TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 53

Sponsored Links

ZAINAB IDRIS  MAKAWA

[3/23, 10:05 AM] +234 803 800 7509: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

5️⃣3️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Duk wata mace data shiga dakin ta tana fatan ta zauna lafiya
da kowa da zata sama a sabon wurin da zata samu kanta don bata fatan ta samu
matsalan rayuwa a lokacin.

   Nima hakanne ya
faru dani don dai sam ban taba kawo wanan a raina cewa zan samu irin matsalan
nan dana fara fuskanta a yanzu tun ba a kai ko ina ba.

   Na gama girkin rana
ban daddara ba na kara zuba masu wanan karon ma daidaicin kula babba na na
farkon a cikin saiti na zuba masu miya kuma na cika kulan aka kai.

    Saidai ba,a dawo
da kayan ba har zuwa yamma banda niyar sake dora girki don ya fada min da zai
fita sai yamma zai dawo don an kawo masu kaya ana saukewa ranan.

   Don haka baici
wanda na dora din ba sai na aje muci da rana saiko yamma don ya dawo bayan
sallah ishe ina cikin part dina sai yan bakin da nakeyi masu zuwa ganin amarya
da kuma yan gulma kamar dai yadda akeyiwa amarya idan an kaita sabo sabo da
wayanda ta sani da wanda bata sani ba.

    Wanan ya debe min
kewa har lokacin daya dawo din yana shigowa part din mu ya nufo sam cikin gidan
basu san dawowan shi ba lokacin ina zaune kanwarshi ta shigo tana fadin.

   Ance in taho in
dauki abincin muna dare kafin na kaiga mata bayanin dalilin rashin girkin
darena sai naji ya bata amsa daga kofan bedroom din mu yana fadin.

  Ku baku girka bane
kice na bata dokan kada ta kara saka abinci a cikin gida iya namu kawai zata
girka nan ba tsayawa yarinyar da bam san sunnan ta ba har lokacin ta juya sudu
sudu ta tafi bata tsaya min rashin kunya ba.

     Ya juya ya koma
ciki dama dagashi sai tawul a jikin shi yana tsane ruwan kanshi lokacin da dan
wani karamin tawul a hannunshi ya fito bata amsa lokacin.

   Ya gama ya fito
falo ya sameni zaune gashi ba wuta sai fama fitar nake da maficin roba a
hannuna O lord rashin wutan nan ya dameni wallahi nasan baki saba dashi ba so
nake na samu dan kudi zuwa jibi in sayo muña generator a dinga kunnawa koda
rana idan sun dauke wuta.

   Ka barshi ai ba
komai na fada ya kai zaune a gefena har ina jiyo kamshin mandaya shafa da
turaren shi a hancina.

   Yace aiba ke kikace
na saya maki ba ninaga hakan ya kamata zan saya din insha Allah tona gode na
fada ya dan dago yana mamakin saurin godiyana hakan gareshi.

    Ga abincin can fa
don nasan bakaci komai ba ya dan kai kanshi baya saman makarin kujera ya jikina
yana fadin nasan Monday zaki fara fita school.

   Don hakane nake son
naji yadda zamuyi kafin na wuce komai adaidai zan samo maki na dinga biyan shi
yana kaiki tunda an karbe motan ki a hannun ki.

    Gaskiya ba zan
boye maki ba karban motan nan yana daya daga cikin abinda ya bata min rai sosai
don saboda ni aka karbe motan a hannunki kingako hakan bazai min dadi ba.

   Idan na tuna nakan
ji kamar ace ni din wani mai haline a yanzu da zan saya maki motar da duk garin
nan babu mai ita zahra amma muyi addua ko nan gaba Allah yai muna falalan
hakan.

   Na dan zauda daga
zaunen ina fadin kada ka damu da wanan wani hani ga bawa baiwa ga ubangijin shi
ni sam hakan bai dameni ba dama ba fita nake da motar ba iyaka school ne dashi
don haka kuma aka saya min shi dama.

   Kiyi hakkuri zahra
nasan nina ja maki duk wata tsana a wurin Abba duk abinda sukai maki duk saboda
haduwana dakene hakan ya faru.

    Ban dauki hakan da
komai a zuciyana idan na runa da nasihan da ummah tayi min akan abinda ya faru
din don duk saboda a musguna matane akai min hakan ita kuma ta nema min albarka
a dakina fakat.

