TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 28

Sponsored Links

 

 

 

   Da alama yau akwai abinda yasaka nishadi
Amadi don na dade banganka cikin wanan yanayin haka irin na yau ?

   Kuma dai ya fada
yana zama daga kofan dakin Dijen tace barin dauko ma abincin kaci saidai yayi
sanyi yanzu don tunda sauran rana na girkashi na zata zaka dawo da wurine ai na
dafa a cikin lokaci.

   Bani hakana inci ya
fada yana kaiwa zaune a hajiye ra shiga daki can ta fito dauke da kwanon tuwo
dana miya dagware da juna ta aje gaban shi kafin ta nufi wurin randan ruwan su
ta dabo mashi ruwan sha.

  Hannu ya wanke kafin
ya bude kwanon da yar hasken wayan shi yake amfani a cikin duhun ya gyara jawo
kwanon kusa dashi yana bissimillah ta kai hannu ya yanki loman tuwon yakai a
bakinshi.

  Tuwon farar shinkafa
miyar shuwaka data daure da kuli kuli sai dan manshanu da tayi amfani dashi ya
ba miyan ma,ana don babu wani wadataccen kayan hadi tankwana busashe sai albasa
da dan manja ta hada miyan dashi sai kayan yaji da daddawa da bussashen kifi.

    Loma kamar uku
yayi Dije din tace dashi yau na nemi uwar garke a gidan nan na rasa tun bayan
fitan ka nake yawon neman ta ban gata na kewaye unguwan nan kaf babu labarinta
.

  Haka har kudi naba
yaron nan dan gidan malam sule duk basu ganta ba hannu ya tsame daga cikin
abincin yana kallonta cikin mamaki don jin abinda ta fada din.

  Yayin da gaban shi
ke wani irin faduwa na tashin hankali dakyat ya iya budan bakin shi yace garin
yaya Dije har ta banye ta fita ba a sani ba ?

   Shine abinda ya
daure min kai nima ai don naga dabbobin nan basu fita ko ina a gida suke kiwon
su yadda na saba masu nakewa bandaki ina fadin in fito in zuba masu sauran
kowan wanken nan daka sayo masu.

  Fitowa na naga wayau
sai sauran bisoshin ke tsaye tsirma tsirma kamar suna cikin tsoro a lokacin
hankan yasa na gane akwai wani abinda ke faru saina duba bata cikin yan uwa ga
igiyar ta na dauri a yadda yake amma banda ita.

    Uwar gareke ta
bata kuma  ba a ganta ba to ina ta shiga
ko kuma waya shigo gidan nan ya banye ta daga dauren da take din ya fada yana
rufe kwanon abincin lokaci guda tare da mikewa tsaye.

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[1/28, 6:13 AM] +234 803 800 7509: .🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2️⃣8️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Iya duba duniya Amadi yayiwa uwargarke a cikin daren nan don
dai ya ganta amma ko mai kalan uwargarke bai gani ba haka ya gaji ya dawo gida
karfe daya da wani abu ya kwanta.

    Da asuba ma hakane
ya bazama cikin garin don tun fitowansu daga sallah asuba yake yawon nemanta
sai karfe daya da rabi na rana kuma ya shigo gida a wahalce daga wurin neman
akuyan.

    Iya tashin hankali
sun shigeshi kan batar uwargarke don na farko ga sabon da sukayi da ita sai na
biyu zaman amana da akuyan keyi a wajen su yanzu gashi ta bata daga hannunsu.

   Duk da dai ba
alaman cewa mai ita din daya saye daga hannunsu zai biyo sawunta amma in son
samune ai ya sameta awurinsu tunda sun masa kiwo na tsawon shekara da wani abu.

    Tun suna mamakin
hakan har suka gaji suka fara sabawa da batan nata a gidan don kowan su saida
ya danyi rama kan hakan daga bayane suka fara warwarewa suna zama daidai.

    Mun samu munyi
jerabawa a dadafe don zafin da kai ya dauka na karatu don haka yanzu zamu shiga
hutu munyi sallama da hannatu cewa zata hutu garin sokoto wurin mahaifiyar ta
da yanzu take aure a can.

