Furar Danko Complete Hausa Novel

Furar Danko 77

Sponsored Links

77

 

……..Yanda take kuma ya tadama Ammah hankali matuƙa, ta dawo kusa da ita da jawota jikinta ta rungume tana jin itama hawayen na cika mata idanu. Yanda Lulu ke kukan nan zai tabbatar maka al’amarin na matuƙar taɓa mata zuciya, dan har Hawwah sai da tai hawaye. Sosai Ammah taji ƙarin ƙaunar Lulu a zuciyarta. Sai da tai shiru

sannan ta fara mata nasiha da bata addu’oi akan ta dage ta dingayi da yawaita karatun Alkur’ani hakan zai dinga rage mata nauyin zuciya, dan masu irin ayyukansu saboda yanda suke tara abubuwan ɓacin rai da damuwar al’umma daga ƙarshe sai kiga sun kamu da hawan jini dana ciwon zuciya. Sosai yanda Ammah ke jero addu’oi a bakinta taji ta sake birgeta da kwaɗayin akan samun ilimin addini. A haka su Asma’u suka shigo ƙarfe biyu. Da mamaki Ammah ke dubansu dan tasan dai sai biyar suke dawowa daga islamiyya duk ranar weekend. Hawwah ta ce, “Kukuma fa naga kun dawo?”. Kallon juna sukayi kafin Maryam tace, “Adda haddace bamu iya ba shine muka gudo, kin san dai malam Jabeer ba sauƙi wlhy”.

 

Ammah data tsira musu ido tace, “Duk karatun da kukai ɗazun da asuba. Kudai faɗi wani ba wannan ɗin ba. Wai Maryam yaushe ma kika fara ƙarya?”.

 

Ƙasa Maryam tai da kanta tana shafa ƙeya, Asma’u dake ƙara rakuɓewa jikin kujera ta ce, “Ammah gaskiya da gaskiya dai saboda Aunty muka gudo, kinga fa yini zatayi amma mu banda mu. ALLAH muna son muma mu yini tare da ita shine mukai shiri tare da Adda Maryam idan akai salla muyima Malam Jabeer ƙaryar zamu rakaki asibiti”.

 

Hawwah dake dariya tace, “ALLAH ya shiryeku Ammahn kukai ma sharrin ciwo kenan?”.

 

“A’a wlhy mu bamuce kowa ba, kawai dai munce zamu rakata asibiti”.

 

“Kuma ya yarda? Bayan nasan Malam Jabeer da shegen bin ƙwanƙwanto”.

 

Dariya Asma’u tai tana kallon Maryam, ita kuma ta harareta alamar dai akwai wata a ƙasa. “Munafukai mi kuke ɓoyewa?”. Cewar Hawwah tana kallonsu cikin waro ido. Alamar zip Asma’u taima bakinta da faɗin “Ba ruwana ba’a bakina ba”. Lulu da ke murmushi ta ce, “Haba Auta bamu musha mana”.

 

“Aunty ba faɗar bane matsalar, sai kun gudu gidajenku ta jibgan a ɗaki ko Ammah bazata bari ta sani ba”. Ranƙwashi kuwa Maryam takai mata. Da gudu tabar wajen tana dariya. “Sonta yake ya kasa gaya mata, gashi kuma ya tsaya kallon ruwa kwaɗo yay masa ƙafa. Dan ga wani tauraro mai babban haske ya faso kai da ƙarfinsa”. Binta Maryan tayi suka shige ɗaki da gudu. Kai kawai Ammah ta girgiza da faɗin, “ALLAH ya shiryeku”. Yayinda Hawwah da ke dariya ta ce, “A gama ɓoye-ɓoyen intai wari maji ai”. Lulu dai murmushi takeyi dan komansu burgeta yake yi. Bakomai ya jawo hakan ba kuwa sai yanayin rayuwar data tashi a ciki ita da nata ƴan uwan. Bayan su Maryam sun cire Uniform suma falon suka dawo aka ɗora hira, anan sukaci abincin da aunty Amarya ta gama, bayan sallar la’asar Maryam tai zaman yima Lulu kitso. Dan nakan Hawwah ta gani ya burgeta ta tambaya duk da ba son kitso take ba. Jin Maryam ce tayi sai tace itama aimata ko kaɗan. Shine sukai zamanyi suna cigaba da hira harda Ammah. Nasreen da suka dawo daga makaranta tana zaune a cinyar Lulu suna shan chocolate dan itama shazumamun ce kamar Lulun. Sallamar Smart ta sakasu tsagaita dariyar da sukeyi dan Asma’u ce ke kwaikwayon Muryar malaminsu Jabeer dake son Maryam wai idan ya ganta har ƙara maƙewa yake yi. Akan Lulu ya fara sauke idanunsa kafin yabi sauran da kallo, ya ƙarasa takowa cikin falon yana kaiwa zaune da faɗin, “Miyay muku daɗi haka kuke kwasar dariya har tsakar gida kun cikama mutane kunne? Ammah duk sun zagayeki sun dameki”.

