TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 70

Sponsored Links

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/18, 9:37 PM] +234 816 310 0038: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

7️⃣0️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Zakice bashi yai tafiya ba a ranan don ya dawo a cikin lokaci yaso ya samu ummah a asibitin amma sai akace masa bata leko ba tun safe haka yasa yaja bakinsa yai shiru da zancen.

Saidai yana kokarin ganin ya samu dama ya shaka min maganin kamar yadda tsohon ya fada mai yayi Allah cikin ikon shi sai ga Dije na fadin Aisha ta kaita gida tayi wanka su dawo tunda Ahmed din nan wajen hannatu kuma taje gidan su tun safe bata dawo ba.

Haka ya tun kareni gadan gadan bai tsaya shakar komai da nufin ya shaka min caraf yaga na bude idanuna dake rufe lokacin don haka zan rufe ido zakice ko barci nakeyi alhalin idona biyu a lokacin.

Wani karfi da bai taba zaton ina dashiba yaji nayi mai a lokacin shima hakan yayita maza baiyi wasa ba ya shaka min maganin tare da murza min sauran a fuskana ya shafe .

A take nake wani gumji a daidai lokacin hannatu ta shigo dakon hannu ya daga mata alaman kada tayi magana ina karewa sai barci mai nauyi dayazo min ban kara sanin inda kaina yake ba kuma.

Wai master yanzu fa gwaggona ta gama fadin anya ba mutanen boye bane suke damun zahra nake cewa a,a likitoci sunce thaphod ne da maleria.

Cikin damuwa yake fadin dama kinsan tana dasu ai basu dai faye tashi mata bane ko wani lokaci don farkon haduwana da itama a cikin irin halin nan na sameta a school cilin mota kowa ya watse ya barta saida nazo na taimaka mata.

Wallahi ban taba sanin hakan ba batama taba fada min tana da wanan laluran ba gaskiya ai kinsa bata da yawan surutu haka balle ki sani.

Ta dan kura min ido na dan lokaci kafin tace iyayyenta sun san da wanan laluran nata kuwa master yace sun sani mana ai don mahaifiyar na tsayene ma abin yai sauki a lokacin.

Yanzunma ina ganin wani abune ya faru har hakan ya tashi mata da badon haka ba ai basa tashi irin hakan har su wahalsheta irin haka tun wancan lokacin don har ina dauka sun bartane kwata kwata ashe har yanzun suna biye da ita din.

Idon shi ya sauke a kaina na fada sosai na rame hancina yafito sosai a lokacin nayi dan wani haske ga ganin shi ajiyan zuciya ya sauke shi kadai yasan abinda yake ji game da hakan.

Makwabata ta shiga diban wutan murhu nan suka tsaya suna tambayanta ya jikin nawa ta fara fadin umm,humm bari kudai yayan masu kudi suna wada suka so.

In banda lalaci shigan ciki aka kwantawa asibiti harda su karin ruwa da kwanciya sai wahal da mutane akeyi suna sintirin asibiti shi dan rawan kan tunda ya dawo sau daya na sakashi a ido ban kara gani nai ba har yau dinga.

Keko dai da wagga maganan wa yanda ma ba diyan kowa ba sun kwantawa ciko balle ita da ad diyan mai kudin gari yanzu ai haka yayina ga matan yanzu abu kadan atai asibiti a kwanta mazan suyi ta wahala koda miji baida shi.

Ashe kegane dauri yaron ga kahin ya auro ta babu dai ababu gidan nan amma tunda ya auro diyaga yanzu daka mai magana zaicewa shi baida shi a,a ankason yayi da rayuwatai .

Amma ita yar mulkin ko cewa tayi tana son kan dan sarki ko wuta zai shiga ya samo yanzun na kana ganin an kawo matashiya muko ko o,oho,ho,ho .

Ai kesan dama haka zai faru tunda ta hito daga gidan masu kudi sai ta dan tabe bakinta kafin ta juya baya ta dawo da fuskanta garesu tana fadin inda ba masu kudin ko wa take ko a gidan nasu suda banza duk daya a gidan ai .

Keko in bashi ba ana daukatan haka zikau a bashi nidai nasan wagga basuwa da ankaimai bata banzata ba da wata a kasa maji magani in gaskiya tta bayana.

