Furar Danko 76
76
……..Itama cikin farin ciki take musu sannu da zuwa, yayinda Lulu ke amsawa tana nufar Nasreen. “Oh oh mi akaima wannan princess ɗin ne haka take ɓarnar hawayenta masu tsada?”. Ta faɗa tana ɗaga Nasreen, zama tai ta ɗaurata saman cinyarta. Itako ta lafe cike da shagwaɓa da kuka ta ce, “Ba Mommy bace ta daken dan na kira Abbana a wayanta”.
“Ayya Mommy ita bata san mun ɗan ara bane muji muryan Abba. Barta daina kukan bazamu bata chocolate ɗinmu ba”. Tai maganar da share hawayen Nasreen ta ɗauka handbag ɗinta ta ciro chocolate biyu masu daɗi da tsada ta baima Nasreen. Tuni ta fashe da murnar dariya ta kaima kuncinta sumbata cike da farin ciki, sai kuma ta ɗaga musu chocolate ɗin tanai musu gwalo. Hakan ya bama Lulu dariya ta saki murmushi, suma duk sai suka fashe da dariya ƙasa-ƙasa. Dai-dai nan Ammah ta idar da sallanta, batai doguwar Addu’a ba ta juyo fuskarta da murmushi mai ƙyatarwa. Akan Smart da ke zaune kujerar kusa da inda take sallan ta sauke, sai kuma ta maida ga Lulu. Kafin tace wani abu ya saukko a kujerar ya zauna kusa da ita yana gaisheta, ganin haka yasa itama Lulu sakkowa da ga kujerar ta zauna ƙasan carpet ɗin da ke a share tas ga ƙamshi mai daɗi na tashi a falon ta ce, “Ammah ina kwana”. Da sauri Ammah ta girgiza mata kai da miƙa mata hannu murmushin ɗunbin farin cikinta na sake bayyana ta ce, “A’a zonan ɗiyata kinji, taso maza taso gareni”.
Abin mamaki sai Lulu ta samu kanta dajin kunyar Ammah. Da ƙyar ta iya miƙewa ta nufo inda take, zata zauna ɗan nesa kaɗan nan ma Ammah ta riƙo mata hannu ta zaunar da ita jikinta sosai. Ajiyar zuciya Lulu ta saki hawaye na ciko mata ido, amma sai ta daure kanta a ƙasa ta sake gaida Ammah a karo na biyu. Shi Smart ma da abin ya girmesa kasare kawai yay yana kallonsu. Ammah ta riƙo hanunta cikin nata tana amsawa da kulawa.tare da ɗorawa da faɗin, “Ki saki jikinki ɗiyar albarka nan gidanku ne, ni ɗin ban son ki ɗaukeni mamar mijinki mamaki ce dan yanzu kinfi Hydar matsayi a wajena….”
Cikin waro idanu da ƴar shagwaɓa ya ce, “Ammah! Hakama zaki ce ina babanki ɗin?”.
“Kai tafi can ai photo copy ne ba original ba wake ta taka. Anata sabon ɗa waketa tsohon ɗa”.
Dariya su Hawwah suka saka, Lulu ta ɗago ta masa gwalo da nuna masa 8-6 da hannu. Lips ɗinsa ya cije da ƙaramar harara. A dai-dai nan Mama ta shigo tanama baƙuwa lale marhabun. Itama sai Lulu ta gaidata da girmamawa, Mama ta amsa da fara’a tana sanya mata albarka, dan ita dai barta da rashin mutuncinta idan ya motsa ko Umma ta tunzurata. Amma tanada kirki a lokuta da dama, sannan bata saka ƴaƴa a kishinsu inba taƙure ba.
Yaranne suka shiga shigowa ɗaya bayan ɗaya suna gaidata kamar yanda Mama ta basu umarni, sai dai a ƴaƴan Umma Mubarak ne kawai ya shigo cike da zumuɗi, dan yaso zuwa gaida amaryar yayan tasu Umma ta taka musu birki akan duk wanda yaje koda a bayan idonta saita tsine masa. Wannan girmamawa da Lulu taga an mata ya matuƙar birgeta, (tana son a girmamata a nuna mata ita mutumce mai daraja) koda Umma ta leƙo itama a gatsine wai tana mata sannu da zuwa da ɗan habaicin basu fara shiga ɗakunan su ba Lulu ba fahimtar komai tayi ba. Hasalima kallo ɗaya taima Umman ta duƙar da kanta dan haka kawai take jin Ammah ta mamaye mata ko’ina. Bata taba jin nauyin mutum da kwarjini kamar yanda takeji akan Ammah ba. Ga tsantsar soyayyar ta data hanga a cikin idanun dattijuwar yasata jin wani irin ƙaunarta ta musamman. Smart da shima yake matuƙar jin farin cikin nutsuwar da yaga Lulu tayi a gaban Ammah ya ce, “Da nasan haka za’amun a gidan nan daban zo ba. Amma ba koma a bani shayi nasha nai gaba. Zaku nemeni ne”.
