Qamshi Complete Hausa Novel

Qamshi 16-20

Sponsored Links

 

 

*✨QAMSHI  16-20 ✨*

 

 

✍️RASHOW

 

A hankali Hatim ya shiga sakkowa daga stairs yana gyara zaman agogon dayake daurawa a hannun shi,yana sanye da wata cotton din yadi milk kala wacce akayi ma dinkin half jamfa yadin sosai ta zauna ajikinshi tare da futo da ainayin kyanshi,Seda yazo dab da matakalan karshe sannan ya dago kanshi ya kalli katon falon su wanda babu kowa aciki se Karan sautin magana dayake fitowa daga cikin qatuwar tv dake cikin falon wacce take aiki duk da volume din ba sosai bane Sabida sanin halinshi na rashin son hayaniya.

dan Jimm Hatim yayi kamar me nazarin wani abun sannan ya qarasa saukowa daga kan stairs din ya nufi wata kofa da take cikin falon amma tana da dan nisa da wajen stairs din,a hankali ya kama handle din kofar ya murda tare da sallama ya shiga cikin dakin.

 

“waalaikassalam”

 

wata farar mata dattijiwa ne ta amsa mishi sallamar duk da hutu da gaye sun boye ainahin shekarun ta,don idan ka ganta bazaka ce itace ta haifi Hatim me shekaru kusan 35 ba,zama yayi kusa da ita ya dauki awarwaron da take jerawa acikin box ya shiga ta yata yace

 

“Ammee barka da warhaka Ina yaran sukayi naji gidan shiru sun barki ke daya.?”

 

murmushi wacce Hatim ya kira da Ammee tayi Kallo daya zaka mata kaga tsananin kamar da sukeyi da Hatim,kallon shi tayi tace.

 

“suna dakin Jiddy sunje dauko magana.”

 

kanshi ya daga mata tare da mikewa yayi hànyar futa a dakin,futowa yayi daga falon gaba daya ya miki wata doguwar baranda ya nufi wani sashi dayake cikin gidan, tsayuwa yayi a gaban wannan sashin wanda tun daga waje kake jiyo hayaniyar mutanan cikin wannan gidan,

gaba daya hankalin matasan guda biyu yayi nisa akan cin kilishin da Jiddy ta basu sannan ga  wani kuma matashin yana buga qafarshi a qasa yana bori kamar wani karamin yaro yana buga kafar shi Wai shi Sam sedai Jiddy ta hada mishi kilishin sa da dambun nama tukunna yaci,sukuma sauran matasa guda biyun suna cewa matukar Jiddy ta bashi to suma seta basu,shine yake borin shi bazai ci kilishin ba harse ta hada mishi duka biyu.

dukan su da suke falon hankalin su yana kan Jiddy wacce ta fito da bokitin roba a hannun ta hakan ne ya janyo hankalin sauran matasan suka nufeta tare da mata rumfa cewar lallai seta basu suma,qamshin turaren Hatim ne ya Sanar musu da wanzuwan shi acikin falon.

Da sauri matashin da yake bori dazu ya juyo da sauri ya dangwarar da filet din hannun shi ya tawo gurin Hatim ya rungume shi yana matsar ido wanda babu hawaye yace.

 

“yaa Hatim kama Jiddy magana tabani dambuna ni bazanci kilishi zalla ba.”

 

rungume shi back Hatim yayi tare da kama hannun shi suka karasa shiga falon ya zauna akan daya daga kujerun falon,sanin zaiyi wuya Hatim ya bashi amsa a lokacin ne yasa sakalallen Yaron nan yayi kokarin cire hannun shi daga na Hatim ya juya zai koma gurin matasan nan da tsohuwar nan wacce taki bude bokitin hannun ta kuma ta daurashi akan cinyarta ta rike gam.

 

“Jiddy a bama Thariq dambu yaci ok.”

 

Hatim yayi maganar a sanyaye kamar yanda ya Saba magana yana kuma lumshe idon shi kamar Wanda zaiyi barci,kallon shi Jiddy tayi ta mele baki kamar wacce bataji me Hatim din yace ba ganin haka da Thariq yayi ne ya kwabe fuska kamar zai mata kuka yace.

 

” Jiddy yaa Hatim fa yace kibani. ”

 

Wani kalan hararan shi Jiddy tayi.