    Don ita hannatu
tun rabuwan mahaifin nata da uwarta a lokacin ya karbe diyanshi dama su biyu ta
haifa a gidan ita da yayan ta wanda take yawan kira da ya  surajo.

   Wanda shima yake
karatun sa a ABU zaria lokacin don akwai lokacin da nina bata kudin makaranta
ta aika mashi don a gaskiya mahaifin mu da yanan basu barin mu zauna hannu babu
kudi a wurin mu don tsaro.

  Wanda sai daga baya
na fahinci cewa suna muna hakane don kada mu hanga a wasu ko mu shiga sahun yan
matan dake rokon samari.

   Wanda hakan bai
hana komai ba sai dai ya tare wani wajen gaskiya don a bangarena dai ba yabon
kai ba zan iya cewa alhamdullahi.

  Don ina samun kudin
ina wa nakasa dani da muke tare laluransu dashi daidai karfina hakama ban karba
daga ummah ba don ko yaushe abinda aka girka min a gida shi nake ci haka kayan
da Abba yai min dasu nake amfani a jikina.

    Wanda hakan yasa
halin mu yasha bambam da yan uwana dasu kulun sai irin kayan karya din nan suke
son sakawa mai matse jiki da nuna hali da son asani ga duk inda suka shiga.

   A nan ma gida ya
suke balle ance zasu fita zuwa cikin gari don ko mutocin su abin kallone gasu
da samari manyan mutane ni saima in rasa a ina suke haduwa dasu haka ?

    Yanzu hutune dole
muna gida muna hutu sam na manta da zancen cewa zan tafi abuja gun hjy karima
ashe ita zancen yana ranta har lokacin.

    Ina zaune a falo
tare dasu ummah naji ummah na tambayana da cewa ashe zaki tafi Abujane hutu
wurin hjy karima ?

    Ni ummah na fada
kafin ta aje ayyah zancen ke mana ta bani amsa tace kunyi maganan hakan da ita
kafin ta tafi ?

   Ni tambayana tayi a
lokacin na fada mata nan da wata daya to zaki tafi Alh yace zai aiko a daukeki
zuwa Abuja ranan jumma,a kinga ba yadda zakiyi ga hakan yanzu.

  Idan kinje dai ki
iya kanki a zamaki dasu don ba halinta muka sani ba ki iya mutuncin kanki kiyi
hutun ki dawo lafiya duk da nasan cewa kedin ba mai rigima bace amma dai ki
kula.

   Naji ance tana
zaune tare da yan uwanta ne a gidan yanzu don hjy jesmi ta fada min tana ganin
fuskoki a gidan suna kuma gidan suke da zama suma.

   A nan kuma nasa
cewa zansha zagi a gidan nan dama wurin wasu to amma ya zanyi tunda shi Alh ne
da kanshi yace hakan dole in barki kije can din na dan lokaci don haka ki kula.

   Raina ya baci sosai
da jin hakan kamar yadda ummah tace ba yadda muka iya kan hakan dole mubi
umurnin Abba din kamar yadda yace din.

   Tunda har hjy
karima ta nuna son hakan ya kasance wanda tayi hakan ne don kawai wani manufa
nata da ban sani ba amma nafi danganta haka da son ta bakanta wa hjy maimuna
tayin hakan dake.

  Don ko yayane sai
hakan ya tabi zuciyan hjy maimuna din itama ta sani don hakane tayi hakan nan
don cinwa manufanta ga hakan da zatayi amma dai mu zuba mata ido muga iya
gudunta a nan din.

    Na dade a zaune
duk bayanin da ummah takeyi a lokacin ban fahince ta ba ina dai zaune ina kulla
dubaran da zanyi don kar naje wanan tafiyan.

    Naso in nunawa Alh
cewa ba zaki ba don kada karatun ki na islamiya ya tsaya tunda wanan lokaci
kike samun yin karin karatun ki ina fada yake fadin so nake yace da ita ba zaki
zoba kome ?

   Shike nan umma zan
tafi din Allah ya tsareni ya karemu daga duk wani abinki daga wanan tafiyan da
zanyi din zuwa Abujan tace amin .

   Sai gashi na fara
shirin tafiya har naga zan wuce ban shedawa Ahmed ba na dai fadawa hannatu da
mukai wayan zancen tafiyan nawa.

