TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 9

Sponsored Links

9️⃣

 

 

AL JABBAR,,,,,,,,,,

 

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Zan iya cewa wanan lokacin na gane sauyin da gidan mu ke
ciki a yadda ni na daukeshi ashe ba haka abin yake ba a dunkule a baiyanene
nake ganin komai normal a gidan namu.

Wata kila kuma
watan hankalinane ya kama a lokacin har yakai ga na fahinci hakan a yanzu
sabanin da da dauka daya nakewa iyayyen namu a zuciyana.

Yanzu na gane kowa
danshi ya sani kuma yake kokarin ganin ya zama wani abu a duniya ya kareshi
daga duk wani sherin kada ya cin mai.

Saidai wani abu da
bai sauya ba shine yaran mama maza manya da suke daukan ummah da matsayi mai
mutunci a idanun su basu fasa hakan ba don suna bugowa ummah waya kamar yadda
suka saba a baya.

Idan sunzo garin
kuma zasu shigo su zauna a nan suyi hira duk da mama zatayi ta aikowa suzo tana
neman su a wurin ta bai hana insun tafi su kara bullowa kafin dare kuma.

Hakama alheri bai
katsewa a tsakanin su da ummah din saidai nasan a boye sukeyin shi don yanzu
sun fara aiki suna kuma kula da harkokin Abba haka yasa kudi ke shigo masu ta
ko ina a yanzu.

Saidai a garemu
yanzu babu daman kwatanta hakan ga mama don bamuga fuskan yin hakan ba gareta a
yanzu babu wani sakin fuska ko kara na jan mu jikinta kamar yadda ummah kewa
nata diyan.

Sai gaisuwa kawai
koshi saida kyat take karba muna a tsatsaye dole mukaja jikin mu da ita ya  kannena idan sun ganta jikinsu har rawa
yakeyi.

Wanan satin ma
kamar kullun sunzo gida don suna garin na fito da shirina zan tafi school a
waje na samu ya musa wanda yaci sunan kakan mu shine da nabiyu ga mama.

Yana tsaye a
farfajiyan gidan mu da kayan motsa jikin a jikin shi wurin shi na nufa ina
gaidashi ya juyo fuska a sake yana fadin .

Sai ina haka yan matan mama da safen nan haka
school na bashi amsa kafin na karaso inda yake tsaye murmushi nayi tare da
fadin ya musa ai yanzun mama ta daina sona kamar da.

Ido ya kwalo waje
yana fadin garin yaya haka ya faru keda maman ki dan shagwabewa nayi ina fadin
nima ban sani ba ya musa na daiga ta daina sona ta daina kulani a yanzu na fada
kamar zanyi kuka.

Kai haba dai baki
dai jida kyauba zarah har yaushe keda mamanki zata daina sonki kuma nace Allah
ko ya musa nima bansan abinda nayi mata ba yanzu har haka ya faru.

Wa zai kaiki
school din ya tambaya ta hanyar kawar da zancen da mukeyi nace nike zuwa da
kaina yaya da wani mota kuma yana raba ido ga motocin dake parke a haraban
gidan.

Nace cikin dan
sakin fuska ga motata can ita nake ja yanzu ina nuna mai motan dayasani na
Aisha da tayi accident da ita kamar ma ba zata gyaru ba lokacin.

What ya fada yana
kwalo ido waje tare da fadin wanan tsohowar motar dai yanzu har an saura
shiganta gidan nan ashe ?

Kai haba yaya
garau take fa da ita nake fita kuwani duk inda zan tafi na bashi amsa ido ya
kura min a zahiri zaki iya cewa ni yake kallo a lokacin.

Kafin na katse mai
tunane da fadin zan tafi yaya kada in makara amma dai aiba yau zaka tafi ba ko
kada in dawo in samu ka wuce.

Yau kuwa yan mata don Abba na jirana akwai
inda zai turani kilama yau din nan nabar kasan nan insha Allahu.