 

Cikin murmushi ta ce, “A’a basu damen ba Hydar, ai ko kurama da ƴaƴanta take wasa a jeji. Sai yanzu muke ganin ka”.

 

“Wllhy ki bari dai Ammah. Da ga wani waje mai nisa muke fa, kin san Ahmad da shegen kutse-kutse can wani ƙauye ya samo gona zai gyara yay gidan gona a wajen shine fa mukaje dubawa”.

 

“Kai masha ALLAH, ai haka mukeso mu kuyita shiga irin hakan dan nan gaba kaɗan kune manyan goben.”

 

Murmushi yay cikin jinjina kansa. Kafin ya maida hankali ga ƙannensa da ke gaishesa. Idon Ammah ya sa Lulu faɗin, “Sannu da dawowa”. Sai da ya maimaita kalmomin guda uku a zuciyarsa yana mai ɗan kafeta da kallo, sai kuma ya janye shima cikin basarwa ya ce, “Yauwa ya gidan”.

 

Abinci Asma’u taje ta kawo masa, sai cewa yay ta maida baya jin yunwa, garama in sunada fura dan yasan dai Ammah bata rabo da ita. Asma’u tace masa akwai, taje ta ɗibo masa a fridge ta kawo masa. Daga haka suka cigaba da hirarsu Lokaci-lokaci yana satar kallon Lulu da akema kitso masu ƙyau. Wajen shida ya kalla agogo da faɗin, “Ku wannan kitson yaushe zaku gama shi har mu wuce? Gashi ina son mu biya ta wani wajen”.

 

“Ina? Ai ni nan zan kwana yi tafiyarka”. Cewar Lulu da iya gaskiyarta. Murmushi Ammah tayi, yayinda Smart dake mata kallon mamaki ya ce, “Kwana fa? Kin manta gobe Monday zakiyi resuming office?”.

 

“Ba damuwa jibi naje”.

 

Murna su Asma’u suka fara yi zata kwana. Ya hararesu duk sai suka nutsu. Ammah dai bata ce komai ba har sai bayan sallar magrib da ya shigo ya sameta a ɗaki, lokacin su suna can ɗakin suna tasu sallar. Zama yay kusa da Ammah, hakan yasata yin addu’a ta rufe Alkur’anin. “Ba dai tafiyarba ko?”.

 

“Da haka nake so dai ta shirya, da anyi isha’i sai mu wuce dan ina son mu biya ta gaida Kakanta ɗazun Uncle Yousuf ke faɗamin baya jin daɗi ya dawo daga Legos ɗazun, gashi kuma tana batun kwana anan”.

 

“Karka damu zan mata magana. Amma Aliyu sai nake ganin akwai wani ɓoyayyen al’amari a rayuwar yarinyar nan dake damunta, na fahimci hakanne a ɗan firarmu da ita ta ɗazun. Sannan bata son kaɗaici, dan ta roƙeni na baku Asma’u ta koma can da zama. Danace mata Abbanku bazai yarda ba ina kula da ita sai da idonta ya cika da hawaye. Mizai hana a ɗan samo mata ko tsohuwa haka da zasu zauna tare, sannan kai kuma ka ƙara ƙaimi wajen janta a jiki dan ka fahimci minene damuwarta. Ko yaya ta sanar maka itama zataji nauyin ya ragu mata a zuciya. Ashe mahaifiyarta bata raye kuma?”.

 

“Ta rasu, tana haihuwarta. Inasha ALLAH zan yi iya ƙoƙarina”.

 

“ALLAHU akbar. ALLAH ya gafarta mata. Wlhy duk sai yarinyar ta sake bani tausayi. Gata da sauƙin kai da sanin darajar mutane. Sai kuma yanda na fahimta akan aikin nan nata kamar zafinta akan al’amarin fyaɗe nada alaƙa da wani abu daya sosa ranta gaskiya. Ya kamata dai ka zama mai haƙuri da dinga ƙarfafata”.

 

“Insha ALLAHU Ammah zan yi iya ƙoƙarina. Batun Asma’u kuma haƙuri zakuyi ta koma can ɗin tunda tana son hakan. Kodan ma tafiyar nan dake tunkarowa.”

 

“To bazance A’a ba, amma ka samu Abbanku da maganar kadai sanshi. In akan tafiyane kuwa bazai yiwu dama a barta ita ɗaya ba. Ko ita da Asma’u kawai dole cikin samarin nan wani ya koma can ya dinga kwana da su”.