  Ta ban mahaifiyar ta
mun gaisa take min godiyan taimakon da nakewa yarta din don ta fada mata komai
a karshe take fadin cewa idan zata dawo zata ba yarta sako ta kawowa
mahaifiyata nima ina kusa da ummah a lokacin na bata waya suka gaisa ta kara
jaddada mata zancen sakon.

   Ahmed din na kira a
wayana muka gaisa ya fara min kame kamen cewa wallahi a dadafe ya karasa exam
dinshi don uwargarke data bata suna yawon nemanta a cikin gari har yanzu.

   Uwargarke mutum ce yace no akuyar Dije da na
taba fada maki cewa mun sayar kuma ta dawo muna gida wanan dai akuyar taki da
kika sani.

    Nace ai gara data
tafi yanzu kaga zan dinga zuwa gidan naku wurin kaka dake tambayana a kai kai
ke nan dama dontane ban zuwa wurinta.

   Dama n akirakane in
fadama cewa gobe zan tafi Abuja insha Allahu a can zan karasa hutuna cikin
mamaki yace dani Abuja dai zahra nace eh ai kasan a can Abban mu yafi zama
yanzu.

    Anya ba Abba ya
shirya zuwan ki bane don kada mu hadu dake ko yasan muna tare har yanzu dakene
?

  Ban tsamani bayan
hannatu akwai wanda yasan da zancen nan yace to shike nan zahra Allah ya tsare
min ke nayi murmushi na amsa da amin.

  Abin mamaki mungama
waya na kwanta sai gashi nayi mafalki da wanan bakar akuyan mai bani tsoro ta
gidan su Amadi.

    Wai ina kwance a
wani gida mai kyau sai naji motsi a waje nafito don ganin wake motsi wanan
akuyan na gani tana kiwo a wani waje mai yawa dausayi mai kyau dan nau,in wurin
zakace ba a cikin wanan nahiyar tamu take ba don sanyi da kamshin furannin dake
tashi ga iska mai dadi yana kadawa ko ina na wurin.

   Kallon akuyan nake
cikin mamaki kafin ta dago kai daga cin ciwan wurin da takeyi tana kallona
nunata nayi da yatsa alaman bake bace ake nema ashe kina nan kina barna.

   Murya naji a bayana
ana fadin kingata nan lafiyanta kalau don kawai mu cirewa Amadi damuwa akanta
muka kawota nan ta huta amma ya kwantar da hankalinshi ai zata dawo gareshi nan
bada jimawa ba.

   Ki rike alkawari
tsakanin ku shidin alherine gareki kamar yadda kema zaki zamo masa alheri a
cikin rayuwanshi amma sai kun daure ga baki dayan ku.

    Na juya banga kowa
ba a bayana saidai muryan dan uwana naji a lokacin watau ya musa don muryan shi
sak naji a cikin mafalkin na juya zan koma inda na fito a daidai lokacin na
falka daga barcin.

    Wani sanyine ke
dukan jikina lokacin wanda nake jinshi har kasan raina hakan yasa naja bargon
rufa na gyara kwanciyana da kyau saidai barcin kuma yaki daukana a lokacin.

    Har akai sallah
ban koma barci ba idona biyu sai bayan nayi sallah ne barci ya daukeni kuma
gashi ranan zan bar gusau din zuwa Abuja wurin su Abba yin hutun dole a can.

   Wanda ni bansan
dalilin da zasu nace akan sainaje wanan hutun wurin su ba lokacin tunda yanzu
ina da yancin kaina da zan iya zabawa kaina abu kamar kowa.

   Karfe takwas ummah
ce tsaye a kaina take tadani daga barcin cikin fada nasan akwai tafiya a gabana
na koma na kwanta kuma to na tashi ga drivers da zai kani sokoto in shiga jirgi
har yazo.

   Gabana ne ya fadi
don tunawa da nayi ban fadawa mama ba kamar yadda ummah ta umurce ni inje da
kaina in fada mata zancen tafiyan .

  Dago kai nayi ina
fadin jiyan ban dadawa mama ba fa don naje ance sun fita ita da Rukkaiya ban
samu ganinta na fada mata ba yau zan wuce.