 

“tunda shi Hatim din uba nane ai sekace yama kurayen qannan shi magana su matsamin akai sannan na baka,ni tunda nake a duniyar nan ban taba ganin yaran da basu da godiyar Allah ba to wallahi kusani duk dai wanda be gode ma Allah ba to Allah ne kadai yasan yanda zaiyi dashi kuma dambu ne bazan bayar ba don babu Wanda yasha wahalar kamo kajin agidan gona ato.”

 

Jin hakan da Thariq yayi ne ya juya da sauri ya nufi Hatim.

 

“please yaa Hatim kayi ma Jiddy magana ta bani ni Allah tana Jamin rai dayawa.”

 

dago da kanshi Hatim yayi ya kalli Thariq wanda  gaba daya yawani futa a hayyacin shi kamar Wanda zai fashe da kuka sannan ya mayar da idon shi kan sauran matasan wanda suka rufu ma Jiddy ita kuma ta rike roban dambun ta qam se wani girgiza takeyi ta daga Kai sama,kai Hatim ya girgiza ya bude baki dakyar da tattausar muryan shi me cike da iko.

 

“Zafeer and Zunnurain.”

 

yayi musu alama da ido jin ya ambaci sunan sune yasa matasan tasowa daga jikin Jiddy suka koma gefe kan kujerun falon suka zauna tare da shiga  hankalin su don sun San waye Hatim bayi son hayaniya.

Gyara zama Jiddy tayi ta sauke roban dambun kazar dayake kan cinyarta tana Mita.

 

“an gaya muku tsintar dambun nayi da zan baku a gabas ba tare da kunsha wuya ba to nima Seda nasha bakar wuya na taka har cikin gidan gona nasa aka kamomin kajin,inace kuna kallona nazo na wuce ta gaban ku amma duk cikin ku babu Wanda yayi tunanin ya karba ya shigo min dasu cikin gida amma dayake gurin cin naman ne kun iya tasowa ku rufeni kamar nice na zama kazar,to sedai kuci kanku Allah kuma ya yafe muku don nikam babu ruwana.”

 

Seda Jiddy ta gama mitar ta sannan ta zuba ma Thariq kusan cikin fulet din ta Sanya mishi kilishin awani fulet ta kwalama me aikinta kira data iso tace.

 

“yi sauri Rabi ki kawo musu lemon gora suci dambun nan dashi seki kawomin wasu fulet din.”

 

da sauri Rabi ta juya ta koma kitchen ta dauko duk abun da Jiddy ta Sanya ta taje gaban kowa ta janyo table din dake jikin kowani kujera ta ajiye lemon gora da malt akai,Seda Jiddy ta kammala zuba ma Kowa Dambun naman sannan ta miqa ma Rabi tace.

 

” ungo yi maza ki ajiye musu akusa da kowa daman rashin hakuri da rashin godema Allah ne yasa suka rufeni idan basu ba ma waye zan zauna nayi ma dambun kazan.?”

 

Kallon Hatim Jiddy tayi tace.

 

“fisabilillahi Hatim idan bama su jikokina nayiba to mawa zanyi? ae idan na hanasu to ya tabbata bani da godiyan Allah kenan,ko ita Hajara mahaifiyar taku duk da ita din ba jinina bane ae bana hana ta ba ball…..”

 

Hadiye maganar Jiddy tayi ganin irin kallon da Hatim yake mata amma seta lauyance tace.

 

“miye kuma na wani kallona ai gaskiya na fada ita Hajaran yanzu ae duk an zama daya wama ya isa yace ita din ba jini na bane tunda ta haifo ma dana ku nikuma ta Sanyamin farin ciki acikin zuciya na na samomin jikoki kamar ku duk da wasu halayyar ku akwai wanda se kun ringa hadawa da istigifari kafun ku samu salama acikin zuciyoyin ku,kudai kawai Allah ya yafe muku shine magana amma ba kuyi ta zare ido kuna lumshe su kamar Wanda suka

shekara bakuyi barci ba.”

 

Kunshe baki Zafeer da Zunnurain sukayi suna dariya qasa qasa don sunsan da yayan su Jiddy takeyi amma ta kasa futowa tayi maganar direct.

 

Duba agogon hannun shi Hatim yayi ya mike ya kalli su Zafeer.

