba.

    Saidai Dije din ta
amsa gaisuwan shi sannan tayi mai sannu kafin tace da alaman dai kunyi fada da
shugaban aikin kuce kwana biyun nan ko ?

    A cikin mamaki ya
juyo yace tun wancan ranan ban koma wurinta ba don na samu labarin cewa tace
idan nazo korata zatayi yasa nayiwa kaina kiyamalleni da ita.

    Ka kyauta gara da
baka tafi ba ina amfanin wullakacin Allah daya bata bai manta damuna muma idan
da rabo namu yana tafe a wurin Allah.

    In sha Allahu ya
fada tare da jingina jikinshi da bangon ginansu ya shiga tunane don yasan
abinda tsohuwar keyiwa dan abincin daya saba shigowa dashi gidan da yanzu ya
daina yasa ta kai ga magana har ta fahinci akwai magana.

   Itama dijen shiru
tayi na dan lokaci kafin taji muryanshi yana fadin sana,a nake son in nema in
fara yi saidai jari shine matsalata a yanzu don sana,a saida jari mai dan tsoka
a hannun ka.

   Tau Amadi kace kayi
sana,a babu wani kudi ko abin sayar a hannun ka indai ba wa yan nan dabbobin da
su kawai muka mallaka a yanzu ba.

  Saidai idan su din
zaka kama ka sayar saika rike dan kudi a hannunka kai ya girgiza mata tare da
fadin mu daiyi addua Allah zai kawo muna mafita ga komai.

    Allah ya nufa ta
fada a sanyaye sai kuma ta dora da fadin dadai kabi shawarana sai ka dauki ita
uwar garken kakai kasuwa kudin sai kayi amfani dashi Allah yasa akbarka kaga
saura kwara hudun in Allah ya raya muna su sai a more masu kuma gaba.

   Dije ki bari na
kara addua a kai insha Allahu Allah ba zai barmu haka ba da yardan ubangiji da
fadin haka yai shiru yana tunane ba komai yake tunane ba sai halin rayuwan daya
tsunci kanshi a ciki .

    Yau ace
mahaifinshi da mahaifiyar shi suna raye amma yana zaman kunci irin na
marayu  don dan wani dalili mara tushe da
mahaifin nasa ke takama dashi a zuciyar shi.

   Har yakai dije na
magana dashi lokacin bai jiba yayi imani da abinda zuciyar shi ta yanke mashi
akan mahaifin nasa.

   Dago kai yayi da
idanuwan shi da suka kade sukai ja kallonshi tayi lokaci daya sai taji jikinta
yayi sanyi ta fasa fadin abinda tayi niyar fada mashi din a lokacin .

    Shirun dayayi yawa
yasa ta dauko mai zance makwacinsu da maciji ya sara a daji jin hakan yasashi
dago kai da sauri yana fadin subbahanallahi shi malam Abashe din ?

    Tace kwarai taci
gaba da fadin dazun nan aka dawo dashi daga gona inda abi

n ya sameshi suje noma gonan su a can ya tabashi aka
daukoshi zuwa gida.

   Yanzun dai suna
asibiti dashi ance magani dubu sittin da biyar na shiga masu  tanzango abin ba dadi gaskiya saisai Allah ya
gyara kawai.

   Bari inyi sallah
sai in leka gidan in yakama har asibitin sai in tafi jn gaidashi can tunda yau
naga babu hadari a garin ya mike ya nufi inda suke aje buta.

     Washegari na
tashi da sauki sosai don haka na shirya zuwa school lafiya lau na shiga mukayi
darasin farko bamu fito ba sai sha biyu da rabi.

    Wurin motana na
nufa na bude shiga na zauna nafito da goran ruwa tulawa cikina saida nayi rabin
ruwan na daga goran na cire a bakina.

    Kainane ya sara
lokaci guda hakan yasa na dora kaina saman sitiyarjn motana na dukar da kaina
lokaci guda motar ta fara horn hakan ya jawo hankalin mutanen dake dan sintiri
a wajen.

    Wai yarinyar can
tana da hankali kuwa tun dazun take duke mota na horn haka wasu gugun matasa
dake zaune suke fadi daga bayan su Amadine zaune yana karatu saye yake a cikin
wani dogon wandon jeans

Pdayo kode sai wata shirt fara mai zanen kanana kana tsaye
jikin rigan duk da farine shima rigan ya kode saboda tsufan da yayi shima.

    Dan  juyowa yayi inda yake jin horn din yanatashi
ya hango mace ta kifa kai saman sitiyari mikewa yayi da sauri ya nufi wajen
kamar wanda ake ingizawa zuwa wajen.

    Ganin ya nufi
wajen ya kara jawo hankalin sauran matasan dake zirga zirga a wajen da sauri ya
karaso yana dan magana daga inda yake boyar Allah lafiya kike kuwa ?

    Shiru yaji ga
goran ruwan da nasha ya zube a jikina rabi a kasan motar yana tsiyayaya kasan
motar kai ya fada yana matsawa wurin ke boyan Allah lafiya kike kuwa ?

   Karan horn din ya
isheshi yakai hannu ya dafa kafadata da sauri ya jaye hannun nasa yana fadin
kai don Allah ku taimaka wanan suma tayi ko bata da rai ?

    Sai suka fara dan ja
da baya  kowa yana gudun jefa kanshi
cikin wahala don haka basuga abinda zasu tsaya sujawa kansu matsala ba a nan.

   Don Allah ba wanda
yasan ko wzcece  ita ya fada da dan karfi
mayanace fa yar gidan mayanace wanan ai ga lamban gidansu nan a jikin motan
wata ta fada a dan tsorace tana ja baya.

     Kai ya fada kafin
yayi kundun bala ya dagoni daga jikin sitiyarin motan na sauke wani ajiyan
zuciya lokaci guda kafin na kara lumshe idanuwana.

    Meke damun ki
hakane ya fada cikin son yasan ko meye matsalana a lokacin kaina nace cikin
wani irin kasalalen murya mai wahala.

    Bai fahinci me
nake fadi ba sai ya kawo kunnen shi kusa ya kara maimaita tambayanshi gareni
nace dago hannu da kyar na nuna kaina.

   Kanki ke ciwo ya
fada yana mai zuba idon shi a kaina na dan bude idona da sukai ja kamar
garwashi lokacin na dan gyada kai da sauri ya fara lalaban aljihun wandonshi.

   Kokarin shaka min
yayi ba tare da shakkun komai ba ya turmuza min a hancina baikai second ba na
sauke wani uban atishawa lokaci guda.

    

Leave a Reply

Back to top button