Allah sarki ashe
da banganka yanzu ba saidai na dawo na samu ka wuce ke nan yace gaskiya kan zan
bar maki sako hannun ummah idan kin dawo sai ki karba .

Nagode yaya Allah ya
saka da Alherin sa kai tun bakiga sako
ba har kike min godiya haka aiko baka bayarba kayi niya kuma na gode
Allah tsare hanya yace amin .

Na juya zuwa wurin
motar ya bini d kallo har lokacin dana bude na shiga na fice daga gidan ina
masa horn ya daga min hannu mukai sallama dashi.

Ajiyan zuciya ya
sauke kafin ya tura hannu cikin aljihunshi ya ciro wayanshi lamban ya jafar ya
kira suna gaisa ya fara fadin wallahi akwai matsala fa idan bamu fadawa mama
gaskiya ba ka  wanan abinda takeyi a
gida  nan.

Meya faru ya jafar
din ya tambayeshi yace yaya za,ace kowa zai shiga jami,a gidan nan ana sai
mashi mota amma yanzu yazo kan zarah ace sai tsohuwar motar Aisha za a bawa
zarah motan da har accident tayi da ita amma ita zarah ke shiga yanzu.

Au kai sai yanzun
kasan da wanan zancen ashe nina dade da sanin hakan da akayi na nuna bacin
raina ga hakan da akayi nayi magana mama tace ina ruwana koni aka ba.

Nayi shiru badon
raina yaso hakan ba at,list ya kama tunda wanan shine karo na farko da za aiwa
ummah haka ya kamata ace an kyautata mata itama tunda anyi muna tana gidan bata
nuna hassadanta ba ita.

I don’t no why
mama take haka na rasa dalilin sauyawan mama a wanan lokacin haka gaba daya ita
da yaran nan yanzu sun tsani mutanen nan yanzu a gidan mu.

Kaidai bari kawai
wanan zuwan da nayi last bakaji irin fadan da mama tayi min bane kan naje wurin
ummah na zauna saida na tattara na bar garin cikin bacin rai.

Gaskiya nikan ba
za  yarda da hakan ba zan mata nasiha
kada son kai yasa mama ta halaka kanta Allah ya tambayeta hakan gobe kiyama.

Wanan matar ta
barsu ga Allah kan duk abinda suke mata kuma hakan bai isa ba sai an hanasu
harda walwala a cikin gida haba don Allah abin yayi yawa mana.

Ya kashe wayan
tare da daga kai ya kalli kayon gidan namu yana sauke ajiyan zuciya lokaci guda
ya fara takawa zuwa cikin gidan kai tsaye.

Yanzu Amadi haka
zaka zauna ba wani sana,an da kakeyi da zai taimakaqa rayuwanmu mu samu muci a
ciki har mu tufatar da kanmu ga hakan.

Da ka dauki wanan
uwar garken ka kaita kasuwa ka sayar sai ka nemi sa,an da dan kudi zai dinga
shigo ma yau wajen kwana biyar fa munacin ganye a gidan nan.

Dije nima hakan
yana damuna ina nan ina ta neman aikin da zanyi inda zamu rika samun abinci
yana shigo muna hakan yana damuna sosai a raina.

Nasani Amadi nasan
da hakan kadai ki shawaranane daka jaraba hakan an gani zaifi ya nisa yana
fadin Dije banaki bane akuyan nan ita kenan muna a rayuwa ina gudun akaita
kasuwa azo a tayata wullakance.

Kinga kuma hakan ba
dadi ai gara dai a bari har Allah ya kaimu sallah saina fitar da ita a hurhura
da wata karama a sake saura  kudin saina
fara juyawa.

Ikon Allah yanzu
dan nan sallah da sai nan da wata shidda ga mai yawancin rai ka dauka ka kai
kawai Allah na nan tare damu in sha Allah kafin sallahn yazo aika tara na
tarawa har ka mayar da kudinta kuma.

Zan gwada hakan
Dije ya yunkura yana fadi ya nufi hanyar dakin shi yaja ya tsaya ya kafawa uwar
garke dake kwance tana gyangyadi a inda turken su yake.