   Wanan kuma ruwa ki
sai ki tashi kije ki fada mata don kinsan ba zakiyi tafiya baki fada mata ba
yazo ya zama min abin magana daga baya bayan kin tafi.

   Mikewa nayi daga
kwancen da nake nabi ummah da kallo don sanin halin mama danayi yanzu a kaina
balle naje da zancen zuwa Abuja gareta.

    Haka na daure na
daura gyale a kaina na nufi part din mama din duk da rufe yake har lokacin ban
fasa nufar wurin ba a lokacin.

   Nocking nayi na
murda kofan ya bude suna zaune har mama saude da tazo ashe a garin ta kwana na
gaidasu da kwana yayin da mama din ta amsa min da kyar ta bangaren ta din.

   Murya na dan
marairaice nace mama dama nazo in fada makine zanje Abuja yau , yayin da mama
din tayi wani irin dagowa tana fadin Abujafa ?

   Yin me kuma nace
Abbane yace nazo wai a can zanyi hutu wanan karon wani guntun murmushi naga ta
sake a fuskanta lokaci guda tana fadin wata sabuwa.

    Shi Alh yace kije
can kiyi hutun a Abuja kuma bansan da hakan ba sai yanzu da zaki wuce zakizo
fada min zaki tafi nace mama nazo jiya ance kin fita da Rukkaiya kuma ban san
dawowan ki ba son nayi barci da wuri jiya din.

   Allah ya tsare ta
fada ba tare data dago kai ta kalli inda nake ba na kara dago kai na kalli su
Aisha nace to ni zan tafi sai nadawo ke nan ba wace ta juyo ta kalli inda nake.

   Na fice ina komawa
part din mu wanka na shiga ashe fitana part din mama din ta fara fada tana
fadin munafucin banza da wofi ansan munafuncin da aka kula da zai kaini can din
wurin su Abba din.

   Mama saude ce tace
anya ba da wani manufa yarinyar nan zata Abujan nan ba nifa tun farko shiyasa
nace a barta da zancen yaron nan data nacewa.

   Amma kin nace sai
kin kula mata wanan sherin son kamal yanzu ga kamal din shima ba ganin shi
kikeyi ba akai akai.

   Anty tunda kamal ya
yarda yana sonta ai gara in hadata dashi shegiya inga bayanta har uwarta don
dole su zauna a karkashina innuwana sai yadda nayi dasu har kamal din.

  Kina ganin ubanta ko
uwarta zasu yarda da wanan zabin naki kuwa idan sun gano kudurin ki akan yarsu
mama din ta tare da fadin ta yama zasu gane cewa ina hada wanan plan din.

  Idan hakan ya faru
aishi kamal yafi kowa cin riban harkan dan iska zai samu zukekiyar yarinya irin
haka a bagas.

  Murmushin gefen
fuska mama ta sauke don tasan irin mugunta data shirya min wanda ba lalai bane
ta fada a fili sai gurinta ya gama cika za a san manufarta akai.

    Mun iso Abuja
lafiya wani sabon driver ya turo ya daukeni airport muka isa gidan babu kowa a
gidan lokacin wai suna wurin aiki dukkansu lokacin.

  Sai yan aiki ke
sintiri a cikin gidan falon gidan da yanzu ya sauya sosai nabi da kallo ina jin
wani abu na taso min a kasan raina.

  Dakin da yake
mallakin ummahna a da yana kulle shina kalla na lumshe idanuna ina jin wani
zafi a zuciyana yana kuna min rai.

    Wanan dakin da ada
muke sauke baki a cikin shi naga an bude min waina shiga shine masaukina banyi
kasa a gwiwa ba nace.

   Wanan ba shine
dakina ba ai don ina da daki a gidan nan dama shi Abba ya sani wai waye ne me
take fadane wai wata murya dake fitowa ta fada a bayana.

    Dan juyowa nayi
ina kallon inda nake jin muryan wata mace ce da ba zan iya fadin ajin da take
ba ko budurwace ko bazawara waye ita me take fadane wai ?

   A,a bakuwar da Alh
ya tura na dauko airport ne dama shine take fadin wai ba zata shiga wanan dakin
ba dama tana da daki a gidan nan.