Keko bar wanga batanci ga danki mana wata yar dattijuwan gidan ta fada daga gefensu cikin takai ke kanki ke nuna ko dan naki ba cikakena bake nan.

A,a wallah nikan dana ai garau yake mi att matsalanai ita daita dole akwai matsalan da yasa suka bashi ita don har gobe bincike nakai ko zanji wata matsala da aggareta.

Ke arr da wanga halin banzan naki abinga da nikaji ashe shin da gaskiyana baki kaunar diyanga da alheri ke kan Rashida anyi mutumiyar banza wuringa.

Shin yanzu mi nice na ganin laihins ga wanga maganan wai gaskiya naka hwadi kuma shina laihi ni kunga ida niyi tana fadin hakan tasa kai ta fice daga gidan da garwashin wuta a hannunta

Nan suka sameta suka zageta tas bayan fitanta din don wanan maganan data sake a gabansu shine kuma a karshe ya zamo silar shirin mu sosai da mutanen gidan da muke makwabtaka dasu din.

A gidan mu kuma mama taso ta dauki zancen da zafi saidai ummah bata kulata ba sam don haka bata samu wurin yadda mata maganan dake cinta ba a lokacin.

Haka kuma koda Abba shima ya bugo yana tambaya ko tana ina da dare  bayan ta dawo take fada mai tana gida.

Hakama da safe ya sake tambaya duk tana fada mai tana gida yake tambaya bata koma asibitin ba tace tunda ga mutanen gidan mu da abokaina a gidan me zata komayi kuma ?

Jin hakan yasa tasan da wata a kasa akwai abinda ake  shirin kulla mata yasa ta share zancen gaba daya shima Abba din yayi shiru ya daina tambayanta tana inane saidai idan sunyi waya a yinin ranan ya tambayi ya taji jikin nawa.

Sai tace bata kira ba don suce na samu barci mai nauyi inayi sun danyi hiran matsalan kafin ya kashe wayan tun wanan lokacin bai sake kiranta ba ya tambaya yasa ta share ta zauna gida ba don bata damu ba.

Yabi taji muryanshi yana fada abinda rabon ta da jin hakan bata san tsawon shekarun da aka dauka ba sai gashi ranan ya kirata da haka kuma a cikon kakausar murya dake nuna bacin rai karara ga meshi.

Ta dago itama ta kafeshi da idanuwanta tana sauke nata bacin ranta cikin nasa saidai ganin shi haka yasa nata ya kawu a cikkn dan kankanin lokaci.

Fada min dalilin ki na yin almubazaranci da abinci a gidan nan don bansan me hakan ke nufi ba saboda hakan ya nuna rashin tarbiya da rashin tsoro Allah kwata kwatama badai tarbiya ko sanin ciwon kai.

Ke nan nice din yau banda tarbiya banda tsoron Allah saboda nace mai aikina ba zata girka abinci a gidan nan ba duk mai sonci ya fito ya girka da kansa aiban daukowa kowa yar aikiba.

Ok ashe ita Asabe din yar aikin kice bata gidana dana dauka yar aikin gidanace ita amma yanzu barin kirata mu raba gardama sai asan hukuncin da za a yanke karshe .

Daga nan inda yake ya dannawa Asabe din kararawan kira da sauri sai gata dakin hjy yabi din a na  ta samesu tsatsaye cirko cirko ba wanda kewa wani kallon arziki a cikinsu.

Ganinsu hakan yasa tayi niyar juyawa saiji tayi yace dakata shigo ta tako zuwa ciki ta tsuguna a kasa yace dama na kirakine naji zaman wa kikeyi a gidan nan ne ?

Yo Alh ai duk a karkashin innuwar ka muke zaune gidan nan yace ke kika san hakan don hjy tace ke yar aikintane yasa na kiraki naji daga bakinki yanzu idan zaman ta kike a cikin gidan nan da hukunin da zan yanke a yanzu kanku dama.

Jin haka yasa da sauri tace dagani har hjy din ai a innuwarka muke zaune ayi hakkuri Alh munyi kuskure dani da uwar dakin nawa hakan ba zai sake faruwa ba Insha Allahu.