  Naga yayi shiru
kamar mai tunane kafin ya zabura ya mike kamar an tsikareshi yana fadin
subbahanallahi na manta shaf da batun dabbobin nan nasan kuma ba kula min dasu
wa tan nan zasuyi ba sai aukin abasu suciwa bakin su.

    Nan dai ya fita ya
barni a wurin ya jima a wajwn kafin naji ya shigo yana rufe kofan part din daga
nan ya zauna yaci abinci ya shigo dakin lokacin har na sauya kayan jikina zuwa
na barci duk da zafi ya addabi rayuwana sai faman juyi da nakeyi saman gadon.

   Shiyasa na damu
wallahi don nasan cewa zaki wahala da zafin nan tunda baki sababa ya fada yana
tsaye yana kallona daga inda yake tsaye ni kuma ina kwance.

   Bandaki ya nufa ya
kara gyara jikin shi har brushe yayi a lokacin a nan dai na fahinci yana da
tsabatan shi iya gwargwado shima ba wai idan zai fita bane kawai yake tsab.

   Yana gama shirin
shi ya nufo gado ni lokaci har nayi barci don dan aikin da yanzun nakeyi ban
saba yi a gida yakesa ina saurin gajiya yanzu sosai.

    A cikin dan barcin
daya daukeni din naji harshen shi cikin kunnuwa abind yasani falkawa a zabure
ke nan da sauri hankalina a tashe don a tsorace nake kwana a gidan nan balle
akuyan nan nasu idan tayi kuka nakan jishi har cikin raina.

   Sannu a hankali
yake bin ko ina najiki da sallon irin na maza tun ban kula da hakan ba na fara
dan yunkurin ina nisawa har yakai ga gangara ya cinwa manufarshi a kaina aka
zama daya a ranan bai barni ba saida ya mayar dani cikakar mace.

   Yadai sha raki don
shima yasan za a rina don ko kallo daya zakai min kasan ni din agidan hutu na
fito don nidai bawai wani jikine dani ba.

  Farace sol din nan
son farin yasani tsakiya ta uwa ta uba haka kuma ni din ba gajera bace ban da
kuma mugun tsawo saidai ina da tsayi madaidaici da akeson mace ta kasance.

   Banda jiki mai yawa
yanayi a daidai yake a fuskama na debo gidan mu sosai amma kuma na biyo ummah a
wurin hanci da dan tsayin fuska shi ya dan bambamtani da sauran yan uwana don
ina da zubin ummah wanda kuma shine ya kara haddasa min kiyayya  gun mama.

  Don yawan cewa da
Abba keyi ke kan kin kwaso suffan uwarki ba ki tsaya a gida ba kawai ta kuma
lura da yana ji dani sosai saidai a cewan ta son da yakewa ummah ne yake min ya
fake ga sunan mahaifiyar shi.

   Ranan dai Ahmed bai
barni ba son sai daya cire min kunya a tsaknin mu don tare muka shiga bayi
dashi mukai wanka muka fito ya gyara muna shimfida muka kwanta yana rungume
dani a jikin shi.

    Sai asuba muka
tashi na dauka daya fito zai fita zuwa sallah kamar yadda ya saba saidana fito
bayi na sameshi a zaune yake fadin ke nake jira muyi sallah don yau a gida
zanyi .

   Da mamaki na
kalleshi cikin dauriya yace yes ba inda zan tafi yau ina gidan nan don zanyi
jiyar matatace ayau tunda nayi laifi.

    Dan hararan shi nayi
na turo baki na nufi wardrobe na dauko hijjab dina kafin na juyo ya tayar da
nafila nima shina shirya na fara gabatarwa

   Muna zaune muna
addua mukaji anyi kiran sallah muka tayar da sallah a baiyanai yake addua yana
muna fatan Allah ya zaunan damu lafiya.

   Allah ya bashi
abinda zai kula da rayuwan mu Allah ya bamu zuria masu albarka Allah yasa mu
gama da iyayyenmu da duniya lafiya.

    Ya shafa nima dake
zaune bayan shi na shafa muka mike a daidai lokacin mukaji dukan kofa anzo
tayar damu sallah asuba din.