“Wake buƙatarka balle ya nemeka anan”. Cewar Ammah da murmushi. Fuska ya shagwaɓe da faɗin, “Ammah! Ammah gara dai ki tarairayeni dan da tsohuwar zuma ake magani”.
“Ga wanda bai sani ba ba”.
Ammah ta bashi amsa.
“Shike nan na daina magana. Hawwah bani shayi na ƙara gaba, itama fa ku nema mata abinci bamu karyaba muka fito dan zumuɗinta”.
Ammah ta ce, “Kai Hydar dan ganganci. Shine kuma maimakon ka kira waya tunkan ku taho a ɗaura muku”.
“Haba Ammah sai kace wasu baƙi”.
“Baƙine mana. Tunda wannan ne karo na farko data fara marabtarmu dan wancan ba’a sakashi a lissafi. Ɗiyata mi kike son ci”.
Ƙasa Lulu ta ƙara yi da kanta tana girgizawa da faɗin, “Ammah bana jin yunwa ma, abarshi har sai anjima”.
“A’a bazai yiwu ba Mawaddatan’warahmah. Ƙarfe goma harta gota ace sai kuma anjima”.
“Ammah bason cin abinci take ba shiyyasa. Idan kika biye nata ma daga nan har dare zata iya kaiwa”. Smart dake ƙoƙarin kai shayin da Hawwah ta kawo masa bakinsa ya faɗa. Ɗan harararsa Lulu tai ƙasa-ƙasa bata dai ce komai ba. Shi kuma yay mata murmushin da take kira na mugunta.
Yana kammalawa ya miƙe da faɗin shi zaije ya gaida Abba ya wuce, sai anjima zai dawo. Addu’a Ammah tai masa da ta ratsa zuciyar Lulu matuƙa harta tsira musu ido. Karo na biyu yaji wani abu ya tsikarar mata zuciya game da ilimin addini, sai kewar mahaifiya data ratsata, itama fa da Mah-mahn ta nada rai da haka zata dinga mata ko? Sai hawaye suka cika mata idanu. Su Ammah daba lura sukai ba Smart ta ɗan dubeta cikin jin nauyin Ammah ya ce, “Madam na barku lafiya, duk abinda kike buƙata karkiyi fillanci Ammah taki ce.”
Kanta ta jin jina masa tana ƙoƙarin maida hawayenta. Da ga haka ya fice ya barsu….
Cikin ƙanƙanin lokaci aka shiryama Lulu breakfast, yayinda gidan ya ɗauki shiru su Asma’u ma sun wuce makaranta. Ammah nata janta da taɗi itako tana bata amsa cike da kunya har Hawwah ta kammala tazo ta zauna. Sai Ammah tace suje ɗaki ko zata fi sakewa ta karya kafin suje ta gaida Abba da matan gidan dan yau dai ba fita zaiyi ba. Jin haka yasa Lulu cewa bari taje ta gaida Abban dan bata jin yunwa. Hakan yasa Ammah jin daɗi, dan haka ta miƙe da kanta domin rakata wajen Abban. Hawwah kuma ta shiga tattare kayan tana maidawa ɗakinsu…
Sosai Abbah yayma sabuwar surukar tasa tarbar mutuntawa kamar yanda yake ma sauran. Yayinda Lulu shima ta kasa ko kallonsa dan tsohon ya mata kwarjini sosai. Shima ta gaidashi da girmamawa ya amsa mata da kulawa da sanya albarka. Sannan ya ɗora da addu’a zama lafiya a gare su Ammah na amsawa da Amin cikin murmushi. Basu jima sosai ba dan sunga Lulun dai kunyarsu ta sata kamar takura suka fito bayan ta ajiye masa leda madaidaiciya mai ɗauke da turarruka masu tsada da ƙamshi, sai agogo. Da sauri Abbah yace, “A’a ɗiyata maza zoki ɗauka. Gaidamun ma da kuka zo kawai ya wadatar mun kumayi farin ciki”. Marairaice fuska Lulu da kanta ke a ƙasa tai da faɗin, “Abbah dan ALLAH karkace haka. Mu albarkanku muke nema, indai bazan sayama Daddy abu dan neman albarka ya dawo min da shi ba kaima haka nake fata daga gareka”. Abba dake murmushi sai ya jinjina kansa da nisawa. Ya ce, “ALLAH yay miki albarka. ALLAH ya tsare gabanki da bayanki….” ya dinga jera mata addu’oi masu ratsa zuciya Ammah na tayashi kafin suka fito.