Ya dan jima tsaye
kamar yana nazarin akuyan kafin ya shige dakin shi bai jima a ciki ba ya fito
ya sauya kayan jikin nasa lokacin Dije ya ambata daga kofan dakinta daya tsaya
din.

Ta amsa mai daga
ciki yake fadin ni zan dan fita naga ko zan samu mai sayen akuyan cikin unguwa
tunda sun santa ai daga haka bai jira ta fito ba yasa kai ya fice daga gidan
koda ta fito yariga ya tafi.

Yana fita ya tsaya
a kofan gidan yana bin gidajen dake wurin da kallo kafin ya nufi gidan
makwabcin su mai irin wanan sana,an na dabbobi ya sallama mashi.

Babban danshine
yafito ya sanar maida mahaifinsu bayana nan ai ya tafi cin kasuwan kauye hakan
yasa ya juya zuwa gidan wani can kasan layinsu.

Shima haka yana
kasuwa bai dawoba ya dawo kofan gidan malam Tanimu da ba kowa sai tarin
gumaguman icce dake zube a kofa  gidan da
wanda aka faskara ya zauna shi kadai kamar yana jiran wani a wurin sai bin masu
wucewa da kallo yakeyi.

Yayi nisa a tunane
yaji ana mashi sallama ya amsa yana dago kai ga maishi wani dattijone a tsaye
ya rataya buhu a kafadan shi da ganin shi kamar mata fiyi bayan sun gaisane
yake tambayanshi malam tanimu yace.

Cikin ladabi nima
ban san inda ya nufa ba baba zamana ke nan wurin nan yanzun  nima ban wani dade ba sai mutumin yace kai
gashi ko ina son ganin shi wallahi wai dama dabba nashigo saye yai min jagora.

Yana fadi yana
kaiwa zaune Amadi yace gashi ko da alama kamar yaje daji daukan icce ne don in
yana gari bai faye zuwa wani wuri ba dai.

Shiru dattijon
tayi kamar yana nazari kafin Amadi ya mike tsaye yana fadin bari na shiga ciki
a amsa maka ruwa da dan farafarau ka kora don alama ya nuna yanzu ka shigo.

Yana fadin hakan ya
mike bai jira jin tsohon ba ya shige cikin gidan malam Tanimu din bai dade ba
ya fito da ruwan randa mai sanyi an surka da kunu anyi farau farau dashi a kofi
mai marfi.

Dattijon ya karba
yana saka mashi albarka tare da mai fatan alheri yana fadin nagode nagode yadda
ka tareni kaga tarbon arziki kaima a rayuwan ka har duniya ta nade.

Shima godiya yayi
yana fadin amin baba nagode nagode kwarai baba ya fada yana kaiwa kasa muryan
dattijun ne ke fadin.

Yaro kasan inda
zan samu yar akuya ita nazo nema da yamman nan na dauka zan samu malam tanimu
mu hada kafa muje tare.

Kallon mamaki yaiwa
dattijo saidai fuskan dattijon na kallon wani wuri a lokacin   yayi karfin halin fadi a cikin mamaki aiko
baba akwai akuya da akai niyar sayarwa dama barin shiga inwa maishi magana sai
a fito dashi ka gani in zai maka.

Ya mike zuwa gidan
su bai jima ba sai gashi jaye da uwar garke a hannun shi yana ja zuwa wurin
dattijon dake zaune saman kututuren da malam tanimu ya heke ya hada ice da ice
a kofan gidan yana zama a sama.

Yazo gab dashi ya
mike tsaye yana fadin kai wanan ai zatayi kudi da yawa da daidai yar madaidaiciya
ce sai insaya ai

Zaka iya saya idan
zatayima baba lalura yasa maishi fitar da ita aiko lalura yakai lalura wanda
zaisa a fitar da guzuma haka iri mai kyau da ita yanzu zata kai nawa wanan ?