Asabe yaushe har kika samu daman yin irin wanan maganan da maigidan nan haka sai taja bakinta tayi shiru tace na fadama Asabe a karkashina take na sake maimaitawa ko a yanzun din kuma.

Idan kayi hakane don ka tozartani dama to yanzunma na sake fada Asabe yar aikinace da diyana ba da wata ba ok idan yar aikin ce sai ki hada da ita yanzun ku bar min gidana bana bukatan bude ido in ganku a gidan nan kuma.

Alh ayi hakkuri ni din zan tafi ku sasanta kanku abin bakaina tafiya tare da hjy ba sai ya daga hannu yana fadin dama abinda nake son naji ke nan kuma najishi a yanzu don haka awa biyu na baku kubar min gidana.

Wani kallon mamaki take watsa mai lokaci guda kafin tace lalai namiji ba dan goyo bane yau Alh ni kake bude baki kace ka umurceni danabar maka gidanka akan wata mace ?

Eh ba dan goyo din nake ba kema ba yar mutunci kike ba tunda har kikaso tozartani a idon jama,a don kina ganin ban iya daukan mataki a kanki ko me ?

Ni kake fadawa na barma gidanka ido rufe haka yace kwarai na fada idan kika matsa gidan zaki barshi a yau ga baki daya don ina nadamar hada zuria dake da wanan hali naki na rashin imani ga kowa.

Baki ta bude cikin mamaki tana kallinshi kafin ita Asabe din dake tsugune gefen su ta mike tana kara bashi hakkuri da fadin Allah adaiyi hakkuri a faki gaba anyi kuskure hakan ba zai sake faruwa ba don Allah.

Juyawa yayi ya fice daga dakin ya barsu a cikin tashin hankali don har lokacin hjy yabi bata samu rufe bakinta dake budeba a lokacin don mamaki dayasa ta dauke dip a lokaci guda.

Sam bata taba tunanen irin haka zaizo mataba a gidan don yadda da amanna da tayi da irin aiyukan mallaka da ake mata akan Alh wanda sai yadda tayi dashi a rayuwa.

Ga wayanta yana kara amma ta kasa dauka don yanayin tashin hankalin da take ciki a lokacin dole maishi ta hakkura da kiran da take mata lokaci.

Shiko na manzo yana fita malam sale na kiranshi ya dawo don haka yace ya kai kitchen yaba Asabe takaiwa bakin gidan suci amma kadata bari a gane ba a gidan aka girka abincin ba.

Zakice bani bace yadda na koma kwana biyu kamar wace ta dade tana jinya a hankali na bude idona ina bin dakin da kallo kafin in juyo ina kallon mutanen dake cikin dakin a lokacin.

Daga can naji muryan gwaggona Shafa wace autace a dakin su Abba tana fadin kin tashi mahmah ya jikin naki jin hakan yasa kowa ya kallo inda nake kwance suna min sannu da jiki.

A daidai wanan lokacin akai sallama a kofan suka shigo su ukune tafe mamace tare da yaranta Aisha da Rukkaiya dake dauke da ciki tsoho.

Nan aka fara gaisuwa tsakaninsu da wa yanda suka sama a dakin sai jan kamshi da mere baki mama din take faman yi kafin tace to ya mai jikin da sauki ko , ?

Yanzun nan falkawanta ke nan daga barci ance tun safe take barci sai yanzu ta tashi saita juya tana kallon inda nake kwancen tace Zahra ya jikin naki ?

Kokarin bude baki na nayi in amsa sai na kasa na dai gyada mata kai alaman amsawa a lokacin gareta wanan karamin asibitin za a kawota haka yaushe mutum zai samu sauki a nan ?

Aiko nan din ma suna kokari gaskiya gwaggo taba Aisha da tayi maganan amsa ballema ina ruwanta aida sanin uwarta aka kawota nan din kece mai bakin magana yanzu.

Kowa yai shiru kafin can ta fara fadin yaya za ayi in ta fada ace ankawota wanan wurin haka amma sai a dinga yin wasu abubuwa a boye kamar ba a son ka sani.

Ku daiyi hakkuri mu ko hakan ma munga sauki sosai wallahi ciwone inyazo sai hankalin na tare dakai ya gushe duk dabara saita bacewa mutane.