    Ji nayi kawai ya
kamani yana fadin koma ki kwanta kada kiyi maganan hakan jna jinsu a inda nake
kwance din maishi ta dan jima tana dukan kofa lafin na daina jin hakan.

    Barci sosai mukayi
zazzafi da taunan jikine ya tayar dani daga nauyayyan barcin dana samu a
lokacin hakan ya jawo min kaduwa da har jikina ya mannu da nasa .

   Can cikin barci
yake jin yadda nake kaduwa ya falka salati ya fara da dan jijigani yana kiran
sunana na asali da zahra meke faruwa meya sameki subbahanallahi.

   Ina ke maki ciwone
ki tashi muje asibiti na samu na bude idona da kyar na sauke a kashi ya kwance
yai min rumfa da kirjinshi yake tambayana cikin dan rudewa.

   Ka bani bag dina
akwai maganina aciki na fada a galabaice ya mike da sauri ya dauko jakkar yana
miko min na tashi da kyar na fara lalube na dauko maganin shi kuma ya mike ya
dauko ruwan ya bare mun maganin na hade .

  Maganin kawai kai
kasan masu tsadane ba irin maganin nan na banza bane da akesha anyhow na hade
na koma na kwanta naci gaba da kaduwana.

   Dama ga raki sai na
kara narke a wurin sai zuwa wani lokaci na fara samun relief a rayuwana barci
ya daukeni ganin nayi barcine yasashi mikewa daga gadon ya sauka.

  Bandaki ya dan shiga
ya fito ya fice zuwa wurin iyayyenshi donsu gaisa ya samesu a waje zaune da
alama rayukan su a bace yake ko kuma suna wani magana mai muhinmanci a lokaci.

   Sallaman da yayine
Dije ta karba mashi da sakin fuska ya nufi wajen iyayyen nasa dake zaune har
lokacin a cikin yanayin daya samesu din.

    Har kasa ya duka
ya gaidasu suka amsa mai ya dago zai mike mahaifiyar shi Rashida take fadin ka
manta yau uwarka zata koma Anka na ka shige daki kaki fitowa ?

   Bakin fitowa nayi
ba inna ina sashen mu matana bata da lafiya da sauri suka kara kalloshi tare da
tambayan halan missameta ?

   Zazzabina ta kwana
dashi zazzabi shin kwana uku da aure ace amarya ta fara zazzabi ko dai sai kuma
tayi shiru.

   Har ya daga ya
kallosu yana fadin ciwon daga darene zuwa safiyan nan zazzabin ya kamata kuma
duk ni na jawo matashiya.

   Saboda ya fitar da
zargin da yaga suna son dora min ne don ya fahinci me suke nufi da hakan da
suka fada suna kokarin zarga min abinda ba shiba yasa ya rufe ido shima ya basu
amsa a funkaice .

    Yau Allah ya gwada
min da mara kunya Amadi wai kanka daya kuwa duk kabi ka sauya lokaci guda haka
kan mace ?.

   Shin talauci hakana
don dai ka dauko wagga diyan kaka kokarin canza dabi,unka da muka sanka dashi
sai kokarin nuna ta fimu gareka kai.

  Dije ya nufa yana
gaida ita bata samu amsawa ba sai tambayanshi takeyi mi samu yar mutane Amadi ?

   A, a Dije rashin
lafiyan alherina kesan yarinyata karama dole taga canji a yanzu ai magani nika
son hita in tambayo ko mi aka basuwa ga macen da ta fara sanin haka ?

    Kai yau Allah ya
gwada min da sagartace ta fada tana mikewa tsaye don fahintar abinda yake nufi
ya faru dani din lokacin.

   Tare suka shiga
dakin da ita tana gaba yana binta baya a hankali zuwa ciki ina kwance takure
yadda ya barni din suka shigo .

   Nan dai ta fada mai
yan dabarbaron da zai min kafin in tashi ya sayo kaji dakwale an gyara min da
kayan yaji sai kamshi ke tashi gashi kasala da samun saukan zazzabin ya hanani
tashi ina ta sharar bacina sosai.

   Shiko yana zaune
dakin yaki fita duk a dakin yai sallah sai falkawa nayi wajajen karfe uku na
samu hanne daya kira tazo harta gyara min dakin nawa. 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

Leave a Reply

Back to top button