Anan kam saita kira Hawwah akan tazo ta raka Lulu kowane ɗaki. Hawwah ce tai mata rakkiya, inda suka iske Umma cike fam, amma saboda shawarar da Hajiya Naqiba data kira ta labartama mata zuwan su Lulun yasata dannewa ta tarbeta da fara’ar yaƙe, ita kuma Lulun sai ta kasa sakin jiki da ita dan ita kam dai haka kawai taji Ummah batai mata ba, basu wani jimaba Lulu ta ajiye mata ƙaramar leda ta miƙe, sai hakan kuma ya sake zafar Umma. Ɗakin Mama ma an mata tarba ta mutuntawa, nan ma sai sukafi ɗakin Umma daɗewa, dan duk da Mama taji hassadar kasancewar wannan zukeƙiyar yarinya ƴar masu kuɗi ba wani acikin ƴaƴanta ya samu ba ta danne a ranta ko a fuska bata nuna ba, sai godiyar ledar da Lulun ta ajiye mata ya shiga jerawa. Ɗakin aunty amarya kam tarba suka samu kamar wata ƙawa. Dan tsokanarta ma taitayi suna dariya. Sunfi jimawa anan fiye da ko’ina kafin su koma ɗakin Ammah bayan itama ta ajiye mata ledar, bakuma komai bane aciki sai kayan turaren wuta data ɗiba musu da su cin-cin. Itama Ammah ta kawo mata harda turmin zani biyu su Asma’u kuwa kayan kwalliya ta basu jiya da sukaje. Basu zauna a falo ba suka nufi bedroom ɗin su Hawwah ɗin inda ta maida break fast. Duk da Hawwah zata iya ɗan girmar Lulu da ko shekara biyu ne jikinta ta saki da matar yayan nasu, hakan sai ya saka Lulu sakewa abunta dan wayayyace dama kai babu duhu. Duk da ba son cin abincin take ba sai gashi ta saki jiki sunci tare da Hawwah suna hira cikin mutuntawa, anan ne ma Lulu ta samu damar sake jin matsalar Hawwah ɗin sosai, a ranta kuma ta ɗauki ƙudirin taimaka mata, dan haka ta amshi address ɗin gidan nata a cikin hikima batare da Hawwahn ta fahimta ba. Bayan sunyi sallar azhar falo suka dawo wajen Ammah, cikin hikima taita jan Lulu a jiki ganin bata sakewa idan suna tare, da yake abune daga cikin abinda take ƙishirwar samu sai gashi ta saki jikin nata fiye da yanda sukai zato, dan hirar tasu ne ta karkata akan yanda matsalolin fyaɗe ke ƙara yawaita da yanda wasu ma yaran kan rasa ransu a take ko a cutar da su ta hanyar saka musu cuta, da yanda wasu iyayen kan rasa ransu adalilin hakan kosan ɓoyewa saboda kar duniya taji ƴaƴan su tozarta da su kansu. Lulu ta ce, “Wlhy Ammah nakanji kamar na dinga kashe irin waɗan nan aladun da hannuna, akwai case ɗin wata yarinya da har yanzu yake cimun rai duk da shegen na prison kusan shekara uku kenan, danni duk wanda nasan na samu nasarar alƙali ya turashi prison akan wannan laifin cigaba nake da bibiyasu a prison ɗin dan karma ayi amfani da wata dama a sakesu ina nan baki buɗe. Yarinyar tana nan ta zama mahaukaciya kamar yanda Nanny ɗina ta kasance kafin mutuwarta….”
Wasu irin hawaye suka zubo mata masu azabar zafi saboda tuna mata da abinda ya shuɗe kuma yake sosa mata zuciya da zama sanadin komai da ake kallon zagaye da rayuwarta a yanzu………✍️