Dije dake zaune gefe ta fada cikin wani yanayi na fahintar abindake faruwa a dakin Rukaiya data fara tafiya tana toshe hanci alaman warin dakin ya isheta lokacin.

Mu zamu tafi mama din ta fada Allah ya sauwaka wasu suka amsa da amin suka fice ba tare da ko mutum dayansu ya karaso zuwa inda nake kwancen ba a lokacin.

Ganin hakan yasa na lumshe idanuna cikin takaici dajin zafin irin cin zarafin da suke min din yanzu don na fahinci suna kokarin nuna niba kowa bace a yanzu din cikin gidan mu.

Muryan mama din na jiyo tana fadin shafa mun biya mu dauko hjy muzo tace ita bata zuwa taga takaici tsuntsunda yaja ruwa shitaka doka suka fice.

Sai naji wata daga cikin matan da muke makwabtaka tace wanan fa wacece ita kuma matar babantane gwaggo shafa ta basu amsa taci gaba da fadin kinsan su yan gayu komai nasu na nuna haline asibitin ne bai masu ba wai yayi karami da kawo zahra nan da akayi.

Duk hiransu idona yana rufe har lokacin jin sallamanshi yana gaisawa da Dije yasa na bude idon don lokacin an rage yawa a dakin naji yana fadin gwaggo ashe kina nan har yanzu na zata zan dawo in samu kin tafi ai.

Tace haba dai na tafi kuma  ai dole wanin mu ya zauna nan din a watse gaba daya kuma aiba komai kinyi kokari Dije ta karba don tana son labarta mashi zuwan su mama cikin hikima.

Wasu aiko zama sin kasayi a dakin sunce dakin yana wari yau aini naga abin mamaki dakin nan ko naga komu muna faman tsabatanshi ai don ko yar nan hannatu yanzu data shigo tana shareshi har ban dakin.

Baidai iskanci bane su nunawa mutane isa da gadara sufa haka suke duk inda sukaje sai sun rainawa mutum suna shiba kowa bane garesu.

Cikin kaguwa da tambaya yake fadin su waye sukazo dije din tace dashi hjyn gidasuce tazo da yaranta shine yar take fadan an kawo zahra asibitin yaku bayi.

Murmushin bakin ciki ya sauke a fuskanshi kadan yace lafiyan ta muke nema ba kyawon wuri ba ai dije ta tashi kuwa ya fada don kawar da zancen nata.

Eh ta tashi amma bata dadeba ta koma barcin ai idonta biyu koda suka shigo din ya tako zuwa inda nake yana fadin sannu zahra ya jikin naki.

Lokacin nayi kokarin bude idona na sauke akanshi ya kara matsowa kusa dani yace zakici wani abu da hannu na nuna mai ruwa nakeson sha.

Yace ruwa na gyada masa kai alaman eh yace da sauri ya dauko goran ruwa ya miko min yana kokarjn tayar dani gwaggo ta taso ta kama mashi goran ya gyara min kai ya ban nasha kadan na cire bakina .

Na koma saman filo gwaggo na kalla nan na hango tausayina zallah a idanunta take fadin ko zaki watsa ruwa ko zakiji dadin jikin naki ?

Na gyada mata kai alaman eh tace to bari a hada ai akwai ruwa a flask sai a juye kiyi wankan dashi inta fito taci abinci hakan akayi naji dadin wanan wankan don jikin nawa na danji ya kara sakewa ba kamar yadda na falka ina jin nauyinsa ba.

Washegari na samu sauki sosai a haka kuma yake fakan idon mutane yana shaka min magani sauki na kara shigata likita dayazo round yace zasu sallameni tunda naji sauki ke nan nayi kwana uku kwance asibitin.

Muka dawo gida ko nan bai bar min maganin ba saidai ban yawan magana sai abin ya kara damunshi dama can ba mai yawan surutu bace ni.

Ganin hakan yasa ya fara tambaya sosai a can wurin tambayan ne ake fada mai abubuwan shege dana tsohon kakana na Funtuwa da yaje.

Maganan dai dayace shine shafata akayi akwai makiya a tare dani mata biyu sune kebina da sheri amma iskan dake kaina basu yarda sun tabani ba.

Kaddaran mu daya dashi ba abinda zai cutar dani sai wani ikon Allah don muna da mabiya masu karfi a tare damu.