Tau baba maishi
tace jakka arba,in amma sai ka taya a, a yaro ba zan taya ba idan har ta bari
ga kudin Allah yasa ta amfana dasu har abada.

Kallon tsohon yayi
cikin mamaki jin ko gardama baiyi ba daga sa suna har ya yarda da hakan shi ya
banye wani kulli ya fito da kudin ya bashi ya karba cikin mamaki.

Dubu biyar ya
kirga ya mayarwa tsohon dashi sai lokacin suka hada ido dashi gabanshine ya
fadi ras lokaci guda duk da tsohon yayi saurin kawar da kanshi gefe daya.

Kai ya girgiza mashi
tare da fadin jeka dasu yaro Allah yasa masu albarka abinda ka dafa yazama
alheri a rayuwanka ya sake amsawa da amin baba yaja akuya ya tafi shi kuma ya
koma gida cike da mamaki da al,ajabin wanan bawan Allah.

Mama ya akayi Zahar
take amfani da wanan tsohon motan bayan kowa saya mai sabuwa akeyi idan zai
shiga jami,a amma ita sai naga tsohuwar mota take amfani dashi na Aisha ?

Uwartace tace
kazo ka tambayeni ko wa ?

Haba mama ya ummah
zatayi min wanan maganan kuma nidai na ganta yanzu ta shiga wanan mota yasa zo
na tambayeki meyasa haka mama ?

Haka naga daman yi
don haka ka barta dashi amma mama baki ganin hakan ba da, , , , , , hannu ta
daga mai tare da fadin kaga na fada ma ra,ayina don haka kada ka dameni.

Koda aka bata
tsohuwar tafi katfin shiganshine ita din uwarta yar waye da yarta ba zata shiga
motan da Aisha ta ajeba ?

Amma ainan gidan
uban zarah ne bana wani ba don haka zarah daidai take da kowan mu a gidan nan
ke nan irin wanan wallahi mama tauye hakkine fa hakan nan ?

Baba ni zaka tsare
kanayiwa fada kome koni zaka nunawa hanyar gaskiya  a yau din na bata wanan din kaje kayi yadda
zakayi ina jiran ka.

Mikewa yayi tsaye ya
saka hannayen shi cikin aljihunshi yana fadin alright ya fice daga part  kai tsaye dakin shi ya nufa ya shiga wanka
zuciyar shi na masa tukuki hakan da sukayi da mama din.

Yana fito part din
ummah ya nufa falo ya sameta ita kadai bayan sun gaisa tace har ka karyane ko
baba naga kamar fita zakayi ?

Eh wallahi ummah
yau zan koma ka karyane ko haka zaka tafi tana kallon shi cikin tsure shi da
idanunta a zuboma kunun gyada yace eh bani nasha kada nabi hanya ban karya ba.

Bayan ta debo
mashi ta kawo mai inda yake zaune a lokacin yasa hannu cikin aljihu yana fadin
ummah wanan sakon Zarah ne idanta dawo abata na fada mata zan barmata a wurin
ki.

Kunyi sallama ke
nan da ita ummah ta tambayeshi yace eh a gabana ta fita dazun amma ummah kina
kallo akaba zarah wanan motar tana shiga ?

Murmushi ummah ta
sauke a fuskanta tana fadin me motar tayi ai da lafiyanta wace Aisha ta ajene
aka bata yafi ta dinga zuwa ana haya ai ko ?

Fuska ya bata ya
dauki kunun yana kurbawa a hankali bai dade ba ya mike zuwa part din mama bayan
tayi ma ummah sallama bai samu mama a falo ba sunce ta shiga wanka.

Ya bar sako idan ta
fito a fada mata cewa ta wuce zuwa Abuja daga can zai koma lagos jin haka yasa
Aisha mikewa da sauri tana kiran uwar duk da tana cikin bayi haka bai hana ta
fada mata gashi zai wuce ba.

Saidai kafin su
fito harya fita ya kuma kashe wayan shi da bai kara budewa ba sai bayan ya
sauka Abuja ya nufi gidan Abba ya bude wayan nasa.