   A,a to ta fada taba
ashe zakisha zama a nan to inane ma dakin naki a cikin gidan nan dama shiru
nayi ban kalleta ba ta juya tana tsuki ta tafice gidan tana fadin kaga ka barta
a nan harsu dawo idan ba zata shiga ba.

   Komawa nayi saman
kujera na zauna ganin hakan ya fice daga falon sai yan aikin dake sintiri suke
gaidani jefi jefi ina amsawa har barci ya daukeni a wurin.

   Ban falka ba sai da
la,asar tashi nayi ina son inyi sallah kitchen na nufa wurin yan aikin nasan
komai nagidan namu don haka mike nufin baya naso shiga bandakin dake baya din
amma yana rufe shima a nan wurin su nayi alwala nadawo falon nayi sallah.

    Bandaga ba daga
wurin hjy karima din ta shigo tana fadin ina daughter na din take sai ta
hangoni a zaune ina addua ga akwatina a gefena aje .

   Ya haka naga kayan
ki a nan bayan na fada masu dakin da zasu saukeki a ciki idan sun iso saida na
shafa nake ce mata sannu da dawowa mummy ta amsa min ta sake fadin wai basu
kaiki dakin danace bane ?

    Dakin baki suka
kaini nikuma nace masu bashine dakina ba don haka ban shiga wanan din na fada
kai tsaye a daidai lokacin da Abba shima ya shigo falon ke nan.

   Kallon mu yakeyi
tunkan ya karaso lafiya bata shiga daki ba ya fada nace Abba ba dakina aka
kaini ba ni kuma ban iya kwana ko wani daki gidan nan idan ba nawa ba kasani.

    Mama meke damun
kine da zuwan ki ko wani daki aka kaiki yanzu ai shine naki tunda ba ummah ki
bace a gidan nan yanzu.

    Ba zan iya kwana
ba Abba  na fada cikin rashin damuwa   zaiyi magana tace kaga Alh dama wanine dakin
nata wacan dayan da kike zama shine nata dayan kuma na uwarta sai wancan dasu
hafsat ke ciki yanzu kannenta ke zaune a ciki dayan na mai aikinsuce.

    Bari a sauketa a
nata din tunda ban faye shigan shi ba dama ta fada kai tsaye ta kira yar aikinsu
Tabitha tazo tace takai mun kaya a dakin tana fadin dama tun da kika iso kina
nan falo zaune ?

   Mummu ban iya zama
ko wani daki sai wancan din na fada ina mikewa nabi bayan yarinyar da taja min
kauyan zuwa ciki komai nawa an kwashe a dakin saina mummy din akwai gado da
mirro da kujera.

   Na aje jakar
hannuna a kujeran dakin na shiga bandaki wanka nayi na fito na bude jakata na
dauko riga na saka na shafa mai ina shirin naji an turo kofa mummy dince ta
shigo dakin.

    Yanzun hankalin ki
ya kwanta ko ni har kin tayar min da hankali wallahi kan hakan zakiki shiga
daki ki zauna a falo yanzu tunda naga kinyi wanka taso muje falo kici abinci.

    Mommy banjin yunwa
na fada tace me kikaci nace nasha cock da snack da muka iso sokoto dama haka
kike wasa da abinci daughter a, a nace tace taso muje ki danci wani abu.

   Banyi musu ba na
mike nabi bayanta muka fito falon zuwa lokacin itama ta sauya kayan jikinta
zuwa rigan shan iska.

   Baya  na dan tsankwara ne na koma daki ban sake
fitowa ba don haka a ranan ban tantace iya mazauna gidan ba a lokacin har na
kwanta wayana ya dauki kara na duba Ahmed ne ke kirana na dauka muka gaisa.

  Yayi min ya hanya na
bashi amsa da lafiya kalau nace yasu kaka Dije tana nan kalau sai nace aff wai
kasan naga akuyarka kuwa a cikin mamaki yace a ina ?

   A cikin mafalkina
wallahi na bashi amsa nan na kwashe yadda mukayi na fada mai komai shiru naji
yayi kafin yace ke nan uwargarke tana raye a wani wajen ?

 

Leave a Reply

Back to top button