Yakanyi tunane wanan wani irin kaddarane haka maigirma da kowa ke fada ma har dai yakai ga tambayan mutumin daya tafi wurinshi a karshe yake fada mai cewa .

Ita kaddara basai ta wani abu ba ai kwai ya barwa Allah sanin sa amma gaskiya tsurarin mu iri dayane a tare suke tafiya daidai.

Tun Daga wanan lokacin ya natsu gida yana jinyata bai koma wurin kowa ba kuma na samu sauki sosai har ina zancen komawa school inci gaba da karatuna don ma Allah ya gyara ba a fara test din exam ba a lokacin.

Kwatsam kira yazo min na bisi cewa goma ga sabon watane tafiyan su zuwa interview don haka ya shirya dama da mukaji shiru an dan dake program din ne zuwa wani lokaci.

Nayi mai godiya tare da fada mai cewa nima nayi ciwone amma naji sauki na zata ai har anyi interview din ko ban sani ba ya tsusaya min tare da tambayan idan banji sauki ba mu shirya tafiyan dani muzo nan a dubani nace na samu lafiya.

Duniya ke nan wanda ban hada komai dashi ba ya nuna min kauna ta gaskiya har yana kokarin fita dani waje a duba lafiyata ga wa yanda muke uba guda suna nuna min kyama a yanzu don kawai ina matar fakiri.

Da yaya musane ya nuna kamar zai tausayawa lamarina amma yanzu har na manta dako yaushe rabon da muyi waya dashi don da farko muna waya amma daga baya kona kirama baya dauka hakan yasa na daina kiranshi.

Ashe abinda ban sani ba shine kamar yadda Abban mu yayi warning din kowa a kaina mama ma ta kara warning din diyan nata sosai kaina da ummah yanzu .

Shiyasa suka fita zancem mu ga baki daya ko ummah din sun daina waya da ita balle dan aiko mata da aike irin yadda sukeyi a baya.

Tun takwas ga wata ya bar Gusau zuwa Lagos abinka da dan tallaka tafiyan mota yayi bata jirgi ba hakan yasa ya wahala a hanya kafin yakai yana zuwa ya samu wanda aka hadashi dashi a cikin daren nan baiko gama hutu ba suka bar kasa zuwa us din.

 

Don Allah ayi hakkuri abubuwane sukayi yawa dole na dakatar da rubutun na kwana biyu yasa bakwa samuna kamar yadda muka saba kuyi min afuwa hakan ba yin kaina bane yan uwa.

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/25, 7:48 AM] +234 816 310 0038: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

7️⃣1️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Abinda ya baka tsoro wata rana sai ya baka tausayi don kuwa wanan karon kuwa ta juyewa hjy Yabi matuka a gidan fafir Alh ya kafe akan sai ta bar masa gida tunda ya furta hakan .

Gashi sai faman kiran duk wanda tasan abaya yana jin nauyinsu tana roko da a bashi hakkuri amma amsa dayane don Allah wani ka gafarceni .

Banaki bin zancen ka bane amma dole sai yabi tabar gidan na  na wata daya ko hakan zaisa ta koyi hankali nan gaba ire iren bayanan dake yawan zuwa mata ke na a bakunan mutanen data tura su bashi hakkuri.

Don sam bata taba tsammani da cewa akwai wani ranan da irin haka zai zo mata a rayuwa ba sanin cewa tsaye take kyam a gidan da kuma kan al,amarin mijin nata ba irin jinin da bata bayar ba akan sha,anin mijin nata.

Yau sai gashi tun bata kaiga ganin cikar burinta ba abubuwa suna son juya mata baya a cikin dan kankani  lokaci haka gaba daya abubuwa sun rikicewa rayuwanta.

Bata da zabi dole ta sauke komai da takeji ta zubar da makaman yakinta ta kwatawa makiyanta ta samu tayi amfani dasu duk da cewa suna cikin lissafin mutanen da bata kauna a duniya ta gansu kusa da mijjnta kuwa.

Alh jabbo dole su zata kira don sune mutane na karshe daya rage ta jeraba sa,anta garesu ta gani ko za ai sa,a yaji maganan su a matsayinsu na abokan,nan sa kuma aminansa tunna zamanin kurciya da har yanzu suna dan biyewa junansu din.