A lokacin ne sakon
ya jafar ya shigo ya bude yana fada mai mama ta kira tana fada sosai don me bai
jirata ba ya tafi ido ya runtse ya kashe wayan nasa ya tura aljihunshi.

Ya samu Abban mu
baya jin dadi yana kwance ranan bai fita ba nan ya soma fada Abba ga irinta nan
ummah na nan zaune ka dauketa ka mayar gusau gasu can basa komai suna zaune
kawai kai kana nan kana wahala kai kadai sai yan aiki.

Murmushi Abba yayi
yana gyara zama yake fadin to ya na iya maimuna tace sai su koma gida dukkan su
ita ta baro lagos ita wana  dake nan dole
itama ta dawo gida su zauna tare dasu.

To amma Abba ya
akayi Zarah take hawa wanan motar tana fita a cikin shi Abba wanan baiyi ba
wallahi zan hada duk abindake gareni in sayawa zarah mota   amma ba zata kara amfani da wanan motar ba
daga wanan satin.

Dakata malam ai
abin baikai can ba wanan zancen da kakeyi ban taba sanin motan da Zarah take
jaba a yanzu ni dai na san muyi magana da maman ku cewa za a samawa zarah mota
in kawo kudi.

Kuma na bata saidai
bazan iya tuna komai yanzu ba kan hakan amma dai nasan an karbi kudin a hannuna
kuma na bata  yanzu kaje kafin tashin ku
sai ka duba mata mota daidai da ita.

Kabar kudinka
wanan nauyinane yin haka amma gaskiya Abba ku kula don abubuwa suna son suna
son rikicewa fa yanzu gidan nan don a gaskiya ummah tana hakkuri da kawar da
kai ga komai amma ya kamata a duba mata hakan gaskiya.

Baba nima nasan
da hakan a yanzu na fara fahintar wasu abubuwan da nakeyi bai kamata ba amma ba
yadda na iya don ban iya rikicin mahaifiyar kune.

Abba kaika ajesu
fa bai kamata ace ka fadi haka ba idan baka fitowa mama ta baya ba gaba dayan
ku zaku halaka kan nu baku sani ba

Sun jima suna
magana na fahinta da dan nasa kafin ya fita zuwa ya duba motan kamar yadda Abba
ya umurce shi dayi ya duba kuma ya samu mai kyau daidai dani anyi service din
ta anyi komai ya dawo da ita gida Abba ya gani.

Duk da saurin da
yakeyi don ya fita zuwa school tunda sauran duhun asuba haka bai hanashi gane
cewa uwar garke tana kwance cikin yayanta ba lokacin.

Salatin daya
sakane ya fito da Dije daga dakin yana fadin uwar garke kece kika dawo ko idona
ke gizone wai yana kara nufar wurin da dabbobin suke kwamce fuskanshi dauke da
mamakin hakan.

Dije cikin dan
dingishawa ta fito tana dadin sai naji kana zancen uwar gareke ko saboda sabo
da itace yasa kake ganin tana ma gizo a idanun ka kuma ?

Itama fitgita tayi
tare da sake salati tana fadin Allah sarki uwar garke dawowa kikayi ta nufi
waje tana cire mata igiya.

Dije daga gidan
wanan mutumin tagudo fa ra dawo nan to kuma aishi yace min daga kauye mai nisa
yake dakatar da abinda takeyi rayi ta tsaya tana kallon shi cikin mamaki.

Kana nufi  ba garin nan yake ba maishi yace haka ya fada
min sai da sauki don abokin malam tanimu ne ai kuma yaga gidan dana fito da ita
ai.

Zan fadawa malam
tanimu din tana nan ta dawo sai suzo su kama abinsu su tafi dashi Allah satki
sabone sabo yasa tayi hakan ai Dije ta fada.

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[12/30/2022, 8:23 AM] +234 701 497 9567: 🌱TUMFAFIYA
UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

🔟

AL 

Leave a Reply

Back to top button