 

“Hakan ma yayi Ammah. Duk yanda kikace haka za’yin”.

 

Sun ɗan ƙara tattaunawa akan abinda ya shafesu musamman akan Hawwah, kiran sallar isha’i ya sashi tashi ya fita. Bayan ya dawo sai da Ammah ta lallaɓa Lulu da wayo sannan ta yarda su tafi. Yanda take zubama Ammah ɗin shagwaɓa sai Smart ya zama ɗan kallo. Dan mamakin yanda tai bala’in sakin jiki da Ammahn yake yi har irin haka a ƙanƙanin lokaci. Koda tajema su Umma sallama har yanzu akwai alamar takaicin ƙyautukan data raba musu ɗazun a tattare da ita. Dan kusan ma a tashin hankali ta yini, ga surukar jiya-jiya a gida daga zuwa tana neman fara haskawa, yarinya da baƙin wayo. Ai zama bai ganta ba, dan kuwa kamar ta kashe maciji ne bata dare kansa ba kasancewar Lulu matsayin surukar gidan nan na nufin disashe tauraron ƴaƴanta da ake gani sama dana kowa. Oho Lulu ba damuwa da sabgar da ba’a sakata ba gareta, dan haka ita bata wani fahimci mi Umman ke ciki ba, dan ko kallon su Huwaila dake falon batai ba. Haka kawai jininta dana Umma baizo ɗaya ba, da ƙyar ma ta yarda ta biyo Smart ɗin suka shigo da tace yaje ita zata je ɗakin Aunty Amarya ya sameta ya nuna mata dole ta shiga ko’ina suyi musu sallama. Ganin babu wasa a tattare da shi yasata bin nasa badan taso ba. Daga wajen Umma sai ɗakin Mama. Nan ma basu jimaba suka fito, nan ko Mama ta bata alawar madara da Hannatu keyi ta saidawa. Hakama aunty amarya ta bata farar data soya mata da rana har kwano biyu. Aiko taji daɗi tanata godiya. Abba ma sunyo masa sallama ya haɗa Lulu da tsarabar zuma da mazarƙwaila kasancewar sa masoyinsu yana ajiyewa. Sai da zasu shiga napep Maryam ta ajiye mata ledar tsarabar Ammah. Duk sai Lulu taji ƙaunar bayin ALLAHN nan na sake ratsata. Shi kansa Smart yaji daɗin wannan karamci da sukai mata. Kasancewar mai Napep ɗin ɗan anguwarsu ne zai kaisu har gida da inda ma zasuje kai tsaye ya nufi Nasarawa G.R.A dan Smart ya riga ya sanar masa tun kan Lulu ta fito. Ganin inda suka nufo ya sata jin farin ciki, a Napep ɗin suka bar kayan suka shiga cikin gidan na Alhaji Sufi Ado Garko. Sun sami yaran gidan da jikoki da yawa, inda kowa yay musu ca aga yaya Lulun ta koma. Sai kuma suka ganta fes har wani ƴar ƙiba kamar ta ƙara musu ma su a ido. Alhaji Garko dake kallonsu da murmushi ya nunama Aliyu kusa da shi. Maimakon hakan sai ya zauna a ƙasa kusa da ƙafafunsa ya gaidashi cikin girmamawa da tambayar yaya jiki. Da kulawa ya amsa masa da sanya albarka. Dada kam sama-sama ta amsa masa tana masa hararar ƙasan ido Lulu na jikinta lafe. Ya gaisa da sauran wanda suke ɗakin suma, daga haka yaja bakinsa yay shiru sai Baba ya takalesa da magana ko tsokana ne yake ɗan murmushi koya bada amsa a taƙaice. Kusan awansu biyu sukai shirin wucewa, anan ne Dada ke cema Lulun “Ku bari sai anjima mana tunda dai mota ce kuma daga nan guda kukai”. Batare da Lulu ta kawo komai a ranta ba ta ce, “Dada a Napep muke fa, babu daɗi mun barsa a waje kusan awa biyu. Kuyi haƙuri zan dawo gobe in sha ALLAHU”.

 

A zafafe Dada ta ce, “Napep kuma? To ina motocin naki? Kodan shi baida motar hawan dan bakin ciki irin na talaka kema bazaki hau ba? Kamarki jikar Garko family a garin nan da hawa Napep…”

 

Yanda Dadan ke maganar a zafafe da ɗaga murya kowa naji ya saka Lulu duban inda Smart yake, sai kuma ta dubi Dada zatayi magana cikin ɓata fuska amma ta dakatar da ita……..✍️

Leave a Reply

Back to top button