Duk da ita din a yanzu tayi wani kokari da zatayi na ganin cewa ta raba alakan dake tsakanin shi dasu don ganin cewa a yanzu shi din ba ajinsu bane .

Abin kunyane a gareta dashi mijin nata a dinga ganinsu tare dashi a matsayin da a yanzu Allah ya kaishi din nan na zama fitacen dan kasuwa mai fada aji a cikin gwaunatin zamanin.

Don haka tayi duk wani kokarin ganin cewa ta raba tsakaninsu din su hudun ta fitar dashi daban a cikin su tayi kuma nasaran yin hakan yanzu sam ya daina ko zancen su arayuwan shi a yanzu.

Sai gashi yau ita da kantace mai bukatan taimako a garesu don gaba daya duk wani dabara nata ya kare don barin ta gidan kamar yadda ya umurceta dayi wani gazawane a gareta yanzu duniya zasu gane halinda take ciki dashi a lokacin.

Dole uwar naki tabi shawaran yar uwanta data samo mata layin wayan shi Jabbo ya dauka tare da tambayan waye don jin muryan mace da yayi a lokacin.

Da kyar ta iya amsawa cikin isa da takama da izza tana fadin kana magana da Yabice daga Abuja sunan ya fara maimaitawa a bakim shi kafin yace bai san wata mai wanan sunan ba gaskiya.

Ta fahinci iya gaskiyan shi kuma yana kokarin kashe waya yana fadin wrong number tace daga gidan dan gaske nake magana dakai ta juya harshe cikin filatanci yadda zai fahince ta.

Yace yabi dai yabi matar dan gaske ko watace dai take kwaikwayon ta a yanzu tace ita dince sai taji yace dewa,ya, i.

To hjy yabi badai wani laifin nayi ba har kike nemana a yanzu duk da kauyancin shi ya isheta a lokacin amma haka ta daure tabiyewa wautanshi din take fadin a a ha wallahi nice dai ma nayi maku laifi ai kasan halinmu na mata da rashin tunane .

Na taba abokin kune yake fushi dani nace barin nemoku ku tayani bashi hakkuri don Allah don nasan yana jin shawaran ku idan kun bashi hakkuri din in yasa daga baya zamu magana daku musan abinyi a karshe zakuji sakona insha Allahu.

Jam jam meyasa ku masu kudi kuke tunanen cewa saboda kudi duk wani tallaka zai maku komai sai ku manta da zumunci da alaka irin ta addine akan zama tare.

Duk da ke matar tsohon abokinane kuma dan uwa a gareni, haka kuma aminina acan baya, duk da nasan irin abubuwan da kikeyi na ganin kin raba tsakanin shi da mu a tinanen ki shiya wuce ajin mu kamar yadda kika sha fada mana a baya din.

Tun bamu gane mai magananki ke nufi ba har mukazo muka gane gaskiyan zancen ki garemu muka kuma tsaya a matsayin da Allah ubangiji ya ajemu don musan dangaske ba finmu yayi ba a wurin Allah shi kadai yasan wanda yafi a wurinsa.

Kuyi hakkuri don Allah kuskurene amma ba wai haka nake nufi bani son Allah kuyi hakkuri da abinda ya faru ta kara fada a karshe.

Bakomai don daga mijin ki har ke bamu taba daukan ku da wani manufa ba a yazuciyar mu har yanzu a matsayin yan uwan juna muke kallon ku a idanun mu.

Nagode dama nasani shiyasa yanzun ma na kiraka don nasan ku kadai zaku iya shawo kan Allah ya janye maganan da yayi a kaina don Allah.

Ikon Allah harmu dinnan  mun isa mu shiga tsakanin ku da Alh saidai mu dan gyara idan muga da bukatan hakan a tsakanin ku.

Zuwa lokacin yakai mata iya rai tana jin haushin sa yadda yake jan maganan tana tsawo kamar ace yana kusa ta makeshi dai da wanan iya yin na samun waje da yake mata din.

Nan dai ta daure ta koro mashi komai daya faru tsakanin su akarshe ta nemi da ya roka mata shi kada ta fice daga gidan kamar yadda ya bukata da tayi bayan bata mashi rai da tayi kan girkin dare data lalata.

