Labaran HausaNews

FG ta Bukaci Jami’o’i su Bada Hutun Zabe Daga 22 ga Feb. zuwa 14 ga March

Sponsored Links

NUC

Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta umurci mataimakan shugabannin jami’o’in Najeriya da su rufe jami’o’i a zaben 2023 mai zuwa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da aka aika ranar 3 ga watan Fabrairu mai dauke da sa hannun mataimakin babban sakataren gudanarwa, Dokta Chris J. Maiyaki zuwa ga dukkan mataimakan shuwagabannin jami’o’i.

“Saboda abubuwan da suka gabata da kuma damuwar da ake nunawa kan tsaron ma’aikata, dalibai da dukiyoyin cibiyoyin mu, mai girma Ministan Ilimi Mal. Adamu Adamu bayan yin shawara da hukumomin tsaro ya bayar da umarnin a rufe dukkan Jami’o’i da cibiyoyin Jami’o’i tare da dakatar da harkokin ilimi tsakanin 22 ga Fabrairu zuwa 14 ga Maris, 2023.”

Wasikar ta ce, saboda haka, Mataimakin Shugaban Jami’o’i, da kuma Daraktoci / Shugabannin Jami’o’i, an bukaci su rufe cibiyoyin su daga ranar Laraba 22 ga Fabrairu 2023 zuwa Talata 14 ga Maris 2023.

Wasikar ta kuma sake sabunta tabbacin babban sakataren hukumar ta NUC, Farfesa Rasheed Abubakar yayin da yake mika sakon gaisuwa ga mataimakan shugabanni bisa fahimtarsu da hadin kai.

Leave a Reply

Back to top button