 

“time is magrib OK.”

 

mikewa dukan su sukayi ba tare dasun daga filet din da suka gama cin dambun naman ba, Zafeer ne ya nufi toilet din cikin falon Jiddy shikuma Zunnurain ya nufi toilet din cikin dakin Jiddy,seda suka futo sannan Thariq ya shiga shima ya dauro alwalan suka futa a falon tare,a bakin barandan sashin suka iske Hatim a tsaye yana duba wayar shi, jin sun karaso kusa dashi ne yasa ya mayar da wayar aljihu ya dago narkakkun idon shi ya zuba musu tare da juyawa suka nufi masallacin waje wanda yake kusa da gidan su.

 

 

*********

 

Da hanzari nashiga falon Alhajin mu don amsa Kiran dayasa akayi ma duk wanda yake cikin gidan,koda na iso na samu duk mutanen gidan sun hallara har Diddy.

a hankali nayi sallama ya bani izini nashiga na nemi gefe na zauna sannan Alhaji Baba ya bude taron da Addu’a sannan ya dubi kowa ya tsaida idon shi akan hajiya ya numfasa yace.

 

“wato Hajiya wani muhimmin al’amari ne ya tasomin yanzu daga can kamfanin da nake aiki,mun samu Kiran gaggawa daga shugaban kamfanin wanda mukayi zama aka tattauna,hakan ya kawo harda daura wasu akan ragamar kamfanin wanda Ina daya daga cikin wanda aka nada.”

 

shiru Alhaji yayi daga maganar yana nazartan dukan mu damuka zuba mishi ido don jin karshen zance.

 

” Hajiya ba mukamin da aka bani bane abun daya dameni ba illah canjin waje dana samu domin anbama kowa gurin zama wanda zai zauna shida iyalin shi hakan na nufin zamu bar nan mu Koma canda zama wannan shine duk abunda ya dame ni.”

 

 

“Alhamdulillah Alhamdulillah tabbas Allah ne abun godiya domin inbashi ba babu me iya baka wannan matsayi.

 

Hajiya Diddy tayi maganar fuskarta dauke da murmushi da alamu abun yayi mata dadi, kallon ta Alhaji yayi da mamaki domin shi duk damuwar shi ita ne don yasan dakamar wuya tabar wannan gida amma se gashi cikin ruwan sanyi ta a mince ba tare da ansami wani damuwa ba.

 

duban dukan mu Baba Alhaji yayi yace.

 

“kunji yanda abun ya zama ku menene ra’ayin ku akai.?”

 

kafun kowa yayi magana Hajiya Diddy tayi caraf tace.

 

“yo Allah na tufa wani magana zasuyi kuma bayan Kai kake da iko da kowa dayake nan kawai cewa zakayi kowa ta hada kayan ta zuwa ranar da za’a tafi can cikin garin.”

 

Kai Baba Alhaji ya daga yace.

 

“Hakane Hajiya daman Shima kwana biyu ya bani sabida yace base munje da komai ba illah kayan sawar mu sabida gidan komai akwai.

 

” masha Allah bari ka gani naje na kimtsa kayana don so nakeyi na fara zaban yanda zamu zauna nida Diya ta, yi maza Qamshi ki taso muje ki hada mana kayan mu idan yaso sedai kayan ya jiramu zuwa ranar da zamu tafin Kar azo ana jiran mu bamu gama Shiri ba, Kaima Mu’azu ya kamata Kayi wuff ka hada naka kayan karka bata masa lokaci yata jiran ka don inka biye ma matan ka seka makara don da ganin fuskarsu kasan basuyi na’am da wannan cigaban naka daka samuba nidai na tafi gurina Ubangiji ya Kara shigema gaba . ”

 

ajiyar zuciya Baba Alhaji ya sauke sannan ya maida hankalin shi kan sauran Yan falon yace.

 

” kundaiji me nace Ina fatan zaku hada kayan ku akan lokaci kuma iya Zallan kayan sawanku zaku dauka se abun bukatar ku wanda kuke ganin zaku bukata.

 

addu’a su yaa Kamal sukayi ma Baba sannan duk yaran suka watse aka bar matan Baba Alhaji don su kara tattauna batun…..

 

 

07052100719 chat me up.

Leave a Reply

Back to top button