Ya nuna mata laifinta tare da mata alkawarin kiran abokin nasa akan zai masa magana tayi mai godiya ta kashe wayan tana tunanen lalai abu ya baci gareta wai yau itace don lalacewa har take neman taimako a wajen wa yan nan mutane.

Shiyasa manya ke fadin wayasan gobe banda Allah ko a cikin yan kwanaki tana ganin kantane a matsayin macen da tafi kowa iya kama miji ta kammalashi da asiri sai abinda tace zuwa gareshi zaiyi.

Saukan safe sukayiwa kasan amma duk da hakan a nan suka samu wanda sukazo taronsu tun a jirgi yaso ya gane cewa bashi kadai bane a wanan tafiyan sai dai ya saka ido yai shiru yana kallon ikon Allah.

Ga wanda yazo taron su din a nan ya gane don sunayen su dake jere a wuri daya lokacin har su biyar maza hudu mace daya.

Bayan gama binciken su suka nufo wajen fita a nan suka samu mutum biyu suna jiransu sukai masu jagora zuwa wajen motocinsu na  suka shiga aka kara gaisawa.

Sai kallon kallon sukewa junan su don ganin nisan tafiyan da sukayi a tare bada sanin cewa wuri daya zasu je ba sai a wanan gaban suka san cewa ai duk tafiya  nasu dayane a lokacin.

Wani babban gina suka nufa bayan sunsha dan tafiya zuwa cikin garin suna baza ido wurin kallon abubuwan mamaki da suke gani.

Shiru Ahmed yayi yana fama  tunane tare da ganin wautanshi na yarda yayi wanan tafiyan gashi bai fadawa kowa abinda zai tafi yi ba a lokacin haka kuma ya dauko hanya yabar garin har kasan zuwa amsa kiran wanda bai taba sanin shiba da sunan taimako.

Ganin tafiyan nasu wuri dayane yasa suka fara sake jiki da junan su inka debe Ahmed wanda yafi kowa takura a cikin su don gani yakeyi shi tasa ta kare ke nan daga nan.

Komai na wajen kusan da fari da blue akayishi blue mai hasken sararin samaniya sai wani tambari dake jikin ko wani gina na unguwar .

Da alaman ansan da zuwan su don suna zuwa wani bature ya taso yana gaishesu tare da fadin Najeriya suka amsa mashi da eh yace su biyoshi nan ya jasu zuwa dakunan da zasu sauka din dakina da a gida sai sarki ko wani hamshaki kawai zai kwana a cikinsa .

Sai gashi nan an ba kowansu nan ne masaukinsu na tsawon kwanakin da zasuyi a kasan har tafiyansu shikan wanka yayi ya dauro alwala tareda fargaban ta ina zai duba a wajen sallah a kasan.

Allah da ikonsa sai ga taswiran nuna yanayi ya hango makale a dakin ba bata lokaci ya tada niya yayi sallalolin dake kanshi da baiyi ba.

Yana gamawa duk da yunwar da yake ji a lokacin hakan bai hana wani barci mai mauyi ya daukweshi ba sai karfe hudu da wani abu na yamma ya falka daga barcin nasa.

A dan razane ya falka daga barcin yake bin dakin da kallo kafin tunanen shi ya tuno mai inda yake a lokacin  hakan yasashi saukowa saman gadon da sauri yana dan dube dube lokaci guda.

Wurin window din dakin ya nufa ya dan daga labulen yana kallon wajen wurin zuciyarshi cike da mamakin komai na wurin don zakace ba hannu bane yayi aikinsu haka komai sai ya burgeka idan ka kalleshi.

Kofan yaji yana kara hakan ya dawo da hankalinshi zuwa inda yake jin kukan na fitowa koface alaman akwai wani a kofan dakin a lokacin karan bani yayi yai amfani da abinda ya gani a rubuce jikin kofan ya bude kofan lokacin.

Wani mutum ne tsaye  a kofan dan gajere ya dan fara manyanta yana tsaye dauke da kayan abinci yace Mr Yusuf ya amsa masa da kai yace abincin rana na kawo ma tun safe muna zuwa muna samun kana barci.

Bayan tafiyan mutumin ya bude abincin ya irin abincinsune nacan don haka ya dan taba kadan don babu dadi a bakinshi irin yadda ya saba cin namu.

Bayan gama cin abincin ya dan fito ya zaga saidai bai yarda yayi nisa sosai ba don kada ya bace ya kasa gane dakin nasa.

Hutun kwana biyu sukayi kafin a sanar masu da taron  da zasuyi washegarin ranan don haka kowa ya kwana dashiri sunawa Ahmed din kallon bakauye wanda baisan komai ba.

Sai gashi ya barsu da mamaki kan tambayoyin daya amsa masu a wurin interview din ya bar kowa da mamakin hakan don yadda ya amsa masu tambayoyin nasu basu zaci hakan ba daga yan kasan nan.

Lafiya dai wanan kiran haka cikin wanan daren don ban taba zaton hakan daga gareka ba Jabbo .

Murmushi yaji yayi tare da fadin kiran ya kamane na kiraka a yanzun din idan ka duba da cewa ban taba ma kira a cikin dare ba haka ai.

Murmushi ya sauke kafin yace nasan dai duk kuna kusa da wayan ke nan tunda naga ka kirani a yanzu din kwarai kuwa kusan kowa na wurin nan in an debe kaida baka kusa damu.

Sai ya kwashe da wani irin dariya wanda ya dade baiyi irinsa ba don fadin hakan ya tuna mashi da wasu abubuwan kurciya da suka faru dasu a baya suna yara.

Ba wanan ba yanzun dai mun kirakane mu baka hakkuri da shawara ba tare dayin binciken komai kayi hakkuri da mai dakinka don Allah.

Au har can kuma takai karana lalai yabi tana da alaman tabin hankali tunda har ta iya rufe ido wai tana neman taimakon ku a yanzu ?

Yaushe idan ita mai hankaline har zata iya tunkaranku kan zancenta dani matan da da karfibda yaji ta rabani da kowa na kusa dani da aka sanni dasu tun farko.

Ba abinda yake ci mun rai a yanzu kamar zancen ysron nan dana baro zamfara a baya koda an gashi yanzu da wani ido zan kalli yaron nan shida iyayyensa har in yana raye.

Abinda ya wuce abar tunashi sai hakkuri da istigifari don neman yardan ubangiji ga bawa amma duk ake tuna irin wanan abin ba zai taba wucewa a zuciyar mutum ba ai.

Amma kasan ko komai ya wuce zancen yaron nan ba zai taba barin zuciyana ba don bansan da wani ido zanwa Allah bayani ba a kanshi.

Jabbo kasan ba karamin cutana yabi da yan uwanta sukayi ba yanzu gashi duk wanda na tura sai ya dawo yace min wai ba a gane komai ba game da yaron da iyayyensa ba.

Don haka yadda ta rabani da kowa nima a yanzun banson ganinta gidanan ta fice min daga gida ko zan samu sallama a rayuwata.

Zaka samu insha Allah kaidai ka kwantar da hankalinka yanzu idan ja yake hukunci a cikin fushi ai baka kaiga cinwa manufarka akanta ba ke nan idan Allah yayi yaron ka ya baiyana kaga bataji komai ba game da dawowan nasa.

Ga hjy murja data dawo yanzu shima ba wani zama sukayi tare da da zaisa ta fara nadaman abinda takewa mutane a baya ba don haka kayi hakkuri ta zauna dakinta don Allah.

Zata zauna amma wanan karon ina son ta fara dandana irin abinda naji a kanta itama don haka kona sati dayane sai ta bar gidan nan taji itama in hakan yana da dadi.

Zata bar gidan na kwana biyu kawai tunda kace hakan amma na sati daya gaakiya yayi yawa to shike nan ta bar min gidan nawa shine kawai saukin zuciyana a yanzu game da ita.

Dole hakan akayi saidai bata dawo gida ba nan ta zauna a Abujan a cikin wani gida nata data saye boye yana jin hakan yace ai idan ba gida garinsu ta koma ba akaje can akai magana ba zata taba dawo masa gida ba.

Gashi wanan tafiyan ya bashi daman tone wasu abubuwa data binne a gidan dama aikin da kowa baisan lokacin da tayi shi sai hakan ya kara sashi cikin sallama yake jin tankar ace hjy yabi din ta tafi ke nan daga rayuwan shi har Abada.

Leave a Reply

Back to top button